Author : Nazeefa Sabo Nashe Category : Hausa Book Store
ganin wani abu, sab’anin haka zuciyar ce a cunkushe ta rasa kuma mai zata yi ta samu sauk’in nauyin da k’irjinta yake mata, Ta faru dai ta k’are ita Ayra Gaya yau aka yiwa aure, auren da ta taso da adawarsa a ranta.
__
A daidai lokacin da take cikin wannan yanayin, shima ango yana can gaban Ummeey ransa a matuk’ar b’ace shi ka’dai ya san me yake ji a zuciyarsa Ga soyayyarta ga kuma k’iyayyarta ga Jin Haushinta duk sun taru sun caku’de masa a zuciya. Ji yake kamar ya fasa kuka. “Tashi ka tafi Turaki, ka bar y’ar mutane ita ka’dai a gida abu ‘d’aya zan sake jaddada maka Ka ji tsoron Allah! Ka kuma amshi matarka a duk yarda ka sameta budurwa ko akasin haka kada ka ja da ikon Allah, ba mamaki ka sameta a yanayin da baka so ba to ka saka a zuciyarka k’addara ce ba kuma da son zuciyarta komai ma ya faru ba, please kada ka fake da hakan ka sakar min y’a, duk da nima ban tabbatar ba amma labarinsu Akwai rikitarwa komai ma zai iya faruwa ba abin mamaki ba ne, a halin da suka taso please ka taimakeni Turaki kada ka ba ni kunya.” Kansa ne ya sara sosai ya ‘dago yana sauke jrikitattun idanunsa a kan na Ummeey da gaske kenan ta san Yarinyar Karuwa ce Amma ta amince da auren su, ya ‘dan cizi k’asan leb’ensa kafin ya mik’e a kasalance yana ha’da hanya ya nufi k’ofa, sama-sama ya jiyo muryar Ummeey tana fa’din “Tsaya Ga abincinku ka tafi muku da shi, sawa na yi aka girka muku don na san yau gaba ‘dayanku ba wanda ya
Saka loma a bakinsa, kun kasa yarda gata muka yi muku nan gaba za ku ga amfanin hakan. Allah ya tashe mu lafiya.” Ta fa’da tana damk’a masa Kwandon abincin a hannunsa.
Ya d’auki mintuna biyar a cikin motar ya kasa Driving ‘din, gaba ‘d’aya ransa dama a jagule yake ga Ummeey ta sake k’ara masa wani tashin hankalin ta tabbata dai da gaske ne disvirgin ce ya runtse idanunsa kafin ya tada motar cikin kasala ya nufi hanyar gida.
Yana isa Gida wanka ya shiga ya da’de cikin ruwan da ya sakarwa kansa kafin ya fito jikinsa saye da bath robe yana tsane gashin kansa da towel. Tsaf ya shirya cikin wasu kayan barci na companyn Hilfiger ya feshe jikinsa da turaruka na musamman. Duk da yunwar da take na’de a cikinsa haka ya yi nufin kwanciya yana runtse idanunsa sai dai ina yunwa ta ce bata san wannan ba abinci kawai cikinsa yake buk’ata
Ga shi bai fiye son abinci mai nauyi da daddare ba. Tsaki ya ja sosai kafin ya mik’e niyyarsa ya je kitchen ya samu abinda zai ci.
Daidai lokacin Ayra tana tsaye a
Kitchen sanye da Riga da wando na barci da suka tsaya mata iya cinya sai y’ar hula da ta saka a kanta, har ta saka hijabi don tsoron ha’duwa da shi sai ta tuna sunan da ya kirata da shi, don haka ta cire Hijabin ta wurgar gwara tun yau ta fara nuna masa ita Karuwance, a duk inda a ka san Karuwa kuwa an san bata da kunya.
Cak ya tsaya daga bakin k’ofa yana k’arewa sassan jikinta kallo zuciyarsa tana wani irin bugawa da sauri kamar zata fisgo ta fito daga k’irjinsa, tunda yake bai tab’a katarin ganin Mace mai cikakkiyar sura irin tata ba, ya runtse idanunsa kafin ya bu’de ya sake saukesu a kanta, daidai lokacin ita kuma ta juyo jin kamar ana kallonta da sauri ta rik’e cup ‘din Lipton ‘din da yake hannunta da ya yi niyyar sub’uce wa saboda yarda idanunsa suka yi tasiri a kanta. Sai a lokacin ta ji haushin kanta na yarda ta bari wani banza na kalle mata jiki a banza, duk da dai dama bai cancanci ta ji kunyarsa ba wanda ake so Ai shi ake jin kunya. Da sauri ya ‘d’auke
Kansa zuwa inda fridge yake Hakan ya bawa Ayran damar ‘daukar Mug ‘dinta ta fice da sauri. Ta gefen ido yake kallon fitarta da yarda duk wata sura ta take a bayyane, tuni duk ya bi ya rikice mazantak’ar ta motsa gefe ‘d’aya na zuciyarsa kuma yana tabbatar da karuwancinta ta yarda rana guda a daren farko ta iya fitowa da wa’dannan fitsararrun kayan, idan ba Karuwa na wace zata aikata haka? Ya saki dogon tsaki yana k’ok’arin jona kettle don tafasa na sa tea ‘din.
Yarda yake zaune a bakin gado yana sipping hot tea ‘din a uzurce idanun sa a kan t.v d’in da take kafe a bangon d’akin sai ka zata kallon yake sai dai ina ba kallon bane a gabansa surarta ce kawai take amsa gizo kamar wani aikin asiri. Ya ja tsaki a zuciyarsa yana raya da gangan ta yi daman ta yi ne don hakan ta faru da shi ya zama dole ya je ‘d’akin ya nuna mata Shi jikinta baya gabansa,
Jikin da maza da dama suka gama banbance sirrinsa da shi zata yaudareshi Ina ba dai shi jikar Turaki ba dole ya gaya mata bata gabansa ya mik’e a zafafe yana fa’din “In dai ni ne ko sha’awarki zata hallaka ni ba zan kusanceki ba, ina da Kishi, kuma shi zai ja na kasa kusantar ki tunda na Riga na san wasu can sun shiga k’ofar da ba ni na fara bu’de ta ba.” Ya bu’de k’ofar ‘dakinta da azama kamar an jefo shi, daidai lokacin da Ayra ta yi wani kyakykyawan juyin da ya kusan sumar da Turaki a tsaye, ta kafeshi da idanunta ha’de da fa’din “Malam Lafiya?” Sai da ya ha’diyi kakkauran yawu kafin ya ce……
*Jikarnashe✍🏽
Takaicin Uba….
Nazeefah Nashe✍🏽
33.
💔💔💔💔
“Lafiyar kenan.” Ya yi furucin cikin dakewar murya, yana sake ‘daure fuskarsa tamau alamar duk zancen da zai mata da gaske yake from the bottom of his heart. Ita ‘din ma fuskar ta ‘d’aure sosai tana jan tattausan blanket ‘din da yake gadon don son suturta jikinta da ta ga yana wa kallon k’urilla. “Bar wani k’udundune jiki… jikin da ban san iya wa’danda suka kalleshi ba, ban san iya wa’danda suka tab’a shi ba.” Ya fa’da yana wani furzar da hucin b’acin rai “Ba abinda zan kalla a jikinki, kamar yarda ba abinda zan yi da mai jikin, idan ma dalilin da yasa kike bayyana shi kenan, ki k’addara a ranki Ni Turaki na fi k’arfin kusantar wannan k’azamin jikin naki, Turaki mai tsarki kuma kamilalle don haka dole ne wacce zata zamo Matar Turaki ta kasance kamilalliya ba irin ki ba, ki saka a zuciyarki duk ranar da na kusanceki kamar na damk’a miki takardar sakin aure ne don haka bar yaudarar kan ki da nuna min wannan jikin…” zuwa lokacin ya gama hassala zuciyar Ayra k’iris take jira ta fashe, ta dinga ha’d’iyar wasu irin yawu masu ‘dacin gaske, tana furzar da numfashi mai tururi mai nuna zallar hassalar da zuciyarta take ciki. Me wannan mutumin yake nufi? Waye ya gaya masa ita Karuwa ce? Ita ‘din da wani ‘da namiji bai tab’a rik’e hannunta ba, sai dai sanda wancan mummunan abin ya afku. K’ok’ari take ta ha’diye maganar sai dai ziciyarta ta kasa bata dama, dole ne ta furta masa mai ‘dacin da shima zai ji b’acin ran da take ciki. “Jikin Ayra Gaya, yafi k’arfin kowane karabitin namiji, Jikin Ayra ba shi da arahar da zata bari ka kusance shi,Jikin Ayra na mazan da suka amsa sunansu maza ne, ba na irin ku da kuke sakin Mata barkatai ko kuma matan suke guduwa da k’afarsu sabida rashin biya musu buk’ata ba, ba mamaki a tsaye kake namiji a ba’dinance kuwa muna Maza ne, ka je ka tambayi wa’danda suka gaya maka ina karuwancin da wasu kalar Maza nake yi? Maza jajurtattu, Mazan da suka amsa sunansu maza a zahiri da ba’dini.” Zuwa lokacin duk wasu k’ofofin jikinsa sun bu’de saboda tsabar b’acin rai, idanunsa sun jirkice zuwa wani launi daban mai bayyana hassalar zuciyarsa, ji yake tamkar ya keta ta k’arfin tsiya ya nuna mata yafi k’arfin ta kira shi muna maza. Bai san sanda ya kai kansa bakin gadon ba yana tsatstsareta da ido cikin b’acin rai ya ce “Banda wani dalili daban da yau na tabbatar miki da cewa Turaki Ingarma ne ya fi k’arfin wulak’ancinki, sai dai kash ba zan iya kusantar k’azamin jiki irin naki ba,ina sake jaddada miki duk ranar da na kusanceki ki tabbatar kamar na katse igiyar aurena guda da take kan ki na fa’da miki haka ne saboda ki tabbatar ba abinda zai burgeni a jikin ki ko da zan ganki (naked) tsirara a gaba na. Daga haka cikin b’acin rai ya juya a sukwane ya bar ‘dakin, ita kuma Ayra ta saki murmushi tana danna save a recording ‘din da ta saka, shikkenan ta samu hanyar rabuwa da wannan mutumin, tunda shi ya yi furucin da bakinsa sai dai fatan Allah ya kai mu lokaci! Ta fa’da tana sakin murmushi a hankali kuma ta ce Mu je zuwa yanzu wasan ya fara.” Ta furta a hankali tana rungumar filo cikin tsananin farin ciki.
Ya da’de yana zagaye faffa’dan falon nasa mai girman gaske da ya ji adon farin painting da ash chairs da dinning set complete set dai na latest chairs na k’asar Turkey. Hannayensa sark’afe a baya yana bitar kalaman Ayra da suka zame masa tamkar Hadda. Da gaske ba mutumin da ya tab’a ba’ta masa rai kwatankwacin yarda Ayran ta masa yau, wani kishi ne yake nuk’urk’usar zuciyarsa da b’acin ran kalamanta wai shi ta kalla take kira bai isa namiji ba, ji yake kamar yaje ya mata irin kusantar da zata san suna da tazarar banbanci tsakaninta da mazajen da suke hul’da da su ya dinga kai mari yana kai gauro cikin tsananin takaici da bak’in ciki. Kafin ya yi k’wafa ya zare kayansa ya kwanta a kan hannayensa. Sai dai fa barci ya ce bai san wannan ba surarta ce ta dinga masa gizo cikin yanayin da ya ganta ‘dazu. Ya dinga juyi yana sakin tsaki akai-kai. (To fa! Anya Turaki hanyar daka ‘dauko mai b’ullewa ce? Kada fa masu supporting Ayra su mana dariya. Tohm ni dai ba ruwana)
Da k’yar Ayra ta mik’e a safiyar ranar ba don komai ba sai don rashin samun isashshen barci. Bayan sallahr asuba kuwa tunda ta sheme bata sake motsi ba sai yanzu da ta dinga jin bugun k’ofa kamar a tsakiyar kwanyar kanta. Ta ‘dan saki guntun tsaki tana mik’ewa. Tattare gashin kanta ta yi da ya barbazu ta saka band ta ‘daureshi sannan ta zura hijabi akan rigar barcinta. Ta d’an fice da azama jin bugun k’ofar yana sake tsananta.
A bakin k’ofar da zata sadaka da babban falon ta tsaya murya cike da alamun tashi daga barci ta ce “Wanene?” Daga can waje su Tasleem suka amsa da “Mu ne bu’de Sis Ayra.” Ta mur’da key ‘don ha’de da sakin murmushin da kai tsaye zata kira na k’arfin hali ita da kanta ta san a iya kan leb’enta ya tsaya. Su kuwa gaba ‘daya suka rungumeta cikin farin ciki har Aman da suka zo da shi ba’a barshi a baya ba wajen kai mata kyakykyawar runguma. Ta ‘dan shafa kansu cike da kulawa tana janye jikinta ha’de da zubawa Aman ‘din ido ko ba’a fa’da mata ta san jinin wancan mutumin ne, ta ‘dan tab’e baki kawai tana juyawa suka bita cikin falon. Zama suka yi a kan kujeru suka gaisa sosai kafin Ayra ta kalli coolers ‘din da suka dire a saman dinning ta saki ajiyar zuciya don dama da wata mahaukaciyar yunwa ta tashi, tana jin kuma k’iwar shiga kitchen ta yi girki. Ta mayar da kallonta kansu kafin ta mik’e ta ce “Excuse me don Allah, tashi na kenan bari na yi wanka na zo mu gaisa sosai.” Har ta tafi ta ji Aman ya ce “Aunt Dada fa?” Cak ta tsaya ta juyo da k’yar ta kalli yaron kamar zata masa tsawa sai kuma ta ‘dan saki tsaki a hankali ta ce masa “Do you know his room?” Ta furta cikin k’asa da murya sosai don bata son su Tasleem su ji. Aman ya girgiza kai alamar bai sani ba, Ayra ta saki tsaki ka’dan kafin ta ce “Oya Go and Sit down zai fito yanzu.” Daga haka ta juya da azama ta shiga ‘dakinta tana tsaki k’asa-k’asa “Ina ruwana da wani Dada da zaka tambayeni shi, Dado ba Dada ba.”
Tsaf ta shirya cikin ha’dadden Swiss brocade ‘dinta, light pink pink mai adon blue ta taje sumar kanta ta kama kafa ‘daurin ture ka ga tsiya sosai ta yi kyau ba k’arami ba, musamman ‘dan bakinta da ya sha pink lip stick da ya sake bayyana tudun lips ‘din ka’dan kamar an dasa mata su. Cak ta tsaya tana kallon yarda ita kanta ta hango kyan da ta yi, tsoronta ‘d’aya kada wancan mutumin ya ce saboda shi ta yi. Ta saki tsaki tana fa’din “Ba don kai na yi ba, dama tun filazal kwalliya a jikina take.” Cikin wani irin taku mai bayyana zallar izza ga wanda ya kalleta kai tsaye zai fassarata ta isa falon da ta bar su. Cak ta tsaya daga bayan kujera cikin takaicin ganinsa a falon zaune suna hira da y’an uwansa cikin farin ciki, ga Aman a gefe yana ta zuba surutu. Ta ‘dan cije leb’e tana tab’e bakinta kafin ta ‘d’auke kanta kamar bata gan shi ba ta nufi dinning area. Abinci ta zuba sosai ta zauna ta nutsu ta fara ci ba tare da ta sake bi ta kan su ba. Tun wucewarta har zuwanta idanunsa a kanta yake k’asa-k’asa, yana mamakin zallar kyan da Allah ya bata amma madadin ta gode masa ta hanyar killace kanta har zuwa gidan Mijinta sai ta zab’i ballagazar da kanta a titi kowane banza yana da damar da zai kusanceta idan dai zai bata ku’di, gaba ‘d’aya sai ya ji ransa ya b’aci ransa ya yi duhu yana jin haushin kasancewarta macen da ya ‘d’au tsawon shekaru yana dakon soyayyarta.
Sai Bayan sun yi sallahr azahar sannan suka ce mata za su tafi Yaya Turaki zai kai su gida. Har ta ce su gaida gida sai kuma ta ga hakan kamar bai dace ba, don haka ta dakatar da Tasleem da sauri ta koma ‘dakinta ta ha’da musu cosmetics ta basu, yaronsa kuwa komai ma ba zan ba shi ba balle ya ce saboda shi zan yi.” Ta yi furucin a fili tana kinkimar ledar ta fita. A bakin k’ofar motar ta tsaya Kuma jikinta ko mayafi babu don a tuaninta amfanin Nik’ab ‘dinta ya k’are. Amin Turaki ya saki tsaki ganin yarda gardener da Gate Man suka kafa mata ido a zafafe yarda su Tasleem ba za su ji ba ya ce “Ai gwara ki nuna musu jikinki a araha dama da irin su kika dace.” Kalmar ta shigeta sosai ta bu’de baki a zafafe zata gaya masa magana ta ga ya finciki motar a mugun speed ya ba’deta da iska ya tafi. Tana daga tsayen ta dinga gartsawa lab’banta cizo wasu hawayen da bata shirya musu ba suka fara suntiri a fuskarta. “Na rantse da Allah sai na rama.” Ta furta tana jin wani ciwo a zuciyarta ta koma cikin gida da sauri. Ta da’de cikin yanayin b’acin rai da takaicin mutumin da ko sunansa bata rik’e ba….
Sai dare sannan ya dawo, tun daga compound ya fara jin k’amshin abincin da take dafawa. Ya dinga jin yawun bakinsa yana tsinkewa tabbacin komai ma ake dafawa ransa ya kai matuk’a wajen son ci.
Daidai lokacin tana tsaye tana shafe jikinta da sihirtacciyar humrar da Majeeda ta ajiye mata ba tare da ta san menene sirrin humrar ba, ta dinga ambulata har kamar tana shirin hawa mata kai, haka kawai ta ji k’amshin humrar ya yi mata har inda take so. Ta zura rigar half boubou da dogon wando don garin ana ‘dan zafi sosai. Da y’ar wak’arta ta shiga kitchen ‘din sai dai cak ta tsaya ganin yarda ya cika plate da abincin da ta dafa arabian spaghetti da Patoosh salad sai Bake fish a gefe mai ha’de da sauce na dankali. K’amshin Humrar da ya dirar masa hanci ne ya sa shi juyowa da sauri idanunsa a kanta tana tsaye ta rik’e k’ugu. Ya ‘dan tab’e baki yana mata kallon sama da k’asa yana jin wani abu yana ziyartar gab’b’an jikinsa wanda yake da tabbacin tsumammiyar sha’awarsa ce take son bujiro masa ta kowane hali. Ya ‘d’aga mata gira “Ya aka yi?” Ta bi plate ‘din da kallo murya a shak’e ta ce “Dalili?” “Gidana ne, kuma dolenki ne ki girka ki ba ni, kin ji da’di da ta nan fannin ba a yi failing ba.” Ya fa’da yana nuna mata abincin, a gefe guda kuma yana k’ok’arin controlling kansa da zuciyar da take ce masa ya je ya rungumeta ko ya samu sauk’in abinda yake ji, kamar wanda magana’disu yake jan sa zuwa gareta ya sauke idanunsa kan k’irjinta da suke masa dangwalaliya ta saman Riga, lokaci guda ya ja hannayensa ya ‘dora a kan… cak numfashinta ya tsaya cak ta waro idanunta a kansa…..
Jikarnashe ✍🏽
Takaicin Uba…
Nazeefah Nashe✍🏽
34. 💬
Kina nan kina lak’e-lak’e abin haushi tuni free page ya k’are, ga tafiya ta fara nisan zango Ayra da Turaki har an yi aure ana zuba badak’ala a gidansu duk kin kasa biya ki kwashi romon labari ana jiran a samu na banza. In dai kin cika mace da ta amsa sunanta mai aji biya 1k dubu guda kacal a watsaki a tafiyar y’an special people idan kuma kin ga ba zaki iya ba har yau k’ofa a bu’de yake ki biya 500 kacal na watsa ki sashen normal group. Ga ‘dand’ano ku karanta ku ji yarda labarin ya fara ‘daukar harami.
Samu numberr marubuciyar don biya kai tsaye.
08033748387.
Yanzu aka fara tafiyar mai nisan zango ce!
💔💔💔💔
Janye hannun nasa ya yi da sauri yana zabga mata harara ha’de da nuna mata ‘dan k’waron da ya mak’ale a kan rigarta mai kama da butterfly. A razane ta daka tsalle don matsoraciyace ta gasken gaske, k’ok’ari