Author : AXEEX Category : Romantic Story
shi ba dan kuma Allah.
Ya miqo hannunsa gun hajiyarsa yace hajiya ki yafemin cikin kuka take fadin na yafe ma Abbakar anman bazaka mutu ba kaji sannu a hankali nunfashinsa ke qasa tuni tari ta turniqeshi Nasir yai waje ya kira doctor duk aka ce su fice.
Jiki a salu6e doctor ya fito ummu tabishi tana tambayarsa jikin Abbakar yai mata banza nasir ya bishi da sauri.
Kasantuwar yasan Nasir yasa shi tsayawa Baka fada mana komi ba kayi gaba yakamata ka fada mana jikin nasa doctor din ya dan share gumi da fadin am sorry we lost him abinda ummu taji kenan ta zube agurin kowa har doctor din akayo kanta.....
[1/13, 4:28 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[1/13, 4:32 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR*
*PAGE 210---220*
Cigaban labari
Kai tsaye mota sukai da gawar Muktasir da driver suka kama ma Nasir suka saka shi ciki me mota ya tsinki ganye ya maqalama mota alamar sun dauko gawa ne.
Mahfuz ne yai ta maza ya miqe yai waje gurin hajiyar Abbakar yai da take ta faman kuka umma tashi muje a hada shi agabanmu dan muyi sallamar qarshe.
Ta dube shi ido jawur cikin da shasshiyar murya take magana pls mahfuz karfa ka fadan da gaske ya mutu din ya dafa ta nima ban yadda ba gani nake kamar mafarki ne sedai yanzu na yadda tunda sun tafi dashi ki taso muje kar akaishi.
Miqewa tai tabishi abaya motarsa da yazo da ita suka shiga ya jasu sai gida.
Ita kuwa ummu Allurar da aka mata ta fara sakinta firgigit ta farka cikin kuka gami da qoqarin miqewa Farida tai saurin riqota tana girgiza mata kai alamar ta koma cikin zafin nama ta tura farida gami da tsinke drip din dake jikinta.
A sukwane ta miqe tai waje sedai kasan tuwar allurar bata gama sakinta ba jikinta kuma ba qwari yasa tuni jiri ya debeta ta fadi gurin da gudu Farida tai gunta cikin kuka ganin kamar bata numfashi yasata fita aguje daga dakin tai inda nurses ke.
Suna isa da gawar ana kiran la'asar hakan yasa da suka shigarta gidansu Abbakar dan can suka kaita ko wannensu ya daura alwala sukai masallaci.
Bayan an idar ne Nasir ke fadawa liman nan da nan ya sanar a lasifiqa hakan yasa tuni wanda suka halarci sallah din suka gar zaya dan ayi jana iza tare dasu.
Kafin wani lokaci tuni lokon ya cika danqam ba wanda baiji mutuwarba dan Abbakar mutun ne me kirki ba ruwansa bashi kuma da abokin rikici.
Tuni yaya Babba ta iso seda su nasir suka qaraso suka fito da gawar zuwa inda za'a mata wanta dan har an dora komi likkafani ma Baba mahmud ya kawo.
Kawunsa wato yayan babansa da kuma qanin habansa sune zasu masa wanka ruwa kawai suke jira.
An kammala hada gawar kwance yake cikin shigar da sedai amaka kuma in anyi babu me cire ma wato sanye yake cikin likkafani jira kawai gawarsa take akaita masaukinta na har abada.
Hajiyarsa aka fara kira tai masa addu'a ba abinda take fade se Allah ya jiqanka kuka kawai take ashe shine zai rigata tafiya abinda kawai tunani kenan tana tuno rana irin wannan da aka ce tazo tai sallama da mahaifinsa.
Alokacin gani take kamar zai dawo sedai gashi shekara ashirin da shida da rasuwarsa be dawoba kenan shima Habunta tafiya zaiyi ta har abada tuni ta fashe da kuka tabar dakin.
Kowa yai sallama da shi masu daukan gawa suka dauka sukai waje ummi.
Ummi qanwarsa ta dawo daga makaranta taga mutane jingim qofar gidansu anata alwla hankalinta ya tashi to wa ya mutu bacin lafiya tabar gidan daqyar ta qarasa zuwa ciki.
Tana shiga taga anyo waje da makara kasa tambayar mene tai kawai ta fashe da kuka me tsuma zuciya.
Daruruwan jama'a suka sallaci Abbakar daruruwa suka bi gawar dan mata rakiya zuwa makwancinta na gaskiya.
Kasan tuwar maqabartar da nisa yasa a motar gawa za'a kaishi ta masallaci wadda daman shi ya siya matsayin sadaqatujjariya.
Mahfuz tare sukaje suka sayo motar ganin Abbakar kwance cikin motar matsayin gawa yasa shi kuka sedai hawaye kawai kebin fuskarsa yayin da yake tuna yarintarsu da samar takarsu har yazuwa shigowar ummu rayuwarsu.
Yasani Abbakar amini ne bashi da kamarsa sansa yake so na tsakani da Allah wanda shi yasan baya masa irinsa takuma san duniya bazai samu wanda ke masa irin sa ba cikin abokansa yasan ko yan uwansa basa masa shi haqiqa nayi rashi ya fada.
A hankula ya bude lullubin da aka masa fuskar nan shar kamar yace Aminin ya Amsa.
Tuni an haqa kabari dan haka suna isa suka hau kiciniyar binne shi.
Ita kuwa farida tana kiran nurses suka qaraso daya cikinsu ta fita dan kira Doctor yayin da sauran suka maida ummu gado se faman fada suke ma farida dan mene zata barta ta miqe ita dai tai shiru dan tasan halin nurses da bala'i.
Koda doctor yazo ya dubata gami da yima Farida kashedin karta kuma barinta ta miqe dan za'a iya rasa cikin jikinta to kawai farida tace dan gabaki daya yaudin bata iya komi tun lokacin da doctor din yace Abbakar ya rasu.
Ummi na shiga gida aka fada mata ai Abbakar ya rasu nan tai waje ita dole adawo mata da yayanta dan be mutu ba dazunnan fa sukai waya bata da kudi ya mata transfer kuma ace mata ya mutu ina qarya ne dagyar aka kamota aka dawo da ita gida tana kuka.
Lokacin da suke shigar da gawar ne cikin kabari mahfuz yai saurin dakatar da fara zuba qasa wallahi da ransa yake fade Nasir ya ruqeshi haba mahfuz me kake haka ne yafa mutu.
Dasauri ya tan kada Nasir gami da juyawa ga kawun Abbakar yana fadin kawu wallahi da ransa da karfi kawu ya girgizashi haba mahfuz wai yaushe zakasan kaddara ne karfa ka kafirta kanka mutuwar ce baka yadda da ita ba kome.
Cikin kuka yake magana wallahi kawu na yadda da mutuwa kawai dai Aminina ne be mutuba naga yai motsi ba motsi yaiba mahfuz gizo ne yake maka.
Wallahi kawu yayi motsi in kuma kun bunneshi to kuwa ku kuka kasheshi zan kuma dinga kallonku matsayin masu kisa dan kun kashemin dan uwa.
Kawu ne ya dubi Nasir kasantuwar yasan Nasir din karatun likitanci yai yana kuma koyar da masu karatun likitanci yasa ce masa Nasiru kuma duba manashi zaka fimu ganewa ko ya mutu din ko da ransa.
Nace yace Kawu wallahi ya mutu tun dazu muka tabbatar a asibiti nace ka dubamin ko so kake mu binneshi qarshe mu dawwama cikin kokonton ko da ransa muka binne shi eyye.
Sosai nasir ya doba shi baya numfashi babu alamar yanada rai zaiyi magana yaji shima kamar yana motsi abin ya bashi mamaki zuciyarsa fa babu alamun tana bugawa.
Hannun yasa dedai jijiyar kansa yai shiru gami da maida hankalinsa kanta tabbas tana bugawa alamar harbawar jini sedai kadan kadan take wato zai iya mutuwa ko yaushe in ba'ai wani abinba.
Da sauri ya juyo da ransa sedai yana cikin danger da sauri suka ciro shi daga kabarin gami da cire audigar da ke hancin sa da karkade kasar da aka fara zuba masa sukai asibiti.
Yadda yake cikin likkafani haka suka kaishi asibitin, batare da 6ata lokaci ba likitoci suka dunguma kansa oxygen aka saka masa dan te maka masa wajen yin nunfashi seda suka samu dagyar zuciyarsa ta fara bugawa yadda ya kamata suka dedaita numfashinsa sannan suka fito.
Mahfuz ka fadan meke damunsa ina ciwon qoda ne inji Nasir eh yaya qarya kake mahfuz alamun ciwonsa bana qoda bane.
Ciwon zuciya ne ya fada anman yana ciwon qodar wallahi nayi zaton ciwon zuciyarsa ya dade da warkewa tun yaushe yake ciwon zuciyar tun mutuwar babansu shi kenan Allah ya bashi lafiya amin yace.
Nasir ya kuma duban mahfuz yace kaje ka fadawa Hajiyarsa be mutu ba bazani ba yace Nasir yace bazaka fa kace eh inkaga nabar nan se ance min Aminin ya farfado.
Gyada kai kawai Nasir yai yai waje dan ya fuskanci mahfuz din yanzu baya hayyacinsa.
Gabaki daya hankalin kowa ya koma kan ganin farfadowar Abbakar sunma mance da baiwar Allah Ummu dake can kwance.
Se washe gari ummu ta farfado allurar ta saketa ta kuma dena jirin cikin kuka ta miqe tana fadin Anti Farida dan Allah karki cemin Yah Abbakar ya mutu ta dafa ta ummu nasanki da juriya ki zama jaruma pls mutuwa dole ce.
Ta miqe cikin kuka ba wata jaruma da zan zama ni inasan mijin kar abinne minshi wallahi zan zauna koda gawarsa ne wallahi.
Seda Hajiyar Abbakar tazo sannan ta tambayi ina Ummu se alokacin suka tuna da ita ba shiri sukai can bangaren da suka barta.
Tana ganinsu tahau kuka da sauri Nasir ya qarasa ya ruqo hannunta cikin kuka take tambayarsa mijinta yaja hannunta se inda Abbakar yake.
Kwanan Abbakar biyu a asibitun malan su mahfuz suka gama komi dan kaishi can qasar waje inda za'a kula dashi sosai duda suma nan din basu gajiya ba.
Da ummu aka tafi dan duk yadda sukai kan ta yi haquri ta zauna taqi.
Satinsu uku a india Abbakar ya farfado sedai baya iya komi se kallo da ido kawai.
Watansu biyu a india Abbakar yaji sauqi sosai jiki yai kyau komai yana iya yi da kansa sa6anin da dasaidai ummu tamai in bata kusa mahfuz.
Lokacin da yaji ummunsa nada ciki murna yai sosai harda dagata yana juyawa da ita tai saurin kwace kanta tana dariya tana fadin rufan asiri kaida baka da lpy da dai zan iya ai da na daga ka.
Shaquwarsu da abotarsu da mahfuz ta dawo kamar da koma fiye.
Daga india jordan suka wuce can gurin mahaifiyar ummu taji dadi sosai seda suka mata wata guda suka baro jordan zuwa Nigeria cike da kewa.
Lokacin da suka dawo Abbakar yai kyau yai qiba kaikace bai jinya ba cikin ummu ma ya dan fara fitowa.
Seda ta tabbatar ya ji sauqi sosai sannan ta kawo batun 6oye mata ciwon sa da yai wato be dauketa da mahin manci ba cikin kuka take magana jin kukanta yake har cikin ransa.
Ya jawota jikinsa yahau lallashinta dagyar tai shiru ummu ban boye miki ba nayi zaton na warke ai na fada miki ciwon qodar da nake.
Abin mata da miji yaita bata baki harta haqura kan alqawarin ya dena boye mata damuwarsa dan mahfuz ya fada mata yawan boye abu ransa da cunkushe damuwa ya jaza masa ciwon dan shima se ya takura yake fada masa meke damunsa.
Shi din mutunne da baya fadin abinda ke damunsa duk girman takaici yakan kunshe shi cikin ransa ne yaita in abu yai yawa ne yakan danyi kuka shima a boye.
Watansu biyar da dawowa ummi ta haifi yaranta yan biyu duk maza murna gurin uban gayya Abbakar bafa a magana.
Ranar suna yara suka ci sunan mahaifin ummu da na Abbakar suke kiransu da Walid da Amir.
Suna akai sosai bana wasa ba anyi gayya sosai.
Akullim inta kalli yan biyunta ta takalli tafkeken hotonsu dake jikin bangon dakin wanda sukai ita da Abbakar da babyn ta da ummi me rainonsa setaga kamar shine ahannunta banbancin kawai wannan biyu ne shi kuma daya ne.
Lokacin da rai arba'in har Niger sukaje ita da Abbakar da ummi dan ko bayan Rasuwar Baby Abbakar bata maida ita ba.
Sosai suka sami kar6uwa abinda ya baima ummu mamaki shine gani jarin fulawarta ya bunqasa ba wai yanzu iya magarya da zender ba state da dama na Niger kanzo siye buhu buhu.
Wajen miliyan biyar innar Ummi ta bata wanda tai tara tarawa cikin riba qin amsa tayi tace innar tasa ayi borehole da masallaci a unguwar dan lokacin data zauna agarin taga yadda suke matsalar ruwa tace sadaqatujjariya ga mahaifinta da kakarta da babansu mahfuz.
Sauran riba kuma tace in an samu araba biyu a ajiye mata daya daya inna ta dauka.
Qawarta Fiddo tayi aure har ya mutu bataji dadin gidan mijinba ummu ta tawo da ita dan ta cigaba da karatu a Nigeri.
Har can inda akama Abbakar masauki a niyame suka je sunyi murna sosai malan musa yace oh ashe zaka tuna damu bayan shekara biyar da tafuyarka Abbakar yai dariya na tafi cikin gaggawa bamuyi sallama ba zanso zumuncin mu ya dore sosai yai musu alkairi sukaita murna.
Ummu tuni ta gama degree dinta dan hartai masters lauya din da baban mahfuz yace dukiyarta nagunsa ma tuni ta nemo shi ta amshi komi nata gami da masa kyauta.
Kamfanin qere qere ta bude gami da tallafawa yara masu kwakwalwa duk yaron dake da fasaha ta qere qere ummu kan daukoshi musanman mara gata ta kaishi makaranta me kyau ta bashi aiki kamfaninta dan baje irin tasa fasahar in ka kammala jami'a inkaga zakai aiki da kamfaninta to in kuma bazakai ba takan tsaya maka dan samun inda kake so sedai bata ta6a tsayawa mutun dan barin nigeri da sunan aiki.
Tuni su Aisha sukai aure suma duk da yaransu zumuncinsu kuwa se abinda ya qaru.
Zaman Fiddo gidan ummu yasa suka saba da mahfuz dan yanzu yana zuwa gidan harsuyi fira da ummu dan itama ta saki jiki bakamar daba da take kullin cikin daure masa fuska yanxu ta mance da komi ta kuma yafe masa.
Ansha bikin Fiddo da mahfuz sosai iyayen fiddo sukaji dadi yayin da take BUk tana karantar BSC nursing, lokacin yaran ummu shida haihuwa biyar maza uku mata uku.
Muktar qanin Abbakar ma ya dawo ya zama kwararren likita yazama shi ke kula da asibitin da mahaifinsu yabar musu gado.
Maryam qanwar Abbakar kuni ta jima da yin aure harda diyarta mace tana da wani tsohon cikin.
Ummi ma qanwar Abbakar tai aure ta auri muktasir qanin Mahfuz zumuncinsu kullin qaruwa yake.
Ummu diyar wato ummi yanxu ana level 3 yayin da tuni suka dedai ta kansu da Ahmad amin ummu jira kawai ake ta kammala asha biki.
Zaman auren ummu da Abbakar abune abin sha'awa ga kowa koyaushe cikin san junansu suke sedai kunsan ako yaushe aka ce aure dole ana samun matsaltsalu nanda can anman in ma'auratan suka iya zamantakewa ba mejin kansu.
*Bayan shekara Ashirin da biyar zuwa da bakwai..*
Duniya ba gurin zama bace tuni Hajiyar mahfuz ta jima da rasuwa, itama ta Abbakar din tsufa sosai kullin gidanta cike yake da jikoki harda tattaba kunne dansu Nur din yaya babba sun jima da haihuwa.
Yau jikinta yaqi dadi hakan yasa sukai asibiti da ita sedai kansuje ta rasu kowa yaji mutuwar nan sosai su Abbakar harda kuka.
Walid dan wajen ummu tuni suka dedai ta da Shukra yar gidan Aisha bayan wata biyu da rasuwar kakar tasu aka sha biki.
Shima Amir yar gidan mahfuz yakeso basu wani bata lokaci ba akai nasu auren.
Fatima kuwa tuni ta jima da mutuwa qawar ummu da Aisha wata sch mate dinsu a buk sedai ta bar diyarta daya wadda ummu ta dauketa take kula da ita duda kuwa dangin fatiman sunso su hanata da temakon Abbakar suka bata.
Itama Kairat din ta girma ansa ranarta lokaci kawai ake jira asha biki.
*Bayan shekara goma sha daya.*
Ummu ce zaune jikoki sun ke wayeta na yaranta dana gurin ummi da na gurin kairat sun cikata da hayani kowa da abinda ke fade daga wancan yace gwaggo kinga wane ko se wancan yace gwaggwo a ina kika ajiye min kazana.
Abbakar ya shigo duk an tsofe kannan ya furfure dan tuni yai ritaya yaransu ke musu komi duda kuwa ummu nada kamfaninta se abinda yai gaba shima.yanada nasa anman basa zuwa ko ina kamfanin ma kula musu ake dashi.
Ya dubeta sweetheart wai yaushe yaran nan zasu tafi ne ta dubesu kowa da abinda yake tai dari se nanda.sati uku what ya fada aikam iyayensu zan kira kowa yazo ya kwashe dansa haba ni nagaji abarnima in hutawa tsofa na da mata ta se ankawon jikoki tai dariya mu lokacin da muke kaima hajiya me tace yai dariya ita daban ai.
Na'im babban jikansu dan wajen ummi ya dubi kakan nin nasa yace kajifa wai Sweetheart har tsoffi sunsan love, Fadila yar wajen kairat tasa dariya bari kawai yah na'im ko kunya basa ji.
Eyye kingani ko yarannan samana ido kawai suke dole su tattafi Husain dan gurin walid yace ta6 ai ba inda zamuje Abbakar ya cilla masa lemar hannunsa kaji mara kunya to dole ku tafi Usman dan qarami da befi shekara hudu ba yazo ya fada kan Abbakar yana dariya.
Nana ma ta fada kansa Abbakar yace kai nidai na banu ummu yasa dariya.
An koma makaranta kowa ya koma gidansu anbar Abbakar daga shi sai ummunsa zaune suke yana shan fura kamar yadda al'adarsa take ya dan jawota jikinsa sweetheart ta ce na'am my D yaushe za'a kuma bada