Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
kaiwa nan ya mike ya fice ya nufi dakin umman tasleem din,yana shiga yasameta zaune tana kallo.
Zuwa yayi ya kwantar da kansa kan cinyarta ya fashe da kukaπππππ
A gigice umma ke tambarshi me yasameshi,amman Auwal fafur yaki mgn kuka kawai yakeyi harda hawaΖ΄ensaπ
Ashe maza sun iya kirsaπππ
Da kyar tasamu ya fara mgn cikin kuka.
"umma kinmin alkawarin duk abinda nakeso inkina dashi ko kina da iko dashi zaki bani?"
Da sauri umma tace tana share hawaye.
"Auwalu na maka alkawari ko menene ka bukata zan baka"
"Umma tasleem nakeso ki bani na aura"
Murmushi umma tayi,dan dama ranar kawai daze furta take jira,dan ta juma da sanin Auwal nason tasleem.
"Yanzu akan tasleem din kake kuka?"
Kai ya gyada mata gamida cewa.
"Eh umma in kuma kika hanani nan gaba rami zaki haka ki sani"
Dariya tayi sannan tace.
"Auwal ko ba kai ba,dama ay kaine madaurin auranta,kai keda ikon ba wanda kakeso,dan haka kaba wanda yadace"
Dariya yayi yace.
"Nafi kowa dacewa da ita umma,dan haka naba kaina,umma kin amince?"
"Na amince Auwalu ko gobe ne ka fito ayi auranku"
Wata kara yasaki gamida rungume umman yana mata godiya.
Mikewa yayi ya fice,cike da nishadi,yayin da umma tabi bayanshi da kallo tana dariya.
Yana fita dakinshi ya koma yayi wanka ya shirya,ya fice yawon zaga gari,zuciyarshi fess,dan ya lashi takobin ze auri yasmin ko bata sonshi.π¨
Muje zuwa.
Surbajo for life.
ππππππππ
*KARAN BANA...........*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*Kuyi hkr na rashin jina kwana biyu,mijina ne beda lfy,amman yanzu yaji sauki,ngd da kulawarku gareni*
*baka iya turanciba an zageka,ka iya dinma shima an zageka,πππchaiii,dere ris God oooooo,*
*Dedicated to billy shantally*
*28*
Tasleem haskali kwance ta gama shirya abincinta me rai da motsi,taje ta shiyasu a inda ta tanada domin sauke dan maliki.
Wanka tashiga tayi ta fito ta tsantsara kwalliya.
tana cikin daurin dankwali ne yusura ta shigo dakin,cikin murmushi yusura tace.
"to ayawata se ina kuma zaki?"
Cikin dariya tasleem tace.
"Kinjiki da wani zance,danmaliki ne fa zezo,shine nake shiryawa"
Annurin fuskar yusura ne ya kauce,cikin fushi tace.
"to dan zezo se me,wai ke wacce irin yarinyace mara jin mgn,uban me zakiyi dashi da har kike rawar kafar zezo?"
"Dalla dakata malama,duk abinda kikeyi ni sa miki ido nakeyi,danmaliki saurayina yayanki ne zezo,shin kina da damuwa ne game da hakan?"cewar tasleem cikim daure fuska.
"saurayinki de amman ni ba yayana bane,wlh tasleem baki da zuciya,ki rasa wanda zaki so,wai se wanda yaki taimakon yayarki har ta mutu shine kike so,turrrr dake wlh"yusura ta bata amsa tana zubar da kwalla.
"can ta matse miki"tasleem ta bata amsa gamida ci gaba da kwalliyarta.
Yusura ficewa tayi adakin tana kuka,dan idan har tabar tasleem ta auri hisham burinta akanshi be cika ba kenan,dole zata kawo karshen hisham da dukkan karfinta.
Yusura Hijab dinta tasaka ta fice agidan cikin sauri,kamar an biyota,ko ina zata oho.
Hisham be iso gidan ba seda azahar.
Tasleem murna kamar zata tashi sama,tundaga bakin get ta ruko shi,tana masa sannu da zuwa.
A haka suka karasa sit room din data tanadar mishi,
Suna shiga,kan cinyarshi ya dorata yana kare mata kallo,itako se murmushi take dake nuna taji dadin ganinshi.
"Baby na kinyi kyau sosai"cewar hisham yana murmushi.
Itama murmushin tayi gamida juya ido,tace.
"ngd baby"
Tana kan cinyarshi suke ci gaba da hirar su ta masoya,duka suna cikin shaukin juna.
Auwal ne ya dawo gidan daidai lokacin,ranshi fess,sede tunda yayi arba da mota me dauke da sunan dan maliki annurin fuskarshi ya bace.
Jikinshi har bari yake ya nufi sitroom din,
Wo hoho ran yan maza ya baci,sanda yay arba da tasleem zaune kan cinyar dan maliki.
A fusace ya nufesu,beyi wata wata ba ya dauketa da wani mahaukacin mari,wanda seda ta kife kasa.
Kwalar dan maliki ya shako,ya mikar dashi tsaye ya ce cikin taune hakora.
"nan ba gidan bariki bane,gidana ne,kuma kanwata ce,wallahi daga yau ka sake kula tasleem sena gigita rayuwarka,ka rubuta ka ajiye"
A zabure tasleem ta dago tana duban ya Auwal jin furucin nasa.
Yana kaiwa nan ya anza dan maliki kofar dakin,wanda kadan ya rage ya fadi Allah ya tsare.
Dan maliki be kulashi ba,dan yana ganin kulawar bata da amfani,ze turo masa wainda zasu kara masa gudu zuwa lahira.
Dan haka ficewa yayi daga gidan yana huci.
Auwal ko kan tasleem ya koma,ya cire belt dinshi ya shiga nada mata na jaki,
Tun tana ihu har tazo ta kasa,ihun,umma ce tajiyo katar ta ta shigo dakin tana tambayar me ya faru.
Ba musu ya kwashe yadda yaganta da danmaliki ya fadiwa umma,ay kan yay aune,umman ta rufe tasleem da naushiπkai kace roman rainge.
Tuni bakin tasleem ya fashe,yana jini,dakyar Auwal ya hana dukanta da hannun da takeyi.
Nan suka barta ko motsi bata yi se ido da take wurgawaπ
Dan maliki nakan hanyarshi ta zuwa gida,wayarshi ta shiga kara.da kamar kar yadauka,amman ganin me kiran yasa yayi parking ya daga wayar,tun kan yay mgn akace daga daya bangaren.
"duk wasu takardunka na kammala karatu kazo mana dasu yanzu"
Hantar cikinshi ce ta kada,baki na rawa yace.
"ok sir"
Jiki ba kwari ya isa gida,ya kwashi takardun,yaje yakai.
Depending results din shi duka abukaci yayi,wayyo abun kunya.
Haka yashiga wara ido ya rasa abun yi,kunya tabi ta kamashi.
Duk wani rusult dinshi yakasa bayyana nashine,dan duk amsoshi ya kasa amsasu.
Id card dinshi suka bukaci ya basu,sannan suka shaida mai sun dakatar dashi har zuwa su gama bincike.
Wayyo Allah dan maliki,rasa inda zesa kansa yayi,take yanke ya rasa natsuwarsa,da kar ya mike ya fice daga office din,
Auwal da umma falo suka koma,inda Auwal yace.
"umma Ya kike ganin zaayi da tasleem? nifa ina tsoron gaba wlh"
"na baka umarni ka gayyato duk wanda zaka gayyato rana ita yau jummaa,zaa daura muku aure"
Tsintar kanshi yayi dajin beson auran tasleem din,hasalima wata tsanarta yakeji azuciyarshi,amman bashida zabin da wuce yasa umma farinciki.
"to shikenan umma,zan turo azo ayi agama"
albarka sosai umma tasa mishi wacce taimasa dadi ba kadan ba.
Yusura ce ta dawΖ gida ranta fess sekace ba itace ke kuka dazu ba.
Bata nemi tasleem ba,taci gaba da harkokinta.
Har dare tasleem na kwance a sit room takasa tashi sabida tsamin da jikinta yayi mata.
Auwal ne yashiga sitroom din dan yaga ko ta fice,kwance take har lokacin dan haka tsaki yayi yafice ba tare daya kulata ba.
Tasleem bata iya fitowaba se washegari.
Daga umma har yusura ba wanda ya nuna yaganta bare aymata sannu,tana dingishi ta shige dakinsu,toilet tafada tashiga wanka,ranta na mata zafi.
Shiko Auwal tun safe yatafi kauyensu ya sanar dasu batun auren sa sati me zuwa.
Dagacan Abuja ya nufa,ya sanar da mummy.
tayi murna sosai,haka shima ammar yayi murna,
Muje zuwa
Surbajo for life.
ππππππππ
*KARAN BANA..........*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*Dedicated to billy shantally*
*29*
Tasleem fushi take da kowa agidan,shiyasa bata musu mgn, suma kuma basa kulata.
Dan maliki takansa yake,domin maaikatarsu ta bukaci daya dawo musu da duk abinda ya mallaka sabida da results din sata ya samesu.
Kuka yake harda hawaye,dan besan yadda zeyi ba.
Tasleem ce ke kokarin kwantar masa da hankali in suna waya,shine damuwarshi ke raguwa.
Umma yusura ta kira tai mata bayanin auran tasleem da Auwal.
Dan tsananin farinciki yusura har kuka tayi,sosai tai farin ciki da hakan.
Mummy kayan lefe na gani na fada ta hadawa tasleem,akwati 24 shake da kayan arziki,sede Ammar yace kar tasa undies su sun siya tun a moscow,zasu ba tasleem din da kansu.
Mamaki abun yaba mummy,data tuno zamanin da ake ciki se ta dena mamakin.
Yan uwa na nesa dana kusa duk sun fara hallara,sabida gabatowar bikin.
Tasleem ganin baki na zuwa gidansu sosai abun yake daure mata kai,kuma taki tambayar kowa ko me ke faruwa.
Sabida batason hayaniyane yasa take tafiya gidan wata kawarta *yar sarki* dan ta samu sukuni.
Auwal na Abuja bashi da niyyar tahowa kaduna.
Har su mummy suka kawo lefe,suka koma yaki tafiya.
Se ana sauran kwana biyu bikin mummy da Ammar suka tilasta mishi tafiya.
Dole tasa ya tafin amman badan yana so ba,dan ya tsani yaje yasa tasleem a idonshi.
Tasleem ganin akwatunan lefe sosai abun yabata mamaki,hakan ya bata tabbacin aure zaayi agidan,to auran wa?shine amsar data gaza samu.
Da yamma Auwal da Ammar suka iso,ayko kowa yashiga masa kirari,ga ango ga ango,
Tasleem wata dariya ta kwashe da ita jin cewa Auwal ne zeyi Aure,ayko fadi take.
"Dankari ashe fir'auna ne zeyi Aure,wlh matarsa ta bani,bakin mugu azzalumi,wlh har tausayin matar ya fara kamani,dan nasan sunanta sorry"πππ
Am sorry for you tasleem.π
Auwal ne zaune cikin dakinsu yana bude wani akwati,daya jima ajiye a dakin.
Kayan ciki ya fito dasu,panties da bra ne cike aciki,kallo daya zaka musu kasan ba na nigeria bane.
rike yake da bra guda daya yana juyawa,yana tunanin ta yadda ze iya ba tasleem su tasaka,bema sani ba ko zasui mata,se yanzu yayi danasanin biyewa Ammar gurin siyansu,tun suna makaranta.
Ammar ne ya shigo dakin,ganin Auwal rike da bra ne yasa shi dariya.cikin dariyar yake fadin.
"kai haba abokina,tun yanzu?"π
tsaki Auwal yayi yace.
"kaifa dan iskane,ni wlh na rasa yadda zanba waccan mara kunyar yarinyar wannan kayan,ni ka hadani da jidali wallahi"
Dariya Ammar yayi sannan yace.
"wayyo garin dadi na nesa,ayni har na kosa bikina da yusura yazo,wlh da kaina zanma sa mata,dan intabbatar da ingancin kayan dana siyo din"
Baki bude Auwal ke kallon Ammar,kana yace
"Lalle kunya ta ratsa ka,tunda har zaka dubeni ni sirikinka kace zaka sawa yusura bra"
Dariya Ammar yayi sannan yace.
"Kai kunyar ce ta ratsaka da yasa ina sirinkinka kake tambayata yadda zaka bawa matarka bra da pant"ππ
Duka Auwal yakai masa suna dariya,inda Ammar ya bashi shawara akan ya kira tasleem ya bata taje ta gwada in yamata to inbeyiba,se asan yadda zaayi.
Yusura Auwal yakira,sannan yasata ta turo masa tasleem,yana son ganinta.
Cike da farinciki yusura taje ta samu tasleem dake zaune tana kallo adaki tace mata.
"kije ya Auwal na kira,kuma yace yanxu yanxu,inkika dade ballaki zeyi"
zugi kuji yusura da karya.
Tun kan yusura ta gama idar da sakon tasleem takai bakin kofa,sanye cikin riga,mara hannu,da wuya me fadi,wacce ta tsaya daidai cibiyarta blue,se wando threequater,pink,kafarta ko takalmi babu ta nufi dakin ya Auwal jiki na bari.
Muje zuwa
Comments dinku,shi ze bani damar tsara next page yadda ya dace.

*KARAN BANA.........*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*ππβ€A'A ummu maryam pls muna jiran na cuceta,ki taimaka ki suburbudo mana,don Allah,ki mana typing,haba ta gurina kar ki mana hukunci mana,kinsan de bazamu jure ba,pls pls amadadin nida sauran masoyanki ki daure yau ki bamu,Allah ya kare mana ke daga sharrin duk me sharri,You are you ummu maryam and nobody will be you,i loves you for no reasonππ*
*πππππππsama mata,Inna Ibrahim kime na ta haihu ta samu baby girl,my baby inna Allah yaraya mana baby yasa cikon Addini ce,ki fadawa shekau ya kwashe yaransa Ahanya,surbajo nanan zuwa sunaπkilometre dubu daya da Arbain da biyar,from keffi to meduguri,on my way comingπ*
*Dedicated to Billy shantally*
*30*
Tana isa bakin kofar Ammar na fitowa,ko lura dashi bata yiba ta fada dakin.
Auwal se ganinta yayi kwatsam cikin dakin jikinta na bari.
A wilakance ya kalleta sannan yayi tsaki yace.
"dan jakanci irin naki shine zaki shigo ba sallama dalla fita kiyi sallama wawiya kawai"
Kan ya karasa mgnr ta fice daga dakin ta tsaya bakin kofa tana fadim.
"salamu alaika"baki na bari.
da kyar yace.
"Amin"sannan ya bata izinin shiga.
Koda ta shiga rakubewa tayi daga bakin kofar tace.
"ya Auwal gani"
"matso nan"ya fadi cikin daure fuska.
Ba musu ta fara jan guiwa har ta isa gurin shi.
Tana zuwa turo mata akwatin yayi gabanta,yace.
"duba ki gani zasuyi miki?"
Ba musu ta bude akwatin,ganin abinda ke ciki ne yasata zabura ta mike tayi baya hannunta toshe kan bakinta.
Wata uwar harara ya watsa mata da gudu ta dawo ta durkusa agabanshi.
"oya check"yace yana watsa mata harara.
Ba musu ta fara ciro duka kayan cikin tana kallo,har ta gama fito dasu duka,tana gamawa ta zuba mishi ido tana jiran karin bayani.
"size dinki ne?"
"Aa duk sunmin yawa wannan"tace tana rawar baki.
Akaro na farko dayakai dubansa,kan boobs dinta,na dan wani lokaci,sannan ya dubi bra din.
Dagowa yayi ya dubi fuskarta dan ya fahimci raina masa wayo zata yi,cikin daurewa yace.
"ok,dama ba anan na siyaba,kuma gashi suna da tsada,baze yiwu na zubar ba dole maidar musu zanyi,kinga in na mayar batare dana tabbatar da sunmiki yawan bana cutar dasu,so yanxu dauki ki fara gwadawa daya bayan daya"πππ
Ido ta ware baki da jiki na bari tace.
"don Allah Ya Auwal kayi hkr,ni vazan iya gwadawa ba wallahi"
Wasu jajayen ido daya kalleta dasu,kan kace me.
ta kwashe rigarta zuwa sama,ta mika hannu tana kokarin balle bra din jikinta,
Da sauri ya runtse idonshi,ya juya baya.
ita ko bata masan yayi ba,cirewa tayi jikinta na bari ta dauki bra din tasaka,
Daidai ita ne bra din,sun mata cip,tana gama sawa sabida rudewa hannu daya amurde tasashi,sannan gurin bayan bra dinma a murde.
da gudu taje tasha gabanshi,tace tana nuna mishi bra din.
"Ya Auwal nasaka ka gani tunda wannan tamin sauranma duk sunyi min yaya"
A hankali ya ware idon shi ya sauke akanta,wasu kibiyoyi yaji suna soke duk wata gaba ta jikinshi.
Itako cike da tsoro ta juya baya dan yaga bayan bra din shima.
Idonshi ne ya sauka,kan hannun datasa amurde,bece komaiba,ya mike ya isa gurinta.
Jinta tayi kamar ta jingina da wani abu,a tsorace ta waigo,idonta ya sauka cikin nashi.
Kauda fuska tayi gefe,bakinta na motsi amman ta kasa mgn,sabida numfashinshi dake sauka a fuskarta.
Hannu yasa ya kama kafadunta,a hankali,da sauri ta bude ido tana kallonshi,
Juya ta yayi,ta juyo bayanta,sannan ya kama maballin bra din,a hankali ya balle.
da sauri tasleem ta dafe gaban,bra din idonta na zubar da kwalla,dan ta dauka boobs dinta ze taba.π
hannun bra din yasa hannu ya gyara,sannan ya daidaita bayan bra din daga burΙewar,yasa mata maballin.
kanshi ya dora kan kafadarta ta gefe ya rada mata a kunne.
"kinyi kyau"
Runtse ido tayi,dan ita ta kosa ya matsa daga kusa da ita
Kan kujera ya koma ya zauna,sannan yace ba tare daya kalleta ba.
"ki kwashe kije ki xuba cikin kayan lefen naki"
Rigarta ta maida sannan tace.
"Ya Auwal ayni ban tashi yin aureba bare har akawomin lefe"
"Jibi ne Auranmu nidake,lefen da aka kawo nakine,so se ki shirya."
Zaman dabaro tayi agurin,tama kasa mgn,kwakwalwarta ta shiga caji.
Zuwa can kamar wacce aka tsikara ta mike,wata kara tasaki sannan ra rushe da kuka,tana fadin.
"wlh bana sonka,bazan aure ka ba,mugu kawai azzalumi,wlh sede ka kasheni ka kai gawata gidanka,ashe shine dalilin da yasa kayiwa hisham cune agurin ayki sabida kasamu damar Aurena Wlh bana sonka,ko acikin irin mazan da nakeso baka aciki,bana sonka Auwal,wlh bana kaunarka"tana kaiwa nan ta juya da gudu ta fice a dakin tana kuka.
Dafe kai Auwal yayi,ya sunkuyar da kai,kalamun tasleem na yawo akansa,tsana da kyamarta na kara shiga zuciyarshi.huci kawai yakeyi kamar wani zaki.
itako da gudu ta nufi dakin ummanta,tana kuka taketambayarta hakikanin maganar data ji gurin ya Auwal.
"da ki kwasomin abun kunya inkasa fita gwanda ki Auri Auwalun ko kasheki ze dunga yi kullum,kinga kinyi shahada,da ki mutu dakin hotel "cewar umma cikin daure fuska.
"wallahi umma bana sonshi"inji tasleem tana kuka.
"Shidin ubanwa yace miki yana sonki?"cewar umma cikin fushi.
"umma kece kuwa kika haifeni?"cewar tasleem cikin matsanancin kuka.
Murmushi umma tayi sannan tace.
"A caca na ciyo ki"
faduwa tasleem tayi agurin tana birgima tana fadin.
"wlh bana sonshi,bana kaunarshi,bazan aureshi ba"
"Aure ko kamar anyi an gama dan kan ubanki"cewar umma gamida ficewa daga dakin.
Tasleem mikewa tayi da gudu,ta nufi,dakin su,ta kulle kanta,kuka take kamar ranta ze fita,aganinta rayuwarta bata da amfani,matukar Auwal ne mijinta.
Muje zuwa
Surbajo for life.
ππππππππ
*KARAN BANA...........*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*Ig zahra_surbajo1*
*whattpad zahrasurbajo*
*Esha Mustaphat,fiddah sokoto,Salma B,Hafsat Dahir jos,surbajo na gaisheku Allah yabar mu tare cikin aminci,ina sonku overπ*
*Dedicated to Billy Shantaly*
*31*
A ranar kawai tasleem har ta rame sabida masifar