Chapter 38 Reading TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt Arewa Novels

TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Hausa Book Store

Chapter   38 / 45

111K to 114K   out of 132.1K words

har rawa yake ya ‘d’au takardar “Na tafi na sanar da iyaye ka sake ni, tunda da bakinka ka fa’da, bana buk’atar aurenka ka k’addara har abada Ayra Gaya ta fita daga rayuwarka.” Gaba ‘d’aya gab’obinsa suka fara rawa ya yi saurin ficewa daga ‘dakin ya nufi ‘dakinsa. Brief case ‘dinsa ya ‘dauko ya shiga bincikawa Dollar card ‘dinta yake nema nan yaga bai gansa ba, hantar cikinsa ta ka’da ya tabbata da gaske Ayra ta bar garin ta tafi Nigeria, ya kuma san ya ka’da har ganyensa idan Ummeey ta ji labari yarda take da saurin fushi ya san kafin ta yafe masa za a sha fama. Ya runtse idanunsa yana dukan hannunsa da ‘daya hannun ya ce “Why Ayra Gaya?” Ya zauna kawai ya dafe kansa kafin ya yiwa wani mutuminsa a airport waya ya tambayesa jirgin da zai tafi Nigeria ta tashi a ranar? Nan aka sanar masa ya tashe tun 7:30 Turaki ya runtse idanunsa ya sake tambayar za’a samu flight mai tashi yau zuwa Nigeria mutumin ya sanar masa babu ko na gobe ba za’a samu ba sai jibi. Turaki ya yi cilli da wayar yana fa’din “Na mutu kawai! Innalillahi wa Inna ilaihirrajiuna!”


𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍 𝕹𝖆𝖘𝖍𝖊✍🏽
Takaicin Uba…


56.


Jirginsu na dira Nigeria Ayra ta saki watt ajiyar zuciya tana lumshe ido, haka kawai sai ta dinga jin kamar abinda zata aikata d’in bai dace ba. Ta dinga ganin tamkar bata kyautatawa Turaki ba, kafin wata zuciyar ta sake k’arfafarta da cewa abinda zata aikata ‘din shine ya dace, gwara ta nuna masa matsayinta ya san ya aikata kuskure.

Bata wuce gidansu ba direct gidan Ummeey ta tafi don ta sanar mata, kuma ko bakomai ita da kanta tana shakkar fa’dan da Amma zata mata.


Knocking biyu kawai aka yi Tayseer ta bu’de k’ofar. Mamaki ya kamata ganin Ayra ‘dauke da trolly. Ayra ta sakar mata murmushi ta ce “Ya dai?” Tayseer da gabanta yake fa’duwa ta saki ajiyar zuciya ta ce “Na yi mamaki ne? Yaushe kuka dawo?” Ayra murmushi ta yi kafin ta ce “Mu shiga ciki, kafin wa’dannan dogayen tambayoyin naki?” Tayseer ta ja trolly ‘din nata jikinta a sanyaye sai kuma zuciyarta ta bata ba mamaki ko Amma tazo dubawa. Sai da ta zauna sannan Tasleem ta juya kitchen don samar mata abin sha kafin ta samar mata abinci don daga ganinta daga airport take.

Ta sha juice ‘din ka’dan kafin ta ce “Ummeey fa?” Tayseer tana sake dubanta ta ce “Ai suna can Abuja wajen Amman.” “Amma kuma? Me ya kaita Abuja?” Ayra ta yi saurin jefowa Tayseer ‘din tambaya. Jikin Tayseer ya yi sanyi tabbacin Ayra bata san Amman bata da lafiya ba hakan na nufin tahowarta akwai matsala kenan, tunda ba Amman ta zo dubawa ba. “Ta ‘dan yi ciwo ne, amma jikinta da sauk’i sosai.” Ayra ta waro ido tana kallonta kafin k’walla ta taru a k’asan idonta, bata san sanda ta rarumi waya ba ta fara booking flight mai zuwa Abuja a yammacin ranar. Ganin hankalinta ya tashi sosai Tayseer ta ce “Ya. Ayra kin kwantar da hankalinki fa, ta samu sauk’i sosai.” Hawaye kawai ya goge tana kallon Tayseer ta ce “In sha Allah thank you.” “Mu je ki samu ki huta naga kin ‘Debo gajiya, Ina Ya.Turakin na ganki ke ka’dai?” Ayra ta saki murmushi tana fa’din “Yana can, nima akwai abinda ya dawo da ni.” Tayseer jikinta a sanyaye ta tura k’ofar ‘dakin tana fa’din “Allah yasa lafiya.” Ayra ta saki murmushi ganin yarda damuwar Tayseer ‘din ta bayyana k’arara akan fuskarta.” Tana kallo ta fice tana ja mata k’ofar. Ayra ta zauna gefen gado cike da damuwa ta fara k’ok’arin kiran Wayar Deejah. Cikin mamaki Deejah Take kallon wayar ganin numberr Ayran ce ta Nigeria. A tsorace ta ‘d’aga kiran. Ayra ta saki ajiyar zuciya tana fa’din “Ya. Deejah, yanzu shine Amma bata da lafiya baku gaya min ba? Sai da na zo yanzu Tayseer take gaya min.” Wata irin zufa ce ta ketowa Deejahn cikin rawar baki ta ce “Kika zo ina Ayra? Kuma ke da wa Kuka zo?” Ayra ta ja tsaki don ita ba tambayar da take son ta ji ba kenan, “Ko ma ni da wa na zo ina ruwanki? Ki gaya min wani hospital kuke kawai, don mugunta kawai Uwata bata da lafiya sai a k’i sanar da ni har sai da na zo k’asar.” Deejah ta katse wayar kawai don ta lura Ayran tsiwa take ji. Ayran ma bata sake kiranta ba sai kawai ta kira Zainab, Zainab ‘din ce ya sanar da ita suna National Hospital “Amma Ayra me ya kawo ki Nigeria?” Nan ma Ayra katse wayar ta yi kawai. Duk ‘dakin aka zubo musu ido,ana son jin k’arin bayani musamman Amma da Ummeey da wani tashin hankali ya ruskesu. “Wace Ayran ce a Nigeria.” Ummeey ta jefo mata tambayar don ta kasa jurewa. Deejah tana sakin ajiyar zuciya ta ce “Ayra Gaya.” Ummeey ta dinga jin kamar saukar aradu a kanta. Murya na rawa ta ce “Yanzu tana ina?” Deejah ta ce “Wai tana gidanki tare da Tayseer amma yau zata zo nan ‘din.” Amma kasa magana ta yi, Ummeey kuma ta yi zugum kafin ta kasa jurewa ta mik’e ta fita waje ta dinga kiran wayar Turaki sai dai ana ta sanar da ita number not reachable. Ta ‘dan dafe kanta kafin ta sauya akalar kiran zuwa wajen Tayseer.


Tayseer da take kitchen tana ha’dawa Ayran abinci. Ta ‘dau wayar da sauri ganin Ummeey ce. Ko amsa gaisuwarta Ummeeyn bata yi ba ta ce “Tayseer Ayra da ita da wa suka zo gidan nan?” Tayseer ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce “Ita ka’dai.” “Tace miki ina mijinta?” Ummeey ta fa’da murya a raunane. Tayseer ta saki murmushi kafin ta ce “Cewa ta yi wai yana can ni na ‘dauka ma Amma tazo dubawa, to ga dukkan Alamu bata san Amman ma bata da lafiya sai da na gaya mata.” Ummeey hankalinta a tashe ta ce “Maza ki kai mata wayar.”

A kwance ta samu Ayran a kan gado idanunta lumshe. Sallamar da ta yi yasa Ayran bu’de ido tana kallonta. Tayseer ta mik’a mata waya tana fa’din “You’ve a call.” Ayra ta bi wayar da kallo tana fatan ba Turaki bane ya kira, da hannu ta mata alamar waye? Tayseer ta ce “Ummeey ce.” Sai sannan ta kara wayar a kunnenta ta mata sallama da gaisuwa. Da sauri Ummeeyn take amsawa burinta kawai ta ji me ya faru. “Ayra me yasa kika taho?” Ayra ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce “Bakomai Ummeey.” “Gaya min gaskiya, gaba ‘daya hankalina ya kasa kwanciya…” tausayinta ya kama Ayra kafin ta ce “Bakomai Ummeey.” “Shikkenan idan kin zo za mu ji, amma idan kin san wani abu ne mai muni pls kada ki fa’di ma kowa, ki fari gani na tukun ki min wannan alfarmar.” Ayra ta ‘d’aga kanta ha’de da fa’din “To Ummeey, In sha Allah.” Hankalin Ummeey sam bai kwanta ba, don haka ta dinga jan wasu addu’oi a zuciyarta kafin ta sake kiran Turaki, sai dai still wayarsa bata shiga.


Har Magriba Ummeey dai kallon kowa take, sam hankalinta ya kasa kwanciya, ana mur’da k’ofa take ‘d’aga kai ta ga waye? Jira kawai take ta ga Ayra. Zainab ce ta je ‘daukota a airport bayan ta musu waya jirginsu Ya yi landing. Tun a mota Zainab take tuhumarta dalilin zuwan ta ita dai murmushi kawai take ta ce “Bakomai.” Har suka isa asibitin bata sanar mata abinda ya faru ba. Zainab dai ta ja bakinta ta tsuke tana addu’ar kada Allah yasa hasashenta ya zama gaskiya.

Ita kuwa Ayra burinta kawai taga Ammanta, don haka ta k’agu su isa ‘dakin da Amman take a hanya Zainab ta dubeta da murmushi ta ce “Ke Abba Jabiru ya dawo.” Ayra ta waro ido don duk bata san shi ba, bata mantawa kullum Sai Amma ta saka su masa addu’a tun suna yara. “Ya. Zee da gaske?” Ta fa’da cikin farin ciki. Zainab ta ‘d’aga kai “Da gaske Ayra, Abba Jabiru ma cikakken Doctor ne a asibitin nan, last month ya dawo daga egypt shine likitan da muka zo gani da Amma, ashe rabon zamu ha’du da shine.” Ayra ta ce “Alhamdulillah! Na san yanzu kam Amma tana cikin farin ciki.” “Sai ma kin ganta.” Zainab ta fa’da tana tura ‘dakin da Amman take ciki. Ayra ta saki ajiyar zuciya ganin Amman a zaune tana ci abinci, da sauri ta k’arasa wajenta ta rungume cikin farinciki. Itama Amman rungumeta ta yi tana fa’din “Oyoyo Auta ta.” Ido biyun da suka yi da Ummeey ne yasa ta ji kunya, sai ta saki Amma ta k’arasa wajen Ummeey ta niyyar durk’usawa Ummeey ta janyota jikinta ta rungume tana fa’din “Na k’i wayon, ita Amma a ka rungume ni kuma a durk’usa min, bayan yanzu ni ce Mamanki.” Ayra ta saki murmushi kawai tana hugging Ummeeyn. Mintuna ashirin kawai Ummeey ta barta ta yi sai ta mik’e tana kallon Ayra “Taso dear mu je masauki, naga kin kwaso gajiya, mu je ki huta, jikin Amma Ai da sauk’i gobe na za su wuce gida, mu kuma za mu biya Gombe za mu je na’din sarautar Kakansu Turaki an ba shi Sarkin Fulanin Gombe.” Amma tana murmushi ta ce “Shikkenan, daga nan Ayra sai ta ga dangi, dama bata ha’du da su ba da biki an yi biki a tsatstsaye.” Ayra ta yi shiru kawai don ita sam wannan hukuncin bai yi mata ba. Haka dai jikinta a sanyaye ta mik’e ta nufi in da Ummeey da Tasleem su ke. Deejah kuwa sai dariya take mata ganin yarda fuskarta ta nuna alamun bata so ba. Ummeey na lura da haka ta janyota “Rabu da Ita Dear, ai gobe kafin su tafi za mu je gidan Jabiru mu ganta, don ma ta k’i ne da sai ta yi zamanta a nan, to ta ce wai Jummai aminiyarta sun zo daga Shagogo ta tsayar da su a can gidanta don haka zata koma.” Ayra dai ta saka k’afa ta bita ba don ranta ya so ba sai don kunyar idon Umeeyn da k’arfi da yaji take neman yiwa Amman k’wacen y’a.

Tunda suka fita Ummeyn take Allaha-Allaha su isa masauki ta ji dalilin zuwan Ayran bagatatan. A gidan Turaki na Abuja suka sauka, wanda yake Maitama drivernsa ne yazo ‘daukarsu.

Hannun Umeey a cikin na Ayra kamar wani zai k’wace nata ita suka shiga tsararren gidan, da ya tafi da Imanin Ayran don tsari kam ita tsari gidan ya tsaru. Ummeey ta jata wani ‘d’aki tana duban Tasleem ta ce “Maza ki samar mana ko Chips ne a kitchen ba ma kwana da yunwa ba, ki dama min oat.” Tasleem ta amsa mata tana shiga wani b’angare da zai kaita har babban kitchen ‘din gidan.


Suna shiga ‘daki Ummeey ta zaunar da ita a bakin gado tana kallonta “Oya gaya min me ya faru? Don dai na san ba k’alau ba. Don’t tell me bakomai.” Ayra ta saki ajiyar zuciya haka kawai sai ta ji k’walla ta zubo mata. Ummeey ta dinga jin sautin bugun k’irjinta yana k’aruwa, da gaske hankalinta ya tashi sosai, har zufa ta fara jik’a mata Riga duk da sanyin A.cn da ake kwarara a zuciyarta ta hau raya in dai har da gaske Turaki ya saki Ayra tabbas zai gane kurensa… ta ciji leb’enta tana fa’din “Ina jin ki Ayra, me ya faru?” Zuwa lokacin sautin kukan Ayran ya ‘Karu sosai ta fara zaro wayarta a jaka kafin ta runtse idonta ta kunnawa Ummeey abinda ya ka’da y’an hanjinta ya razanata lokaci guda, b’acin ranta ya bayyana fuskarta ta canja daga Ummeeyn da aka sani mai fara’a mai yalwar murmushi zuwa wata irin fuska mai bayyana b’acin ranta a fili k’arara…….



𝔍𝖎𝖐𝖆𝖗 𝕹𝖆𝖘𝖍𝖊.
Takaicin Uba….

57.


Ummeey ta sake jan ajiyar zuciyar, da take nuni da tsananin tashin hankalin da take ciki, kafin ta saka hannayenta ta kamo na Ayra cikin kwantar da murya ta ce “Ayra ina neman alfarmarki don Allah kada ki bari kowa ya ji wannnan maganar ta Turaki, idan da hali ka ki gogeta da kaina zan yi maganin abin, wallahi zan k’watar miki y’acinki a wajensa har sai ya amsa laifinsa da kansa mun kuma hukuntashi ba tare da kowa ya sani ba, ba dai kin ce ya janye sakin ba tun kafin ki dawo.” Ayra ta ‘d’aga kai tana jin tausayin Umeey da yanayin da ta shiga, da na sani ya fara rub’anya a zuciyarta sai dai hakan da ta yi ta tabbatar shine abinda zai siya mata mutuncin ta a wajen Turaki ya dawo ya sake neman aurenta da soyayyarta ma gaba ‘d’aya duk da ba a buk’atar sake auren. Ummeey ta sake dafa ta, murya a raunane ta ce “Za mu wuce Gombe, daga can akwai inda zan kai ki a b’oye min ke zan kuma sanar dake cewa ba ki zo ba, zan garga’di su Tasleem ma, zan kuma san hanyar da na bi na hana shi zuwa wajen Amma ko kuma na sanar da Amman ba don komai ba sai don kada ta sanar masa kin zo gari. Zai gane shayi ruwa ne.” Ayra ta saki murmushi tana jin wani farin ciki a ranta.

Umeey ta fita bayan lokaci ka’dan ta sake dawowa tana kallon Ayran “Tashi maza ki koma ‘dakin Mijinki ki kwana a can kafin gobe mu tafi Gombe.” Ayra ta mik’e tana jin wata matsananciyar kunyar Ummeeyn. Ummeey kuwa bata ma lura da ita ba tana ta danna wayarta don neman layin Tayseer don ta sake garga’darta kada ta sanar da Turaki zuwan Ayran.


Ayra ta saki ajiyar zuciya bayan Ummeeyn ta fita, ta cigaba da kallon Bedroom ‘din Turakin da yarda aka tsara shi kamar ba za’a mutu ba. Sannan gaba ‘d’aya ‘dakinsa wani k’amshi yake fitarwa wanda ya ha’de da nasa k’amshin na turaren da yake amfani da su kullum. Ta gefen gadon ta hango hoton matarsa da na Aman sai na sa, Matarsa sai sakin murmushi ta ke, a ‘d’aya side bed drawer ‘din ta ga nata hoton da ya fisgi hankalinta, don dai zana da aka yi ta kuma fito ra’dam kamar dama itace a zanen. Bata san sanda ta saka hannu ta ‘dauki hoton ba daga ganin yanayin hoton lokacin ba zata zarce shekaru sha takwas ba, ta tuna irin ha’duwar da suka yi da Turaki a airport da yanayin kallon da yake mata wanda ya ja tayi saurin jan nik’ab ‘dinta ta rufe fuskarta, lamarin ya shiga dawo mata kamar majigi, a yanzu kam ta tuno inda ta san fuskarsa da a kallo guda ta dinga tunanin kamar ta san shi. Wanka kawai ta yi ta saka nightwear ‘dinta kafin ta ‘Dane gadonsa ta kwanta tana lumshe ido, k’amshin turarensa ya dinga tayar mata da wani irin feeling da zarar ta rufe idonta sai ta ga Turaki yana mata wasu irin wasanni da suke ‘dauke mata wuta, da kyar ta samu barci mai nauyi ya ‘d’auketa cike da tarin mafarkin Turaki mai tsayawa a zuciya.




___________________


K’arfe 9:45 jirgin su Turaki ya sauka a k’asar Nigeria, don ya kasa hak’uri sai da ya nemi Jirgin da zai isa Nigeria ko da ace zai yi transit ne.

Bai kira kowa ba kamar yarda bai sanar da kowa zuwansa ba ya tari taxi ta nufi da shi gidan su.

Gidan tsit kamar yarda yanayin gidan yake daman can musamman kasancewar rashin yara a gida sai Aman kawai shi kuma yana boarding a Nigerian Turkish. Mai gadin gidan ya yi saurin amsar jakar sa y wuce da ita sashen sa, shi kuwa Turaki Direct part ‘din Ummeey ya tafi don burinsa ya ji labarin zuwan Ayran.

Shiru wajen kamar ba kowa sai da Tayseer ta fito daga bedroom ‘dinta jin motsi sannan ta yi arba da shi. Sannu da zuwa take masa Amma hankalinsa sam ba ya kanta ta ji ya jeho mata tambaya “Ina Ummeey?” Tayseer ta danne dariyar da take son kamata ta ce “Bata nan Ya. Wani abu ne?” “Ina taje?” Ya fa’da yana fesar da numfashin tashin hankalin da ya cunkushe masa zuciya. “Tana Abuja. Amma na ji ta ce yau za ta wuce Yola wajen…” da sauri ya tsayar da ita “Kin ji labarin Ayra ta zo?” Tayseer ta ‘dan yi jin kafin ta girgiza kai ta ce “Nop, gaskiya ban ji ba, but am not sure ko tana gidansu.” Ya zauna yana murza goshinsa kafin ya ‘dago idanunsa har sun shige sabida tashin hankali ya mik’e “Oya ba ni key ‘din motar koma waye? Ki zo mu je gidan nasu.” Tayseer zuwa lokaci ta kasa danne dariyar da ke cin ta sai ta wayance da tari kafin ta dakatar ta ce “Ammanta fa bata da lafiya suna Abuja, Umeeyn ce ma ta kaita tun last week.” Ya sake komawa ya zauna yana jin kamar jiri ne ma yake neman ‘dibansa ya san shikkenan yanzu kam ya ga ta kansa Ayra ta sanar da kowa duk abinda taga dama. Wayarsa ya laluba ya fara booking flight da zai tashi in the next few Hours zuwa Abuja. Sannan ya mik’e zuwa sashensa don yin wanka bayan ya karb’i numberr Ayra da take amfani da ita a Nigeria. Ya dinga kira amma wayar ana gaya masa busy take da alama ta sakata a Do not disturb, mik’ewa kawai ya yi yana zirya a ‘d’akin cikin tashin hankali zuciyarsa kuwa gaya masa take Turaki you are finished, ya san in dai Ummeey ta san maganar nan ya ka’de har ganyensa. Jikinsa a sanyaye ya shiga wanka duk da gangar jikinsa ce kawai take buk’atar wankan zuciyarsa da ruhinsa ba ta wankan suke ba. Burinsa kawai ya ga Ayra kafin ta kai ga kunnawa Ummeey wannan recording ‘din.



_____________

Sanda Turaki yake can hankalinsa a tashe, su su Ayra tuni sun isa jihar Gombe wajen na’din sarautar Kakan Turakin wanda za’a bawa Sarkin Fulanin Gombe. Tuni ainahin Family House ‘din nasu ya cika dank’am da jama’a da alama ba k’aramin taro aka shiryawa na’din sarautar ba. Tun daga harabar gidan Ayra take waige-waige don al’ajabi da mamakin ginin da kai tsaye

38 / 45