Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
you all, with all my heart*
*Dedicated to Billy shantally*
*50*
Tasleem cikinta me laulayine,wanda hakan sosai ya takurasu,komai Auwal ne ke mata.
Shiyasa ko lokacin kanshi bashi dashi senata dana cikinta.
Cikinta na wata shida yusura ma tasamu ciki,murna gurin ammar baa magana.
Kullum adduar iyayensu Shine Allah yasaukesu lafiya.
Danmaliki,tuni Auwal ya bashi jari yana juyawa,wanda hakan sosai ya taimakeshi,dan dashi yakeci yake sha.
Yayi danasanin duk abinda ya aykata musu,kullum cikin neman yafiyarsu yake.
Kanin yusura,tuni ya kammala karatunshi na secondry school,.
Auwal ke nemamasa gurbin karatu a jamia.
Cikin tasleem nada wata tara mummy tazo da nufin maida ita gidanta.
Ayko fafur Auwal ya shafawa idonshi toka,akan be amince ba.
Dole mummy ta barta,amman tana yawan zuwa dubata.
Ayko wata safiya ta tashi da ciwon nakuda.
Auwal beyi kasa aguiwaba,yashiga bata taimakon gaggawa,dan tuni ya tanaji komai domin zuwan ranar.
Cikin abinda be wuce awa guda ba,ta haifo danta sankacece me kama da ubansa.
Murnar da Auwal yayi bata misaltuwa.
Mummy ya kira,ayko bata bata lokaci ba ta iso.
Gyara mejego tayi da jinjirin.
Tuni yusura ma ta iso gidan da Ammar,dan baya bari tai nesa dashi.
Tasleem taga gata gurin danginta,dan danmaliki,akwati guda yay mata ita da babyn.
Haka su yusura ma baa barsu abaya ba gurin hada mata sha tara ta arziki.
Ranar suna yaro ya amsa sunan mahaifin Auwal,suna kiranshi Ameer.
Rayuwarsu gwanin ban shaawa,dan zaune suke lfy.
Yusura ma ta haihu ta samu da namiji itama.
Inda ya amsa sunan mahaifin Ammar,suna kiranshi Khalifah.
Kowa shaawar rayuwarsu yake,dan rayuwace me cike daso da kaunar juna.
Bayan watanni goma da haihuwar Ameer,tasleem ce zaune tana ba Ameer abincinshi.
Auwal ne ya shigo sanye da kayan shan iska.
Gefenta yaje ya zauna yadan rungumota jikinshi yana murmushi yace.
"baby na,aji tausayina haka,kullum baa bi takaina seta babana"
Dariya tayi tace.
"to da baban be samun kulawa taya zan sameka,kaga dole akula da baba"
Rungumeta yayi yana dariya yace.
"shiyasa nake sonki,baby na"
"son da kakemin yasa nima nake sonka"
Dariya sukayi,ya hadata ita da Ameer din ya rungume.
*ALHAMDULILLAHI*
*nan na kawo karshen wannan littafi,kuskuren dake ciki Allah ya gafartamin,ladan dake ciki Allah ya bamu,tare daku.*
*SURBAJO SABON SALO AUDIO,Bazan samu damar cigaba dayinshi ba,sakamakon shawara daga bakin mutane masu daraja,Fatima Radda,Humaira shuwa,Maman gidado,dan shawarar su na ajiye littafin badan hayaniyar social media ba,dan ni wannan baya damuna*
*ZAKU JINI AWANI SABON LITTAFIN ME MATUKAR NISHADAN TARWA,DA FADAKARWA,KAMAR YADDA NASABA*
*SEDE BAZAN FARA POSTING BA SENA DANYI NISA,*
*NAGODE TAKU HAR KULLUM ME FATAN NISHAƊANTAR DAKU DA FADAKAR DAKU AKODA YAUSHE*
*ina barar adduarku akan wata bukata don Allah,Allah kada ka dora mana abinda yafi karfinmu amin*
*ZAHRA MUHAMMAD MAHMUD SURBAJO*