Author : Nazeefa Sabo Nashe Category : Hausa Book Store
ana ganinsa za’a danganta shi da sarauta.
Bata tsinke da lamarin ba, sai da suka isa ainahin babban falon Matar Kakannasu, duk da tsufanta hakan bai hana bayyanuwar kyanta ba, game da nutsuwarta, tana ganin Ummeey ta ‘dan saki murmushi tana nuna mata wajen zama. Ummeey ta zauna cike da girmamawa hakan yasa itama Ayra ta samu waje ta zauna kamar yarda ta ga Umeey ta yi, suka gaisheta a nutse irin gaisuwar da ake wa Sarauniyoyi masu ji da mulki. Murmushi kawai ta yi tana duban Ayra ta ce Noy belle Didi? Matar Aminullahi ce?” Ummeey ta ‘d’aga kai, Fulani ta ‘d’aga kai “Ma sha Allah, kin ga wani abin mamaki sai ta yi min kama da Kwairanga Ko kuma idona ne?” Ummeey ta ce “Ba mamaki, kin san a duniya sai ka ga wani yana maka kama da wani.” Ta fa’da ba tare da kulawa ba ko don bata san wacce ake nufin bane, don tun kafin a aurota ta rasu ita ce Mahaifiyar Kakan su Turakin. Ayra dai duk ta bi ta takura saboda duk sanda zata ‘d’aga ido sai ta yi arba da Fulani tana kallonta irin kallon da ake kira na k’urilla. Ummeey ta lura da hakan don haka sai ta mik’e tana kallon Fulani ta ce “Bari mu isa masauki.” Fulani ta sake ‘d’aga kai tana sake bin Ayra da kallo, har sun ‘dan fara tafiya suka ji ta ce “Hameeda, Ku zo nan.” Suka sake juyawa suka isa wajenta ta ‘dan mik’e zaune tana kallonsu kafin ta ce “Wannan yarinyar y’ar waye? Kuma daga wace jiha aka aurota?” Hameedah ta ji tambayar ta mata wani banbarakwai sai dai ta dake ta ce “A garin Kano aka aurota kuma sunan Mahaifinta Kabiru ‘dan garin Shagogo mahaifiyarta kuma Talatu duk daga can suka zo?” Jinjina kai
Ta yi kafin ta ce “Ku je.“ ta mayar da idonta kawai ta lumshe tana jin dama abinda take hasashe ya tabbata. Ayra dai ta bi Ummeey jikinta a sanyaye tana mamakin wannan tambayar ta ya Uwarka ta haifeka.
Jirgin k’arfe 8:30 na dare ne ya dire sa a garin Abuja, zuciyarsa cike da tarin tsoron yarda za su ha’du da Ummeey. Tun daga bakin gate ya tambayi Maigadi Ummeey tana nan? Maigadin ya girgiza kai kafin ya ce “Sun tafi Gombe yesterday Morning.” Turaki ya rik’e kansa kawai ha’de da fa’din “Ya Allah! Ita da waye?” Da yake Ummeey ta garga’di mai gadin hakan yasa ya ce “Ita da Tasleem.” “Babu wata a tare da ita?” Turaki ya fa’da hankalinsa a tashe. Ibro mai gadi ya girgiza kai “Gaskiya Yallab’ai su ka’dai ne kawai.” Turaki ya ja tsaki yana shiga gidan jikinsa a sanyaye ya tabbata Ayra tana gidan su kenan ta kuma sanar da Ammanta abinda yake faruwa duk da bai so hakan ba.
Wayar Tasleem ya danna ya kira bugu biyu ta ‘dauka da alamu suka nuna tana cikin hayaniya zata fara gaishe sa ya yi saurin tsayar da ita “Dakata, ke da wa kuka zo Abuja?” “Ni da Ummeey.” Daga haka ta ja baki ta tsuke kafin ya sake watso mata tambaya “Ayra fa?” “Ba ita Ya, wani abu ne?” Ya sake cizar leb’ensa kafin ya ce “Is she coming or not?” Ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce “She isn’t. But am not sure ko tana gidansu yau dai Amman suka koma Kano.” Turaki ya daki hannunsa da bango kafin ya ce “Sun koma Kano?” Ta ‘d’aga kai kafin ta ce “Sure, na ji suna waya da Ummeey, tana ce musu sun je lafiya.” Turaki ya saki ajiyar zuciya kafin ya katse wayar ya sake calling Ayra still busy kawai sai ya yi cilli da wayar yana mik’ewa ya shiga ‘dakinsa. Mamaki ne ya kamasa jin mayataccen k’amshin turaren Ayran a ‘dakinsa ga toilet ‘dinsa yana fitar da k’amshin Almusk ‘din da take yawan Using. Ya shak’i k’amshin sosai ya tabbatar ba hancinsa ne yake gaya masa ba, K’amshin Ayransa ne. Kawai sai ya samu kansa da sakin murmushi A fili ya ce “Sure, Ayra ta zo gidan nan.” Ya k’arasa bakin gadon yana jan pillow ya kai hancinsa still dai k’amshin Ayra ne, kawai sai ya samu kansa da sakin ajiyar zuciya yana rungume pillow ‘din tsam a k’irjinsa kamar ya samu Ayran.
Da safe kuwa Ayra tana gama shiryawa Ummeey ta shigo tana kallonta tana murmushi ta masa gaisuwarta tana fa’din “Jiya Turaki ina ji ya min missed calls sun kai ‘dari, don haka yanzu muna zuwa kika gaida Mai martaba zan wuce da ke gidan Sisterr mai gidan nan, Adda petel ki yi zamanki a can.” Murmushi Ayra ta yi, Ummeey ta mik’a mata babban mayafi ta ce “Yafa maza mu je ki gaida Mai martaba Jauro.” Ayra ta amshi mayafin da yake zuba wani k’amshi kamar an tsoma a ruwan turare suka fita ta wata k’ofa da zata kaika sashen Mai martaba kai tsaye. Duk inda suka shige sai an durk’usa an gaida su har suka shiga k’aramar fadarsa. A kishingi’de suka same sa da carbi a hannunsa gefensa Fulani ce tana sake dama masa furar da zai sha kafin ya fita fada. A nutse yake kallon Ayra kafin ya mik’e cikin tarin mamaki ya ce “Ikon Allah wannan kam Ai sai na ce K’anwata Danejo ce tana yarinya.” Ummeey ta ‘dago tana kallon Ayra da take durk’ushe a gabansu. Fulani ta saki murmushi ta ce “Abinda nake gaya maka kenan, kamannin nasu har sun b’aci.” Ya sake k’ura mata ido yana sake ganin tsananin kamarsu ba banbanci ko ka’dan. Ya amsa gaisuwarta yana fa’din “Sannu yarinya, ni kuwa zan so ganin Mahaifiyarki akwai tarin tambayoyin da zan mata ina ji a jikina ke jinin Danejo ce.” Ayra ta sunkuyar da kanta tana matsa hannunta kafin ta sake ‘dagowa ta kallesa gabanta yana fa’duwa tana fatan duk hasashenta ya zama gaskiya ace wannan su ne dangin Ammanta da wani irin farin ciki Amman zata shiga. Itama Hameeda tunanin da ta shiga kenan, da sauri ta ce “In sha Allah zan kirata za kuma za su zo kafin na’din sarautar gobe.” Ya jinjina kai yana fa’din “Haka ya kamata a yi, kullum addu’ata na ga jinin Danejo ko da ace ita bata raye, ashe ma tana raye don jikina yana ba ni wannan daga duk inda ta zo jinin Danejo ce. Suka masa sallama suka tafi, zuk’ata cike da tunani kala-kala, da jiran zuwan gobe su ji daga bakin Amma, idan hakan kuwa ta tabbata ba su san wani irin farin ciki zuri’ar za su ji ba, shikkenan tafiya gidan Adda petal ya sha ruwa. Aka zauna zaman jiran gobe a ga mai Amma Talatu zata ce….
𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍 𝕹𝖆𝖘𝖍𝖊✍️
Takaicin Uba…
58.
Da mugun speed ya danna hancin motarsa cikin harabar ajiye motoci ta masarautar.
Ya saki ajiyar numfashi bayan ya yi parking ya lumshe idonsa yana addu’ar Allah yasa komai ma yazo masa da sauk’i kada Ummeey ta yi masa bore. Tsawon mintuna biyu ya ‘dauka zaune a cikin motar kafin ya kalli mudubi yana kallon yarda rashin nutsuwa ya ranar da shi in just a few days. Wayoyinsa kawai ya ‘d’auka ya sauko daga motar tasa don long driving ya yi from Abuja zuwa Gombe. Nan da nan Hadimai suka yi cincirindo a gabansa kasancewarsa mutum mai barkwanci da yawan kyauta. Hannu kawai ya zira a aljihunsa ya ciro ku’din da bai san adadinsu ba ya mik’a musu, sannan ya ‘d’aga musu hannu alamar ba ya son dandazon rakiyar da za su masa. Ya cigaba da takunsa cike da nutsuwa yana kallon gefe da gefen masarautar yarda bak’i suka fara cika wajen.
Sashen Mahaifinsa ya nufa don ya tabbatar Ummeey tana can tunda a can ‘din ta saba sauka.
Yana tura k’ofar idanunsa suka fa’da cikin na Ayra da take tsaye da Tasleem tana nuna mata wani abu a waya.
Wata irin fa’duwar gaba ce ta samu Ayra, da sauri ta juya tana runtse idonta, ashe shine zai zo shi yasa tun safe take jin yanayin sauyawar bugun k’irjinta. Ya k’arasa wajen su yana niyyar yi musu magana Ayran ta yi saurin shigewa ‘dakin da ta sauka ta murza key. Murmushi Turaki ya saki yana kallon Tasleem da ta zuba masa ido ganin yarda ya bi k’ofar da Ayran ta shiga da wani kallo yana cije leb’ensa “Kallon fa?” Ya fa’da yana gimtse fuskarsa “So na fara wasa da ke kenan, shi yasa na tambayeki ta zo kika ce bata zo ba ko?” Tasleem da sauri ta fara ja baya tana fa’din “Am sorry Ya. Ummeey ce ta ce kada mu fa’da maka.” Ya ‘dauke kansa yana zama kan kujera ha’de da cusa hannayensa cikin tarin sumar kansa a hankali ya hau furta “Ayra!” Sai kuma ya
Lumshe idanunsa yana tunanin wani irin hukunci zai mata idan ya kamata don ta wahalar da shi sosai, Tasleem dai tana tsaye tana kallonsa tana sakin murmushi k’asa-k’asa. Idanunsa ya ware a kanta ya ce “Samo min coffee mai zafi Malama.” Da sauri Tasleem ta juya ta shiga babban kitchen ‘din su tana y’ar wak’a don idanun Yayan nasu kawai za ka kalla ka hango tsagwaron soyayyar da yake wa Ayra Gaya.
Tsam ya mik’e ya isa bakin k’ofar ‘dakin ya ‘dan yi knocking , Ayra da take ciki da sauri ta ware ido tana fa’din “Waye?” “Idan kika bari na kamaki ko? Zaki gane kurenki, ina wasa da ke ne?” Ayra ta tab’e baki tana fa’din “Ba zan bu’de ba, me ye naka a wajena.” Turaki ya yi k’wafa yana barin wajen, jin takun tafiyar Tasleem. Sai da ya karb’i Coffee cup ‘din sannan ya kalleta “Ummeey fa?” Ta nuna masa ‘daki. Ya rik’e cup ‘din ya nufi ‘dakin Ummeey yana fatan Ayran bata gaya mata komai ba.
Ummeey ta bi shi da kallo bayan ta kashe wayar da take amsawa. Kallon ne ya tada hankalin Turaki da k’yar ya ‘daga k’afarsa ya isa inda take, idanunsa a rusune ya zube daf da k’afarta. “Ummeey ina yini?” Bata amsa ba illa zuba masa ido da ta yi tana jin wani takaicinsa yana cika mata zuciya. “Me kazo ka ce min Turaki? Ko ka zo ka kawo min takardar sakin ne? Tunda magana da fatar bakin ba ta yi ba?” Hanjin cikinsa ne ya ka’da ya ware idonsa sosai yana fa’din “Saki kuma Ummeey? Sakin wa?” “Sakin Ayra da ka yi mana.” Da sauri ya ajiye cup ‘din da yake sipping coffee ‘din ya ce “Haka ta zo ta ce miki Ummeey? Wallahi ni ban sake ta ba, ban kuma furta mata saki ba, wancan furucin da na mata idan ma shine na janye.” “Saboda yanzu ka sameta a cikakkiyar budurwa ko? Sab’anin da da kake tunanin fanko ce, shi yasa ka janye sakin? Ashe Turaki ba zaka iya rufa wa Ayra asiri ba, ko da ace abinda kake tunani haka ne, to bu’de kunnenka da kyau ka ji, tunda har ka yi wannan furucin to ina tabbatar maka dole ne ka saketa don ni ba zan bari ta zauna da wanda bai san mutuncin mace ba, ce maka aka yi duk macen da ta rasa budurcinta bata da mutunci kenan? Kada ka manta wasu fa tsautsayi ne yake ruftawa da su, ya zaka yi idan k’anwarka
Ko y’arka aka yiwa fya’de shikkenan za ka ji da’di idan wani ya saketa saboda rashin budurci, to ba zan amince ba dole ne ka saki Ayra, tunda ka tabbatar bata rasa budurcin ba, ni kuma ina goyon bayanta ba zan saka ta zauna da kai ba dole, idan ka ga har na amince Ayra ta koma gidanka sai dai idan da kanta ta furta tana son komawar, don haka sai ka je ka fara shirin kafa gwamnatinka a wajenta har sai ta amince a kan kin kanta Zata koma sai ku zo ku same ni tare ku sanar min kun sasanta.” Turaki ya zaro ido kafin zuciyarsa ta shiga bugu da k’arfin gaske tunaninsa ta ina zai fara shawo kan Ayra, a hankali ya furta Ya Allah! Ummeey ta kalleshi tana tab’e baki ta mik’e tana nufar k’ofa “Idan ka fito ka kulle min k’ofa.” Turaki ya ‘d’aga kansa kafin ya mayar da ido ya lumshe yana tunanin ta wace hanya zai shawo kan Ayra Gaya, daga ganinta zata yi kafiya da taurin kai…. Ya saki hucin numfashi yana fa’din God help me!
Yana kwance a ‘d’akin Ummeeyn ya ji an turo k’ofa. Ayra ce a tsaye ta yi kicin-kicin da fuska Ummeey ce ta aikota ‘daukar mata Hijab zata gaisa da bak’i a fada. Turus ta yi ganinsa kwance a kan hannayensa idanunsa a lumshe kafin ya bu’de ya ware su a kan Ayra da take tsaye ta ha’de rai. Mik’ewa ya yi a hankali da niyyar gyara kwanciyarsa ya shammaceta ya jata jikinsa sai gata a kan ruwan cikinsa ta zaro ido tana kallonsa kafin ta ce “Malam me ye haka?” Ya ja karan hancinta kafin ya ce “Mele ne, ke zan tambaya me ye haka? Me kika zo kika cewa Ummeey?” Ta hau zame jikinta a hankali tana cewa “Abinda ka ce min, ni ka sake ni.” “Na k’i na sake ki ‘din, ashe baki da kai, wa yace miki ana wasa da kalmar saki, Karen hauka ne ya cije ni da zan sake ki? Kin san tsawon lokacin da na ‘dauka ina dakon soyayyarki, sannan na je na ‘dan d’ano abin can ba dama ki ce kuma na sake ki, Auren mu na nan mutu ka raba.” Ta sake k’ok’arin k’wace jikinta don tana jin wani irin yanayi a duk sanda ya yi magana hucin numfashinsa ya sauka a wuyanta, “Ka cika ni na kai mata Hijab wajen ba’ki zata je.” K’ura mata ido kawai ya yi yana kallon yarda lab’banta masu d’an tudu suke shining suna fusgar hankalinsa idan tana magana. Yatsansa ya saka yana zagaye leb’en kafin ya kai masa kyakykyawar sumbatar da ta kusa matar da Ayra a zaune, ya saketa yana ja baya ha’de da runtse idanunsa “Je ki Ayra kada ki jawo na aikata komai a ‘d’akin nan, don Allah ki yafe min ki ce ma Ummeey kin yafe min kin ji?” Ayra ta mak’e kafa’darta irin yarda yara suke yi idan sun so rigima. Turaki ya lumshe ido yana jin yanayin nata yan saka a duk wasu gab’ob’insa amsawa “Ki wuce tun kafin na sauke gajiyar da na kwaso a jikinki yanzun nan, ba ki san yarda nake missing ‘din ki ba ko?” Ta tureshi da sauri tana mik’ewa jin inda hannunsa ya kai. Da sauri ta fice daga ‘dakin tana ‘dan haki, sai da ta tsaya a corridor ta gyara gashinta da ya barbaje da yamutsewar rigarta sannan ta nufi falon, duk da bata san k’amshin turarensa ka’dai ya isa a gane daga inda take.
Wayam ta ga parlourn ba kowa, da sauri ta isa kitchen wajen Tasleem da suke shiryawa su Amma girki ta tsaya tana kallonta kafin ta ce “Tasleem Ummeey fa?” Dariya ce ta so kama Tasleem ta ce “Ta gaji da jiranki ta ‘dauki nawa ta fita.” Ayra ta lumshe ido tana sakin ajiyar zuciya “Toilet na shiga shi yasa na da’de.” Wannan karan Tasleem kasa ha’diye dariyar ta yi sai da ta dara sosai sannan ta ce “A toilet kika kwaso k’amshin Turaren Mijinki kenan?” Ayra ta waro ido tana shinshina jikinta da sauri ta fice a guje, Tasleem ta bita tana fa’din “Kina canja kaya kuma zata yi tunanin babban lamarin ne ya afku, kin ga shikkenan sai ta tattara ta koreku ke da mijinki.” Ayra ta dafe kanta tana zama a kan kujera ta ce “Ya Allah! Yanzu Tasleem ya zan yi?” “Mursisi za ki yi, ki daina wahalar da Yaya na haka Wallahi yau ya bani tausayi.” Ta ha’de rai tana mik’ewa ta ce “Never! Kin san kuwa me ya yi min? Mu je dai kawai mu k’arasa aikin mu.” Shi kuwa Turaki da k’yar ya mik’e ya isa ‘dakinsa da yake nan sashen ya baje a kan gado
Gaba ‘d’aya kwanyarsa ta tsaya masa cak, matarsa kawai yake buk’ata. Mafita kawai yake nema.
Suna aikin Ummeey ta dawo daga wajen bak’in, Ayra na jin shigowarta ta ji kamar ta nutse a wajen don kunya, Ummeey kallonta kawai ta yi ta ‘dauke kai tana murmushi ha’de da bu’de dishes ‘din ta ce “Yauwa komai is ready sai jiran zuwan su Amma.” Ayra ta saki murmushi tana saurin ficewa ha’de da cewa “Bari na yi wanka kafin su zo” Ummeey ta bita da kallo tana murmushi kawai ganin yarda duk take a firgice ga k’amshin turaren da ya mak’ale a jikinta. Tasleem ma murmushin take tana mamakin rashin wayo irin na Ayra kamar yarinya k’arama.
___________
Sai Yamma su Amma suka iso, a guje Ayra ta taresu tana jin kamar ta mayar da su cikinta. Amma ta dafa kanta kawai tana murmushi ganin yarda Ayran ta sake cika ta kuma yi fari tas da ita. Nan suka baje don cin abinci kafin su yi wanka a rakasu wajen Mai martaba.
Bayan sun yi wankan suna zaune a parlour Turaki ya fito cikin rantsatstsiyar shigarsa ta Farin voile tas da shi, sai baza k’amshi yake ga hula da ya kafa a kansa ta sake fito da tsananin kyansa da cikar kamalarsa. Kallo ‘d’aya ya yiwa Ayra da ta mak’ale jikin Amma kamar zata shige cikinta, ya durk’usa ya gaida Amma a ladabce kafin ya gaida Majeedah, Zainab, Aysha da kuma Deejah sai Inna Jummai. Suka amsa masa da walwala fal fuskarsu, kafin Umeey ta ce “Ka gaida Babanta Kamilu yana Babban falo, k’anin Babanta ne shak’ik’i.” Turaki ya ‘d’aga kai kawai yana sake kallon Ayra ta gefen ido da itama take kallonsa a sace. Ya mik’e ya wuce ta gefenta ta shak’i k’amshin turarensa ta ‘dan lumshe ido ka’dan tana jin fa’duwar gaba na sake kamata.
Sai da suka gama abinda suke, sannan Ummeey ta mik’e don musu iso duk da bata sanar da su dalilin kiran ba, ta ce dai ya kamata suma su zo na’din sarautar shine suka zo a zuwan y’an gayya.
Tunda Amma ta saka idonta cikin na Mai martaba ta ji fa’duwar gabanta ta