Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
gaba daya ya rude fadi yake.
"haba *AUWAL BUKAR BORNO*, ka dawo cikin natsuwarka mana,yau ka fara ganin watsatstsun yanmata da maza,pls be a man mana"
Sunan da aka kirane yasa yusura fitowa da gudu daga inda ta boye,hannunta rike da glass din fuskarta data cire.
Muje zuwa
Surbajo for life
ππππππππ
*KARAN BANA.......*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*A gaskiya comments dinku baya gamsar dani,shiyasa kiwyar in yi page biyu nake,inaga in wanda ya rubuta be gaji ba me comments ba abinda ze gajiyar dashi,π*
*Dedicated to Billy Shantaly*
*15*
Baki a bude yusura ke kallonsu,so take ta gano waye auwal din acikin su.
Shima auwal cike da mamaki yake kallon yusura,dan dazu be ganeta ba sabida glass din fuskarta,se yanzu ya ganeta.
Da kyar ya iya cewa
"yusura"
Wata kara ta saki gami da runtumawa da gudu ta rungumeshi,se yanzu ta gano yaya auwal din nata,da muryarshi ta gane shi.
Kuka take sosai ta rukunkumeshi,tana fadin..
"Yaya Auwal dama kana raye bakin ciki ke neman kashemu?"
Kanta yake shafawa hawaye na bin idonsa ya gaza mgn.
Suna haka direban da aka turo daukarsu ya iso dan haka jansu ammar yayi zuwa mota suka bar airport din.
Gidan su yusura sukasa direban yakaisu,inda har yanzu yusura na jikin auwal din tana kuka.
Da sallama suka shiga gidan,umman tasleem ce ta amsa musu.
Itama bata gane auwal ba,dan haka sannu da zuwa ta shiga yi musu.
Seda ya duka yana gaisheta ne ta zabura tace.
"wannan ko ba auwalu bane?"
"ni ne umma"auwal yabata amsa.
Dan tsananin farinciki batasan sanda ta kamo hannunshi ta rike tana kuka ba.
Dakyar tayi shuru,sannan tace.
"kasan maryam bata ko?"
Runtse ido yayi wasu hawaye nabin fuskarshi,yace.
"na sani umma"
Da sauri yusura ta juyo tana kallonshi,tace. "yaya taya kasani?" Wasu hawayen ya share sannan yafara basu labari. "A yadda momy ta shaidamin,tace sanda aka kaini asibitin 44 akan idonta akayi,sabida tana gurin,har zuwa sanda hisham yaki biyan kudin aykin kafata duk tana gurin lokacin mijin auntyn ammar ba lafiya tazo dubashi a asibitin.
Koda aka daukoni zuwa gida,ta biyomu abaya tazo taga gidanmu,
Bayan kun fita keda maryam,hisham ma ya fita shine ta shigo cikin gidan,tazo har dakin da nake ita da driver ta.
Bata jira komaiba tasa driver ya daukeni zuwa mota.
Ta maidani asibitin,inda ta tambayesu in akwai yadda zaayi ba tare da an yankemin kafa ba.
Shine suka shaida mata sede akaini india,canne akwai likitoci kwararru.
Mummy ta tafi dani abuja,tamin duk abinda yadace game da tafiya dani india.
Inda muka tafi nida ita da ammar domin ya taimaka mata kulawa dani.
Tsawon shekara guda mukayi acan,zuwa lokacin kuma maryam ta rasu,mun sami sakonne daga bakin auntyn ammar,wacce taganku a asibiti sanda maryam ta rasu.
Shine ta kira mum tana fada mata wata yar uwata ta rasu sabida sunganku tare dani a 44.
Koda tayi bayanin kamannin me rasuwar anan na gane maryam ce.
Nayi kuka sosai da rashin adalar matata wacce har gobe nake kewarta." Kukane yaci karfinsho shiyasa yayi shuru.
Dakyar ya daure yaci gaba. "tun daga nan nasha alwashin bazan dawo gareku ba se na samu ilimin dazan iya rungumar rayuwarku.
Mummy tamin komai ta turani kasar moscow nida ammar muka karanci fannin kiwon lfy.
Shekaranjiya muka dawo kasar,"
Sosai labarin ya girgizasu,bayan yan koke koken da baa rasa ba.
Auwal ya koma auwal dinshi na aynihi.
Wani wawan mari ya kifawa yusura wanda yasata sakin fitsari a zaune.
Seda ganinta ya dauke ya dawo,mikewa yayi yafara dukanta,da sauri ammar yayi kanshi ya rikeshi,yayinda yusura ta rukunkume ammar din tana kuka.
Da kyar umma tasamu auwal ya zauna yana huci tace.
"Auwal.me tayi maka daga zuwa se duka?"
Hawaye ya share yace.
"umma me yusura take nema daze sa ta fada harkar karuwanci? "
Daga yusura har umma sun girgiza dajin kalma
"wanne irin karuwanci kuma auwal?"
"umma inda kinga hamshakiyar karuwar danaga yusura tare da ita wlh sekinyi mamaki"
Muje zuwa
Surbajo for life.
ππππππππ
*KARAN BANA.......*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*Yawan sharhi yawan page*
*dedicated to Billy shantaly*
*16*
"Auwal yusura bata da abokiyar yawo se tasleem,tare suke fita tare suke dawowa,anya yusura kuwa ka gani"cewar umma cike da wasi wasi.
"ba tare da tasleem na gansu ba,ita kadai na gani tare da karuwar"
"wlh umma nida tasleem yaganmu,tare muka fita"cewar yusura cikin kuka.
Duka yakaiwa bakinta Allah yasota ta kauce.
"eh tare kuka fita,ina tasleem din take yanzu"inji umma.
Daburcewa yusura tayi tace cikin inda inda.
"suna tare da yaya hisham"
"what!!kina nufin wacce naganku tare tasleem ce?"inji auwal yana huci.
"eh itace"inji yusura.
Shide ammar tunda yusura ta cukuikuyeshi taki sakinsa,dan tama manta rike take da mutum.
Haduwar jikinshi da nata ya haifar da bakon alamari a rayuwarshi,shiyasa ko motsin kirki yagaza yi,
π su @xianoxy banza ta fadi,dama ina zaa motsaπ
Umma ta rude tanason jin abinda ya faru da tasleem din.
Auwal sanin da yayi in ya fadi mata ranta ze baci yasa yayi shuru kawai,yamike ya fice kofar gida.
Se alokacin ammar ya kama hannun yusura yafara kokarin rabata da jikinshi,
Se alokacin idonta yakai kan irin rukon da tai mushi,kunyace ta kamata da sauri ta sakeshi ta fara sosa kai.
Murmushi yayi mata gamida furta.
"Kin fa daku ba laifi"π
Dago kai tayi tana kallonshi,murmushi yayi ya kashe mata ido gamida daga mata gira ya bi hanyar fita daga gidan.
Zama tayi dabas akasa,sanyin dataji jikintane yasa ta tuna tayi fitsari da yaya auwal ya kifa mata mari.
Da sauri ta mike tsaye tana waige waige,lokacin ammar yakai bakin kofar fita,hango bayan rigarshi tayi ajike da fitsarin,wanda tasan besan dashi ajikinshi ba,kuma intabarshi ya fita zeje yayi sallah.
Rasa abunyi tayi kawai seta dauki buta tabishi da gudu,rigarshi ta ruko ta baya.
Waigowa yayi dan yaga waya rikeshi.
Suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kai.
Ta kasa magana,se wulkita idanuwa take,ga buta shake da ruwa ahannunta.π
Tsayawa yayi yana kare mata,kallo yana murmushi,ganin ta kasa magana ne yasa yace.
"to kin gama kallon nawa na tafi?"
Dago manyan idanuwanta tayi da sauri ta dubeshi bakinta na rawa tace.
"ba kallonka nakeyi ba,dama..."se kuma tai shuru.
"dama me?"ya tambaya yana murmushi.
"fitsari..."ta kasa karasawa.
Dariya yayi yace.
"ah lalle kin daku yanzu dan zakiyi fitsari kuma ay base kin fadi min ba"yakarasa maganar yana dariya.
Sosai kunya takamata amma bata da zabi dole tai mgn.
"aa dama na riga da nayi ne shine..."πππ
"shine me to"
"zansa maka ruwa"ta bashi amsa a birkice.
Dariya sosai ta kamashi cikin dariya yace.
"keda fitsari ni kuma zaa sawa ruwa?anya dukan be taba kanki ba kuwa"ya karasa maganar yana dariya.
Kuka tasa mishi abunta,ta turo baki gaba.
Tsayawa yayi yana kallon yadda kukan ke mata kyau,ganin da gaske takeyine yasa ya natsu,ya matso kusa da ita ya rike hannunta yace.
"shshhhh,"ya dora hannun akan bakinta.sannan yace cikin sanyin murya.
"fadamin abinda kikeso ki fadamin kinji kanwata"
Cikin muryar kuka tace. "Dama tun dazu a airport inajin fitsari inaso in na dawo gida nayi shine yaya da ya mareni fitsarin ya fito,ya bata maka riga,shine nakeso nasa maka ruwa"ta karasa maganar idonta arufe tana kuka.
Sosai yaji tausayin yusura,dan yasan in watace bazata taba kunyata kanta agabanshi tace taimasa fitsari ba.
Waigawa yayi yaga inda fitsarin ya taba,cike da kulawa yace
. "to amalala bude idon naki kisamin ruwan"π
Budewa tayi ta saukesu acikin nasa,da sauri tai kasa da nata dan bazata jure kallon shi ba.
Dukawa tayi ta wanke dede inda fitsarin ya taba,sannan ta dago takai dubanta gunshi,shima ita yake kallo da sauri ta yar da butar agurin ta ruga da gudu zuwa cikin gida.
Juyawa yayi ya fice yana dariya yaje yasamu auwal dake mota yana jiranshi,shiga yayi direba yaja suka nufi gidan auntynsu.
Ita ko yusura mamakin kyau da haduwar ammar take,dan ita bata taba ganin namiji kamarsa ba in aka cire yayanta Auwal.
Nida ke gefe nace dama yusura ta ina zaki gani bayan kinsaba ganin irinsu @xianoxy yan uku ashirin.π
Muje zuwa.
Surbajo for life.
ππππππππ
*KARAN BANA.........*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*Sharhi akan littafin ne ke karamin kwarin guiwa,*
*Dedicated to Billy Shantaly*
*17*
Tunda suka tafi Auwal ke faman huci,ya kosa yaji labarin abinda ya faru bayan tafiyarshi da har ya maida kanwarsa da kanwar matarsa karuwai.
Ammar cike da jin dadi yacewa Auwal.
"mutumina nifa naga iri a gidanku,dan Allah ka gyaromin wasan"ya fadi yana dariya.
Da sauri Auwal ya juyo yana kallonshi gami da furta.
"shashancin banza,kai yanzu har kaga abin so a tattare dasu,toni ba karamin mutum bane wlh bazan yada girma na ba,"
Dariya Ammar yayii sannan yace.
"Tab ayko ni naga abun so, ba kadan ba,kai da baka gani ba Allah ya makantar dakai,kuma wlh sena gabatar da kaina agurinta"
Cakumoshi Auwal yayi yace cikin fushi.
"kada ka kuskura kayi gangancin furta kalmar so gareta,dan faruwar hakan raini ze janyo mana kaji na fada maka"
Kwacewa yayi daga rikon da yay masa yace.
"look Auwal nifa ba ladifi bane,namiji ne ni lafiyayye kaga ko dole seda mace acikin lamarina,naga yusura tayimin ayadda nakeson mace ta kasance,kuma nima inada iko akan yusura matukar kai yayantane,dan haka wlh ba ja da baya,dan dama so daya take zuwa arayuwa"
Tsaki Auwal yayi yace.
"ay kai wlh adduar mummy ce ke natsar dakai amman da ba karamin dan taure zaayi ba"
Dariya ammar yake harda hawaye,cikin dariyar yace.
"yau naga masifa,daga na bukaci aure se kuma ace min dantaure,?eh de naji akuyancin da nai shekaru talatin da biyar ban yiba shine nakeso nayi da matata,dan bakin ciki kawai dan kai kasan hanya shine ni kakeso kar na sani"
Takaici ne ya hana auwal mgn,har suka karaso gidan autyn.
Aunty zainab tayi murna da ganinsu,ta rasa inda zata sasu.
Cikin lokaci kankani aka cika musu gabansu da kayan abinci kala kala.
Da yake sun kwaso yunwa,zama sukai suna cin abinci.
Bayan sun gama ne,suka zauna hira da auntyn tasu.
Sosai suka ji dadin yadda ta tarbesu.
Yarinyarta ce ta shigo cikin shigar daukar hankali,da dan gudunta taje ta rungume ammar tai masa kiss a kumatu,gamida masa barka da dawowa.
Sannan ta isa gun auwal shima ta rungumeshi tai masa kiss din a kumatu,darab ta zauna kan cinyarshi,tasa hannunta ta sakalo wuyanshi,tana murmushi tace.
"yaya Auwal kayi kyau sosai moscow ta karbeka"
Auwal gaba daya ya daburce,zaman da zukekiyar budurwar tayi akan cinyarsa.
Ba abinda yafi daurewa Auwal kai kamar ganin yadda aunty tayi kamar bataga abinda yar ta tayi ba.
Ammar dake gefe dariya ce keson kwace masa yana maida ta,dan yasan anyiwa auwal ba daidai.
Cikin murmushi me kama da yake,Auwal yace.
"thanks you my sis"
Yarinyar me suna,zaitun,murmushi tayi gamida fari da idanu.
Ganin bata da niyyar dagashi ne yasa yace mata.
"sis me mummy ke baki ne kike da nauyi haka,nide dagani kar ki karya ni"
Murmushi tayi,gamida rufe ido ta mike ta zauna kusa dashi.
Gaba daya zaman gurin ya ishi Auwal dan haka mikewa yayi,yacewa Aunty zasu su dawo.
Suna fita kofar gidan Ammar yafara dariyar daya tara,cikin dariyar yace.
"kai mutumina yau fa zaitun ta mori cinya"yasake tuntsurewa da dariya.
Duka Auwal yakai masa gamida fadin.
"Ay kai dama dan iskane wlh,kuma bazan sake dawowa ba,"
Sosai Ammar kecin dariyar Auwal,a haka suka shiga mota zuwa gidan su yusura.
Tasleem ko tunda suka tafi da danmaliki hotel suka nufa.
Sosai danmaliki ya kwadaitu da tasleem,dan haka nuna mata manufarshi yayi a fili.
Tasleem tsoro ne ya kamata,amman ta daure,cikin dakewar murya tace
"baby,se rawar kafa kake,kadan jira zuwa anjima mana"
"baby kedince hot cake,bazan iya jurewa ba zuwa anjiman pls"
Murmushi tayi me kamar kuka tace,
"To amman ay ni ban shirya ba"
Dariya yayi sosai sannan yace
"ay shi dama baa shiri dan haka zan saki ki shirya da kyau"
Ganinfa da gaske yake ne yasa tasleem,shiga tashin hankali.
Kokarin hada bakinsu yake guri guda,ita kuma taki yarda,kwace kanta tayi ta fara ja da baya,yana binta.
Nanfa kokawa ta kaure tsakaninsu,idon dan maliki ya gama rufewa burinshi ya biya bukatarshi akan tasleem.
Wayyo tasleem,kuka take iya karfinta,zuwa lokacin ya cire rigar jikinta daga ita se dogon wando da bra.
Ganin ba sarki se Allah ne yasa tasleem bude kofar dakin ta fice da gudu.
Da yake tana da gashi me tsayi kuma ya sakko kan fuskaeta yasa bame ganin fuskarta.
Hannunta kare da boobs dinta ta fice daga hotel din a 360.
Tana isa bakin titi,Auwal da Ammar na isowa dede gurin cikin motar Gidan auntyn su Ammar zasu gidan su yusura.
Tofa ga Auwal ga tasleem ba riga abakin hotel.
Muje zuwa.
*Surbajo for life*
ππππππππ
*KARAN BANA........*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*πππππππko ina ka leka karan bana gaskiya yau naji dadin comments ba kadan ba kuma jin dadinne ma yasa na baku wannan page din yau,Allah yasa ku doreπ€£*
*Dedicated to Billy shantaly*
*18*
Dan malikine ya karaso bakin titin da gudu yana karasowa su Auwal suma na karasowa.
Fara jan tasleem yayi da yake unguwar GRA ce yasa ba mutane se jefi jefi.
Ihun take tana kai masa duka,shi kuma bawai yana janta dan yaje yayi iskanci da ita bane kawai beso wani ya kallarmasa ita a hakane shine yakeso ta koma tasa kayanta.
Ita kuma da yake ta firgita dashi ne yasa ta dunga yimasa kuka tana dukanshi.
Su Auwal har sin wuce,suka hangi ana cin dambe tsakanin tasleem da danmaliki.
Da Auwal be gane ko waye ba seda dan maliki ya waigo Auwal ya gane dogon wandon da yaga tasleem dazu dashi a airport.
Karar burkin daya takane,yasa tasleem da dan maliki waigawa gurin.
Bude motar yayi yafice zuciyarshi na kuna ya isa gabansu.
Danmaliki,tass ya gane auwal jikinshi ne ya fara bari kamar mazari yanaso ya ambaci sunan auwal amma ya kasa.
Shiko Auwal ko kulashi beyi ba,hannun da ya rike tasleem yasa hannu ya cire.
Janta yayi da duk karfinshi,yayinda ita kuma se kuka take,tanason kare boobs dinta ba hali tunda ya rike hannun.
Mota ya jefata,yana shiga be jira ammar ya shigo ba yaja motar da mahaukacin gudu.
Se alokacin natsuwa tazowa dan maliki ya tuna Auwal yatafi masa da tasleem.
Da gudu ya bi bayan motar yana.
"noooooo ka tsaya ka saukemin ita,dani zakayi ba ita ba"
Ina Auwal bemasan yanayi ba.
Ammar tsaye ya rasa guein zuwa dan haka waya ya ciro yakira auntynsa yay mata kwatancen inda yake ta tura masa direba.
Danmaliki da gudu ya koma cikin hotel din ya dauko motarshi yabi bayan Auwal.
Sede Auwal ya bace masa be ganshi ba.
Kuka yake harda hawaye sabida bakin cikin ganin masa tasleem da auwal yayi ba riga.
Zuciyarshi na zafi kamar zata fashe,ya rasa yadda zeyi.
Auwal ko da tasleem be zame ko ina da ita ba se tsohon gidansu na rigasa.
Akwai mukulli ajikin kofar gidan amman duka daya yay masa ya bude ya wurgata ciki.
Yana shiga ya maida kofar ya rufe.
Tasleem mamakin dawowar yaya auwal din take,dan ta ganeshi.
Auwal belt din jikinshi ya zare ya fara tunkarota yana huci.
Baya ta fara ja tana fadin.
"yaya me nayi naga kamar zaka dakeni"
Shimfida mata daya yayi a cinya,wayyo tasleem,ay tuni ta saki hannayen data kare boobs dinta ta fara sosa gurin.
Ci gaba yayi da dukanta yadda yaga dama,ihu take iya karfinta amman be kyaleta ba,seda jini yafara fita ajikinta sannan ya nemi wani tsohon turmi ya zauna akai,
Tasleem ko na kwance tana kukan bakinciki.
Wayarshi ya ciro yace mata. "bani number yusura"
Ba musu ta karanta mishi dan tana masifar jin tsoronshi yanzu.
Kira daya yusura ta dauka.
"yanzu kizo tsohon gidanmu ki sameni,in kika bata lokacina zaki sha mamkin abinda zan miki"
Yana fadin haka ya kashe wayar.
Wayyo yusura cikinta ne ya karta seda ta zaga sannan tazo tasha babban hijabiπta tafi kiran da ya Auwal ya mata.
Tayi gumi kashirban kamin ta isa sabida tsoron haduwa dashi.
Har ta iso kofar gidan bata dena ambaton Allah ba.
Tura kofar tayi ta shiga,gidan nanan yadda suka barshi sede kurar da yayi.
Ganin tasleem kwance jiki duk jinine yasa yusura fara kuka tun kan ta gama karasawa cikin gidan.
Ayko tana karasawa ya rufeta da duka itama seda yamata yadda yawa tasleem,sannan ya tirkesu su shaida masa abinda ya faru bayan baya nan.
Kuma yabasu tabbacin in suka masa karya seya musu abinda yafi haka.
Cike da dumbin danasani suke shaida mishi duk abinda ya faru.
Dan tsananin takaici seda yayi kuka.
Seda yadan natsu tukuna yace.
"gidan da ya baku yau zaku baroshi ku dawo nan,banzaye marasa hankali,ubanme kudinshi zasu muku,da har zaku zubarwa kanku mutunci sabida su,"
Haka yay ta balbala balai yadda yaga dama,sannan yace su sundawo kenan,zeje ya dauko umma da mubashshir,kan ya dawo su tabbatar sun gyara gidan.
Yusura ce me kwarin amsawa amman tasleem ba baka se kunne dan ba karamin dakuwa tayi ba a hannunshi.
Ficewa yayi ya kullesu acikin gidan,ya nufi wanxan gidan domin dauko umma da mubashshir.
Muje zuwa.
surbajo for life.
ππππππππ
*KARAN BANA..........*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*Wlh inajin dadin comments dinku sosai,Allah yabar mu tare ina yinku akoina kuke Allah yabar zumunchi*
*Dedicated to billy shantally*
*19*
Da kyar yusura tasamu ta daga tasleem suka shiga gyaran gidan wanda yusura ce karfin yin aykin dan tasleem har jiri ke dibarta.
Auwal na fita can gidan yanufa,koda ya isa be jira komaiba tafara jidar kayan sawar su yana kaiwa mota seda ya gama sannan yazo yacewa umma wacce tun dazu bakinta ke bude.
"taho umma kubar gidannan dan be dace daku ba"
Ba musu umma taja mayafi ta kama hannun mubashshir,suka nufi kofar gidan.
Suna fita sukaci karo da dan maliki yazo gurin yusura yaji ko tayi waya da tasleem.
Kallon kallo suka tsaya yiwa juna,zuwa can de danmaliki,ya fara murmushi ya matsa kusa da auwal yace.
"naji dadin ganinka Auwal Mun nemeka har mun gaji bamu ganka ba,ashe da rabon zamu gana "
Kallon arziki Auwal be masa ba ya budewa su umma kofa suka shiga ya shiga ya tada motar,sannan ya leko yacewa danmaliki.
"matsiyaci ga gidanka nan sun bar maka ka Ζara akan sauran,watakila ka mallaki dukiyar da karuna be mallaka ba"
Yana kaiwa nan yaja motar tabar dan maliki aguerin.
Ay da gudu danmaliki ya fada mota,yabi bayanshi dan yanaso ya fada masa inda yakai masa bakuwarsaπ. Auwal na kallonshi ta mirror yana binsa amman ko ajikinshi har suka karaso gidan.
Su Auwal shiga ciki sukayi,shima danmaliki kanshi tsaye ya shiga yana fadin.
"kai Auwal duk yadda kakeji da rashin kunya ni babankane,wlh ka taka a sannu,ni ba saanka bane,dazu ka tafi min da bakuwa ina ka kaimin ita,?" "na kaita gidansu"cewar Auwal yana huci. "kutumar uba,uban waye yace ka kaita gidan?kaine keda iko da ita koni da tazo gurina?"
Dariya Auwal yayi sannan ya kwalawa tasleem kira da yusura.
Jiki na bari suka fito rungume da juna,dan sin dauka wani dukan zasu sha.
Suna fitowa Auwal yace.
"Na fika iko da tasleem shiyasa na daukota zuwa gida,tasleem kanwa ce ga maryam matata uwa daya uba daya,da yake kai baho ne yasa baka gano hakan ba,na dauka bayan tafiyata hisham kwakwalwarka ta fara ayki ashe dakikancinka ba iya karatu ya tsaya ba,har akan muaamala da mutane kai dakikine,yusura da tasleem sun maida kai sekace rakumi sunyi wasa da rayuwarka yarda ya dace,sun tabbatar maka