KAREN BANA COMPLETE BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.txt

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 14

27K to 30K   out of 39.4K words

yadace,wanda tasleem ta jima da ficewa hankalinta,dan har kara kamoshi takeyi,in yayi kamar ze bari😝


Sunfi awa suna romance din juna,kamin daga bisani Auwal yay ma tasleem wata irin matsa wacce tasata dawowa cikin hayyacinta.

Yadda taga yanayi jikinshi na rawa,ga gumi dake keto masa kamar an sashi a oven,sosai abun ya tsorata,gashi ya riketa kamar ze karya,

Zuwacan taga ya kife kan gadon kamar wanda ya mutu.

Abun na Auwal sosai ya firgita tasleem sekace wani me aljanu.

Cikin shi ta kalla taga yana numfashi,se alokacin ta samu kwanciyar hankali.

Rigarta ta fara nema ta mayar amman bata ganta ba,rasa yadda zatayi tayi,dan so take tabar dakin kamin Auwal ya tashi.

Har kasan gadon ta sauka ta duba bata ganiba.

Dana sani ta tunga yi gameda bin shawarar yusura,da tazo batayi wankan ba,ay ko tsamin jikinta baze bari ya tabata ba amman shegen iyayin yusura yasata tazo gashi tana data sani.

Tana tsaye duhu ya mamaye dakin sakamakon dauke wuta da akayi.
rasa yadda zatayi tayi,dan arayuwar tasleem ta tsani duhu,dan haka da lalube ta karasa kusa da gadon da yake kai yana bacci itama ta haye kan gadon,

Bargo taja ta rufe jikinta,gamida adduar Allah yasa akawo wuta ko akunna generator.

Tana nan kwance zaman jiran nepa,bacci yay awon gaba da ita.

Sabida tsabar jin dadin baccin hayewa kanshi tayi abunta tana cigaba da shirgar baccinta,

Asuba tagari tasleem.

Muje zuwa.


surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA..........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAHRA SURBAJO*



*Dedicated to Billy shantally*



*36*



Baccin su dukan su sukayi cikin kwanciyar hankali,

Sede cikin dare Auwal yaji numfashi na mishi wuyar shaka hakan yasa ya farka ba shiri,

Har ze kai mata wani naushi,danshi azatonshi ammar ne,

Cak ya tsaida hannun ganin tasleem kwance dare dare kanshi tana bacci.

Da sauri yakai dubansa kan agogon dakin,karfe biyu na dare.

Hannu ya dora a kai sabida tsananin kunyar su mummy data kamashi,in suka san tasleem gurin shi ta kwana.

A hankali ya kwantar da ita kan gadon,ya shiga safa da marwa,tunanin shi in safiya tayi.πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Gashi yasan ammar farfesa tuni ya fesa acikin gidan.

Ganin ya rasa abunyi ne kawai yasa ya fada toilet,domin tsarkake kanshi.

Inda yadunga tuno abinda ya wakana tsakanin shi da tasleem,wata kunya yaji ta sake kamashi.

Wani sashi na zuciyarshi ne yace masa.

"ya kamata de kadunga dan kama kanka,kar ka bari yarimyar ta rainaka da yawa"

Murmushi yayi yaci gaba da wankansa.

Yana fitowa doguwar riga yasaka da gajeren wando,sannan yaje kan gadon ya dan dagata ya maidar mata da rigarta,sannan ya kwanta,ya maida ita jikinshi ya kwantar da ita gamida sa hannu yaja musu bargo.

Tasleem mage uwar son jiki har da sake gyara kwanciya ajikin nashi.

Sosai yake jin dadin kasancewarsi ahakan,jawai tunaninsa yadda zasu kare da safe.


Ahaka bacci me nauyi shima yay awon gaba dashi.

Tunda baccin ya daukeshi,basu suka farka ba se bakwai na safe,duk sun makara.

Tasleem ce ta fara farkawa,jinta jikim mutum ne yasa tai saurin duban inda take kwance.

Azabure ta mike tana waige waige.ganinta adakin ya Auwal ne yasa ta saki kara.

Azabure ya farka dan yadauka wani abunne yasameta.

Itako kuka ta rushe dashi na bakin ciki da kunya na kwana agurinshi da tayi.

Dafata yayi yana tambayar.

"meke faruwa kikewa mutane ihu aka irin haka?"

doke hannum nashi tayi sannan tace.

"Ban sani ba,wlh ka cuceni,kasa na kwana agurinka yanzu ni bansan da idon da zan iya fita zuwa cikin gida ba"ta karasa maganar cikin gunjin kuka.

"kaji yarinyar nan,na cuceki kode kin cuceni,duk ke kika jawo min ni bansan ya ma zanyi ba"cewar auwal yana murmushi.

Tsaki tasleem tayi gamida ci gaba da kukanta.

Auwal alwala yaje ya dauro yazo yayi sallah bayan ya idar ne yacewa tasleem dake zaune tun dazu tana kuka.

"se ki tashi kije kiyi wankan tsarki kizo kiyi sallah"


Wata zazzafar kunya ce ta kamata data tuno,abinda ya faru jiya.

Sum sum ta mike ta shige toilet dinshi.

Tayi wankan,ta daura towel iya cinya sannan ta rufa wani akanta,tayi alwala.

kanta akasa ta fito daga toilet din sabida kunya dan duk bakinta ya mutu.

Koda ta fito yana kan abun sallah har lokacin.

Kan doguwar kujerar dakin taje ta zauna,dan bata da hijab bare kaya adakin da zata saka tai sallar.


Shafa adduar da yakeyi yayi sannan ya mike ya dauko wayarshi,dake gefen gado.

ya koma kan kujerar da ta ke kai,ya zauna.

Number yusura ya dannawa kira,ayko ba jimawa ta daga gamida cewa.

"ina kwana yaya ya karfin jikin?"

Gyara murya yayi da kyau shi adole beson wasa yace mata.cike da shan kamshi.

"lafiya lau,ki kawowa tasleem,kayan sawa da hijabi,yanzu"yana gama fadi be jira amsarta ba ya kashe wayar.

Dubansa yakai gun tasleem din wacce tai tsuru kamar ruwa ya jika zakara.

hannu yasa ya kwanto ta jikinshi,ayko kamar jira,ta shiga yimishi kukan shagwaba tana fadin.

"me yasa ka kira yusura,ni wlh banso tazo ta ganni haka,kasanta kwai surutu,"

Lakace mata hanci yayi sannan yace.

"to zan boyeki in tazo bazata ganki ba"

suna haka yusura tai sallama kofar dakin.

Ayko azabure tasleem ta sake rike Auwal.



Hannu yasa ya rungumeta da kyau ta yadda ba me ganin fuskarta.


Sannan yaba yusura izinin shugowa.


Yusura,tsinto tasleem tayi jikin auwal,daure da towel,ga kai ajike.

Kadan ya rage ta fadi gurin kallonsu,dariya takeson yi amman ba hali,dole ta gimtse ta aciki gudun karta sha duka.

Mika masa kayan tayi sannan ta juya sum sum ta fice a dakin dariya fal cikin ta.

Fitar yusura ke da wuya tasleem ta mike ta amshi kayan ta saka,tasa hijab ta shimfida abun sallah tayi sallah.

bayan ta idar Auwal yace tazo suje cikin gida dan su gaisa da su umma.

Da kyar taslee. ta yarda ta bishi,amman boye take abayansa,dan kunya sosai take ji.


Muje zuwa


surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*SANADIN KIDNAPPING*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAHRA SURBAJO*


*Masoya na kuyi hkr don Allah, ina gani sakwanninku akoda yaushe na cigiyata da littafina,kuma inajin dadin hakan sosai,shiyasa na dauki aniyar ganin nayimasa zama daya domin ku,surbajon ce yanzu ba irin ta da ba,nauyi ne yadan karu wanda ke cinye duk lokacina dan haka kuyi hkr,bayan Sallah da yardar Allah akwai show me dadi,*

*Zanyi amfani da wannan dama domin mika gaishe gaishena wanda suka faru abaya.*


*Mrs mahmoud ina miko taaziyata game da rasuwar mahaifinki Allah yajikansa yasa aljanna ce makomarsa,Esha mustapha mama ta tafi mama ta dawo,Allah yajikan mahaifiyarki yasa aljannace makomarta,little mama da muka samu kuma Allah ya rayata bisa tafarkin tsira,Hafsat dahir jos Allah yajikan babyn mu ke kuma Allah ya baki lfy,ya maida alkhairiFiddah sokoto ta ayman bada kanki asare😜tunda ayman ya koroki yanzu iro ya dauka to ina miki adduar samun dauwamamman zaman lfy fiye da yadda ummu aymana ta samu agidan ayman,asha shayi lahiya😜,kuna da yawa wasu har na manta sunan da akwai mutane biyu da suka haihu kwanaki a group dina na zahra surbajo novels,i think jamur yar baba na ciki,da maman zainab data haihu yarinyar ta koma,duka ina miko sakon taaziyata da taya murna,ngd*

*mmn gidado,inna ibrahim kime,billyn shantali,minash,jidda abbas,hassan atk,salbiyya adam,fatima radda,esha mustapha,hafsat dahir,fidda,mrs mahmoud,salma b etc,you mean everything to me,*


*Dedicated to Fatima Abubakar Radda*


*39-40*


Hon suke mata akan ta tashi akan hanyar amman ina kojinsu batayi,ganin haka ne yasa sojoji fitowa dauke da bindigu sukayi setinta da su domin atunaninsu yar kunar bakin wake ce.

Ganin bindigane yasa rahama dawowa hayyacinta,akidime ta ruga da gudu gurin sanaya da nufin daukarta su gudu.

Bin ta sojojin sukayi dan koya mata hankali,dago sanaya tayi,wanda hakan yay daidai da waigowar me girma gomna dake cikin mota yana kallon meke faruwa.

Ko a mafarki yaga sanaya dole ya ganeta sabida son da yake mata yafi gaban wasa,jikinshi har bari yake gurin bude motar ya fito,

Da gudu ya nufe su yana kiran.

"my baby sanaya"

A razane sanaya ta farka tana bin shi da ido,hannu ta mika masa kamin ya karaso ta sake sumewa,yana zuwa rungumeta yayi yana kukan kiran sunanta,

Se alokacin ya lura da cikin jikinta,ga jini dake zuba akidime ya dauketa sukai mota rahama nabin su abaya.

Kai tsaye asibiti na musamman suka nufa da ita wanda tunkan su iso anyi waya dan haka komai ready sukawai ake jira.

Ana gungurata agadon daukar marasa lafiya daddynta rike da hannunta yana kuka har suka karaso kofar labour room.

dakatar dashi likitocin sukayi awaje sannan suka shige da ita.

Duk abinda yadace shi sukai mata,yayinda awaje daddy yakasa tsaye ya kasa zaune kuka yinshi yake kamar yaro,dan wannan ne karo na farko daya taba ganin sanaya cikin mawuyacin hali.

Cikin ikon Allah da taimakon kulawar likitoci ta haifo yaranta guda biyu duka maza,masu kama da mahaifinsu.

Sede rayuwarsu na cikin danger dan babu isasshen jini ajikinsu daga su har mahaifiyarsu wacce batasan inda kanta yake ba.

Sanda likitoci kema daddy bayani komawa yayi kamar dutse dan tsananin tausayi,taya zaace jariri ba jini,rasa abun yi yayi seda likitan ya sake mgn.

"your Excellency ba bu isasshen lokaci zamuje lab aduba in akwai wanda zeyi daidai da su se asa musu"

"ban amince asa musu jini wani ba,jikokina ne fa,muje aduba nawa in zeyi"cewar gomna yana share hawaye.

Koda akaje lab jininsa donor ne dan haka beda matsalar bawa kowa,seda aka dibi leda hudu ajikinshi,😜,

biyu akasawa sanaya daya daya kuma akasawa babys din duk da basu shanye shi duka ba.

Seda jinin ya kare sannan aka fito da babies din da se kuka suke.

Rahama rasa inda zata zauna tayi don murna yayinda daddy shima baa barshi abaya ba gurin murnar samun karuwar.

Sanaya se magrib ta farfado,sanda tai arba da daddy kuka ta rushe dashi,tana mika masa hannu da sauri yaje ya kama hannunta yana shafa kanta.

Cikin kuka take fadin.

"daddy ka yafemin,wlh son mijinane yafi karfin zuciyata kayi hkr"

"haushin ki kawai nakeji baby na amman na jima da yafemiki,ki kwantar da hankalinki kinji,"cewar daddy cikin sigar rarrashi.

"daddy nagode,saura safwan shima ka yafe mishi don Allah daddy"

"taya zan yafewa wanda besan darajarki ba,kinsan aya na ganki kuwa inda ban zoba kinsan meze faru,no sanaya babu yafiya tsakanina da safwan he hurt me alot,and yoo too,"

Zata sake mgn ya zare hannunshi anata ya nufi gadon jariran dake ta faman cilla kafafunsu sama.

Sosai yakejin son yaran azuciyarsa,duk da kamannun dasuke da safwan hakan be hanashi sonsu ba.

Waya yayi gida ya sanar da mahaifiyarta da mubina,baa jimaba suka iso asibitin cike da kewar yar uwarsu.

Tunda suka rungumeta sun kai minti goma basu sake ta ba dan murnar ganinta.

Rahama ko nacan wajen dakin tana ta faman kiran safwan wanda ta gagara samunshi.

Kwatsam se gani tayi yana kiranta,da sauri ta dauka tana fadin.

"haba yaya ina kashiga irin haka,nemanka nake kamar zanyi hauka,yau wlh saura kiris sanaya ta mutu,"

Ji tayi alamun faduwa yayin da ta jiyo hayaniyar mutane awayar ana fadin.

"Ku kira ambulace sagent safwan ya fadi,"

Agigice rahama ta mike tayi cikin dakin tana kuka ,

Arazane sanaya take binta da kallo inda ta kasa daurewa tace.

"sister lafiyarki kuwa?"

Cikin kuka tace.

"aunty yayane nakirashi ina fada masa abinda ya faru dake nace yau saura kiris ki mutu be jira na karasa ba se ji nayi hayaniya agurin ana fadin wai akira ambulace ya fadi"ta karasa maganar tana kuka.

wata irin kara sanaya tayi itama ta koma ta kwanta sharab,agigice ayi kanta sede ina ba numfashi jikinta.

Daddy gurin gudun kiran doctor har faduwa yayi sabida rudewa .


Doctor na gaba daddy na binshi abaya gudu suke amman daddy har hankadashi yakeyi,dan ya raina gudun nasa.

Doctor be jira wata wata ba yasawa sanaya oxcygen,

Duk wani taimakon gaggawa shi aka mata,inda akasamu ta farko,sede fa ta dage ala dole se ankaita gurin mijinta,hankalin daddy in yayi dubu ya tashi,ko kadan taki jin rarrashi,ita sede akaita gurin safwan.

Shiko safwan yanacan rai ahannun Allah dan dan ji yayi rahama tace mishi sanaya ta mutu.

Koda aka kaishi asibiti babu sauyi,dan ko numfashi bayayi.

Rahama kuka tasa su daddy agaba itama tanayi akan ataimaki dan uwanta.

Akaro na farko da daddy yaji tausayin wani abu da ya shafi safwan,

Wayar babban sojan dake kula dasu safwan din ya kira,inda ya bukaci da asako safwan ajirgi zuwa kaduna yanzu yanzu.


Cikin awa biyu an iso da safwan kaduna,karkashin rakiyar sojoji,ciki harda babban sojan.

Ambulance ce ta daukoshi zuwa asibitin garden city dake kaduna.


wayyo sanaya jin ance an iso dashi da kyar ta iya mikewa rahama da munaya suka riketa zuwa inda aka doroshi akan gadon daukar marasa lfy,yayinda duk jikinshi an daureshi da belt,

Jiki na bari sanaya ta dora hannunta akanshi tana fadin,

"hubby pls katashi,karkaimin haka,ban mutuba gani nan da raina harda yaranmu katashi kazo muje ka gansu"ta fadi tana kuka.

Hmmm love magic ya wuce wasa,se gani sukayi safwan na motsi,gamida tari😜


Da sauri aka karasa dashi dakin da yadace,wanda tunkan ashiga ya bude idonshi yana kallon sanaya hawaye nabin idonshi.


Daddy komawa gefe yayi yana kallon sarautar Allah,danshi ko a film betaba ganin so irin wannan ba,se ayau ya yarda babu me rayuwa cikinsu in ya rasa dan uwansa,sosai ya gamsu da son da sukewa juna.

Sanaya fafur taki daukar yaran bare ta gansu wai acewarta se safwan ya miko mata da hannunsa atare zasu ganiπŸ˜‚




Muje zuwa anjima.


Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA.........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAHRA SURBAJO*



*Amin afuwar rashin jina kwana biyu,wani uzurine yadan sha kaina amman yanzu alhmdllh komai normal*


*Dedicated to Billy shantaly*



*37*



Falon gidan suka nufa,yusura se sake boyewa take abayansa.

Suna shiga shima wata kunyace ta kamashi,ganin mummy da umma zaune sun zubo musu ido.


Da sauri ya tsuguna daga inda yake,ay tasleem na ganin shida ya kareta ya tsuguna,da sauri itama ta tsuguna abayanshi ta yadda bata ganin fuskokinsu.

Mummy murmushi tayi sannan tace.

"Ango idonka kenan,?"

Wayyo kunyata Auwal keya kawai yake sosawa,ya kasa magana.πŸ˜‚πŸ˜‚

Mummy dariya tayi tace.

"to ina ka baromin yar tawa ko bata tashi barci bane?"

Akunyace yace.

"ta tashi mummy tare muke ay gata nan"yasa gannu ta bayanshi yana kokarin zaro tasleem.

Ay zaku rantse da Allah zaneta zaayi,tunda ya rukota tashiga shirga mishi duka,tana fadin.

"wlh bazata ganni ba,ni ba abinda nayi wlh kaine kasa nai barci adakinku,wlh bazata ganni ba"magana take cikin kuka bilhakki da gaskiya.


Kowa na falon dariya yake,dan koni na daraπŸ˜‚πŸ˜‚

Auwal ji yayi kamar ya nutse agurin sabida shirmen tasleem.

Suna haka Ammar ya shigo duk yayi gumi,yana ganin auwal ya fara cewa.


"Ango ango kasha kamshi,wlh wahalar da nayi da sassafennan bashi ne in nawa yazo dole aramamin ehe"

Cikin rashin fahimta yake kallonshi.

Shiko Ammar dukawa yayi gaban mummy yace.

"mungama zuba kayan,naje nayo full tank din,kuma anyi service,ba wata damuwa zasu iya tafiya"

"to Allah yayi Albarka"cewar mummy sannan takai dubanta gun Auwal tace.

"To Auwal tashi ku tafi kar kui rana ahanya,ga hanyar ba kyau"

Cikin in ina auwal yace.

"mummy ina zamuje?,kuma ni da wa?"

"Gidan ku Abuja mana,kai da tasleem"cewar mummy tana murmushi.

Tsilim tasleem ta fito daga bayanshi,tafara zunduma ihu.

"wlh bazan tafi koina ba,mummy don Allah karki koreni,laifinshi ne shi yadace ki kora ban da ni,don Allah karkumin haka"cewar tasleem tana kuka gamida birgima akasaπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Dagota mummy tayi tana dariya tace.

"waya cemiki korar ku mukayi?ko kinmanta ba a gidan iyaye ake zaman aure ba,dole dama ay ku tafi can,da badan rashin lafiyar da yayi ba ay da tuni kuna can,dan haka ki dena kuka,daga ke har shi ba wanda yay laifi"

sam tasleem taki yarda ihunta kawai takeyi,ita bazata tafi ba.

Shiko Ammar cike da murna yaje gun auwal yamika mushi key din mota gamida cewa.

"ayi tuki da lura dan Allah,kar ku jefa kanku rami"yayi maganar cikin tsokana.

Auwal ba baka se kunne,dan abun ya girmameshi.


Dakyar ya iya cewa.

"mummy to ay bamuci abinci ba"

"yana mota an zuba muku a kuloli,kwaci ahanya"cewar umma dase yanzu tai mgn.

Shuru yayi yarasa kuma abin fadi.

Suna ji suna gani akai musu kora da hali,πŸ˜‚,tasleem koda aka fito rakasu fun mota dambe take bilhakki bazata tafi ba.

umma komawa falo tayi ta dauko wayar radio ta biyo ta,ayko ta samu ta shimfida mata daya a duwawu.

Wata kara ta saki sannan ta runtuma da gudu ta shige motar.

Auwal akunyace ya duka gabansu yace.

"mummy da Umma in mun muku laifine kuyi hkr ku yafe mana"

Atare suka bashi amsa.

"Ba abinda kukai mana Auwalu,Allah ya baku zaman lfy"

Haka ya mike jiki ba kwari ya shiga motar,ya tada ita,suka fice agidan kowa na daga musu hannu yusura har da hawayenta na rabuwa da tasleem.

Ba kunya Ammar agaban su mummy yakai mata duka akafada yace.

"ke dalla meye na kuka,ay wannan part one ne,mune zamuyi part two,su ansan zasu tafi namuko sede aduba aga bama nan"πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜πŸ˜


wayar radio hannun umma Mummy ta amsa ta zuga masa gamida fadin,

"zakaci gidanku ne wlh tunda baka da kunya"


Da gudu yabar gurin yana dariya.


Seda suka dena hangosu sannan suka koma cikin gidan.


Ango da Amarya kuwa,tafe suke tasleem na zazzaga mishi masifa ta inda tashiga batanan take fita ba,shide ya mata shuru ya kyaleta.

koda yay mata shurun ita taki dena mgn,har suka var kaduna tasleem masifa take,wai ya sauketa ta koma gidaπŸ˜‚

Auwal be kulata ba har suka shiga dajin jere.suna shiga daidai tsakiyar dajin yayi parking abakin titi.

yace cikin daka tsawa.

"fita ki koma din"

ba musu tasleem ta bude motar ta fice abunta ta banko mishi kofa.

dayake gurin duk direba in yazo daidai dajin jere gudu yake bana wasa ba.yasa Auwal sa signal alamar yanason hawa titi yaci gaba da tafiya.

Tasleem jira take motocin sudan ragu ta tsallaka hannun komawa.

Idonta ne ya sauka kan allon signboart dake gefen titin,inda taga ansa.

*JERE* da manyan baki.

Sake ware ido tayi ta sake kallo,ilai shi din tagani,wanda in bata manta ba,gurine dayay kaurin suna gurin kidnapping,da kashe mutane.

Waigawa tayi ta hangi Auwal yana tafiya Ahankali kamin yasamu damar hawa titin sosai.

wayyo Allah kafa me naci ban baki ba.

gudu tasleem take kamar zata tashi sama tuni ta zubar da takalmanta ahanya,danji take kamar an biyo ta zaa kama.

ihu take tana kiran sunan shi tana daga hannu alamar ya tsaya.

Ta gaji da gudun,tana hango shi sanda yasamu damar hawa titi ya jefa motar da gudu ya kama hanyar abuja.

Kifewa tayi agurin tana kuka,


Tofa


muje zuwa.


surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA............*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAHRA SURBAJO*


*Wattpad@zahrasurbajo*

*ig@zahra_surbajo1*


*facebook@surbajo maman yusuf*


*whatsapp@😝😝😝😝*

*Dedicated to Billy Shantaly*


*38*



Kuka take harda majina,durkushe agurin,gashi ba me ko kulata wucewa kawai akeyi,

Gashi aduk iya hangenta bata hango gida kusa da ita ba bare taje.

Sede abinda bata saniba shine.

Koshi Auwal daya sauketa ba iya tafiya zeyi ba,dan tunda ya sauketa duk abinda ke faruwa,har biyoshi da tayi da gudu duk ya gani ta madubi,dan ya kara firgitata ne yasa yayi kamar ya tafin😝

Tasleem na duke taji alamar tsayuwar mota kusa da ita.

Azabure ta dago dan taga waye.

Ya Auwal ne zaune yana mata murmushin mugunta.

Bata jira baasin komai ba ta bude motar ta shiga da gudunta.

Jafa motar kan titi yayi yana ci gaba da dariya.

Tasleem rasa yadda zatayi yadena mata dariya tayi.

Shiko be dena dariyar ba,dan har kifa kanshi kan sitiyari yake dan dariya.

Da taga ta rasa abunyi kawai seta rushe da kuka har da diddira kafafuwa.

Ayko kamar anzugashi dariyarshi yakeci bilhakki da gaskiya.

Seda ya gaji dan kanshi yadena dariyar,

kallonta yayi yaga yadda tayi zuru zuru,da gani akwai yunwa tattare da ita ga kukan da tayi .

Signal yasa ya koma gefen titi,yayi parking

10 / 14