KAREN BANA COMPLETE BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.txt

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 14

12K to 15K   out of 39.4K words

da cewa kai jaki ne,"

Tunda Auwal ya fara magana danmaliki ke gumi,jikinshi na rawa.


A fusace yaje ya shake Auwal yana mgn cikin cije baki.

"in kana mgn ka dunga tuna cewa ni yayanka ne,kuma ko ma menene sukamin ni agurina ci gaba ne tunda hakan ya zama sanadin haduwata da tasleem,inason tasleem son da bana yiwa kowa kamarsa,ciki har da ni kaina,sanin wacece ita ya karamin jin sonta araina,dan haka kasan dawa kake mgn,danmaliki nake"

Auwal kwacewa yayi daga rukon da hisham yamasa sannan yace.

"Allah ya tsinewa soyayya irin taka,inde irin hakane so to Allah ka tsinewa duk wani meyin so,kana son natane kamaida ita karuwar ka?"

Azabure tasleem ta dago tana duban Auwal wasu hawaye masu zafi nabin idonta,yauce rana ta farko datayi dana sanin haduwa da danmaliki.

Shiko Auwal ko ajikinshi yaci gaba da cewa.


"Duk namijin dake son mace domin Allah gidansu yake binta,bawai ya ajiyeta a hotel suna fasikanci ba,dan haka kadena cewa kai me sonta ne," Yana kaiwa nan ya wuce yabarshi tsaye agurin.

Yusura kama tasleem tayi suma suka tashi suka shige daki,dama ita umma tuni ta shige tana kukan takaicin halin da danmaliki ya jefa tasleem.

Danmaliki rasa yadda zeyi yayi,dan haka ficewa yayi agidan ya nufi gidanshi ranshi na kuna.

Auwal ko mota ya shiga,se alokacin yaji natsuwa aranshi,tunowa yayi da ammar,wani murmushi yayi,dan yasan zesha masifa.

Kiranshi yayi awaya,ayko kamar jira ammar ya dauka yace.

"Wlh kaide akwai bakin mugu me raba masoya,sabida tsabar wulakanci ka tafi da mota kabarni a titi inda masu satar mutane sunzosun sasheni baka da asara,wlh sena maka rashin mutunci,kuma kazo kadaukeni gidan aunty muje in ga masoyiyata"

Dariya Auwal yake tunda Ammar ya fara mgn,

Seda yabarshi ya gama sannan yace.

"da girmanka waye ze sace ka,?ay nace ma bazan sake zuwa wannan gidan ba sede ka fito waje inzo in daukeka"

Hakade Ammar yayta zazzaga masifa har Auwal din yaje ya sameshi,ya daukoshi bedena balai ba.

Har suka karaso gidan.

Lokacin ankira sallar ishai dan haka masallaci suka nufa,suka bi jam'i

Bayan sun idar ne suka shiga cikin gidan.

A tsakar gida suka sami umma da yusura da mubashshir,suna hira,

yayinda tasleem kecan daki sunan karuwa da Auwal ya kirata dashi ya hanata sukuni,ga jikinta dake zafi sabida dukan daya mata.


muje zuwa


surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA..........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*ZAHRA SURBAJO*



*Dedicated to Billy Shantally*



*20*



Guri suka samu suka zauna suka gaisa da umma,

Yusura da tun shigowar su Auwal tayi natsuwar dole,da kyar ta gaishesu,Ammar ne ya amsa banda Auwal.

"ke ina Tasleem tayi"inji auwal cikin zare ido.

Jikinta har bari yake tace.

"bari na kirata tana daki"bata jira amsar shi ba ta ruga da gudu zuwa dakin domin kiran tasleem.

Tana shiga dakin ta samu tasleem kwance,numfashi a kirji idonta ya kakkafe.

Da wani mahaukacin gudu yusura ta fito a gigice tana ihun kiran tasleem.

Auwal ya riga kowa isa gurin yusura yana tambayarta abinda ya sami tasleem din,cikin dakin kawai take nunawa.

Da gudu ya shiga dakin su Ammar da umma na binshi abaya.

Sosai ya firgita da ganin halin da take ciki.

Da sauri ya duka ya dagota ya dorata kan cinyarshi,da yake likitanci suka karanta shida ammar.

Tunkan yayi mgn Ammar ya debo ruwa ya mika masa,dankwalin kan yusura Ammar ya ciro ya mikawa auwal ya tsoma acikin ruwan yana matsewa yana sama tasleem akan goshinta.

Sannu a hankali,ta fara sauke numfashi,sede har zuwa lokacin bata dawo hayyacinta ba.

"da akwai pharmacy anan kusa?"ammar ya tambayi yusura.

"eh da akwai amman da dan nisa,"inji yusura.

"to muje ki kaini asiyo drip da allurar da zaa mata"cewar Anwar

Ficewa sukai shida yusura cikin sauri,yayinda umma kuma ta fita domin taje ta dauke mubashshir a tsakar gida,yana bacci ta kaishi daki.

Auwal kurawa tasleem ido yayi yaga yadda duk yabi jikinta ya fasashi da duka,abun gwanin ban tausayi,se alokacin ya fahimci irin dukan da ya mata yafi karfin jikinta.

Hannu yasa yana gyara mata gashin kanta daya rufe mata fuska, se alokacin ya lura da shatin dukan daya mata saman kirjinta ya taba har kan boobs nata gurin ya fashe sosai dole se anyi Ι—ressing din gurin.

Wata zazzafar iska ta fitar sanda ya tuno laifin da tayi ya mata hakan.

Ammar da yusura ko dan sauri yusura ko dankwali babu dan gaba daya ta gigice.

Haka suka shiga mota yaja su zuwa gurin da zasu sayi maganin.

Da yake va gurin parking kofar gurin,dan gaba yayi kadan sannan yayi parking.

Gurin akwai layi dan haka jira sukayi layin yazo kansu.

Suna nan tsaye,aka fara ruwa,sanyi na kadawa,yusura na rawar sanyi,dan ko itama dauriyace kawai takeyi amman ta daku


Ganin yadda take rawar sanyine yasa Ammar mika mata hannu,ba musu ta rike hannun,janta yayi ya rabata gefen kafadarshi,sannan yayiwa me maganin mgn akan suna da patient a gidane emmargency.

Basu duk abinda suke so yayi ammar ya biya kudin,ta juya rike da yusura zasu fita.

Ruwa akeyi kuma in yace ta shiga ruwan may be zazzabi ya rufeta.

Dan haka rigar jikinshi ya cire yabar singlet kawai ya rufawa yusura akanta.ya rike hannunta suka nufi gurin motar.

Hhhhh @xianoxy uban yan neman suna haka ya ratsa ruwan yana dukanshi ita kuma ya rufeta da rigarshi.

Suna zuwa gurin motar ya bude mata ta shiga sannan ya rufe ya zagaya shima ya shiga ya tada motar suka nufi gida.

Heater ya kunna acikin motar dan haka kan suje gida jikin yusura ba sanyi shine de dan ya jike ne ma.

Duk motsinta idonshi na kanta ahaka har suka kai gida.

Suna zuwa yusurace ta shiga da maganin.

Dan haka auwal amsa yayi yafara amfani dashi yadda ya dace.

A haka yasawa tasleem ruwa.

Sannan ya dura ruwan allura,seda ya waiga yaga ammar be shigo ba ne ya danyi kasa da dogon wandon dake jikinta yayi mata allurar duk bata san anyi ba.

Hhhh malam Auwal waigen na menene.

Seda yayi mata komai da yadace sannan suka musu seda safe suka wuce dakin kofar gida shida Ammar.

"mutumina naga wannan takun dazu an hau cinyarka kana masifa se gashi yanxu da kanka ka dora tasleem"cewar Ammar yana dariya.


"Kaji wawa nifa likitane,dan haka duk abinda yadace da mara lfy shi zan masa,wanda ko kaine kaima hakan zakayi tunda ka karanta ka sani"cewar Auwal cike da tsare gida.

Dariya Ammar yayi gamida mikewa yayi hanyar kofar fita yana fadin.

"kuma fa hakane bross ay aykin likitanci seda tausayin mara lfy kaga ka tunamin,bari inje inyiwa tasleem din allurar Chloroquine sabida zazzabin jikinta"yana kaiwa nan yasa kai ze fice.

Da wani mahaukacin gudu Auwal ya damko rigarshi ta baya,yace.


"uban wa zakayiwa allurar?"πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

"tasleem mana"cewar ammar yana murmushi.

"to dan ayi jikan na saba,amatsayinka nawa?"cewar auwal cikin hada gira.

Dariya ammar yayi yace.

"likita"

"to na mata an hutashsheka,uban azagwaigwai"😁

Ba musu ammar ya koma cikin dakin ya zauna yana tuntsira dariya.


Muje zuwa



Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA.........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAHRA SURBAJO*



*dedicated to Billy shantaly*



*21*




Suna shirin kwanciya kiran mummy ya shigo wayar Auwal.

Duk abinda ke faruwa ya sanar mata,sosai ta tausayawa auwal din dan tasan yana son yan uwansa.

Bayan sun gama wayane suka kwanta,Ammar na mitar sauron dake cizonsa.

Washe gari,tasleem ta farka da sauki jikin nata,yusurace ta taimaka mata tai wanka tai sallah,amman ta kasa cin abinci.

Umma ma tazo ta rarrasheta taci abinci amman taki,ga boobs dinta dake mata ciwo sabida dukan da aka mata akai.

Koya ta motsa ji take har kanta.yusura ta rasa yadda zatayi da tasleem,

Suna nan tsaye su Auwal suka shigo cikin gidan.

Tasleem ce ta fara ganinsu,tunkan su karaso ta zabura ta tsuguna tana fadin.

"ina kwana ya Auwal"πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Kadan ya rage yusura ta kwashe da dariya,ganin ya auwal dinne ya hanata yi.

Ko kulata beyi ba bare ya amsa,dukawa sukai suka gaida umma ta amsa cikin sakin fuska.

Yusura ma datayi gaisuwar be amsa ba,se ammar ne ya amsa yana murmushi.

Dubanshi yusura tayi har yanzu ba riga ajikinshi se singlet.

Abunka da fari duk ga tabon cizon sauro nan ya bayyana ajikinshi,sosai taji tausayinshi ya kamata.

Ficewa tayi ta nufi inda ta shanya rigar tashi,ta shiga dakin umma ta fesama rigar turare.

Bayan fitar yusura,ledar magungunan da ammar ya siyo jiya Auwalya dauko,ya ciro kayan dressing ciwo.

Dama tuni umma tabar dakin daga shi se tasleem dake tsugune kamar me neman gafara da ammar.

Yana gama fito da kayan,yakai dubansa gurin ammar yace.

"likita na bakin ayki seka bani guri ko"

Dariya ammar yayi yace.

"ay ko baka fadi ba zan baku"

Juyawa yayi ya fice daga dakin yana dariya.

Fitarshi tayi daidai da fitowar yusura daga dakin umma,sede be ganta ba ya nufi zaure.

Binshi tayi da sauri,tana zuwa kusa dashi kan ya juyo ta yafa mishi rigar akan kafadarshi ta yadda xira hannu kawai zeyi.

Da sauri ya juyo ita kuma ta juya zata bar gurin.

Hannunta daya riko ne yasa ta tsaya cak.

Janta yayi ta dawo kusa dashi.

Sunkuyar da kai tayi,hannu yasa ya dago habarta yace.

"ni da na cire ay sa miki nayi,ke me yasa kika ajiye a kafadana kuma kika juya ba tare da kinmin mgn ba?"

Duk ta gama daburcewa dan haka baki na rawa take fadin.

"Aa dama naga sauro sun cijeka ne shine yasa na kawo maka"

Murmushi yayi sannan yace.

"au har kallemin jiki kikeyi kenan?"

A tsorace ta dago ido tana kallonshi baki na rawa tace.

"aa ba kallonka nake ba"

"in baki kalleni ba taya kika ga sauro ya cijeni?"

Shuru tayi ba amsa,kunya duk ta gama kamata,dama tasani bata kawo mishi rigar ba.

"au ba zakiyi mgn ba?"

"don Allah tsautsayine kayi hkr bazan kuma ba"tayi mgnr kamar zatai kuka.

Murmushi yayi yace.

"na miki afuwa yanzu,amman ba na hakura bane,next time kika kuma nima kawai ramawa zanyi"

Da sauri ta kwace hannunta ta ruga cikin gida tana tafiya tana waigenshi.

Dariya yayi ya karasa ficewa daga zauren.

Acan kuryar daki kuwa,tasleem ji take kamar ta saki fitsari sabida tsoron yaya auwal.

Shiko ko ajikinshi hada magungunanshi yake tayi,seda ya gama,yasa safa a hannunshi sannan yakai dubansa gurinta.

Carab idanunsu suka hadu guri guda.agigice tasleem ta runtse ido.

Tabe baki yayi sannan yace.

"oya taso ki matso nan ki cire wannan rigar ta jikinki"πŸ˜‚ BalaiπŸ˜‚


πŸ˜‚ Idon tasleem kamar goruba haka ta watsa masa su tana kallonshi.

Sake maimaitawa,yayi agigice tace.

"ya Auwal iya rigar ce kawai fa ajikina"

"to se me cewa nai kicire ki matso nan"

Cikin in ina tace.

"ba ba ba ba bra aciki ya auwal"

"ay ban tambayeki ba,kuma dama ko akwai zaki cire,ciwon dake kan boobs dinki zanyiwa dressing"ya fadi cikin hada gira.

"What!!!dressing a kan boobs dina"tasleem tayi tambayar ba tare da tasan tayi ta ba.

"yess and so fucking what"Auwal ya bata amsa

"wlh ya Auwal,ni banaso kabarshi kawai"

"dallacan kwaila dake ma ubanme zan gani ko zanji danna gani,taimakonki zanyi,kina batamin lokacin,zaki matso koko sekinji ajikinki" πŸ˜‚πŸ˜‚ karya kake@xianoxy

Kan ya rufe bakin ma ta karaso kusa dashi,rigarta a hannu.jiki na bari.

Wayyo tasleem wannan kayan kunya har ina,

Sata yayi ta kwanta sannan ya shiga wankewa,ga azaba ga kunya abun biyu ya hadar mata.

Shiko kamar gaske ka rantse da Allah tayar mota yake wankewa,ba milk factory ba.πŸ˜‚a yadda ya nuna.

Haka ya gama yasa mata bandeji se kuka take mara sauti.

Yana gamawa yasa kai ya fice ba sannu bare Allah ya sauwake.

Muje zuwa


Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAHRA SURBAJO*



*mmn baby😍,mummy pheenat,daga surbajo novels,surbajo na gaisheku Allah ya barni tare daku cikin aminci,#Ana mugun tare*

*Salma b😏 sabida ansamin recharge card na 200 shine ake bina inyi godiya inyi godiya,to ga godiyar nan zanyiπŸ™„,salma b me kan goruba,salma b buhun kenkeso,salma b me hancin roba,ta jb me warin gawasaπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†πŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ˜ay dama nace miki zaki ga godiyataπŸ˜‚,amma fa duk da haka ina sonki salameme na😍*


*Dedicated to Billy shantalyπŸ€’*



*22*




Kai tsaye gurin ammar ya nufa ya daukeshi suka shiga gari domin neman boutique da zasu samu kayan sawa.

Basu dawoba se da rana tayi.

Wanka sukayi kowa ya sauya kaya.

Sannan suka shiga gida suka yiwa umma sallama akan zasu dawo wani satin.

Kudi dubu hamsin Auwal yaba umma sabida hidimar gida.


Umma se albarka take ta sa mishi.

Sosai Auwal yaja kunnen yusura gameda danmaliki.


Har sun kai zaure ammar ya dawo yacewa yusura.

"kanwata bani no dinki sabida gaisawa da umma in mun tafi"πŸ˜‚

Ba musu yusura ta bashi,ya fice yana daga mata hannu.


Mota suka shiga zuwa airport dan duk yadda Ammar yaso suje gidan Aunty Auwal yaki yarda sabida zaituna.

Suna isa airport ajiyar motar suka bayar gamida kiran auntyn ammar ya shaida mata ta turo direba ya dauki motar su sun tafi.

Aunty seda tayi fada akan tafiyar tasu ba sallama.


Da laasar suka isa gida,mummy ta rasa inda zatasa kanta dan jin dadin ganinsu.

Nanfa suka shiga hirar kd.

"Auwal tunda ka rabosu da gidansa,wannan gidan da ka maidasu zasu kuntata,dan haka akwai tsohon gidanmu sanda muna kd,zansa auntyn ku ta nemi maaikata,aje agyara gidan asa duk abinda yadace dan ba komai aciki kuma ya jima a rufe,inyaso sati me zuwan da zaku koma se ku maidasu cikinsa,ammar yasan gidan"

Sabida tsananin farinciki Auwal rungume mummy yayi yana godiya,harda hawayenshi.

"wannan godiya tayi yawa dan gidan mummy,kode baka daukeni uwa bane"cewar mummy tana shafa kanshi.

"mummy na daukeki uwa,dan yanzu aduniya kece kawai uwata mummy,kuma ko lahira inaso Allah ya hadaki da mahaifiyata amatsayin iyaye agareni,mummy kinmin komai"yayi maganar yana share hawaye.

Itama hawayen ta share tace "Amin dangidan mummy"


Ranar wuni sukai tare da mummy se dare sukai mata sallama suka nufi dakin baccinsu.

Kowa nada dakinshi amman shakuwarsu tasa basa raba gurin bacci.

Suna shiga daki Ammar ya fada kan kujera yazaro wayarshi yana fadin.

"Allah yasa batai bacci ba"

Kallon rashin fahimta Auwal ke masa,amman bece komai ba.

Ammar number yusura ya kira,wacce alokacin zaune take ita da tasleem suna hira.inda tasleem ke fadin.

"yusura ya Auwal yamin dukan da tunda nake aduniya ba wanda ya taba yimin irinshi,ki dubi yadda ya sauyamin halitta"tayi maganar hawaye nabin fuskarta.

Murmushi yusura tayi sannan tace.

"hakane Tasleem,amman in mukai duba da hukuncin nasa abinda yamana daidai nesabida se yanzu nake ganin hatsarin da muka so jefa rayuwarmu ciki,yanzu kinga da da tsautsayi zaki rasa virginity dinki,gaba mukaci ko baya,taba jikinki da hisham yakeyi ay ba daidai bane"

shuru tasleem tayi tana kallon yusura alamun batun ya shigeta,ajiyar zuciya tayi sannan tace.

"hakane yusura,amman ay kp turmi da tabarya ya kama mu irin wannan dukan yayi yawa,kidubi yadda ya ajiyemin tabo akan boobs,wanda inba saa ba har in mutu baze bace ba,wannan ay cutace,kinga yanxu wannan tabon ze janyo duk mijin da na aura ya tambayeni ya akayi naji shi,ni wlh ya cuceni"


Dariya yusura keyi harda hawaye ita ko tasleem hawayen takaici takeyi.

Suna hakane wayar Ammar ta shigo.


Ganin bakuwar number yasa yusura kin daga wayar ta tsinke ya sake kira.

A karo na biyune yusura ta daga dan taji waye,cikin sassanyar muryarta tace.

"hello"

Ajiyar zuciya Ammar ya saki jin muryarta,dan haka shuru yayi yana jinta tana sake fadin.

"Hello wai wake mgn,"

"yayanki ne"


Take ta gano muryarshi,dan haka a hankali ra furta

"ya Ammar"ba tare da tasan sautin ya fita ba.

"Ashe kinsan sunana?"ammar ya tambaya yana gyara kwanciyarshi.

Murmushi tayi me sauti,ba tare data bashi amsa ba.

"me kikeyi har yanxu da baki bacci ba?,ina fatan ba zance kika fita ba ko?"

Cike da shagwaba tace.

"kai ya Ammar wanne irin zance kuma,ay ni banma da lokacin samarin inbanda karya ba abinda suka iya,ka fita kasha sanyi abanza su cikama kunne da karyar banza"

Dariyar Ammar yakeyi harda kyakyatawa,jin tayi shurune yasa yace.

"to me ya hanaki bacci?"

"Tunani"ta bashi amsa.

"tunanin me ?"

"Yaya Auwal mana,wlh ya ammar inde yaya Auwal yace irin dukan daze dunga mana kenan wlh mu guduwa zamuyi"tayi mgnr tana kuka.

Sosai yaji tausayinta,kukanta na taba zuciyarshi,runtse ido yayi yana jinta.

Tasleem dake zaune tana jinsu da sauri ta kwace wayar a hannun yusura,tace.

"yaya Ammar pls,kaba ya Auwal shawara"

jin tasleem na mgn yasa Ammar sa wayar a handsfree,dan Auwal yaji.

"wacce shawara zan bashi tasleem?"

Da sauri Auwal ya dago kai jin Ammar ya ambaci tasleem.

"Ya ammar ka bashi shawara,yadena dukanmu haka,mu bafa yara bane mun girma,ni wlh ko alabari ban taba jin andaki yanmata kamar mu ba,,duk kyauna yanxu ya Auwal ya maidani kamar wata dodanniya,fuska akumbure,yayiwa kowacce gaba ta jikina illa,kuma wlh Zalincine,kuma kace mishi ni ba karuwa bace wlh,yaje can yanemi karuwai amman ba niba"tana maganar tana kuka.

Shiko Ammar dariya yakeso yayi amman ya danne.

Auwal ko kamar kurma haka ya koma.

"A gaskiya be kyauta ba,kice ya maidake mummuna kenan?"cewar Ammar yana murmushi.

Abunka da yarinta ay tasleem cewa tayi.

"mummuna ay da sauki,kamar dodanniya ya maida ni,inma kishi yake nafi budurwarshi kyau ay da bemin dukan mutuwaba,sabida yin Allah ne,nide kawai na barshi da Allah kuma wlh wuta bal bal"

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚


Dariya Ammar yake harda tuntsirawa,

Auwal duk yadda yakai da mazewa seda yayi murmushi,jin ance mishi wuta balbal.

Mikewa yayi yaje ya amshi,wayar hannun Ammar yace.

"Baki yafemin ba ko,kuma wuta bal bal,zan hadu dake ne"


wata kara tasleem ta saki gamida zabura ta yarda wayar fadi take.

"wayyo yusura mugun Ashe yana jinmu,na shiga uku,dama karyanine kawai beyiba,wlh in yadawo nasan dagargazani zeyi"

Yusura ma jin muryar ya Auwal seda hantar cikinta ta kada,dan haka da sauri ta kashe wayar gaba daya.

Ammar ne keta kokarin sake kiransu amman wayar akashe dan haka mikewa yayi ya isa gaban Auwal yace.

"kai wlh da sake,taya zaka maida yara sekace filin training,in zakayi zalincinka ka tsaya kan tasleem me jan kunnen nan,kadena hadawa da yusura ehe,haba sabida tsabar zalinci ji yarda yara suka rude daga jin muryarka,ina tsaka dajin dadin rayuwata ka katsemin dan haka kaje kawai nima irinta tasleem din,wlh wuta bal bal"🀣🀣🀣🀣


Wata dariya Auwal ya fashe da ita gamida kaima Ammar duka,yace.

"Ay wlh ko ita setasan tacemin hakan"

"can ta matsema nide kawai kai da Allah wlh"cewar Ammar sanda ya kwanta kan gado yana tsaki.

Auwal be sake mgn ba shima yabi bayanshi suka kwanta,

Tuni Ammar yay baccinshi.

Sede shi Auwal kiyamul laili,ce ta kamashi,koya ya runtse ido muryar tasleem yakeji tana fadin.

"wuta bal bal"

da zaran ya bude kuma zuciyarshi na hango mishi,hoton su sanda yake mata dressing ciwo.

Yadda yaga rana haka yaga dare yarasa me ke damunshi.

muje zuwa


surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA.........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€




*ZAHRA SURBAJO*



*Shamsiyya,miss mufash,Abdjam😘,dukan ku daga surbajo novels,surbajo na gaisheku Allah yabar zumunci,Ana mugun Tare😍*


*Dedicated to Billy shantally*


*23*



Ranar Auwal beyi bacci ba,yayinda itama tasleem anata bangaren ta kasa yin baccin sabida tsoron haduwa da ya Auwal.



Gari na wayewa,Auwal ya fice a gidan ya tafi gun shan iska ko sabon lamarin da yakeji atare dashi ze barshi.

Sede me ko da yaje gurin aduk sanda iska sassanya ta taba jikinshi,ji yake tasleem kawai yake bukata.

Rasa yadda zeyi yayi dole ya tarkata ya koma gida.

Cikin kwanaki Auwal har wata rama yayi,danshi sp yake yacire abun a ransa amman kullum kamar kara masa akeyi.


Tasleem ko ita tsoronta kawai ranar daze zo garin shine damuwarta.


Yau jummaa zaune suke,gaban mirror yusura da tasleem,tasleem na daurawa yusura dankwali,sabida Ammar ya sata dole ta tura masa

5 / 14