Chapter 16 Reading ABBAKAR BOOK COMPLETE DOCUMENT by AXEEX.txt Arewa Novels

ABBAKAR BOOK COMPLETE DOCUMENT by AXEEX.txt

Author :  AXEEX Category :  Romantic Story

Chapter   16 / 20

45K to 48K   out of 57.6K words

sabida Allah kullin yana nanne.


Gabaki daya ya damu musanman ganin anyi bikin Yah nasir ba Amininsa ya kuma tambaya yah Nasir yace masa wayasan masa tun lokacin yakesan zuwa gidansu sai dai yana tsoron jarrabar Hajiyarsa dan inta mahfuz ne daman sun saba suyi su shirya.


Yanke shawarar zama abakin lokonsu yai ko zaiga aqallah wucewar Aminin nasa dan tabbacin lafiya yake sedai yau kwana hudu babushi bare labarinsa.


Zaune yake gaban hajiyar Mahfuz duk ta rame tai baqi yadda ta amshe shi ya bashi mamaki dan yayi zaton da fada ne sai wani nan nan take dashi.


Sun gaisa yake tambayarta mutumin me makon ta bashi amsa kawai sai ta fashe da kuka yai yai tai shiru taqi sai da tai me isarta cikin shessheqa take fadin Habu haqqine ke cina nakuma san bana kowa bane saina ummulkhairi da iyayenta.


Shi dai da ya samu tai shiru ya danji dadi kadan duda zuciyarsa cike take fal da tunanin me yasamu Aminin nasa "nace uhum Abbakar kenan Allah ya baka zuciya me kyau"


Hajiyar mahfuz bata boye komi game da halin da mahfuz ke ciki ba harda wanda data je gidan ta tadda matarsa, sai dai bata fada masa zuwa gurin bokan da taiba da dalilin zuwa Hankalin Abbakar ya tashi yasan mahfuz yana shaye shaye dan baya boye masa komi anman baya bin mata shi yasa lokacin ya fada masa game da ummu yaita masa fada yanzu tsoronsa daya kar matarsa ta saka masa cutar wannan zamanin.


Nan yaita lallashin hajiyar yana bata haquri yasamu ta dan dawo nutsuwarta kamin ya dora yanzu addu'o'i yakamata ayi tayi masa zansa a masallatai da makarantu ki yawaita masa sadaka da niyar Allah ya karya koma mene taji dadi sosai dan ita tama mance da batun addu'a din.


Kai tsaye gidan Nasir Abbakar ya nufa ya sanar dashi duk yadda sukai da hajiya shima hankalinsa ya tashi ya yadda da shawarar Abbakar tun daga lokacin su ka duqufa sosai ko sallah ce ta kai Abbakar masallaci sai ya roqi asa abokinsa a addu'a.


Sannu a hankali farraqun da aka masa da hajiyarsa yaji ya tsani zuwa gurinta ya kau dan yanzu yana zuwa sosai fiye da da, duda har yanzu cike yake da tsoron matarsa gidan nasu ma aboye yake zuwa.


Da zuwan da yake ne Babban wansu muktar yai anfani tofin da yake masa azam zam ya hada da dabinon ajuwa indai yazo se yasha in yaqi dole suke masa.


Awayo a wayo yayan nasa yake nusar dashi sallah dare in addu'o'i kamin kwanciya bacci da neman tsari dan shi din ba daga nan bane yasan illimin addini sosai kawai dai irin ansani ne bashi da anfani tunda ba'a aiki dashi.


Sannu ahankula tsoron matarsa ya fara barinsa har mamaki yake in yaga tazo ta tsaya masa aka tana bashi umarni kawai kallonta yake sedai ya kasa daukan mataki.


Hankalin Salma da hajiyarta yai mugun tashi ba kadan ba ganin har Niger sun kai sunan mahfuz gurin hatsabibin bokansu wanda duk wanda suka kai ya gama yawo anman kulin abubuwa qara tabarbarewa suke.


Yau sunyi da matarsa zaiyi tafiya zuwa university of ibadan dan yin wani abu murna take sosai dan ta gaji dashi sosai gashi tsoro ya hanata kawo kowa dan daya fita yake dawowa.


Wanda zasuyi tafiyar tare ke fada masa su bari se gobe hakan yasa ya wuce gidansu suka taisa da hajiya sukai yar fira kafin suyi sallama ya wuce gidansa.


Da ace nasan mahfuz yasan me zai tadda da tabbas da bazaiyi sha'awar zuwa gida ba hankalinsa yai matuqar tashi idanunsa duk ya rife bema san me ya rarumo ba yai kansu.


Duka kawai yake babu qaqqautawa ganin zai ita kashesu yasa kwarton yin ta maza yai waje a miliyan ya koma kan salma dake gefe a rakube tama kasa motsawa duka kawai yake tai mata lilis dagyar ta rarumi zanin gado ta arta aguce.


Biyota yai yana ci gaba da duka yana fadi Allah ya isa tsakani na dake na sake ki saki uku har farfajiyar gidan dagyar me gadi da driver suka riqeshi ita dai data samu tai waje adai daita ta hau se gidan ubanta.


Agurin Mahfuz ya zibe yana kwasar kuka shi kadai yasan abinda yakeji yanzu ransa bai taba yadda cewar inkayi zina da wata mace se anyi da wacce take mallakinka ba sai tau matarsa ta sunna kuka kam yayi shi bakadanba tausayin yaransa mata ya kamashi innalillahi wa'innailaihi raji'un yake fade kawai Allah ka temake ni katsayarmin iya nan wallahi nayi nadama ya Allah karka dorawa yarana abinda ni nayi sanbatu kawai yake.


Gidan ji yake gabaki daya ya zame masa kurku ku ba abinda yake gani sai matarsa da wani gidanma gabaki daya ya bari yai gidansu.


Cikin kuka yake fadawa hajiyarsu komi baima qarasa ba suka jiyo masifa a waje da sauri hajiya ta miqe tai waje Hajiya Batulu ke ta sirfa masifa salma na bayanta.


Fadi take ina Karimar take wallahi dukan da dan iskan yaronki yama yarinyata akanki zan rama mata ganin hajiyar yasa tai kanta gadan gadan aikan daga hannu tai zata zuba mata wayar dake hannunta aiko muktasir yako riqeta kul bazai yiwu kizo mana gida dan rashin mutunci kice zaki dakar mana uwa ba kinyi kadan.


Kamin ya qarasa tasakarma Hajiyar tasu nari itama taji kuwa an dauketa dashi wa zata gani mahfux ne namfa yaran suka mata lilis ita da salma sai da hajiya taga zasuyi kisa tasa baki suka kyalesu.


Hajiya batulu fadi take wallahi, Wallahi sai kinyi danasanin ni kika ma haka kinsan da cewar gabaki daya a tafin hannuna kike shirya karbar sakamakonki, hankalin hajiyar mahfuz ya tashi dan tasan me take nufi su kuwa yaran ina suka sani fadi suke abar mana gida yayanmu ya rabu da bunsurar yarinyarki ya wuta da kuda.


Kai tsaye maqabartar dan dole ta nufa daga gidansu mahfuz din yaron da ta baima aikin binne binne tace duk ya je ya haqo mata ya kawo mata yace an gama.


Inda ta sa aka kai na tsohuwar rijiya ma duk aka ciro ta tara shirgin asiri tim gabanta ta zuba musu kalanzir gami da kunna ashana tuni suka hau ci da wuta.


Tasaki wata dariya Wallahi hajiya karima dani kike zancen kin riga kinyi sake da kika bari ni nasan sirrin komi naki waike uwar san jiki sedai ki bada kudi ni inje miki gun boka inkuka miki aikin yadda nasa aka binne na haqesu yadda naje nayi miki kike rayuwar fantamawa kike mulkar kowa gidanki to kuwa kinyi kadan.


Tun safe hankalin Hajiyarsu mahfuz yai mugun tashi ganin Baba tijjani da baba usman matsayinsu na qannen mijinta me rasuwa da sukazo gaidata suke tambayarta ina Ummulkairi ne basu ga tazo gaidasu ba wato tunaninsu game da yar qanin nasu ya dawo yanzu in mahmudu ya dawo me zata ce masa wato wanda yake me matsayin babba gidan yanzu.


Tasan ko mijinta be kaishi san diyar qanin nasa ba.


Ilai kuwa yana dawowa yaran kowa yaje ya masa barka da dawowa yana ta zuba idon ganin diyar tasu sedai shiru bayan yai wanka yaci abinci ya debo tsarabarta yayo bangarensu wato bangarensu Hajiya karima tunda anan yasan take tun rasuwar mahaifiyarsu.


Dakinta ya shiga sai dai yadda yaga dakin ya tabbatar babu mutun aciki duk yayi qura yai cudun cudin.


Tun yayansa nada rai basu cika shiri da karima ba hakan yasa take shaskarsa afusace ya futo yake kwala mata kira ta fito da sauri ina kuka maida yarinyar nan cikin rawar murya take tambaya wace yarinya fa.


Cikin fada yake magana zan tambayi wata yarinya bayan ummulkairi ta gurin Yasir hankalunta yai mugun tashi tama rasa amsar bashi dan gabaki daya ta gama rudewa.


Nasir ne ya shigo jin rikicin da ake hankalinsa ya tashi daqyar ya samu kawun nasa yai shiru ya zauna ya masa bayanin komi game da ummu har aurenta yanzu sedai bai fada masa wata aura dinba.


Hankalinsa yai qololuwar tashi yanzu duk yaushe hakan ta faru bamu sani ba yama akai haka cikin kuka hajiya ke fadin abin duk tayi ya miqe yana salati wallahi karima kinban mamaki ashe zaki iya haka nasan duk bazai wuce kan wannan gidan ba da yake mallakinta to gabaki daya kinja muku kowa gobe zai bar gidan daman ai ba namu bane muna zaune dan iyayenmu ne yanxu tunda suma basa raye se abarma me gida gidanta.


Gidansu Abbakar


Sabo sosai da shaquwa me qarfi ta shiga tsakanin Abbakar da ummu kullin suna farfajiya tare duda yawanci da maryam ko ummi ake karatun anman kallonsu kawai kai kasan da masoya ne masu san junansu iya so.


Duk yadda Abbakar yai yayi da hajita tace ina itafa babu zancen tarewa yanxu dole se ummu ta gama katatu ganin da gaske take yasa zuwa ya sami kawunta ya rattaba masa komi.


Aikam yasha fada kanyin aure bada saninsu ba yaita bashi haquri yace zaije ya sameta yaje ya fadowa nasa kawunnan yace to.


Gidan qaramin kawunsa yaje ya fada masa dan yasan inyaje gidan wan babansa dukansa ne kawai bazai ba dan mutumin kwai fada.


Shima kawu Barau din da bai cika fada ba yau ya ta6a dakyar Abbakar yai ta bashi haquri har ya yadda zaije ya fadawa wan nasu.


Aiko dakyar yasha kan yayyen nasu suka yadda zasu saka baki akan auren dan nasu.


Hajiya ta yadda ummu zata tare da sharadin dole aje dangin ummu su san da batun auren ba musu suka amince.


Gidansu Mahfuz


Washe gari da sassafe Baba mahmud ya tara qannensa ya fada musu komi harda hukuncin da ya yanke sun yadda kan jibi iyanzu sun bar gidan agurin ma wasu cikinsu suka fara kiran motar da zata kwasar musu kaya.


Ba wanda bai jin jina halin da ummu ta shiga ba da tausayinta agurin suka yanke shawarar sanya cigiyarta dan nasir bai fadi inda take ba zatonsu ta bace yanxu, hankalinsu bai qara tashi ba sai jin abinda mahfuz yai wasunsu ma ji suke kamar su dakeshi tada kam yashashi harda masu cewa basu bashi tunda ya rasa wanda zai ci mutunci sai yar uwarsa.


Abbakar ne yazo gidan kan kawunnansa nason zuwa ganin su baba mahmud yai mamakin ganinsu gabaki daya mahfuz nafaman kuka.


Ada baba mahmud yace sedai in wani satin anman jin yace kan ummulkhairi ne yace su zo yau da yanma kawai.


Tarba sosai suka samu duda gidan a hargitse yake kowa na qoqarin hade kayansa ne sosai hankalin su Baba mahmud ya tashi kanjin har wani aure akama ummu bama da saninsu ba.


Budar bakin Baba mahmud se cewa yai ai ina maganar tarewa bai taso ba yadda akayi mata dole barin gidan nan ina da tabbacin dole aka mata aka mata aure dan haka kawai kuce ya bata takardar ta yarinyar mu nada gata in ta sami wanda take so to lokacin zamu aurar da ita.


Komi suka ma Abbakar bayani game da yadda sukai da iyayen ummulkairi aikam hankalinsa ya tashi sosai da kansa yaje yasamu baba Mahmud aikan rufe ido yai kamar be sanshi yahau yazauna sakin ummu dole gida Abbakar ya dawo ya sanar da hajiyarsa.


Itama hankalinta ya tashi taje har gida ta sami baba mahmud sun gaisa cikin mutunci ta masa bayanin komi yai murmushi fiddausi kenan nasan kun mana da kuka riqe mana yarinyar nan anman hakan baya nufin zamu biya ku tukwici da yima yarinya auren dole dan kawai danku nasanta.


Duk yadda hajiya taso ya fahinta ya kasa fahinta haka ta tawo gida rai babu dadi.


Ganin yayi duk yadda zaiyi ne kan sakin ummu Abbakar yaqi yasa yanke shawarar zuwa har gidansu Abbakar din ya dauko ummu ya kuma sanar musu tabbas qara zai shigar indai nanda kwana uku bai kawo sakinba.


A gidansu Abbakar tabar yaron nata Abbakar gurin hajiya dan ta yaye mata shi.


Ummu tai mamakin ganin gidan da ya kaita can unguwar karkasara me makom nan naqotansu Abbakar bata tambayi dalili ba dan ranta duk babu dadi bataso barin gidansu Abbakar ba tayi sabo sosai dasu bana wasa ba tanajinsu aranta anman batasan nunawa kawun nata iyakarsa.


Komi sabo aka saka mata adakinta ita da Abbakar dinta ahankula tadan fara sabawa da zaman gidan babu inda take zuwa dan anyi hutun sch balle tasa masoyinta a idanunta ko bacci basosai take ba cikin tunaninsa take.


Bata taba zaton tanasansa haka ba sai yanzu dan ada tana qoqarin yakice shi zatonta bazai taba santa ba anman yanzu da ta riga ta saba dashi ta saba fira dashi ya koya mata sansa ji take raba ta dashi kamar ta'addanci ne babba sedai ita batasan me zatai ba.


Satinta biyu gidan baba mahmud yaje ya amso Abbakar qarami dan ganin ummu taqi sakewa zatonsa ko rashin yaronta ne tunda Nasir yasanar masa tanasan dan dayawa.


Kwana biyu yaron ya saba da kowa dan baida rikici musanman gidan da yake da yara sunzo hutu jikokin gidan sai warkajaminsa yake abinsa.


Tunda ummu tazo gidan bata ta6a farin ciki irin na yauba taji dadi sosai Baba mahmud ne yazo yafada mata ta shirya zasu Jordan can gurin ummanta tai murna ba kadan ba.


Nan ta shiga hada musu komi dan gobe ne tafiyar ita da Abbakar dan su uku zasu tafi daga ita sai danta sai baba mahmud.


Yanzu abu daya ke damun ummu rashin masoyinta Habunta anman indai fannin iyayene duk cikin yayun babanta kowa nan nan yake da ita danma taqi sakewa dasu kamar da.


Sun shiga mota ta tuno ta dauki wayarta ta turawa Abbakar saqo pls izini zamu jordan a samu a addu'a afadawa hajiya.


Baba mahmud na kallonta tai kamar be ganta ba yace kawo yaron jeki kice ma kadija ta baki saqona tace tota miqa masa yaron tai ciki ya dauki wayar yana duba saqon.


Har ya turo amsa Allah yasaukeku lpy abar sona dan Allah kiyi wani abu kar a rabamu pls ajiye wayar kawai yai ganin ta tawo.


A Jordan


Bayan sun sauka mota ta daukesu sai gidansu ummanta kowa yaji dadin ganinsu musanman kakanninta sai washe gari aka dibesu zuwa gidan umman nata.


Tunda ta shiga falon ummun nata kishi ya rufeta ummanta ce jikin bango a hoto sai yara suma larabawa uku manne jikinta mijinta gefe tai saurin dauke idanunta daga hoton duk inda ta duba sune.


Yan matan biyu masu kama da ita suka fito dan ganin su waye ganinsu yasa komawa ciki da gudu dan kiran momy dinsu suka fito tare har namijin wanda da gani shine qarami befi 9years ba kishi ya rufe idon ummu hawaye ya fara kai kawo aidonta.


Wato ummanta ta ma mance da tana da yarinya a Nigeria tayi aure ta samu wasu ita ta badda marainiya ba uwa ba uba tunda ta yayeta ta tafi bata kuma nemanta ba.


Danta ta sura taja baba mahmud mu tafi nafasa banasan ganinta muje Kawai take fada tana kuka ganin bazai tafi bane yasa sakinsa tai gaba.


Dasauri umman nata tai gunta dan tana dan fahintar hausa ba sosai ba ta ruqota gami da dorata a kafadarta tana lallashi dakyar tai shiru.


Haba ummu kin taba ganin inda uwa ta mance da danta kina raina babu yadda zanyi ne.


Yaran sukaita kawo mata abu buwa wasu duk hotunan tane jiki tana qarama sunata murnan ganinta seda ta kula sosai taga ashe hoton farko ma kana shigowa shi zaka gani kamin nasu dukansu itace rungume jikin umman nata da alamu ma ranar da zasu rabu ne tadan share hawayenta kamin tace cikin harshen turanci dan larabcinta be kwari sosaiba.


Anman mum me yasa haki kuma wai wayata ba.


Ummu babu ce tasa tun bayan dawowata daga qasarku babana yai rashin lafiya sosai duk abinda muke dashi dana gadona duk ya qare gurin jinya har bashi muka dinga amsa qarshe ya rasu.


Shekara daya da rasuwarsa na auri babansu Nasrin shi ba wani me arziqi bane da zai iya daukan nauyi na inzo nageria albashi nama haka muke hadawa gurin kula da yaranmu da iyayenmu dan da nasa iyayen da nawa duk suna buqatar temakonmu.


Ummu ta kuma rungume ummanta tana qara bata haqurin fahintarta bai bai.


Koda Dahir ya dawo bakowa falon sai ummu yana ganinta ya ganeta dan yasan basu da dan uwa baqar fata sai diyar matarsa bayan mugun kama da sukai da matar tasa.


Da sauri ya qaraso ya rungumeta yana fadin ummulkhairi ya kuma dubon fuskarta dadi ya cika ummu tabbas ummanta bata mance da ita ba tunda har mijinta da akasan larabawa da kishi yasan da ita.


Watanta guda cif taji dadin zama dasu sosai soyayyar uwa kam se yanzu tasan me ake nufi da ita dabadan tanasan mijinta ba babu yadda za'ai ta yadda tabi baba mahmud Nigeria.


Sunyi shawara dashi kan tanasan kudinta na account dinta ya cire mata zata baima ummanta dan ta fusksnci suna wani hali tunda ita ba abinda take dasu ya amince.


Aikam tasha albarka dakyarma umman nata ta yadda suka

16 / 20