Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
iska.
Fitarsu kenan,sega mutumin da yusura taiwa alkawarin zuwa gurinshi.
Ya nufota yana murmushi.itama murmushin tai masa.
Yana karasowa yace.
"ya me jikin?"
"da sauki"yusura ta amsa.
Sannan yace.
"to ya batun alkawarinmu?"
Dariya yusura tayi sannan ta kara matsawa kusa dashi tace.
"malam jiya wanne yare ma nace maka zamuyi?"
Murmushi yayi yace.
"nigerianci"
"Good,to kaje ba inda zani"
cewar yusura tana dariya.
"amman fa alkawari kikamin yazaki karya?"
cewar mutumin cikin damuwa.
"yaren nigeria nace zamuyi,wanda kasani nasani,tun zamanin sardauna aka dena cika alkawari,dan haka ba inda zani kai gaba ko in tara maka mutane,"
ππto @xianoxy haka ya juya jiki ba kwari,yana waigenta,yaga samu yaga rashi,dan da har abokinsa @nazeefi_bm yace ze gayyato,ππππππto se gashi ta bare.
Bayan tafiyar shi dariya suka kwashe da ita yusura da tasleem.
Suna nan zaune wayar yusura ta fara kara,koda ta duba me kiran.
Atm ne.
Dagawa tayi cikin muryar kuka tace.
"baby i miss you,"
Cikin sigar rarrashi yace.
"i know baby,kiyi hkr,ya jikin maman yake?"
"da sauki ta bashi amsa"
Hakade yay ta kwantar mata da hankali har tai shuru.
Sallama yay mata akan ze kira anjima.
Tana kashe wayar,ta ciro wata wayar a jakarta ta sake kiranshi.
Seda ta bashi ten missed calls sannan ya dauka cikin fada yace.
"yusura wallahi in kika kuma yimin kira irin haka se naci ubanki,bashin ubanme kike bina da zaki ajiyemin missed calls har guda goma"
Cikin rawar murya tace.
"yaya kayi hakuri,dama jikin aunty maryam ne yay tsanani, ba kudin zuwa asibiti shiyasa na kiraka"
"au yanzu dama sabida maryam din kike kirana haka,to kinyi na farko kinyi na karshe,shasha kawai,ni na dora mata ciwon?"
Kasa daurewa yusura tayi kawai seta rushe mishi da kuka,cikin kukan take fadin.
"yaya kaji tausayinmu,bamu da kowa sefa kai,wakakeso muje gurinsa ya bamu"
"kibi titi zaki samu"
ya bata amsa gamida kashe wayar shi.
Rushewa yusura tayi da kuka ta fada kan tasleem wacce tun dazu take kukan,rungume juna sukai suna kuka,me isar su.
Kiran da nurse tai musune yasa suka mike da sauri zuwa cikin dakin,
Aunty maryam ce ke aman jini har ta hanci,gunta suka nufa,a gigice,sede likitoci sun hanasu zuwa kusa da ita,sabida suna kokarin ceto rayuwarta.
Duk da halin da take ciki haka ta dunga miko musu hannu,sede ba halin su isa gareta,sabida naurorin da suka zagaye jikinta.
Kuka suke daga inda suke sun rungume juna,suma suna mika mata,hannu,
Wayyo gidan duniya ba matabbata ba,yadda Allah yaso yakeyi asanda yaso koda kuwa ba wanda yaso.
Akan idonsu Aunty maryam ta amsa kiran Allah.
Yanke jiki yusura tayi ta fadi sumammiya,
Da gudu tasleem tai kanta tana kiran sunanta tana kuka,dole likitocin suka bata taimakon gaggawa.
Koda ta farko kuka ta rushe dashi,tana fadin.
"Aunty kin wahala damu dashi gaba daya,se gashi shi yagaza tallafawa rayuwarki,shi wanne irin shaidanine,da baya iya tausayin na kusa dashi,me muka masa me zafi irin haka da yajanyo sanadin mutuwarki aunty"
kukane yaci karfinta kawai ta fada kan gawar aunty maryam din tana kuka me tsuma zuciya.
Tasleem ko ta gaza kukan se na zuci,shuru kawai tayi tana kallon gawar yar uwarta abar kaunarta,wacce bata da kowa gidan duniya sama da ita,
"aunty Allah yamiki rahama yasa iya karshen wahalarki kenan,,sede aunty baki mutu banza ba wlh,inde ina da rai zan dauki fansar abinda aka miki aunty "cewar tasleem da take maganganu kamar ta zare.
Hakade suka gama koke kokensu suka biya kudin motar daukar gawa akasa gawar aunty ciki zuwa kaduna,
Kamin su isa duk sun kira yan uwa sun shaida musu dan haka suna zuwa wanka aka mata aka mata sallah,sannan aka kaita gidanta na gaskiya.
Kowa na kukan rabuwa da ita sabida mutunci da kirkinta.
*ASALIN LABARI.*
muje zuwa.
Surbajo for life.
[20/06, 10:51] Hajiyan India 3: ππππππππ
*KARAN BANA.........*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*kuyi hkr tun jiya nai posting instagram wallah na mantane ban kawo muku ba*
*Instagram @zahra_surbajo1*
*Dedicated to Billyn shantali*
*7*
Malam Bukar dattijo ne dan kimanin shekara 50 a duniya.
Haifaffen garin barno ne,amman fatauci ya kawoshi garin kaduna.
Malam Bukar na zaune da iyalinshi awata anguwa me suna hayin rigasa can layin taro taro dake kaduna.
Matarshi daya me suna hindatu,suna da yara hudu,uku maza daya mace.
Hisham,shine babba,se Auwal,se yusura,se karaminsu mubashshir.
Rayuwar gidan rayuwace ta masu karamin karfi,dan haka komai cikin maneji suke yinsa.
Da kyar malam Bukar yasa yaran a makaranta suna zuwa.
Ba laifi Auwal yafi hisham kokari nesa ba kusa ba,tun hisham na gaba dashi har yazo ya kamoshi.yazama ajinsu daya.
Kokadan hakan beyiwa hisham dadiba,dan yafiso komai ya kasance shine a sama.
Sannu a hankali har Allah yakaisu matakin yin ssce inda cikin hukuncin Allah Auwal yaci hisham ya fadi.
Hisham ji yayi kamar ya kashe auwal ya huta sede ba hali,haka ya dunga yaken tayashi murna,yayinda shi kuma se wata shekarar ze sake rubutawa.
Yau litinin yau sakamakon Auwal yafito inda yaje ya amso cike da murna ya kawo gida.
Iyayensu sunyi matukar farinciki da samun nasarar auwal ,haka yusura ma ta taya yayan nata farinciki ba kadan ba.
Cikin dare hisham wanda ya gaza yin bacci sabida bakin ciki ya tashi,ya saci jiki yaje ya kwashe duk wata takarda data shafi karatun Auwal ya kona,ya kwashe tokar yasa a bola.
Babu wanda yasan yayi hakan har tsawon wata guda,sanda Auwal yasamu kudin zana jamb,anan ne ya waiwayi takaddu amman babu.
Tashin hankali baa sa maka rana.
Wasa wasa neman takaddu ake amman basu ba dalilinsu,sabida makirci irin na hisham dashi ake yawon neman takardun,amman baa gani ba.
Kuka Auwal yayi shi babu adadi,bawan Allah har ciwo seda yayi,haka mahaifinsu ko kadan abun be masa dadi ba.
Koda yaje makarantar yamusu rahoto yawo sukai ta masa da hankali,wanda dole tasa Auwal ya hakura,shima yashiga jerin masu rubuta wata jarabawar shekarar me zuwa.
Dadin da hishaM yaji baze faduba domin burinshi yacika,dan baze taba yarda Auwal yafishi ba.
Haka sukai ta gwagwarmaya har zuwa sanda zaa kara wata jarabawar.
Inda cikin ikom Allah nambobinsu na jarabawa yazo atare,auwal na 131 hisham na 132.
Tunda aka fara jarabawar Auwal ke rubutawa hisham,
Yau suna da jarabawa ta karshe wato english,
Kowanne daliΙi ya maida hankalinsa kan karatu.
Koda aka fara jarabawar hisham in banda tauna biro ba abinda yake yi,
Ganin hakane yasa Auwal amsar,takardar hisham ya fara rubuta masa.
Ashe wani supervisor ya gansu,dan haka kai tsaye yayo gurinsu,
Hisham na hangoshi yayi wuf ya kwace takardar Auwal,ya rike yayinda Auwal besan meke faruwa ba ya dukufa gurin ganin ya rubutawa hisham tashi.
Mutumin na karasowa hisham yace. "sir don Allah acanjamin gurin zama dashi,wlh tun dazu yake copy a nawa"
Da sauri auwal ya dago kansa dan ganin meke faruwa.
A gigice yake kallon hisham,dan jin abinda yake fadi.
Shiko hisham ko ajikinshi haka yay ta zabga karya.
Wayyo Auwal dan tsananin mamakin yayan nasa ya kasa mgn.
Ganin hakane yasa mutumin tambayar numbar Auwal din.
Ay tun kan yay mgm hisham ya riga fadi.
Yana fadi,mutumin yacewa auwal ya fice a exam hall din.
Haka auwal ya juya ze fita,fuskarshi na zubar da hawaye,har ya fara tafiya se ya dawo gurin hisham.
Ya mika masa takardarsa da yake rubuta masa yace. "yaya gashi saura kadan na gama yimaka,ka kalli wannan tawan ta hannunka ka karasa sauran"
Yana kaiwa nan ya juya ya fice.
Ko ajikin hisham haka ya gama rubuta abinsa yaje ya bada.
Ba komai ya hana Auwal fadin gaskiya ba,sedan yasan ko ya fadi dukansu masu laifine,dan haka da duk su rasa gwanda shi ya rasa.
Haka hisham ya fito yazo yasami auwal dake kuka,da yake munafukine shima se yasa kuka ya rungume Auwal din yana bashi hakuri.
Allah sarki bawan Allah,rarrashin hisham din yakeyi gamida shaida mishi babu komai,next year ze sake yin wata,dan yasan english de kam ya fadi.
Muje zuwa
Surbajo for life.
ππππππππ
*KARAN BANA........*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*dedicated to billyn shantaly*
*kullum page daya zan dunga yi,sena samu dama inyi sama da haka,ina fatan zakumin uzuri*π
*instagram @zahra_surbajo1*
*8*
Suna tsaka da rayuwa cikin rufin asirin Allah,kwatsam mutuwa ta kawo bara gidan,inda ta dauki jigo kuma babban bangon gidan wato malam bukar.
Kafatanin iyalinshi da mutan anguwa babu wanda beji mutuwarsa ba domin mutumin kirkine,
Haka rayuwar ta Ζara tsananta garesu,komai auwal keyi shi hisham dan aci banzane,mahaifitarsu sosai take masa fada kan halinshi amman ko ajikinshi,
Rayuwa ja take,auwal tuni ya hakura da karatu,ya rungumi aykin hannu domin kulawa da danginsa.
Gaba daya yayi wani tsufan dole sabida wahala kai kace shine ya haifi hisham.
Ana haka jarabawar fita tasu hisham ta taso,ko ajikinshi,haka auwal yaje yay jarabawar,yadawo gida.
Cikin ikon Allah jarabawa tayi kyau,har anfara hada hadar tafiya nysce,sede babu kudi.
Duk wani fadi tashi anyi amma anrasa madafa,ganin yadda auwal ke wahala ne yasa maryam kwashe kayan dakinta duka ta siyar batare da sanin auwal dinba.
Sannan takawowa auwal din kudin tace "kaba yaya yayi hidimar karatunshi,nasan nan gaba in yazama wani abu baze barmu haka ba"
Auwal rungumeta yayi yana kuka,dan shi kadai yasan son da yakewa yayan nasa,bashida buri da yawuce yaga yayanshi yasamu ayki shima ya maidashi makaranta,
Haka yadau kudin yaba hisham,ba kunya ya amshe,gamida cewa. "thanks"π Haka yay hidimarsa cikin wadata,ya daga birnin ibadan inda aka turashi.
Tunda yatafi ko so daya be taba zuwa gida ba,sede in beda kudi yakira auwal yasa ya nema ya tura masa.
A haka har yagama bautar kasarshi yadawo,gida,
Bayan dawowarshi ne ciwon sugar ya tasowa mamansu,inda tai ta fama daga karshe itama tace ga garinku nan,bayan ta damka amanar yayanta a hannun hisham.
Tun bayan rasuwar mahaifiyarsu kulawa dasu yusura ya koma hannun aunty maryam,itace komai nasu.
Hisham ko na kwance kullum daki ko kuma zaune rike da newspaper shi adole dan boko.
Auwal neman kudi yake da dukkan karfinsa,inda Allah yataimakeshi yasamu ayki agurin wasu magina,inda yake tayasi in an tashi su biyashi.
Cikin ikon Allah hisham yasamu aykii da kamfanin man petur na kasa wato nnpc,amatsayin karamin maaikaci me daukar albashin dubu talatin.
Wayyo dadi dan tsananin murnar samun aykinshi,auwal da yusura da maryam har azumi sukai najin dadi.
Yau Auwal sunada ayki agurin ginin su dan haka da wuri yabar gida yatafi.
Yayinda hisham kuma ke cike da murna dan yau ze fara daukar albashi.
Isar auwal gurin ayki keda wuya yafara kamar yadda ya saba.
Aka zuba masa kwababben simint,ya dauka a kwanon gini,ya tafi zuwa saman gidan da suke ginawa domin yakai.
Cikin rashin sani,yataka katako me kusa,azabar dayaji yasa yamance inda yake,yafara tsalle,ay beyi aune ba seji yayi ya rikito daga saman benen.
Agigice jamaa sukayo kansa,sede tunkan suzo ma ya suma,haka suka debeshi zuwa asibitin 44 dake kaduna.
Likitocin sunmasa allurar daya farko,sede yasamu karaya har uku akafarshi.
Inda kudin dori aka bukaci kudi naira dubu talatin domin adorashiπ
Wainda suka kaishi gidansu suka nufa,inda sukai saa hisham yadawo daga gurin ayki,aljihunsa shake da dubu talatin na albashinsa.
Koda sukai masa bayanin abinda ya faru da auwal,sosai ya gigice yabisu zuwa asibitin inda maryam da yusura ma baa barsu baya ba.
Sanda yaje aka miko masa,takardar biyan kudin aykin wata zuface tashiga ratso mishi goshi,
Ajiye takardar yayi kan table yace yana zuwa.
Yana fita be zame ko inaba se inda ake saida mashin rober rober,yayi cinikin wani na hannu me kyau akan kudi dubu talatin yabiya aka bashi,farinciki fal ranshi,domin shi dama burinshi kenan albashinshi na farko mashin xe siya.
Yana hawa mashin be zame ko inaba se asibitin,inda yana shiga yaje kan gadon da auwal yake yacd masa. "auwal akwai dubu talatin dazu ajikina,se nayi tunanin inna biya aka maka dorin asibiti zakuma adunga zirga zirgar kawoka asibiti,shima kudin motar kudine masu zaman kansu,hakanne yasa naje nasiyo mashin da kudin,yanzu zan daukeka muje amaka dorin gida yama fi kyau"
Murmushi kawai auwal yayi na karfin hali,yayinda maryam da yusura suka rushe da kuka.
Shiko ko ajikinshi haka yaje ya amshi sallama,yazo ya dauki auwal yakai kan mashin din tare da taimakon maryam inda suka sashi a tsakiya,ya burga mashin din suka fice daga asibitin.
Se gidan ta sidi me gyaran karayaπ
Muje zuwa
Surbajo for life.
ππππππππ
*KARAN BANA........*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*intagram@zahra_surbajo1*
*Dedicated to Billy Shantaly*
*9*
Koda sukaje gidan tasidin,da kyar ta iya gyara karayar,ko kudin sadaka maryam ce ta biya,sannan suka dauki,auwal zuwa gida.
Tun daga lokacin kullum auwal na gida,gashi basu da kayan abinci,abun yafara damun maryam,dan haka hisham taje ta sama da batun.
"yaya kasan auwal beda lfy,gashi yanzu kayan abincunmu wlh sun kare na rasa ya zanyi"
Wani kallon uku saura kwata ya watsa mata sannan yace.
"wai ku me kukeson maidani?shikenan kunbi kun sawa salary na ido,da da ban dashi wa kuke tambaya?"
"Auwal ne,to yanzu beda lfy,kaga tunda kai kana dashi seka bamu muyi amfani dashi"
"to wlh baze yiwu ba,bazan kashe kaina in raya ku bs,ehe,"
"amman shi ay kashe kansa yayi damu baki daya domin gobenka tayi kyau,shi me yasa bazaka taimakeshi ba?"cewar maryam wacce zuwa lokacin ta fara fusata.
Ran hisham in yayi dubu ya baci amman ya gaza mgn,hannu kawai yasa a aljihu ya dauko dubu biyu ya cilla mata,gami da cewa.
"gashinan na iya tsawon wannan watan,dan wlh ko kun cinye ba bada wani zanyi ba"yana kaiwa nan ya haye mashin dinshi ya wuce.
Dan bakin ciki maryam rushewa tayi da kuka,seda tayi me isarta sannan tayi shuru.
Ganin zama haka baze yiwu bane yasa maryam fara wankau da kitso,domin rufawa kansu asiri.
Shiko hisham ko ajikinshi,se yafi sati be leka gaida auwal ba.
Kafar auwal yanzu ta kumbura tayi suntum,babu wata alamar sauki,gashi se zabure zabure yake kamar wani hauka sabon kamu.
Maryam da yusura sede susashi agaba suna kuka gamida masa addua.
Ana haka kafar ta fara wari.zuwa lokacin auwal ko mgn baya iyayi,hakane yasa maryam yin duk me yiwuwa wajen daukarshi zuwa asibiti.
Gwajin farko,aka gano akwai tetenus ajikin auwal,sakamakon taka kusa da yayi,wanda ya gama bin jikinsa.uwa uba kuma kafarshi ta rube,sede a yanke.
Wayyo rayuwa,maryam da yusura ranar kamar zasuyi hauka kuka suke kamar ransu ze fice.
Hisham sukaje suka fadawa,sannan suka mika bukatarsu tason asaida gidan su ayiwa auwal magani.
"amman kude akwai mahaukata,uban wa ze samar mana inda zamu dunga kwana in mun siyar,wallahi vaze yiwuba,muna da tabbacin in mun siyar auwal ze samu saukin ne,wlh bazaa siyar ba,kuje ku kaishi bakin masallacin sultan bello ranar jummaa"
Tunda ya fadi haka be sake mgn ba,ya bar gurin.
Daukarshi,sukayi suka maidashi gida,
Maryam kuka yusura kuka
,yawo sukai tayi a gari neman taimako,basu dawo ba,se magrib,suna shiga,dakin da auwal yake,babu shi babu alamarsa,sede shimfidar shi.
Wasa wasa suna nemanshi,har goman dare ba labarinsa.
Wayyo duniya,wasa wasa auwal tsawon wata guda kenan suna nemanshi babu shi,
Daga maryam har yusura babu me cikakkiyar natsuwa acikinsu,gaba daya sun firgice.
Hisham ko ko ajikinshi,shi murna ma yayi,da faruwar hakan.
Tun suna sa ran ganinshi har suka hakura suka fawwalawa Allah.
Tun daga wannan lokaci maryam yau lfy gobe babu lfy,ahaka de suke lallabawa ita da yusura da mubashshir.
Hisham duniya sabuwa,sabida kyan takardunshi kullum cikin samun nasara yake agurin ayki,kudi shigowa suke kamar ruwa.
Tuni yayi aure da amaryarsa fatima,sun tare awani makeken gida daya gina musu.
Tunda yayi aure,su yusura se su shafe wata shida basu ganshi ba.
Matar tashi itama mara mutunci ko takan danginsa bata bi.
*Maza akula,mace bata isa ta wulakanta danginka ba matukar kai ka nuna suna da daraja agurinka,a yadda ka daukesu haka itama zata dauka.*
Sannu a hankali likafar hisham ke dagawa,wanda zuwa yanzu shi kanshi baze iya fadin yawan dukiyarshi ba.
Tuni sarakuna sukai ta bashi sarautu,wanda yanzu yana rike da sarauta,har hudu,amman ciki yafison Danmaliki.
Rashin imanin shi kan yan uwanshi se karuwa yakeyi,ko kadan be tausayinsu,komai daga matarshi se yayanshi.se kuma karuwan kan titi.
Jikin maryam yayi tsanani,kasancewar babanta ya rasu,mamanta ke kulawa da ita da yusura,
To maman ta manyanta,hakanne yasa,kanwar maryam Tasleem zuwa gidan domin su kula da yayar tata.
Ganin sun rasa mafaka ne yasa yusura,gwada sauya dp na whatsapp dinta,da wayarta y2 tasa hoton tasleem,tayiwa hisham mgn
Dayake besan no dinta ba,kuma gashi bunsuru,duk wani abu da yashafi siket da wrafer baya iya dauke ido.
Wannan tarko da yusura ta dana shine ya kama hisham,ze kirata a waya susha hirar soyayya batare da sanin sa kanwarsa yake mgn ba.
Yayinda beda buri kullum sena son yaganta
,ita kuma taimishi karyar ita yar yola ce kuma iyayenta hamshakan masu kudi ne.
Wannan shine asalin labarin,
yanzu zamu dora
Muje zuwa
surbajo for life
ππππππππ
*KARAN BANA.........*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*instagram@zahra_surbajo1*
*mrs nuruddeen Allah ya raya baby yasa cikon addini ne,Allah ya baki lafiyar shayar dashi,Ameen*
*Dedicated to Billy shantaly*
*10*
*Ci gaban labari.*
Koda danmaliki yasamu labarin rasuwar maryam,be wani ji komao ba,hasalima besamu damar zuwa gaisuwa ba se bayan sadakar bakwai.
Yusura da tasleem sosai abun ya bata musu rai,amman in yasan wata ay besan wata.
Bayan rasuwar maryam da wata biyu,yusura ne da tasleem kwance kan sabon gadon da suks siya,
Tasleem na chartting,yusura kuma waya take,da atm.
Kashe murya tayi,can kasa tace, "baby,ina kewarka sosai"
Wani dadi ne ya tsirga masa kai,cike da kulawa yace. "nafiki baby,kullum dare dake nake kwana nake tashi,dumin jikinki,yaki barin jikina baby"
Wata ajiyar zuciya tayi,ta daukar hankali,sannan tace. "baby inason jina jikinka wlh,ga faffadan kirji,ga kamshi me dadi tattare dake baby,wlh i miss my palace"
Kanshi ne yayi gingirim shi ala dole ya gama haduwa. "to baby tunda mama tasamu sauki,zaki zone koni nazo?" "baby kazo de kai da kanka,dama inaso kazo gidanmu gaskiya" "to shikenan baby,insha Allahu gobe zanzo"
Wata yar karar murna tayi,sannan tace. "can't wait to see you baby"
Hakade sukai ta hirar soyayya batare da yasan da kanwarshi yusura yakeyiba.
Bayan ta kashe wayar,idonta ne yasauka kan na taslim data kureta da ido alamar tuhuma.
Kasa daurewa taslim tayi tace. "you are not serious yusura,how can you invited him to go yola?we are here not there." Dariya yusura tayi sannan tace. "tasleem kenan,wallahi am serious,zeje yola yaga gari gari yaganshi,sannan ya dawo gida kd,bama iya yola ba,wlh har uk sena kaishi da china"
Dariya tasleem tayi,gamida cewa "baki da kyau,yusura ko kinyi wanka"
Dariya itama yusura tayi tace. "shiyasa tunda bunsurunnan ta fado komata nadena wankan ay"
Dariya duka suka tuntsure da ita gami da tafawa.
Washe gari ko da misalin 12:00pm danmaliki ya shirya se airport,be bata lokaci ba,yasai ticket,se yola domin ganawa da masoyiyarsa,ππππ Awa guda tsakani ya isa yola,bayan ya isa ne ya kira wayar yusura,ba bata lokaci ta dauka. "baby gani garinku fa,ina zan nufa?"yace cikin kwanciyar hankali.
Dariya yusura tayi gamida cewa. "wayyo baby na ya iso,ina zansa kaina dan dadi,baby kasamu taxi,kataho titin Ahmadu bello,dede gidan man aa rano...."kit ta kashe wayar.
Ba tare da damuwar komai ba,yahau taxi zuwa inda tace masa,(ko ma akwai gurin ohoπ) Basu jimaba suka isa,wayarta ya kira sede switch off ,yayi iya yinsa yasamu wayar abun yaci tura,dan haka sa me taxi din yayi yakaishi wani hotel mekyau,ya kama daki yayi wanka yaci abinci,yaci gaba da kiran no din tasleem kamar yadda yayi zato akashe.
Suko tasleem da yusura suna gida in banda dariya ba abinda sukeyi,kuma suna sane suka kashe wayar domin su wahal dashi.
Danmaliki haka fa ya kwana a hotel cike da zullumin me yasami babynsa danshi ko kadan be dauka ta kashe wayar bane,dauka yake