TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Hausa Book Store

Chapter   18 / 45

51K to 54K   out of 132.1K words

da take da y’ay’ansa shekara da shekaru madadin haka mummunar sakayyar da zata biyo baya kenan? Duk a dalilin rashin gata, a dalilin bata da inda zata je, shikkenan burinsa ya cika, burin da ya da’de yana mafarki za’a koreta daga Shagogo za kuma ta fita yawon duniya tunda ba ta da inda zata, ita kukan ma ta kasa ashe kuka ma guri yake samu, wani bak’in ciki ya zarta na hawaye sai tafasa da k’unar zuciya, ji take da ba haramun bane aikata kisan kai, tabbas da ta shek’a kanta barzahu a wannan daren kafin wayewar gari labari ya yi shela abinka da k’aramin gari, mutane su fara mata kallon mazinaciya, ta tabbata sunan yaranta ya gama b’aci har abada, abu na gaba bata yarda za’a yi mutanen Shagogo su yarda su cigaba da zama da ita garin.

Kafin wanzuwar asubahi tuni Talatu ta zuge tas, ta yi wata irin rama kamar me, saboda tashin hankalin da take ciki, ita da kanta ta tabbatar ba abinda ya shiga tsakaninta da Jabiru don ko rantsuwa zata iya yi akan Jabiru ba zai iya rik’e ko da yatsanta ba da sunan alfasha balle ya keta mata haddi, zalunci ne kawai irin na Kabiru me son sai ya rabu da ita kamar yarda yake kiranta alak’ak’ai, da wannan tozarcin da ya mata gwara ai Ya tsaida wuk’a a mak’oshinta ya fille wuyanta ta iske kushewarta. Yarda ta ga rana haka ta ga dare ba tare da ta ji ko alamun barci a tare da ita ba.



Jabiru kuwa tsaye ya yi a ‘dakinsa kamar Soja cikin mummunan tashin hankali, ba zai manta ba ya ji sanda Kabiru da Hadi suka mak’ureshi amma ba shi da hujja don haka ya zama dole ya amsa laifin da ba nasa ba a wajen mai gari, bai damu da kansa ba, ya san shi namiji ne kuma zai iya barin garin ya isa duk inda yake so cikin salama. Amma Talatu fa? Wani kallo zata samu daga wajen jama’ar gari? Yaya kuma yaranta za su zama a cikin mutane? Yaran da ya so su girma a gabansa su zama abin alfaharin da Kabirun zai yi da na sanin rashin kula da su da bai yi ba, sai ga shi cikin lokacin k’alilan Kabirun ya ruguje duk wani buri na su da suka jima da shi. Ya runtse idanunsa yana dukan kansa da bangon ‘dakin cikin mabayyanin b’acin rai, tuni idanunsa suka jirkita daga ainahin kalarsu zuwa jajaye kamar garwashi, ji yake idan aka ba shi dama zai iya hallaka Kabiru ya masa kisa mafi muni. Dole ne ya samu mafita, tilas ne ya samo musu mafitar da za su Tsira da mutuncinsu shi da Talatu kafin wayewar gari. (To fa! Ko ta yaya Kabiru zai samo musu mafitar?)




Tun bayan idar da sallahr Asuba mai garin Shagogo ya tabbatar akwai magana a bakunan mutanen garin da suke zagaye shi a bakin fadar tasa inda yake amsar gaisuwa a wajen mutanen garin duk bayan Sallahr ta asuba.

Wasu daga cikinsu tuni labari ya iskesu don haka suka yi dandazo a bakin fadar garin da son sanin ainahin gaskiyar abinda kunnuwansu suke jiye musu ana ra’de-ra’dinsa, hakan duk suka yi shi ya tabbatarwa Mai gari babu lafiya don haka Ya gyara zamansa yana gyaran muryar da ta ankarar da jama’ar da suka yi dogon kiwo cikin tunani. “Ko zan iya sanin me ya faru?” Mai garin ya fa’da cikin son kawar da y’ar hayaniyar da take ta shi a wajen. Tsit wajen ya yi ana sauraran ‘daya daga cikin mutanen nan na Majalisa da suka ga komai a kan idanunsu. Ya sake tashi ya tabbatar da zahirin abinda ya gani. Salati da Salallami aka ‘dauka a wajen, cikin tsananta mamaki da tsananin al’ajabi, mafi yawan mutanen wajen suna danganta hakan da al’mara, don abu ne da kai tsaye za su kira shi da farau a garin tunda hakan bata tab’a kasancewa ba kafin faruwar wannan ‘din don haka duk suka k’addara dole ne a zartar da mummunan hukuncin da zai ka’dar da y’an hanjin kowa ta yarda wani ma ba zai yi kuskuren sake aikata irin hakan ba. Mutane da dama suka dinga furta Allah wadai ga Talatu da Jabiru, don haka Mai garin ya yi tsit yana nazarin fuskokin jama’ar wajen da kai tsaye ya san idan ya furta abinda yake tasa zuciyar za su masa tawaye, don haka ya shanye nasa hasashen don ya san Kabirun zai iya aikata fin hakan ma, amma a yanzu ba shi da muryar da zai fa’dakar da mutane hakan kowa idonsa ya rufe so suke kawai a yiwa Talatu hukunci. “Hukunci ba ya yiwuwa, har sai na ji daga bakin Talatu da Jabiru don haka a je a taho min da su.” Furucin Mai garin kenan, da bai yiwa jama’a da’di ba, musamman an samu shaidun gani da ido da suka tabbatar da faruwar hakan to wace shaida kuma za’a nema bayan hakan? bayan abinda idanuwan mutane Har bakwai suka ga ni suka kuma shaida. Tausayin Talatu shine a zuciyar Mai gari shi yasa yake addu’ar Allah yasa Talatun tana da makamin da zata kare kanta, don ba ya raba ‘d’aya biyu tabbas wannan Sharrin Kabiru ne, muguntarsa ce da son lallai sai ya tozarta rayuwar Baiwar Allah.



Tana can k’uryar ‘dakinta cikin ma’daukacin Tashin hankali, yaranta gaba ‘d’aya Sun tasa ta a gaba suna hawaye, ranar ba Wanda ya karya a cikinsu, don duk da yarintar Majeedah ta hankalce da sharrin da aka yi wa Mamanta ita da Zainabu. Majeedan ce ta yi k’ok’arin dama musu ruwan koko sai dai ko ka’dan ya k’i shiga cikinsu, Deejan ma ka’dan ta sha duk hankalinsu a tashe yake da yanayin da Ummansu da Abba Jabiru suke ciki. Wata irin tsanar Mahaifinsu ta k’ara rub’anya a kan wacce suke masa da, tsana mafi munin da za ka yiwa wani abin halitta.

Yarda na ta hankalin yake a tashe haka na Jabiru yake, ban da yana tausayin halin da zata shiga idan ya arce ya bar garin da tun a daren jiyan ya yi b’atan dabo a Shagogo, to ya san yana tafiya zargin da ake musu za’a tabbatar da shi ba tare da jayayya ba don haka zai tsaya a kashe shari’ar kafin ya bar garin, don sam ba zai iya cigaba da zama a Shagogo ba bayan afkuwar wannan lamarin gwara ya yi nisa da Talatun duk da yana jin tsananin tausayin barin ta da yara, Amma gwara ya je ya dinga yi musu addu’a a duk halin da ya tsinci kansa. Don haka ya kammale kayansa wata y’ar jaka kaya kala biyu ya saka a ciki sai tarkacen litattafansa.



Tunda suka fara jiyo Sallamar daga sama a zauren gidan, gaba ‘d’aya hantar cikin su ta ka’da don sun tabbatar sak’on Mai gari ne, hakan yana nufin labari ya gama kara’de Shagogo. Talatu da Jabiru kusan a tare suka runtse idanunsu suna jin amsa kuwwar Sallamar cikin kunnuwansu.


Da k’yar Majeedah ta mik’e a hankali k’afafunta suna rawa ta isa bakin dangar gidan. Murya a raunane cike da k’unci ta amsa sallamar. “Yauwa maza ki ce da Uwarki Mai gari na kira yanzu-yanzu ya ce a same shi a fada da ita da abokin shai’danancinta.” Maganar ta zowa Majeeda a bazata, ta dinga Kallon mutumin tana zubar da hawayen takaicin furucinsa da ya yi a kan Ummanta da Abba Jabiru, a shekarunta Ya ci a ce ta gane abinda ake nufi. Jikinta a sanyaye ta juya tana jin da zata iya da ta canja k’addarar mahaifiyarta na Auren Kabiru da ta yi… da zata dawo da rayuwar baya da ta so ta ga mahaifiyarta cikin ahalin danginta na Uwa, don na Uban bata ga abinda suka tsinana mata ba, tunda Babanta ya Mutu ta zama tamkar ma bata dangi tsaf suka zareta daga cikinsu ko maganarta ma ba’a yi.



Ta sauke idanunta a kan mahaifiyarta tana jin kamar ta ce mata Su gudu kafin jifa da tsinuwar mutane garin ta fa’da kan Mahaifiyarta. Amma idan Sun gudu ina za su je? Sai dai a wannan gab’ar barinsu Shagogo ya zama dole.

Talatu kallonta take kamar mutum mutumi ta kasa magana sam sai sautin shiga da fitar numfashinta na iskar da take shak’a kawai ake ji. “An aiko ko?” Ta yi furucin kamar ana tilastata yawun bakinta ya k’afe k’af wani irin ‘daci take ji a bakin nata. Majeeda ta ‘daga kanta tana tattare hawayen da yake son zubo mata Wanda suka kasa tsayuwa tun daren jiyan don a kan idonta mutanen suka shigo. “Ki zauna da su Majeedah kada ku fita ko ina, bari na je na ji me ake ciki, idan kuma Sun kashe ni ne, na horeku da hak’uri a rayuwa a duk yanayin da zaku riski kan ku, don na tabbata ba za su bar wannan laifin ya tafi a banza ba. Allah ya isa Kabiru!” Ta furta tana jin wasu hawaye na rubdugun zubo mata, tausayin y’ay’anta take ji, don ta ita tuni ru’danin duniya yasa ta cireta a zuciyarta, zata iya cewa a lokacin ta fi mararin mutuwa fiye da rayuwa banda tana tausayin halin k’uncin da y’ay’anta za su shiga, sai dai ta bar su a hannun Allah y’a cigaba da kula da lamarinsu don ta tabbata anzo gab’ar da Jabiru zai farrak’a kansa da su.
Ta saka Majeedah ta je ta gayawa Jabiru sak’on Mai gari. Kansa kawai ya ‘daga.




Taf fadar take a cike mak’il, Kusan za’a iya cewa kaf mazan garin manyansu sa yaransu Sun hallara a k’ofar gidan Mai garin, don haka Talatu k’afarta ta dinga harhar’dewa kafin ta isa ainahin in da zata zauna, tana jin sunayen da mutane suke kiranta da shi kala-kala a kunnuwanta “Fasik’a Mazinaciya Ballagaza yau sai mun jefeki, Ishara ga duk wata Mace mai shirin kwaikwayonki……..” Talatu ta runtse idanunta tana jin sautin zuciyarta kamar zata bullok’o daga k’irjinta da gaske Kabiru ya gama cutarta..




Jikar Nashe…..✍🏽

Takaicin Uba…

26.

Nazeefah Nashe.✍🏽

_______

Saura k’iris ta afka kan dandazon jama’ar, saboda jiri da yake kwasarta, da k’yar ta dake ta sakawa zuciyarta k’warin gwiwa ta zauna a inda Mai garin ya nuna mata da yi mata alamun ta zauna. Yarda zuciyarta ke rawa, haka duk gab’b’anta suke girgiza kamar mai cutar kakkarwa. Tausayinta sosai ya ratsa zuciyar Mai gari ya dinga tunanin hanyar da zai bi ya wanketa daga wannan mummunan zargin. Shi kuwa Jabiru fuskarsa a ‘d’aure tamau ya samu gefe can ya zauna yana k’ok’arin ‘dauke idanunsa daga Kan Kabiru da yake jin kamar ya mak’ureshi huta.

Zuwa lokacin Fadar ta yi tsit ana sauraran Mai gari da dukkannin jawabinsa, da yake yin su a nutse kamar baya so, kalamai yake zubarwa cikin ilimi da Basirar da Allah ya ba shi ba don komai yake kwararo wa’azin ba sai don ya sanya tsoron Allah a zuk’atansu.
Sai dai ga hasashensa ba Wanda ya damu da wa’azin nasa, don ba wannan suke son ji ba, burinsu su ji matsaya, su ji yarda aka kwana, ‘dai’daikunsu ne wa’azin Maigarin ya girgiza musu zuk’ata, har ya ‘darsa musu tausayin Talatun a ransu.

Mai gari Ya sauke ganinsa a kan Kabiru da yake zaune gefe ‘daya cikin tunani, sosai ya yi zurfi a tunanin yana ganin kamar abinda ya yi bai kyauta ba, yana jin kamar ya wanke Talatu daga zargin nan, amma Ya san matuk’ar ya wanketa to dole ne Maigari ya mayar masa da aurenta, abinda ba ya so baya fata don ya gama shawarar rabuwa da Talatu rabuwa kuwa ta har abada. “Kabiru!” Kiran sunansa da Mai garin ya yi cikin kakkausar murya ya farkar da shi daga wancan tunanin da sauri ya ‘daga kai yana kallon Mai garin. “Ka fa’di tsakaninka da Allah, abinda ka fa’da a kan Talatu gaskiya ne? Ka tuna Allah yana kallonka idan ka yi mata sharri a kan abinda na ta ji ba bata gani ba, Allah yana kallonka kuma shi zai hukuntaka irin hukuncin da ake yiwa mai laifi irin naka.” Kabiru ya sunkuyar da kansa yana son k’aryata kansa, yana tunanin makomarsa a wajen mutane, bai San da wani ido za su kalleshi ba, k’arshenta ma duk wani hukunci da yake tunanin za su yiwa Talatun su jirgeshi a kansa. Don haka murya na rawa ya ‘daga kansa “Duk abinda na fa’da gaskiya ne, kuma ba ni ka’dai na gani ba sai da na kira shaidu suka tabbatar da abinda na fa’da ‘din.” “Rantsuwa zaka yi.” Maigari ya bashi Umarni cikin dakiyar murya da Takaicin Kabiru don a matsayinsa na Wanda ya fi Kabirun shekaru da mu’amala da mutane tuni ya gano tsagwaron rashin gaskiyarsa. Murya a dake Kabirun ya ce “To wace rantsuwa kuma zan yi, banda abinda mutane suka shaida, amma tunda rantsuwar ka ke so zan rantse maka, Na rantse da Allah duk abinda na fa’da a kan Talatu gaskiya ne…” maigari ya runtse idonsa, jin yarda jama’a suka kaure da hayaniya kowa yana fa’dar son zuciyarsa. Talatu dai tana zaune tsabar bak’in ciki ta zama kamar mutum mutumi, mutuwa kawai take rok’a a wajen Allah, tabbas Kabiru ta cuceta cutar da ba mai iya wanketa sai Allah…
Jabiru kuwa ido Ya kafawa Kabiru cikin takaici a zafafe ya ce “Allah Ubangiji Ya tsinewa mai k’arya, tabbas ba mu da shaida sai Allah, don haka na barka da Allah akan abinda ka yi min In sha Allah kafin mutuwarka sai ka wulak’anta, dalilin wannan sharri Maigirma da ka yi min.” Tuni mutanen wajen suka yi yo ca a kan Jabiru,
Har da masu k’ok’arin jifansa da duwatsu sai da Maigari ya tsawatar cikin tausayawa ya kalli Jabiru da ya yi k’asa da kansa yana zubar da hawaye idanunsa jajur, ji yake dama duk wannan abin da ake ya zama
Mafarki, sai dai Ina? Ya san k’addara ta riga fata, Kabiru ya yi musu bak’in fentin da zai yi wahalar gogewa a idanun mutane. “Jabiru ka ji abinda Kabiru ya ce shin ka amsa laifinka?” Ha’diyar zuciya ya ragewa Jabiru kawai ya mutu ya huta, saboda yarda zuciyar tasa ta k’ulle ta daina aiki yarda ta kamata me zai ce? Ko ya ce ‘din ma babu mai yadda don haka gwara ya yi shiru kawai. “Baka ji na Jabiru? Kana da damar da zaka kare kanka.” Girgiza kai Jabiru kawai ya yi “Allah ne shaida ta ban aikata abinda yake zargina da shi ba, asalima ban san Wanda ya kai ni cikin ‘dakin ba, abu ‘d’aya na sani dama ya sha alwashi a kaina, ya ci burin sai ya b’ata min suna a gari, don haka ina masa murna, ina ta ya shi murna da ya samu dama a kaina tabbas wata shari’ar sai a lahira, ka gafarce ni Mai gari amma a kan hanyata nake ta barin Shagogo ina neman afuwar duk Wanda na b’atawa na yafewa kowa amma ban yafewa Kabiru ba kuma har abada Babu yafiya tsakani na da shi. Na bar ku lafiya.” Daga haka ya mik’e jikinsa a salub’e yana k’ok’arin kawar da kai daga kallon Talatu, don yana jin wani irin kuka da take na fitar hankali, Wanda ba ya raba ‘d’aya biyu kukan tafiyarsa ne, kukan rabuwa da shi ne, shima kukan ne ya taho masa, har ba ya iya ganin abinda ke gabansa, saka sawayensa kawai yake ta inda yaga dama kamar mai tafiya a kan iska, jakar hannunsa ce kawai damk’e a hannunsa haka ya saka kai ya mik’i hanya ba tare da ya san inda za shi ba. Wannan ce silar rabuwar Jabiru da Yaya Talatunsa.

Wasu da dama daga cikin fadar Sun tausayawa Jabiru, har ma suna jin kamar su ruga da gudu su kira shi, yayin da wasu suka bi shi da kallon banza da tofin Allah tsine. Mai gari bai hana shi tafiya ba don ya hango tafiyar itace abinda ya fiye masa alheri fiye da zamansa a garin, tunda shi Namiji ne ba shi da Kaico a duk inda zai riski kansa sab’anin Mace da shigarta duniya yake nufin al’amura da dama.

Fadar ta samu bak’uncin shiru, tun bayan da Maigari ya yi gyaran murya alamar yana son cigaba da magana daga inda ya tsaya. “Kabiru me ye matsayar magana? Abin nufi za ka cigaba da zama da Talatu ko kuwa ka samu hanyar rabuwa da ita kamar yarda ka ke fata?” Maganar Maigari ta masa dirar
Mikiya ya ‘dago da sauri yana kallon idanun Maigarin sai dai da sauri ya ‘d’auke kansa don ba zai iya cigaba da kallon k’wayar idanun Mai garin da suke nufin abubuwa da dama ba. “Ka gafaceni ranka ya da’de, na sake zare igiya ‘d’aya a aurena da Talatu.” Mai gari ya kalleshi yana murmushi kafin murya k’asa k’asa ya ce “Burinka ya cika Kabiru, amma me yasa ba zaka kalmashe auren gaba ‘daya ba, ma’ana Ka sawwak’e mata duka igiyoyin auren, tunda dai ban ga amfanin barin ragowar igiyar ba.” Tsit ya yi yana kallon Maigari k’asa k’asa, abinda ya so yi kenan,wato sakinta gaba ‘d’aya sai dai Amininsa Hadi ya ankarar da shi abinda ya manta daga shara’din boka a kan kada ya sake ya saki Talatun gaba ‘d’aya don siririn arzikinsa yana cikin igiyar auren Talatun, don haka yake shakkar sakinta gaba ‘d’aya kada ya koma y’ar gidan jiya. Don haka ya ja bakinsa ya yi gum. Yana sauraran Mai garin da ya yi gyaran murya.

“Abisa duk abubuwan da muka ji daga bakin duka b’angarori guda biyu, Wannan hukuma Mai adalci zata bawa Talatu mafaka a gidanta, sannan ina yiwa Kabiru Umarni ya tattare yaransa ya rik’e a hannunsa dukkan wata ‘dawainiya tasu ta koma kansa, wajibi ne ya basu cima mai kyau sutura da karatu mai inganci, ba kuma mu amince da yin tozarci ga Talatu ga zuri’arta ba, duk wanda aka samu da aikata haka akwai mummunan hukunci a kansa. Allah yasa mu dace.

Tsit fadar ta yi saboda da yawa mazauna cikin ta wannan hukunci na Uban gari bai yi musu ba, har da wa’danda suka jefa ayar tambayar ga Mai garin shi kansa, akan wace hujja zai bawa Talatu wajen zama idan dai ba da wata a k’asa tsakaninsu da ita ba, ba su tab’a ganin shari’ar da Maigari Ya

18 / 45