KAREN BANA COMPLETE BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.txt

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 14

6K to 9K   out of 39.4K words

akwai abinda ya faru. πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚hhhhhh wasawasa @xianoxy seda yayi kwana biyu garin yola batare da yaga wacce yaje gani ba,hakura yayi ya koma kd,zuciyarshi cike da zullumi.

Bayan uku sannan yusura ta kunna wayarta ay kamar jira yake kiranshi ya shigo.

Dauka tayi tana dauka ra rushe mishi da kuka.

Hankalinshi ne yatashi ya shiga rarrashi,dakyar tayi shuru tace. "baby akanka kamar zanyi hauka,muna waya dakai vayan na gama nayi sauri na tawo inda nace mu hadu,se alokacin na tuno na manta wayar gida koda na koma gida,wlh ba ita ba alamarta,gashi ban rike no dinka ba,nayi iya yina in sameka baby abu yaci tura,se yau nasamu akamin wlc back na sim dina"ta karasa maganar cikin matsanancin kuka.

Wayyo dan tausayinta har wasu hawayene kebin idon dan maliki,dan yayi imani da cewa gaskiya ta fada masa,kuma ya yarda tana sonshi.

Cikin sigar rarrashi yace. "ya isa haka baby na kinji ko,kiyi hkr,nidama nasan akwai dalili ba haka nan ba,kwana na biyu ina jiranki baby,danaji shuru ne na dawo jiya,ki kwantar da hankalinki kinji ni naki ne har abada," Cikin sigar shagwaba tace. "duk rashin phone ne yajanyo haka baby amman kayi hkr kaji ni ina nan zuwa next week"

Sosai yakejin dadin yadda tasleem ta damu dashi,cike da kulawa yace. "wayar taki wacce irice?" "iphone 8 plus ce"mazugal sunan wata unguwaπŸ˜‚ "nawa take" "295k baby" "send me your acct no,"itace amsar daya bata.

Dayake tun kwanaki sunje sun bude acct a banki ba tare da tunanin komaiba ta tura masa na tasleem.

Ba jimawa suka sami alert na 500k

Dariya suke harda hawaye,lalle dan maliki wawa ne na karshe.


Muje zuwa


Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA.........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€




*ZAHRA SURBAJO*



*YA ALLAH KA TURA MALAIKU JOS KAMAR YADDA KA TURAWA AHLU BADAR,KISAN DA AKEYI YA ISA HAKA,WANDA YAJI DA WANDA BEJI BA BI AKE ANA KASHEWA,YA ALLAH KA TAIMAKI MUSULMI DA MUSULUNCI,ALLAH KA KAI MUSU DAUKIπŸ™πŸ™πŸ™πŸ™πŸ˜­*


*Dedicated to Billy Shantaly*


*11*




Sosai su tasleem suka ji dadin kudin.

Shiryawa sukayi suka tafi kasuwa,suka siyo duk abinda basu dashi na kayan abinci.

Bayan sun dawone,suka ci gaba da tsara yadda zasu ci uban dan maliki.

Yusura ce ta kirashi a waya,bugun farko yadauka.

Cike da salon daukar hankali,tace.

"baby albishirinka"

Cike da zumudi yace

"goro baby"

"wata friend na da muka hadu a facebook,tana nan kd dinku,kuma ta shaidamin anyi musu rasuwa tun kwanaki ban zo ba,to yanzu gobe zanje gidansu kaga base mu hadu acan ba"

Dan tsananin farinciki danmaliki har ihu yayi na murna,kana daga bisani yace.

"gaskiya wannan albishir ne me kyau baby,Allah ya kaimu gobe,da kaina zan zo in daukeki in kaiki gidan"

Hakade sukai ta saita masa hanya,yana hawa.

Washe gari,da rana tasleem ta nufi airport dauke da akwatin kayanta,ta kira dan maliki akan gata ta iso.

Ay be bata lokaci ba,ya iso cikin wata arniyar mota.

Tasleem na hangoshi ta ruga da gudu ta rungumeshi,dagata yayi suna jujjuyawa agurin.

Koda yayi yunkurin sauketa ki tayi ta sake makaleshi,haka ya riketa yaja jakar kayanta zuwa mota,ya bude gidan gaba yasata sannan ya dawo ya ajiye jakar a baya,ya shiga ya tada motar suka fice daga airport din.

Kiss tasleem tayi masa a kumatu,gamida fadin.

"kai baby,kaga yadda kayi masifar yin kyau,kuwa?"

Shafo kumatunta yayi yana murmushi yace.

"har na kaiki baby?"

"Ay harma ka fini"

Haka sukai ta hira,

Waya tasleem ta ciro tace.

"bari inkirata inji awacce anguwa suke"

Tana gama fadin haka ta kira yusura,bayan ta dagane,tayi saurin mikawa danmaliki tace.

"baby tambayeta kaine dan gari"

Murmushi yayi sannan yasa hannu ya amshi wayar yasa akunne yace.

"to kawarmu ykk,"

Yusura dakewa tayi tace.

"lafiya lau nake,kuna ina ne yanzu?"

Yaso ya taba jin irin muryar amman ya mance ko aina ne,dan haka bata amsa yayi da cewa.

"muna kan titin mando,inane anguwarku?"

"hayin rigasa layin taro taro,in ka shigo layin kace anuna maka gidan marigayi malam bukar,nan ne gidanmu"

Wasu zufa ne masu dumi kebin fuskarshi,a hankali ya furta,

"yusura"

Cike da nuna halin ko inkula tasleem ta dora kanta kan kafadarshi tana wasa da hannunshi tace.

"ay baby yusura akwai mutunci,Karkaga yadda take nunamin so shiyasa nima na damu da ita wallahi".

Wani mugun miyau ya hadiye,sannan yace.

"Allah sarki,gaskiya ne"

Gaba daya natsuwarshi bata tare dashi,abirkice yake,haka yake driving tasleem nata jan shi da hira,har suka iso kofar gidan mahaifinshiπŸ˜‚. Suna parking yace wa tasleem.

"baby munfa karaso gidan"

Kallonshi tayi da sexy idon ta tace.

"baby dama kasan gidanne?"

Murmushi yayi gamida gyara zamansa yace.

"ay gidan ba boyayye bane,baby nasan gidan"

Murmushi tayi wanda tasan yana matukar daukar hankalinshi tace.

"ok to bari inkirata"

Kiran yusura tayi ta shaida mata sun iso kofar gidan.

Ayko kamar gaske sega yusura da gudunta ta fito daga gidan.

Tasleem itama fita tayi ayko da gudu suka rungume juna suna murnar ganin juna.

Bayan sun dan natsu ne,tasleem ta zo ta gefen da dan maliki yake ta bude kofar ta kamo hannunshi tace.

"Baby fito ku gaisa da kawata"

Rasa yadda zeyi yayi dan tabbas da kunya ya hadu da yusura.

Gashi beso tasleem ta gane cewa yasan yusuran,haka ya daure ya fito.

Tasleem shigewa jikinshi tayi,tace

"Baby ga kawata yusura,yusura ga babyna hisham"

Yusura ganin hisham se tayi pretending a zuwa ta firgita da ganinsa,zabura tayi ta boye abayan motarshi tana lekowa.

Shiko hisham kunyarshi daya ganin da yusura tayiwa tasleem ajikinshi,kuma tasan ba matarshi ba ce.

Kame kame ya fara,ya rasa ta ina ze fara.

Yusura daga inda ta boye,tadan leko tace.

"yaya don Allah kayi hkr,bansan kai bane"πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚.

Muje zuwa.


Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA.........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*ZAHRA SURBAJO*



*DON ALLAH DUK WACCE NA CIRE GROUP KARTA DAUKA TAYI LAIFINE,KAF GROUP DIN NA CIRE HARDA KAINA NA RUFE GROUP DINNE,SO AMIN UZURI,PLS,NA RUFE NE BA LAIFI KUKAMIN BA,*



*Dedicated to billy shantally*

*12*



Sosa keya yayi sannan yakai dubansa gurin tasleem,wacce ta saki baki tana kallonsu azuwan tana mamaki. "yaya kuma yusura,kinsanshi ne?"inji tasleem.

Murmushi yusura tayi tace. "big bross nawa kenan danake baki labarin kirkin shi,yayana hisham"

Juye juye ya kama a gurin kunya kamar zata kasheshi,

Yusura ta ce.

"amman nayi mamaki ya akayi kika sanshi?"

Murmushi tasleem tayi,gamida kara shiga jikin dan maliki tace.

"shine fa wanda na taba fada miki,nazo gurinshi kwanaki zan kwana biyu,muna hotel tare ma aka kirani mamana ba lfy,to tunda na tafi ban dawo ba se yau,dan haka muje inyi gaisuwa,na fito mu wuce masauki dan alamun baby sun nuna a gajiye yake"tafadi tana sake nanikeshi.

Wayyo kunyar hisham,ji yayi kamar kasa ta tsage ya shige,ko kadan ya kasa dago ido ya dubi yusura,sosai tasleem ta yarfashi gaban kanwarshi.

Ita ko yusura murmushi tayi tace tana duban hisham.

"ikon Allah kice kunyi aure ashe,amman bross ba ko labari"

Da dariya tasleem ta tabo kafadar yusura tace.

"ke dallacan ba aure mukayiba,muna de dating ne tukuna ko baby"ta karasa maganar tana duban hisham.

Kai ya mirgina,kamar kwakwa,πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ Yusura batace komai ba,ta juya ta shige gida.

Binta tasleem zatayi,da sauri danmaliki yajata cikin mota,yace.

"haba baby me yasa kike haka gaban kanwata,zaki jamin rainine wlh,don Allah kar ki sake fadin komai"

Murmushi tayi,tace.

"ok to shikenan baby bari inshiga in fito mu wuce"

"mu wuce ina?"dan maliki ya tambaya a firgice.

"hotel mana"tasleem ta bashi amsa.

"look tasleem,baze yiwu muje hotel ba,yusura zata yadani a dangi,ni kuma banso sunana ya baci,kiyi hkr ki kwana anan kawai,kinji"

"what,meye nufinka,nice zan kwana cikin wancan akurkin gidan da koyaushe ze iya rugujewa,wlh baze yiwuba,ni nayi mamakin kasancewarka ma jinin gidan amman gidan ke a haka har yanzu,"

Sosai yaji kunya amman se ya daure yace.

"Ay tuni na gina musu gida me kyau acan unguwar kanawa,kawai na barine se next week su koma,"

"ayko tunda ka gina musu,sede ka kwashemu duka ka kaimu can din su tare ayau ko kuma mutafi hotel nida kai mu kwanacan dan ni da kewarka nake tafe"

Wayyo Allah @xianoxy πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚baki shi ke yanka wuya.

Wata zufa ya goge,sannan yace cikin in ina

"to to to to shi kenan,bari inkirasu muje can din zefi baby,amman muje hotel nidake da sanin yusura akwai damuwa"

Ayko yana kai nan ya fice a motar ya shiga cikin gidan tasleem nabinshi abaya tana dariya aboye.

"oya yusura ina mubashshir,ki kirashi ku fito mu tafi sabon gidan dana gina muku"cewar dan maliki.

Da yake yusura batasan da batun gidanba agigice ta dago tana dubansa tace.

"yaya mune ka ginawa gida?" "eh mana,sabida banson zamanku anan,"

Idon yusura ne ya fada kan na tasleem,kifta mata ido tasleem tayi.

Ayko da gudu yusura tayi jikinshi ta rungumeshi,tana fadin.

"mungode yaya Allah ya kara budi,tasleem kinga halin kirkin brother na ko?"

Kai tasleem ta daga tana murmushi.

Hhhhh kan kuce kwabo,bayan range rover din @nazeefi_bm Ta cika da tarkacen kayan su yusura har saman motar kamar yadda tasleem ta bukaci asaka,ga boot abude,πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ Haka suka shige,yajasu zuciyarshi na tafasa,zuwa dankareren gidanshi daya gina domin hutawa da yanmata.

Sosai gidan ya hadu ba kadan ba,yusura bata jira iso ba,ta shige cikin gidan ta fara bude bude,har ta isa dakin da danmaliki ya ware a nashi,loka ta bude ayko sega takardun gidan,daukowa tayi ta fito da gudu,tazo gabanshi tace cikin murna.

"wallahi bross ka gama haduwa,ga takardun gidan nunamin gurin da zamuyi signing nida mubashshir,tunda mu kaginawa"

"wanne irin signing kuma,kede ba gashi na kawo ku ciki ba"cewar dan maliki cikin daure fuska.

"ah ah baby yusura tafika gaskiya,konice ace ga abu anbani baa bani nayi signing a ya zama nawaba ay kamar aro ne dan gaka nuna musu suyi signing mu tayasu murna bross dinsu naji dasu,gaskiya nayi dace da masoyi"

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ @xianoxy bakinsa kamar ze tabo sama haka ya nunawa yusura inda zata sa hannu a takardun,wanda ke nuni da gidan ya dawo mallakinta.

Darab yusura ta rattaba hannu,sannan ta fada kan danmali ta rungumeshi tana kuka gamida godiya.

Shiko wasu zafafan hawaye ne kebin zuciyarsa,bejiba be ganiba budurwa tasashi kyautar gidan da yakai naira milyan ashirin batare daya shirya ba.

Sallama ya musu yabar gidan azuwan ze dawo anjima.

Yana fita yusura ta fada kan tasleem suka rungume juna suna dariya,mubashshir shima dariyar yake.

Muje zuwa


Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA..........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAHRA SURBAJO*



*Instagram@zahra_surbajo1*


*Masoyan surbajo group nagode sosai da sona da kuke nima ina kaunarku,Allah yabar zumunci,admin mum barrister,Allah ya bar kauna,ina yinku sosai*


*Dedicated to Billy Shantaly*


*13*





Danmaliki be dawo ba se dare,

Lokacin su yusura sunyi abinci me rai da lfy sun baje a falo suna ci suna kallo.

Yana shigowa,ya tuno da cewa gidan yanxu ba nashi bane,take ranshi yay mugun baci.

Daurewa yayi ya karasa ya samu guri ya zauna,

Da faraa tasleem ta taso tazo gurinshi cike da kwarkwasa,ay take ya mance duk wani bacin rai,dan irin son da yake mata koshi baze iya fadin adadinsa ba,yana mata so da dukkan zuciya da jinin jikinsa,yanaji ya rasata shima baze iya rayuwa ba,hmmm dankari.

Yana zaune tazo ta zauna gefenshi ta dora kanta kan kafadarshi,ta fara yimasa kukan kirsa.

Gaba daya rudewa yayi ya daburce ya rasa meke masa dadi,dan in akwai abinda danmaliki ya tsana to shine kukan tasleem.

Cikin sigar rarrashi ya fara tambayarta.


" baby me aka miki fadamin kinji,ko wani abu kikeso ki fadamin komai tsada da girmansa nayi alkawarin baki matukar inada shi"

Cike da shagwaba tace.

"baby dazu munaso musai ruwa dan babu agidan,gashi munaso mu sha,baby munci wiya kamin muje gurin siyarwa,kaga da ace akwai mota hannun yusura ay duk bazamu sha ba,nifa dazu da rana danaga wata mota kofar gidanku na dauka ma tatace daka sai mata,se danake tambayarta se tace ay batata bace,ban yarda ba dannide nasan baby na adaline,babu yadda zaayi ace kanwarsa guda daya tak da Allah ya bashi bata da mota"

Wata zuface ta karyo masa ya goge,sannan ya kirkiro murmushin dole yace.

"eh hakane baby,da da mota da baki wahala ba baby na, yanzu de zaa duba yiwuwar bata mota din kinji,sabida kinga bata iya ba kar aje asamu matsala"

Shuru tasleem tayi dan taji tarkon ta baze kamaba,dan ta mance daga ita har yusura ba wacce ta iya motar.

Sun jima suna hira,sannan ya tafi,

Kwanan tasleem uku dan maliki yazo ya dauketa yakaita airport azuwan zata tafi gida,yana baro gurin itama ta baro ta koma gida.

Zama suke lfy asabon gidansu,inda,yanzu sun dauko mahaifiyar su tasleem ta dawo gidan da zama,dan zamansu su kadai abun beyi tsariba.

Da kudin da suke tatsa agurinsa duk suka koma makaranta.

Kuma basa wasa da karatunsu har suka kammala secondry school.

Rayuwar na musu dadi,

yayinda danmaliki yanzu beda buri da ya wuce ya auri tasleem,gashi ko garinsu taki barinsa yaje.

Kullum haka takemishi hanya hanya,da yake yana sonta dole ya hakura yaci gaba da lallabata.

Bayan shekaru hudu,yusura da tasleem suna gara dan maliki yadda yadace,har wata rama yayi,sabida tsananin son da yakewa tasleem.

*MURTALA MUHAMMAD AIRPORT.*

Saukar jirgin kenan dan haka baa bawa pasinjoji damar fita ba.

Zaune suke cikin jirgin sanye da rigunan sanyi,da hula wanda ko baa fada maka ba kasan kasar da suka baro ana zabga sanyi.

Maza ne su biyu,wanda shekarunsu basui kasa da 35 ba,kallo daya zaka musu ka fahimci hutu yasamu gurin zama,ko acikin mazan kunsan akwai maza to su din mazajeneπŸ˜‚

Daya daga cikinsu wayarshi a hannun shi yana ta latsawa,yayin da dayan kuma ya kwantar da kansa kan sit dinsa,ya lumshe ido.

Kyawawa ne bana wasa ba,

Me danna wayar ne,ya waigo yana duban dayan cikin yanayin damuwa yace. "ABB nafa gaji da zamannan,haba yakamata abude mu haka"

Wanda aka kira da ABB yamutsa fuska yayi kamar mace,dagani kasan yanaji da kanshi,uwa uba kana kallonshi kasan magana tafi gold tsada agurinshi.

Memakon yabashi amsa kawai seya zura masa shanyanyun idanuwansa.

Tsaki dayan yayi yace.

"wlh dadi na dakai wani lokacin baho ne kai,ayta mgn kazubawa mutane ido,"

Wannan ma ba amsa,maida kansa kawai yayi ya kwantar ya lumshe idon.

Anba pasingers din damar futa dan gaka mikewa sukayi,kowa goye da katuwar jaka abaya,kafafunsu sanye cikin snickers na Gucci,hannu sanye cikin agogon rolex,kayan jikinsu ma abin kallone.

Takowa sukai zuwa kofar fita,

Wata sassanyar iska dukansu suka shaka,ta kasarsu ta gado,yayinda sukai sallama da kasar Moscow,

Takowa sukai suka fita.

Arrivals area suka nufa,cikin takunsu na kasaita,kai wainnan matasa ba karamin haduwa sukai ba.

Tunda suka shawo kwana dukansu naga suna murmushi,dubana nakai inda suke kallo,wata dattijuwace,me kimanin shekaru hamsin da biyar,ta nufosu fuskarta dauke da faraa.

Da sauri suka karasa gurinta suka rungumeta.

"masha Allah naji dadin ganinku yan biyu na,Allah ya muku albarka,Allah yasa karatun ya amfaneku damu baki daya,"cewar dattijuwar,sanda ta rungumesu gaba daya.

Daukarta sukai su biyu suna jujjuyawa da ita suna fadin.

"mummy munyi kewarki sosai,"

Cike da faraa,taja su zuwa inda mota take.


Muje zuwa


Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAHRA SURBAJO*


*Amin afuwa,rashin jina jiya,na raka messi da ronaldo airport ne jiya sun koma gidaπŸ˜‚*


*dedicated to Billy Shantaly*


*14*


Koda suke tafe a mota dayan me suna Ammar se shagwaba yakewa dattijuwar itako se biye mishi take,shiko mr no talk gum yayi da bakinsa a haka har suka karaso gida.

Fadin tsari da kyan gidan bata lokaci ne,abu guda kawai zan fadi shine dollas sunyi kuka agurin.

Koda suka isa gida samu sukai gidan cike da yan uwa anzo taya su murnar kammala karatu kowa se nan nan yake dasu.

Basu samu kansu ba se da kowa ya watse,wanka sukai sannan suka isa falo domin ganawa ta musamman da mahaifiyarsu.

A falon suka sameta.ammar da sauri ya karasa jikinta ya rungumeta yana fadin,

"my mummy"

"naam autana"ta amsa gamida shafa lallausan gashin kansa.

Turo baki yayi gamida nuna Abb dake zaune kan carpet yana murmushi yace.

"Mummy ga autankican ba ni ba," Se alokacin yayi mgn.

"kai kai ka iya bakin ka waye autan,?"

Seda naji muryar na gane dadinta ne yasa be son yawan mgn(kamar ta oga)πŸ˜‚

Dirowa Ammar yayi gaban Abb yace.

"kaine autan mummy"

Duka Abb ya kai masa da sauri ya goce yana masa dariya.

Mummy da tun dazu take musu dariya se alokacin tai mgn.

"kai iya shegenku ya isheni haka,haba,kunfa dawo kenan bakina ze kara tsayi"

Dariya ammar yayi,yayinda Abb kuma ya murmusa.

Namfa aka shiga hirar yaushe gamo,wacce yawanci ammar yafi yin mgn, mr no talk ko daga eh se aa,se murmushi.

"ya kamata jibi de ku daure kuje kd ku gano su dan auntyn ku kullum seta dameni kuje kuje,dan haka jibi adaure aje adubosu,ko dan gurin mummy"ta kai dubanta gurin Abb.

Wanda duba daya zaka masa kafahimci irin tsantsar farincikin da ya shiga jin batun na mummy.

Da sauri ya gyada kai,gamida cewa.

"me yasa jibi mummy kawai muje gobe,ko bross"ya fadi yana duban Ammar.

"Ba za a je goben ba "

cewar ammar yana dariya.

"Jibi zakuje,nima gobe inaso in wuni da twins dina"

Abb beso haka ba amman haka dole ya hakura ammar na tsokanarshi.

KADUNA.

Yau akwai babban tarkon da su yusura keson danawa danmaliki dan haka tun safe suke shawarar yadda shirin ze kasance.

Wasu kaya ne jikin tasleem wanda kallo daya zaka mata ka dauka batasan gabas ba.

Duk wata sura ta jikinta kayan sun nuna,gudun kar mamanta tai fada yasa ta dauki wata after dress tasaka,tayi rolling dan kwalin,

Yusura kuma wata doguwar rigace ajikinta wacce ta dace da zubin jikinnata.

Fitowa sukai rankai rankai zasu fice,da sauri mama ta tsaidasu. "ina zaku haka?"

Kame kame suka fara hakanne yasa ta gane inda zasun.

"wai meyasa bakwajin mgn ne nace kubar yaronnan haka amman kunki ji,ko tunaninku abinda kuke masa ze dawo da maryam da auwalu ne?banaso nace kubarshi haka". "mama kiyi hkr don Allah insha Allahu zamu daina,"cewar yusura tana sosa keya.

Tasleem ko shuru tayi,tanakallon maman.

"nide abari banaso,gaskiya wannan ay seku zubarwa da kanku mutunci idon mutane"

Hakade tai ta fada daga baya ta barsu suka fice.

Airport suka nufa yauma,

Guri suka samu suka zauna,kowacce sanye da glass a idonta irin manyan nan,sosai yay musu kyau.

Kiran danmaliki sukai azuwan tasleem ta iso.

Sosai yayi murna,dan shi yasan tasleem nasonshi dan daga yola kd bata mata nisa dan kawai tazo ta ganshi,shi yasan ya gama dacewa da me sonsa.

Isowarsu kenan,tagwayen mummy,hmmm kyau iya kyau abin se godiyar Allah.

Tafe suke suna takun kasaita,kai da ganinsu kasan sun gama haduwa.

Ammar ne yayi waya akawo musu mota gasu sun iso airport a kaduna.

Da yake ba kaya garesu ba daga su se wayoyin hannunsu,takowa sukai suka fito zuwa wajen arrivals din.

Idon su ne yasauka kan su yusura dake zaune.

Masha Allah dukansu suka ayyana a zuciyarsu.

Ganin su cikin shigar mutunci kar ma de tasleem data rufe kanta ruf.

Suna nan suna kallonsu,Danmaliki ya iso gurin,

Mamaki ne ya kama twins din mummy ganin yusura ta kwasa da gudu ta buya bayan flowers,tasleem kuma da sauri ta cire doguwar rigar jikinta,

Waiyyazubillah ita Abb ke nanatawa a zuciyarshi sanda yaga shigar dake jikin tasleem,

Mamakin Abb ya karune sanda na cikin motar ya fito.yaga tasleem ta ruga da gudu ta rungumeshi,shi kuma ya dagata yana jujjuyawa.

Luuuuu ya tafi ze fadi da sauri ammar ya riko shi.

Sabida ganin yanayin da Abb ya shiga ammar

3 / 14