Author : AXEEX Category : Romantic Story
damu ji nake kamar intambayeshi ina zai kaini kawai dai nadaure nai shiru hirarsu suke da salma sosai har mamaki abin ke ban dan banyi zaton yana magana ko ta minti biyu ba nayi zaton daga eh sai a'a yafi fade saidai hard kwashewa da dariya.
Wani gida naga munyi parking a dedai shi Salma ta bude ta shiga shima futowa yai har ya je bakin qofar ya dawo futo mana na futo na bishi jiki ba kwari.
Gida ne qarami mai kyau dedai zaman amarya ko ince nace daya da yaranta ya birgeni gidan duda alokacin duk raina a bace yake.
Zaune muke a falo yah nasir yana min bayani nan ne gidan da zaki zauna wannan sunanta salma yar Kaduna ce tana karatunta anan Buk so batasan zaman hostel sai ta kama haya na roqeta ne kan ku zauna tare ta kuma yadda murna nai sosai nagode mata aqallah yanzu ina da gurin zama.
Washe gari duk wasu kayan da mace kamata ke anfani dasu yah nasir ya sayon sai dai kayan sawa ne kawai duk dogayen riguna ne nai masa godiya ya tafi.
Ko zuwa yai gaisuwa kawai ke hadamu sai dai suyi ta firarsu da salma tun inta sani bana shiga har nafara sakewa dashi sai gashi ko batanan yakan zauna muyi fira har ya tambayen yan matsalolina.
A hankula yake kawon yan abu buwa na masu mahinmanci dake gida kaya ne dai yace inyi haquri dasu ahankula zai dinka wasu banji komi ba nace to.
Yau kam murna nake sosai dan yau yah nasir ya kawon wayata kullun da ita nake kwana nake tashi inata so ince ya daukon sai dai ina jin nauyinsa sai gashi ya kawon agida ba wanda yake da number ta dan haka baice in canza layi ba kawai dai ya amshi number ta ya ajiye a wayarsa.
Tunda ya fita naje nasata a caji 10% kawai tayi na kunna ta kamar yadda na zata message din Abokina ne ya fara shigowa bansanshi bantaba ganinsa ba anman azahirin gaskiya mun shaqu dashi sosai achat kawai muka hadu tun ina SS 1 muke chat dashi a Facebook.
Farkon haduwa ta dashi in ban mance bashine lokacin da Baba mahmood yai tafiya wato yayan mahaifina tsaraba shine waya da ipad sai yan sauran tarkace nai murna sosai duda ni bansan me zan dasu ba.
Washe gari na gama komi na kinkimi kayan tsaraba a jaka nai gidansu Walida wata Aminiyata yanxu tana Malaysia tana karatu tun bayan candy dinmu, ta tayani murna sosai kafin ta bude kwalinsu ta saka su a caji muka ci gaba da firarmu.
Wayar ce ta fara cika ta kunna mun muka sha selfie kafin ta dauko tata wayar dan ita tun muna Jss 3 take da waya ta ciro sim daya kin ga wannan sabo ne jiyama na siyoshi nai masa sub na 2month bari in bude miki email account ta budemin sannan aka buden Facebook da WhatsApp lokacin shima bai cika gari ba duk yawanci 2go mutane sai facebook din nai mata godiya ta rakoni gida dan maqota muke nai gida ta koma gidansu.
Da daddare bayan naci abinci na gama aikina kawai na dauko wayata na kunna data banbi takan WhatsApp na shiga Facebook nafara duba posting din mutane na dariya in dariya na tsaki inyi tsaki.
Tun budemin account da Walida tayi kullin sena hau facebook sai dai ba na magana da kowa banma taba shifa inbox dina ba, kusan kullin sena duba posting din mutumin har yazame min jiki dan posting dinsa masu ma'ana ne ko joke yai inka duba sosai sai kaga abin anfana.
Nakanyi commenting sosai aduk post dinsa wanda na rasa abin cewa kuma nakanyi liking.
Yau ina zaune bani da data kawai dai inabin previous post ne na mutane ina kallo sai dai nai nai gabaki daya suyi loading sunqi iya goman farko ne kafin Data ta ta qare kawai inbox na shiga inda ban taba gwada shiga ba sai yau tsawon wata biyu da fara chat dina.
Duba mutanen da suka min magana na shiga yi kamar me naga nashi manar sai dai nai nai ya bude yaqi hakan yasa na gane rashin data ne kudi na ciro daga account dina ta waya na kira walida.
Pls ya zanyi ne insai data tawa ta qare tai dariya eyye ai dayake data ce yau kin kirani tunda kikai waya baki taba kirana ba nai dariya to ni kirana kike eyye nan ta basar ta fadan yadda zanyi.
Kashe wayar nayi na sai Data din dan ganin saqon nasa sallama ce afarko sai qanwata shine kikaqi karbar request dina ko dan murmushi nayi duda kuwa bansan me yasani ba sauri nayi naje nai accepting dinsa.
Na koma nace amsoryy yanxu naga saqon sai dai me naita jiran replay shiru.
Sai da aka kwana uku sannan ya turo tun daga time din muka saba sosai harta kai ga ya amshi wayata dan yace shi yana japan yana karatu mukan gaisa hakan yaqara qarfafa shaquwarmu saidai abu daya ke hadani dashi in yace yazo hutu yaushe zamu hadu saima inkashe wayar indena hawa online gabaki daya sai na dedaici ya koma.
Yauma din tambaya ce qanwata kwanaki da yawa kin dena hawa online inna kira ki bata shiga ko dannace miki na dawo kenan nai murmushi kawai dan bani da amsa din bashi.
Bai cika tambayata abinda ya shafi personal life dina ba duda shi yakan dan fadan wani abun da ya shafeshi duda ban cika cewa komi kaiba.
Online na hau na bashi haquri mukasha firarmu.
Zaman gidan Salma ya fara gundurata gashi inaso inma yah nasir magana kan karatuna dan alissafina yanxu shine dedai lokacin da ya dace ace an fara admission duda nasan ba lallai insamu jami'a ba tunda nasan banyi post UTME ba sai dai nakasa.
Yau aunty Salma suke final paper murna take sosai duk yan nima ina tayata ji nake dama nice ita da sassafe taimin salma ta tafi makaranta.
Sai yamma liqis ta dawo daga makaranta ina zaune ina sana'ar chat dina ta shigo ta fada kaina tayani murna little sis exam tayi dadi kai anman nayi murna fatan Allah yasa adace tace amin kamin tace kuma Allah yasa afara asa'a nakalleta kawai bance komi ba.
Washe gari Tace in shirya zamu unguwa na shirya cikin doguwar riga yah nasir yazo ya tafi damu tafiya muke sosai mamaki na shiga yi ganinmu a BUK Aunty salma ta juyo ta kalleni kina mamaki ko nai saqare ina kallonta ta miqon takarda surprise na karba ina bude emblem din admission letter ce tawa bansan sa'adda na saki qara ba inamasu godiya.
Screening Mukaje ranar kam munna ba'a magana kowa yaganni yasan ina cikin farin ciki nan naqara san yayan nawa ashe shima yasan abinda nakeso wato in zama engineer godiya har gajiya yai da yimasa.
Bayan convocation dinsu anty salma ta koma gida qanwarta da batafi sa'a ta ba tazo itama tare zamu fara karatu inda ita zatayi MBBS su suna tsohon makaranta mu muna sabuwa.
Watanmu daya da fara lectures akayi bikin aunty Salma sai yanzu na gane alaqarsu da yaya Nasir ashe budurwar Amininsa ce da shi yake can university of ibadan yana koyarwa shi yasa yah nasir kular masa da ita har kaduna mukaje gurin bikin tai ko murna sosai.
Akan hanyarmu ta dawowa be naita sheqa amai ga zazzabi lokacin cikina watansa uku da wasu kwanakin hankalin yah nasir shida farida ya tashi sosai asubuti mukaje inda aka bashi tabbacin ai ciki gareni hankalinsa ya tashi danni ban fada masa ba agida kuma baiji ba dan bai taba tambayar inda nake ba.
Zuwa yai ya titsiyeni in fada masa gaskiya wayamin nan nafada masa ai dalilin korata da akai kena yaita fada me yasa tun farko ban fada masa ba ai da tuni ya zubar nidai nai shiru dan daman zubarwar ne banaso ayi.
Da muka koma gida yai yai inyadda azubar naqi ya haqura ya qyaleni kawai.
Shine ya dauko min ummi diyarki dan min akace akace tunda ga ciki ga karatu ita kuma farida itama ba zama ta cikayiba tunda tare yawanci ma muke fita nakanma rigata dawowa wataran aiki duk yabi yamin yawa.
Karatu yana zuwa mn da sauqi dan ba qarya ina gane abu indai an koyan gashi kuma yah nasir na iya qoqarinsa na koyamin.
Lokacin da muka fara lectures na rage chat cikina bai fito ba sai dai yana dan ban wahala haka nake jurewa akwai wani malaminmu maisuna Abbakar tun gani na dashi na farko naji inasansa sai dai shi din irin malaman nanne da ko dariya baya yi magana ma kamar siye yake sai yaga dama yakeyi ni kadai nasan me ke damuna game dashi.
Ko gaisheshi nayi sai yaga dama yake amsawa kallo ban isheshi ba balle insa ran zai soni inna koma gida bani da aiki sai kuka in dare yayi musanman duk lokacin dan cikina ya motsa na tuno da malaminmu sai kukana da tsanar yah mahfuz ta cikan rai dan nasan babu tayadda za'ai yasoni balle ya aureni tunda masu mutunci da basuyi cikin shege bama suna nuna masa so abanza.
Lokacin da na haihu yah Nasir yasama yaron mahfuz ni kuma azahiri na tsani me sunan shi yasa nace da nawane ni Abbakar nasa masa bai ce komi ba yadai qi kiransa da Abbakar sai mahfuz yace in yaro ya girma ta zabi sunan da yake so.
Sati biyu da haihuwar Abbakar yah nasir ya kawon takardar gidan da muke ciki ya bani yace yanzu yazama nawa watansa guda da siye so dama yake sai na haihu nai nai ya karbi abinsa yace ina inya mutu kuma ina zani nai murmushi kawai dan baisan inada kudi da yawa ba.
Koda yake lokacin da mahaifinsa ya bani ATM dina yace kudadena suna ciki in ina buqata ba wanda ya sani dan yasan halin matarsa ko sauran yan uwansa bai fadawa ba.
Yadai min kwatance inda wani abokinsa yake yace sauran abubuwa na da inda zan sami mahaifiya duk innaje zan samu dai dai ni ban taba bi takan hakan ba dan ban dauki abin da mahinmanci ba.
Lokacin da nahaihu ne Abokina Abbakar ha facebook ya takura sai mun hadu dole na nemi izinin yah nasir ya yadda dan daman yasanshi dan har gausawa sun tabayi munyi dashi zaizo inbashi shawara dan nasaba bashi shawara yaji dadinta sai dai yace alokacin yafiso muhadu face to face dan matsalarsa babbace.
Lokacin da na fita dan ganinsa sai ganinsa nai da yah mahfux wanda daman yace min da amininsa zaizo dan yasha fadamin kusancinsa dashi abu nagaba da ya tsoratani shine ashe shine lecturer dinmu danake masifarso.
Koda na koma daki na shige nakira tah nasir na fada masa komi yazo ya kori yah mahfux da Abbakar matsayin besansu ba duda dakewa kawai yai.
Lokacin da rikicin yah mahfux yai qarfine kan waini masoyiyarsa ce yasa yah nasir samo wani amatsayin mijina kanni bani bace ummun da yasani dole hajiyarsa ta yadda yasamu tabuwa.
Ganin rikicin mahfux yai yawa yasa yah nasir yanke shawarar aurena duda cewar yasan da nasan irin san da yakema Farida fada mata ne kawai beba danni ya tambaya kan yanake gani nace ai sun dace sosai yace kar in fada mata sai yagama nazari kanta saidai kawai ya bijiromin da batun aurensa.
Naqi yadda danni harga Allah matsayin yaya na daukeshi saidai shawarar da qawayena suka ban na amince zan aureshi dan na yadda bazasu ban shawara mara kyauba dan tun farkon fara karatuna na basu labarina duka sun tausayamin bakuma su sauyamin ba bankuma tabajin sun fadawa kowa va hakan yasa na yadda dasu sosai.
Sai dai mahaifiyar yah Nasir taqi yadda qarshema sai cewa tayi ina ita ai aure dole in auri Mahfuz ni kuma ganin haka yasa cikin daren na baro kano ummi tace muzo nan.
Innar Ummi ta nisa gami da share hawaye kiyi haquri Na zargeki kan abinda baki aikata ba ummu tai dariya bakomi inna ai hakan shi ke nufin ke uwa ta gari ce inna tai murmushi kawai.
Wasa wasa Abbakar ya gama karade maradi da yawo yau kwana uku anman ko alamun ummu babu gashi ko hotonta bashi dashi hausar yan garin ba cika ganeta yayi ba gashi su basa jin turanci ma sai France suke ji abin duniya duk yabi ya ishe shi hankan yasa yau ya yanke shawarar barin maradi zuwa wani garin
Kasuwar grand marshé ya fara shiga dake nan maradin danyin siyayya yan abinda ba'a rasa ba ya siya abinka da namiji bai wata iya siyayya ba ya fito ya koma unguwar da ya sauka mai suna kawo acan yabar duk kayansa sai abinda ba'a rasa ba ya dauka ya tambayi kwatancen tasha yai can.
Mota ya hau da yaji ana kiran niyame niyame bai wata tambaya ba yai shigewarsa shidai burinsa bai wuce yaga ummu ba yakusa minti talatin cikin motar kafin ta cika su yi gaba.
Ita ko ummu inna ce ta dafa ta tace to yanxu ummu zuwanku nan kina ganin shine dadai ummu ta gyada kai to anman me yasa baki nemi wanda mahaifinki yace ki nema ba ada ban niyar nemansa ba to lokacin da naso nemansa sai na tuna da abinda Abbansu mahfuz yace min.
Mutumin lauyansa ne yakuma fada masa duk sanda na nemishi hakan na nufin da wata matsala to ko gidan da su yah Nasir suke ne asaida dan cireni daga matsalar dan gida nawa ne to ni kuma tun kanma ahaifen suke cikin gida tayaya zance injanyo abinda zaisa subar gidan.
Inna ta gyada kai ai da sai kije kimasa bayani ba matsala bace kinaso ne kawai yakaiki gun mahaifiyarki ummu ta share hawaye kamin tace innar ummi ada inaso inje gunta da burina kullin bai wuce inyi candy inje inganta ba dan Baba mahmud wanda yake ayanxu babba agidanmu yasha fadamin zai kaini Jordan innai candy kafin ashiga tsakani na da duk yayun babana yakai yakawo cikinsu ba wanda yasan da zamana ko ya damu dani.
Inaso inga ummata duda ita bata damu dani ba tunda tun randa ta tafi tabarni kafin ta yaye ni bata kuma nemana ba saidai inna banasan inje in tada mata da hankali inna kinsar ba uwadda zata so ace yau diyarta ta haihu dan ya girma kuma bada aure ba inna ta rausayar da kai haka ne ummu.
Amma ga shawara kinsan kudi duk yawansu ana anfani dasu dole su qare kuma in sun qare baki da na baima mijina da sirikata zasu koreku ne ni kuma bazanso haka ba mai zai hana kuje cikin zender ku sassaro kaya inyaso sai kizo kike saidawa irinsu mai magi gishi fulawa dasauransu ki dinga sai dawa tiya tiya rabin tiya kai har gwangwani.
Ummu tai murmushi nagode inna da kika fahince ni kika yadda in cigaba da zama daku gobe sai muje nida meron inna ta miqe ni bari inje in dora sanwa.
Washe gari da wurwuri ummu suka fita su gwaggwo harda bada sauti alhalin ko ficika vata bada ba.
Siyayya sosai ummu tai suka hawo qurqura ta dawo dasu sai yamma liqis suka shigo unguwarsu mai suna unwala, daki gwaggo ta baima ummu wanda zata zuba kayan nata bayan ta vata tsarabar da tayo mata.
Zaman ummu gidan babu wata matsala dan sau da dama ma ita take bada abinda za'a dafa hakan yasa kakejinsu shiru ko fada malan musa ya dena dan zatonsa karyayi ummu ta tattara tabar gidan.
Shi ko Abbakar duk yabi ya gaji tun yana baza ido yaga anzo har ya gaji yai bacci sunyi azahar ahanya anman har lokacin basu isa niyame ba.
Awarsu goma sha biyu a tafe kafin sukai niyame garin ya birgeshi dan yafi maradi kyau da girma da anan tasha aka saukesu kafin ya fito daga motar.
Sai da ya fito daga motar sannan hankalinsa yadan tashi sai alokacin yafa tuna bashi da masauki ga gajiyar da yai sosai shi ba abin ya koma maradi ba wannan uwattafiya haka.
Can ya hango me shayi tafe irin buzayennan yai saurin kiranshi sai da yasha shayin wajen kofi hudu dayake irin qananun kofunanne sannan yadanji dadi ya bashi kudinsa shi kuma yai gaba inda yaga taron matasa gurin wani me saida kasa kasai.
Sai da aka dan watse ya masa salma sun gausa kafin mutumin yace anman dai ke daga nigeriya kike ko Abbakar yai murmushi eh mutumin yai dariya haba koda naji ai daga jin maganarki na huskanta yanzu ina anki zuwa hakanna na cikin almuru.
Abbakar ya nisa nazo neman qanwata ne da tazo nan sedai bansan inda zan sameta ba gashi na gaji da yawa wallahi kuma bani da masauki.
Mutumin yai dariya ayya ayya seki jirani in kammala sai muje can gidana na in baki masauki Abbakar ya washe baki aiko da na gode sosai.
Anan sukai sallah kafin mutumin ya goya Abvakar a mashin dinsa sukai unguwar francophonie wadda nanne mazaunin mutumin me suna muntari.
A gofar gida ya saukeshi ya shiga gida yafi minti biyar sai ga yaro da tabarma