KAREN BANA COMPLETE BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.txt

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 14

15K to 18K   out of 39.4K words

pics dinta shine suke sosui masa na musamman.

"Gaskiya yusura da ammar zece yana sonki da kin dace da miji"cewar tasleem tana murmushi.

Wani murmushi yusura tayi sannan tace.

"wlh tasleem tun ranar da na fara ganin ya ammar naji ina sonshi,sede shi har yanzu be ce yana sona ba"ta karasa maganar cikin yanayin damuwa.


"kar ki damu with time,ze zo ya furtamiki kalmar so,tunda alamunsa sun nuna yana sonki"cewar tasleem tana dafa kafaΙ—ar yusura.

"Allah yasa tasleem,kinga da yaya Auwal ze yarda da kema se ya aureki muyi aure tare"

"What!!!!!!!"

Tasleem ta fadi agigice gamida zabura ta fadi bata tsayaba ta mike tayi kofar daki da gudu ta dauki buta ta zaga toilet,sakamakon gudawar data kamata take yanke sabida yusura tace ta auri ya AuwalπŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…


Ta jima a bayin sannan ta fito tana share gumi kai ka rantse da Allah zaki ta gani.


Da kyar ta lallaba ta koma dakin.

Tana shiga gefen gado tane ta zauna,

cike da kulawa yusura ta nufota tana fadin.

"lafiyarki kuwa tasleem,?daga cewa ki auri ya Auwal shine kike abu sekace wacce Aljani ya shafa"

"Ba gwanda Aljanin ya shafeni ba so dubu akan kice ya Auwal ya aureni,haba yusura nifa adduar Alkhairi nai miki,meyasa ni kika bini da sharri?"

Dariya yusura tayi sannan tace.

"in Allah ya kaddaro mijinki ne wlh ko sokawe zaki koma sabida kashi,sekin aureshi,dan haka ni taso kimin hoton inje in gyara tawa tafiyar"

Sake kwanciya tasleem tayi tana maida numfashi,sannan tace.

"wlh bazan iya ba"

"sabida me?"yusura ta tambaya.

"wlh babu kwari ajikina inaga ruwan jikinane ya kare,akwai bukatar akaramin ruwa"πŸ˜†


Duka yusura ta daka mata abaya sannan tace.

"to ay ba damuwa in ya Auwal yazo se ya karamiki har da jini"

Tana kaiwa nan tafice daga dakin bayan ta dauki mayafinta

Tasleem ko kwanciyarta tayi,tana jawa yusura Allah ya isa.


Yusura na fita,gidan su wata kawarta *BINAFAT* ta shiga sabida ta kirata tazo taimata hoton.

Binafat kawar yusura ce tun yarinta,yarinya ce me matukar kirki,ga tarbiyya,haduwar yusura da tasleem ne yasa yusura jan baya da binafat,amman duk da haka suna mutuncinsu.

Da sallamarta ta shiga gidan,lokacin Binafat na wanke wanke,da sauri ta saki wanke wanke tazo gurin yusura ta rungumeta tana murnar ganinta,tace.

"ina hasanar taki ko kunyi fadane?"cewar Binafat tana dariya.

Tsaki yusura tayi sannan tace.

"Kede bari wlh iskanci takeji yau,hoto fa zata daukeni amman dan tsabar wulakanci wai ruwan jikinta ya kare,se anmata karin ruwa"


Dariya binafat ta tuntsure da ita,

yusura dakin maman Binafat ta wuce,taje ta gaisheta sannan ta nemi izinin binafat tazo ta dauketa hoto agidansu.

Dattijuwa me kirki,bata hana binafat zuwa ba.

Gidan su yusura suka dawo Binafat taita daukarta a hoton irin yadda takeso.

Ana gama daukanta ta tura masa ta Whatsapp,inda yashiga yabonta wanda hakan sosai ya mata dadi.

Yau Dan maliki ne ya zo gurin Tasleem.kuma yau sati guda kenan da tafiyar su Auwal,wanda yau dinne zasu dawo.

Be shigo ba awaje ya tsaya ya ayka aka kira mishi ita.

Ba musu ta fito,dan tanason ganinshi dama dan ya bata wayarta da jakarta data manto a hotel ranar nan.

Tunda ya hangota yake mata faraa,itama ba laifi ta sakar masa fuska.



Tana karasowa ya bude mata kofa ta shiga ta zauna sannan shima ya shiga ya zauna.

fuska dauke da faraa yace.

"baby am really sorry,wlh nakasa controlling kainane ranar,amman kema kinsan ban taba yimiki haka ba,ki yafemin don Allah"

Murmushi tayi tace.

"ya wuce baby karka damu,kaine ma yadace mu nemi gafarar ka bisa wasa da hankalinka da mukayi"

murmushi yayi yace.

"ba damuwa ya wuce baby na me wayau"

"baby phone na da handbag dina fa?"tasleem ta tambaya.

juyawa yayi ya mika hannunsa bayan motar ya dauko mata jakar ya bata.

Amsa tayi tana masa godiya.

Dago kan da zatayine,ta hangi yaya Auwal da Yaya Ammar cikin wata bakar mota sun nufo koΙ—ar gidan.

idan kuka ga yadda ta bude motar tayi tambul a kasa zaku dauka ta karya wuya.

Da wani mahaukacin gudu ta fada gida kamar walkiyaπŸ˜†


se alokacin danmaliki ya lura da abinda ta hango da yasa ta gudu ra barshi.

Wata zazzafar iska ya fesar sannan yace.

"Zanyi dukkan me yiwuwa dan ganin na mallaki tasleem ni kadai Auwal zanyi maganinka"

Su Auwal na karasowa shi kuma yana jan motarsa yabar gurin,dan haka basu ganshi ba.


Tasleem koda ta shiga gida ta kasa shiga daki tsakar gida ta tsaya tana kuka jikinta na bari.dan ita ta dauka sun ganta nanko batasan basu ganta ba.

Da sallamarsu suka shiga cikin gidan.

Da tasleem sukaci karo a tsakar gida tana bari,ay tana hada ido da Auwal ta zube a gabansa ta kama kafafunsa tana fadin.

"wlh ya Auwal jakata na amso,na rantse da girman Allah jakata kawai ya kawomin,"πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

tsayawa sukai suna kallon kallo,dansu basu gane kan zancan nata ba.

yusura dake kwance adaki kunnenta ya tsinkayo mata muryar tasleem na fadin ya Auwal.

A zabure ta fito da gudu,carab idonsu ya hadu ita da yaAuwal din,da gudu ta juya ta ciccibi bokiti cike da ruwa tayi hanyar toiletπŸ˜†


"ke gidan uban wa zaki daga ganin mutane?"cewar yaya Auwal sanda ya hangi yusura.

Agigice ta waigo,jikinta na bari,tace baki na rawa.

"zan zan zan kama ruwane yaya"

Mamakine ya kama Auwal da Ammar jin tace zata kama ruwa amman da bokiti gudaπŸ˜†

"Ko kashin kwance kikayi inaga bokiti guda yayi yawa gurin kama ruwa,"cewar Ammar dake gefe.

dayake yusura akidime take dan haka dauka tayi Auwal dinne yayi tambayar,a rude ta shiga bashi amsa.

"eh wlh ya Auwal tun daren jiya nake kashin ka tambayi tasleem"



Ammar jin ze fadine yasa ya dafa bango ya shiga kyakyata dariyar data taru acikinshi.

Itako tasleem jin yusura ta ambaci sunanta,tunkan auwal din yay mgn tace.

"eh wlh ya Auwal tun jiya muke kashin,nida ita"πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†

Tasleem ta fadi hakane sabida a tunaninta sauki zaawa yusura sabida kashin,dan haka itama ta sa kanta aciki dan tasamu rangwameπŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†πŸ˜†


Auwal ganin gaba daya sun zarene yasa ya wuce su ya shiga dakin umma wacce ke dakin tana ta faman shan dariyar su tasleem.

Shide ammar ko tafiya ya kasa,dan dariya.

tasleem na ganin Auwal ya shiga dakin umma ta mike a 360 ta fice daga gidan ta nufi gidan su kawarta *JAMEESHA*


Yusura ganin tasleem ta fice ne yasa itama ajiye bokitin kama ruwan😁😁ta falla da gudu zata fice.

Cike da zafin nama ammar ya damko hannunta,hakan yasata dawowa baya da karfi ta fada jikinshi.


dukansu shuru sukai suna kallon juna,se alokacin yusura ta ga ammar dan ita tun dazu Auwal kawai take ganiπŸ˜†πŸ˜†.


Muje zuwa.



Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA.........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*ZAHRA SURBAJO*

*Instagram @zahra_surbajo1,domin samun post dina da wuri follow my ig acct*


*Dedicated to Billy Shantally*


*nayi mistake din number last page yanzu 24 zamu tashi*


*24*


"shine zaki tafi bayan kin ganni?"cewar ammar bayan ya saketa.

Murmushi tayi ta dukar da kai sannan tace.

"ba haka bane ya ammar,kawai de inason in tseratar da lafiyata ne"

Murmushi yayi sannan yace.

"yayi kyau,to jirani in gaida umma in fito"

Yana fadin haka ya juya ya nufi dakin umman bayan sun gaisa Auwal zama yayi suka ci gaba da hira da umma.

Shiko Ammar ficewa yayi zuwa gurin yusura da ke kofar gida tana jiran ko ta kwana,dan ta kasa imanin jiranshi acikin gidan.


Fitowa yayi ya sameta tana leken cikin gidan yace.

"tsoron ki yayi yawa Wallahi"

Murmushi tayi tace.

"tsoro halak,bazaka gane bane ya Ammar,ya Auwal fa so yake ya fasa jikina kamar yadda ya fasawa tasleem"

"ayko da yaga masifa dan bazan yarda yacimin mutuncin jikin ki ba wallahi"cewar Ammar yana dariya.

Cikin rashin fahimtar inda zancan nashi ya nufa tace.

"to meyasa ya Ammar?"

"sabida inasonki yusura,ina son ki zama matata ta aure,kinga ko inya dakeki ayni ya daka"ya bata amsa cikin wata murya da bata dauka yana da ita ba.

Juyawa tayi da sauri zata bar gurin,hannunta ya ruko yana murmushi yace.

"kar ma ki fara andena wannan yayin tun su xianoxy suna matasa,bare yanzu da suka tsufa,kawai in kina sona ki amsa min pls"

Kokarin kwacewa take shi kuma yaki sakinta,cikin muryar shagawaba tace.

"pls Ya Ammar lets me go"

"Answer me first bf you go"ya bata amsa yana murmushi.

Ganin da gaske baze kyaleta bane yasa tace.

"Ina sonka Ya Ammar"cike da kunya tayi maganar


Sosai yaji dadin amsa mishi da tayi,addua da fatan alkhairi yayiwa soyayyar tasu,ita de yusura da so samune ya barta ta tafi gidan su Binafat amman yaki barinta ya tsareta da hirar soyayyarshi.


Malama tasleem ko ba sallama ta shige gidan su jameesha tana haki.

Jin motsin shigowarta ne yasa jameesha lekowa taga waye.

Ganin tasleem na haki ne yasata mamako gamida karasawa gurinta tace.

"yarinya me kyau lafiya kuwa kike?"

"hmm bari kedai,annoba ce ta sauka agidanmu,shiyasa nake gudu"cewar tasleem cikin alamun gajiya.

"Annoba wacce iri kuma tasleem?"jameesha ta tambaya a dan tsorace.

"Yaya Auwal ne fa yazo"

Dariya jameesha tayi sabida tasan labarin dukan da ya musu kwanaki,cikin dariya tace.

"kice fiya fiya maganin kananan kwari"

"koma de me zakice eh shine yazo,dan haka bazan koma ba se anjima in ya fita"

Dariya jameesha take ta mata haka taja hannunta zuwa gurin mamanta dake daki.


Yusura da Ammar hirar soyayya tayi dadi,dan haka daukarta yayi a mota suka shiga zaga gari.

Auwal fitowa yayi daga dakin umna,ganin ba kowa agidanne yasa yagane sun gudu sabida tsoronsa.

Murmushi yayi daya tuno diramar da sukayi.

Dakin zaure ya wuce,ya rage kayan jikinshi,dan so yake yay wanka,

da yake akwai bayi a jikin dakin shiga yayi yayi wankan da ruwan sanyi dan yasan in yace ruwan zafi ze jira bame dora masa se umma shiyasa yayi da na sanyin.


Kanin jameesha da Tasleem tasa gadi in yaga fitar bakar motar kofar gidansu yazo ya fada mata,shine yaga wucewar Ammar da yusura,dan haka da gudu yaje ya shaidawa tasleem masu motar sun fita.


Da sauri ta mike taiwa su jameesha sallama ta nufi gida cike dajin dadin zata shige daki kamin su dawo.

Koda tazo kofar gidan sake tabbatarwa tayi basanan,kai tsaye ta shige cikin gidan.

Har ta wuce kofar dakin zauran,se ta dawo ganin kofar dakin turota kawai akayi.

Zuciyarta ce tabata shawarar ta tura kofar ta leka taga yawan kayan dasu ya Auwal din sukazo dashi dan ta fahimci ko zasu jima kan su tafi.

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Turawa tayi a hankali,ta tura kanta ciki,batare da tunanin komai ba.


tana shiga laptop ta gani akan katifar dakin,jikinta har bari yake ta karasa gurinta.


Budewa tayi gamida adduar Allah yasa ba password.

Ayko tana budewa lafiyayyen hoton ya Auwal ne a fuskar yana murmushi.

Ay budar bakinta se cewa tayi.

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

"An fa mori fuskar zuciyarce baa mora ba,"

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

sake kallon hoton tayi sannan tace.

"bakar zuciya kamar firauna,in banda dukan mata a boobs ba abinda ya iya,dan rainin wayo kuma wai yazo dressing sabida tsabar iskanci,sunan yana likita amman besan ran mace na hade da boobs dinta ba,wlh in ya kuma duka na,zesha mamaki,"ta karasa maganar cikin nuna masa yatsa.

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚


Auwal da tun shigowarta ke zaune yana shafa mai,kallonta kawai yake yana dariya a zuciyarshi,dan yasan da zata ganshi yanzu may be tayi kashin da tace.

Hankali kwance ta shiga cikin laptop din tana ta bincikenta,tanayi tana lekawa ta window gudun kar ya dawo ya sameta.

Har ya gama shafa man tasleem bataji motsin shi ba.

Gashi kayan daze saka akansu ta zauna,dan haka nufarta yayi yace.

"Dan dagamin kayana zan saka"

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚


kuyi hasashen next page.

Muje zuwa



surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAHRA SURBAJO*


*IG @zahra_surbajo1*


*tun ina rubuta surbajo na dena tura novel ta pc,kudena wahalar tambaya bana turawa iyakata in tura group sabida nasan inada masoyan da inkun wuni tambaya zasu wuni turawa,Adding numbers a group ma banayi sauran admins dinne keyi,so ku dinga tambayarsu don Allah,kaf admins dina bame wulakanci,kuna tambaya zasu saku,pls,inkunji haushin fadin hakan kuyi hkr,gaskiya na fadi*



*dedicated to billy shantally*



*25*




Cak tasleem ta dauke hannunta daga kan laptop din.

Sede yadda jikinta ke rawa zaka dauka ranta zaa zare.

Mikewa tayi tsaye ba tare data juyo ba,hannu a sama alamun tayi saranda.

Waigowa tayi bakinta na makyarkyata,tanaso taga inda gaske muryarshi taji.

Koda ta waiga,tsaye yake dagashi se gajeran wando se tawul dake rataye a wuyanshi.ya kafeta da shanyanyun idanuwansa.

"ya ya ya ya ya ya ya au........."tasleem ke kokarin kiran sunanshi amman ta kasa hada kan sunan.

Idanunta ne suka fara yin sama,ga wata shakuwa data kamata.

Luuuuuuuu ta tafi zata fadi,da mahaukacin gudu Auwal ya isa gareta ya tareta ta fado jiknshi.

Jijjigata ya shigayi yana dan marin kumatunta yana fadin.

"ke ke tasleem,tasleem tashi ba abinda zan miki open your eyes pls"yana fadi yana girgizata.

Amman ina ko motsi batayi,Auwal sosai ya gigice rasa abinda zeyi yayi,janta yayi zuwa gefen katifar ya zauna sannan ya kwantar da ita kan cinyarshi,yana ci gaba da kiran sunanta amman shuru kakeji.

Ruwa ya mika hannu yadauka ya bude ya shafa mata a fuska amman dif kakeji.

Fifita yake mata amman tasleem kamar gawa,zuwa lokacin zufa har diga take ajiikin Auwal.

Ga shi Ammar ya fita da mota bare ya kaita asibiti danshi gaba daya ya gama susucewa yama rasa abin yi.

Zuwacan tunaninsa ya basa wata shawarar,dan haka dagota yayi ya rungumeta da kyau ya hada bakinshi da nata ya shiga hura mata iska ta cikin bakin.

Hhhhh ay su @xianoxy sabida irin wannan agajin gaggawan aka shiga aykin likitancinπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚.

Tari ta fara yi da karfi dan iskar taso kwareta.

Idonta ta bude a hankali tana kallonshi.

Sakale yayi da ita ahannunshi labbanshi akan nata,yana kallonta.

Tsananin mamakin inda take da kuma jikinta da ba kwari ne ya hana Tasleem yunkurin kwace kanta ajikin Auwal.

Komawa tayi kamar wata wawiya,ido take zarewa bada wasa ba.

Yadda take kada idonne ya shagaltar da auwal gurin kallonta.

Kamar wacce aka tsikara ta tuno a kan cinyar wa take.

Da dukkan karfinta ta shiga kiciniyar kwacewa tana kuka tana fadin.

"wallahi bada kai nakeba,don Allah kada ka dukeni,kayi hakuri ya Auwal don Allah karka dakeni kaga batamin jiki kake da duka mijin da zan aura baze ji dadin ganina a haka ba"


Shi yadda take motsa bakin ma burgeshi take,itako dauka tayi kallon da yake mata duka zata sha.

"to naji ki natsu ba dukanki zanyiba"ya furta a kasalance.

Ido ta ware tana kallonshi,bakinta na kakkarwa,tace.

"wlh matukar ina kan cinyanka bazan taba natsuwa ba pls ka kyaleni na gudu don Allah"tayi maganar hawaye nabin fuskarta.

"is ok zan kyale ki amman ban amince ki fita ba kinji ko"

Yadda take gyada kai kai ka rantse,kadangare ne ya hangi abincin manjaπŸ˜‚.

Sakinta yayi,da gudu tayi birgima ta sauka akan cinyarshi,kamin yayi mgn,tuni se bayanta ta ranta ana kare tayi cikin gida.

Kai tsaye dakinsu ta fada,kan gado ta haye ta kwanta tana ta jero ajiyar zuciya.

Bayan fitarta murmushi Auwal yayi ya mike,yaci gaba da kintsawa.

Sosai kayan sukai masa kyau,ba kadan fa,kyanshi da tsarin zubin halittar jikinshi suka kara fitowa.

Takalmi yasa sannan ya fesa turare,yaja kofar ya nufi cikin gida dan ya kara firgita yar darun shiπŸ˜‚.


Umma ya tambaya ina take ta sjaida mishi tana dakinsu dan haka dakin ya nufa,cikin takunshi me burgewa.

Daga labulen kofar yayi ya shiga,lokacin tana zaune tana hada kayanta a jaka.tana fadin.

"wallahi bazan zauna ba gwanda inje kauyenmu yako in kaiwa inna uwani ziyara,in ya tafi na dawo,dan naci gaba da zama ciwon zuciyane ze kamani"tana maganar tana share hawayen ta.

Tsayawa yayi yana binta da kallo,sam beji dadin tafiyar da takeson yi ba sabida shi.

Motsinshi taji ta waigo,a gigice ta mike rike da kayan undies dinta da takeson sawa cikin jakar,kan gadon ta haye ta mike tsaye takai karshen bango,jikinta na tsuma.

Wani kallo ya wurga mata wanda yasa tsigar jikinta tashi,da sauri tayi kasa da kanta.

Takawa yayi ya taka shima yahau kan gadon so yake yaga me take boyewa a hannunta da tayi baya dashi,ayko hakanne yasa ta sake boye hannun nata abayanta,

Daya lura da gaske bataso yaga abin hannunta tsayawa yayi yana kallonta yace

"tunda bazaki bari in gani ba to sakko ki zauna zanyi mgn dake kinji ko"

Ba musu ta sauka ta zauna gefen gadon tana kara boye hannunta,nanko gurin sauka batasan yaga abinda take boyewar ba.

Sauka yayi shima ya zauna akusa da ita.

Azabure ta sauka kasan gadon tana binshi da kallo.




muje zuwa.



Surbajo for life.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*KARAN BANA...........*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€



*ZAHRA SURBAJO*




*Maman Gidado,tawa ina gaisheki,kuma ina ganin kima da girma da darajarki fiye da tunaninki,kece farkon fara ganina face to faceπŸ˜‚kaf social media,ina alfahari da hakan my sweety,wallahi ina matukar kaunarki,Allah yabarmu tare ya tsaremu ya tsare mazajanmu da zuriarmu daga sharrin duk abun ki,we are together for ever😍😍😍😍*


*Dedicated to Billy shantaly*

*whatsapp no dina kenan,08093235081 gaisuwa kawai,karkice insaki a group karkice in turo miki novel,ba nayin daya daga cikiπŸ˜…,ko kin kira bazaki samuba,whatasapp kawai nakeyi da ita*

*Ig @zahra_surbajo1*


*Wlh na rasa nomba dinki wacce kika bani recharge card,na gani na gode,Allah ya kara arziki*



*27*


Auwal duk yadda yake tunanin lamarin tasleem ze zo masa da sauki abun ba haka bane.

Duk yadda zeyi wajen ganin ya cireta a ranshi amman abun yaci tura.

Ita ko Tasleem zuwa yanxu ta fara son danmaliki so na gaskiya da Amana.

Sabida sosai yake nuna mata kulawarshi,shiyasa zuciyarta ta gamsu dashi.

In suna waya har bataso su dena sabida sonshi.


Yau ne ta bashi damar zuwa sabon gidan da suka koma,dan haka tun safe take hidimar tarbar shi,se girke girke take masa.

Ammar da yake ya samu Ayki a Abuja yasa,be fiye zuwa kd ba se weekend.

Shima ya Auwal yasamu ayki a Abujan Amman ya nuna bayaso yafiso yasamu a kd ta yadda ze kula da gidansu.

Mummy bata musa ba tasa a nemar mishi.

Shiyasa kusan kullum yana kd yana fama da zuciyarshi akan tasleem.

Fitowa yayi daga dakin da yake training,yaji kamshin girki duk ya cika gidan.

Da sauri yayi hanyar kitchen din dan dama yunwa yakeji.

A tsaye ya sameta tana soya kaza.

Tsayawa yayi yana kare mata kallo,kana daga bisani yayi gyaran murya.

Waigowa tayi adan tsorace.

Ganin shi ne yasa ta saki murmushi tace.

"ya Auwal a kitchen?"

Murmushi yayi ya fara takawa zuwa cikin kitchen din yana goge zufar jikinshi da tawul.

"eh nine da kaina,naji kin kaure gidan da kamshi yasa nazo naci nawa a kitchen din"ya karasa maganar sanda ya isa,gurin kulolin abincin yakai hannu ze bude.

A zabure tasleem ta karasa kusa dashi,ta ruko hannunshi.

Waigowa yayi yana kallonta yana murmushi.

Ita ko cikin inda inda tace.

"don Allah ya Auwal karka taba wainnan,na bako na ne,ka bari in yunwa kakeji yanxu zan dafa maka indomie"

Maganar tata dariya ta bashi,dan haka yana dariyar yace.

"ni zaki dafawa indomie,cemiki akai ni yaro ne?,wannan wanne bakone da yafini a gurinki da bazaki bani abincin naci ba?"

Cikin murmushi tace.

"ya Hisham ne ze zo anjima,kuma yacemin anan zeyi dinner lunch shiyasa"

Take yanke annurin fuskarshi ya kauce,zuciyarshi ta shiga tafasa azuciye ya fisge hannunshi daga nata ya juya ya fice daga kitchen din.

Tasleem tsaye tayi tana bin bayanshi da kallo,tanason tasan me yasa yay fushi,ganin ta rasa amsa ne yasa ta daga kafada sama,ta juya taci gaba da girkin ta.


Auwal ko gaban shi be gani haka ya haura sama,dakinshi,kan gadonshi ya fada,yana huci.


"Dole in dauki mataki,wlh ya hisham bazaka samu tasleem ba,nasha bar maka abinda nakeso,amman bazan bar maka tasleem ba,zanyi duk me yiwuwa wlh"

Yana

6 / 14