Chapter 7 Reading ABBAKAR BOOK COMPLETE DOCUMENT by AXEEX.txt Arewa Novels

ABBAKAR BOOK COMPLETE DOCUMENT by AXEEX.txt

Author :  AXEEX Category :  Romantic Story

Chapter   7 / 20

18K to 21K   out of 57.6K words

ciro dubu ta miqa masa ya amsa ta juya tana kallon kofar gidan yace hajiya canjinki riqe tace ya juya yana murna dan be mamakiba ganin tamfatsetsen gidan da yasaukesu da alama yarinyar gidan ce ya fada.


Gidan su Abbakar


Tun jiya suke ta gyare gyare da kin tse kintse yau kam girki siketayi tun safe dan hajiya da kanta tashiga madafa ita da maryam da ummi dan yau muktar zai zo hutu da autan hajiya.


Yadda hajiya ta zage tana ta hada kayan datasan yanaso koya kai mistake yanzu ta hau fada abinda ba sabonta bane haushi duk yabi ya ishi ummi dan duk fadanda hajiya dake yawanci akanta ne koya tai mistake. Sai kace ba ita ce take kuka lokacin da zai tafiba kishin sakun takan ya motsa.


Tana sane cikin zobon da hajiya ta gama masa ta zuba zuma duda tasan bayasan zuma a abu me sanyi aikuwa hajiya ta hau fada har saida taji dama batasa ba aikuwa idonta yai rau rau kamar zatai kuka maryam ta faki idon hajiya ta mata gwalo nan da nan hawayen ya zubo hajiya kinganta ko hajiya ta cillama maryam harara fita idona maryam tunkan raina ya baci bansam tsokana ummi tasa dariya gami da mata gwalo zatai magana hajiya tace karki kawon qara aike kika fara shiru maryam tai tana hararar ummi dan tasan kobata ummi komi ba hajiya bazata mata magana ba dan duk gidan sun sani in abu ya hadaka da ummi dole kaine mara gaskiya sedai in ita da dan autane to dole ta dau rashin gaskiya.


Sun gama komi sunyi wanka inda hajiya tai tafiyarta dan cewarta bazata bar dan lelenta ta jirasu ummi su bata mata lokaci wajen kwalliyarsu ta tsiya ba.


Suma sun fito tsab shigarsu iri daya sunyi kyau sosai ummi tai daki da gudu tana kiran hajiya wayam ta gani gaji mai aiki ce take fada mata ai tuni hajiya ta tafi aikuwa ta zunburo baki tai waje tana bubbuga qafa ita ala dole taji haushi da Abbakar taci karo ya riqota yar kelen hajiya ya akaine ta kuma kumburo fuska ba hajiya ce ta tafi ta barni ba yasa dariya ba dole ta tafi ta barki ba mowanta zaizo kin zama bera tasa kuka yaya yai saurin goge mata hawayen da wasa nake muje inkaiku ta tirje ita bazata ba haba mowar hajiyarta kidaure muje kinji tawan ta dan murmusa yajata suka fice maryam biye dasu.


Seda suka Abbakar ya amshi powder gun maryam yashafa mata kar yaroncan ya rainaki yaga kinyi kuka tai dariya tanasan yayanta sosai duda duk sauran yan uwanta haka sijeji dasu ita da autan hajiya shi yada suke tsula tsiyarsu se kace yara inda azahiri shekarunta ashirin cif kazalika autan hajiya twins ne ita dashi saidai ita aka fara haifa saidama takwana biyu akama hajiya CS aka ciroshi.


Gabaki daya sunyi mamakin yadda autan hajiya ya girma inba kasani ba kai ka rantse shidin yayan maryam nema ba ummi bama.


Tun saukowarsa ajirgi hajiya na hangoshi ta gilas sai washe baki take aikuwa suna fara tawowa suka fito inda zai hangosu ganin yan uwansa wanda rabonsa dasu shekara uku kenan yasa sanyi ya ziyarci ransa.


Yana zuwa inda suke yai gun ummi wanda tunda ta hangoshi murmushinta yaqi tsayawa hajiya ta zuba musu ido eyya wato abun haka ne yar uwarka ka sani banda uwakka yasaki ummi yazo gun hajiya ya rungumeta yana cewa haba hajiyata aikema kinsan ke nafara gani kinsan kishinta ina kula wani ba itaba har in koma ana mita suka saka dariya baki daya.


Agida ummi ce tai dakinta da gudu ta fito riqe da roba tace qanina bude bakinka yasha kunu waye qanin naki ta dubi Abbakar tace yaya dan Allah waye babba yai dariya gami da daga kai alamar tunani bari in tuna kai yaya ya auta shine auta ya daka tsalle yeeee tasa kuka yaya yai saurin cewa shine qarami tai dariya muktar ya amsa yakalla gami da tabe fuska wannan wace qazantarce ta gallah masa harara gami da amshe abunta tai ciki yai saurin bunta sorry babbar yaya ya amsa ya fara sha Vanana ice cream ce tamai dan yanasanta sosai.


Sai da yai wanka yazo yaci abinci sannan suka hau hirar yaushe gamo yadinga basu labarin qasar waje basu ankaraba sukaga daya duk suka miqe sukai daki dan kwanciya.


Anman hajiya ta daga masa hannu na riga na yanke wukunci dole agoben za'a daura mata aure anman bada kaiba da mahfux shi kuma yaron da kake cewa naka ne koma nawaye na qwaceshi na baima mahfuz tunda shi zai auru uwadda............
[12/31/2020, 5:53 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[12/31/2020, 5:54 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR*


*PAGE 90---10*


*Godiya gareku masoyan books dina inajin dadin yadda kuke karantawa gami da addu'o'inku garenk nagode sosai ina Alfahari daku*


Wajen qarfe bakwai Babbar yayarsu ta iso gidan ganin duk suna bacci yasa tai kitchen ta hada musu kari ita da gaji da sauran masu aikin gidan tana cikin jerawa Hajiya ta fito itada ummi ummi ta daka tsalle yaya saikar yaishe tun jiya nazo kunyi bacci gami da durkusawa ta gaida Hajiya ummi tai waje.


Wajen takwas aunty zainab tazo hajiya tai ta fada dan tace tasan ita tasa dole sukayi irin wannan sanmakon bacin tasan cewa batasan tafiyar duhu hajiya wallahi seda aka idarda asuba muka tawo ahab ai duk daya nan cikin wayo zainab ta basar da batun suka shiga wata hirar.


Gabaki dayansu sun taru a falo suna fira Muktar ya sawko suka miqe suprise suka fada da dan qarfi yasauko yana murna sosai yaji dadin ganinsu.


Durkusawa yai ya gaida hajiya da sauran yayyansa kafin yaya babba tace haba autana come give me a hug i miss u sosai ya manne kai bacin jiya kika qi zuwa taroni auni din kaima haka zainan tasa dariya zonan nawan ya juya qeya bacin kinmin buqulu naso yau inzo katsina ke kuma kika wani diro da sassafe gabaki daya suka sa dariya daman sun san halinsa ba'a iya masa fakar yaya babba yai ya fada kanta yana fadin suprise hug wayyo zai karyani ta fada ya miqe yana dariya zainab ta miqe yai dinning wannan suprise din badani ba akaini a baro suka saka mata dariya.


Ita ko ummu gidan take bi da kallo yayin da wani abu dabatasan ko mene ba yazo ya tsaya mata a wuya ada tasa aranta tabar gidan kenan ko unguwar bazata qara zuwa ba sedai yau tanajin kome za'ai ba wanda ya isa ya hanata shiga.


Kukan karen da taji yafara tashi yasa tai saurin dawowa daga tunanin data tafi ta fara buga gidan daga ciki me gadi yace waye ummulkairi ce ta fada bai dauki murya ha be kuma gane sunanba anman jin mace ce yasa ya bude.


Qofar gidan cike yake da hasken wuta hakan yasa yana budewa ya ganeta yadan saki fuska a'a ummu daman kinanan idonta kuwa ya kuma cikowa da qwalla kamin tace baha Sale ina wuni ya amsa lafiya qalau ban taba zaton ganinki yanzu ba.


Ta qaqaro murmushi wanda kana ganin kasan na yaqene nima baba ban taba zaton zuwa na nanba ya gyada kai kafin ya kuma magana tace Yah nasir kuwa yazo.


Eh yazo da wani dan kyakkyawan yaro gabanta ya fadi cikin rawar murya tace ya fito dashi yace a'a tun dazu inanan banga fitarsa ba to baba bari mu shiga ciki.


Bata jira amsarsa ba suka yi ciki.


Kai tsaye bangaren yan mazan gidan tai gabanta sai faduwa yake zuciyarta fal tsoro ta dai daure ta shiga qofar da zata sada ta da gurin nasu.


Ba qaramin mamaki abin ya bata ba ganin gurin shiru ba kowa dan ada saninta dedai wannan lokacin inkazo gurin cike yake da samari kowa na sabgarsa masu hira nayi masu chat masu tireni dan duk suna da kayan yi.


Hakan yaqara tada mata da hankali da sauri tai dakunansu kai tsaye dakin da tasan na Nasir ne ta nufa ta tura a bude take sedai bakowa duk ta shiga ba kowa tabbas akwai abinda ke faruwa ta fada tai cikin gida.


Ai kuwa afalo ta taddasu tsai tsaye sunyi jugun jugun hajiya nata zazzaga bala'i Nasir ta hanga can nesa azaune hawaye nabin kuncinsa Abbakar na gefensa yana ta faman wasansa a jikinsa ba abinda ya shafeshi sai lokaci lokaci yakan daga ido ya kalli Hajiya dake faman fada.


Da sauri ummu ta qarasa ta suri danta gami da juyawa zata fita aiko mahfuz da sauri ya miqe cikin murna yayo gun ya rungumeta tai wani kukan kura ta tankada shi gami da bashi mari ya riqe gun yana kallonta dan gaskiya yaji zafin marin daga hannu yai zai rama kome ya tuna kawai yasauke hannun yana murmushi yaja tsaki gami da fadin kada ka qara kuskuren tabani dan akuya kawai.


Murmushi ya kumayi yai gabanta ya durkushe yana kuka pls ummu kiji kaina duniya ke kadai zuciyata takeso nasani inban aureki ba mutuwa zanyi ta ja hannun ummi gami da fadin wallahi saidai ka mutu in dagani kadai muka rage aduniya to gwara in mutu ba aure wallahi inda zaka mutu zanfi kowa farin ciki ta juya zata fita.


Hajiya tai saurin fizgota ganin cikin yaran nata bame iya tsai da ita tasa hannu zata fizgi Abbakar tana fadin inadai yaro jika nane dan haka baki isa kin fita dashi a gidan nanba kema kanki baki isa ki fita ba aure keda Mahfuz yazama dole.


Fizge rigarta tayi gami da fadin wallahi ko gawata ta fi qarfin auren dan iskan danki tasa hannu ta mareta har ta daga hannu zata rama ta sauke gami da fadin wallahi kinci darajar yah nasir da sauri ta faki idonta tai waje da gudu ita da ummi Abbakar na faman sheqa dariya zatonsa wasa take masa.


Mahfuz ne ya miqe zai bisu saidai jirin da ya dibeshi yasashi faduwa kasa tim da sauri kowa yayo kansa hajiya cikin tsawa take fadin ku bita ku bita dasauri su muktasir suka miqe sukayo waje dan nemanta saidai fa ina duban duniya batanan.


Ita kuwa ummu tana fita abakin gate taji an rufe mata baki da tsumma haka ma Ummi cikin qarfi aka jawota zuwa dan dakin da ke qofar wajen tanata wutsil wutsil din so ta juya taga ko waye ina abu yaci tura..............


*Da yawa suna min test wasu nakan samu in amsa musu da wuri wasu kuma sai ya jima ina mai baku hakuri kan hakan dan bawai hakan na nufin wulaqanci bane saidai abubuwa sukamin yawa anman kusa aranku F.A.Ya'u mai san masoyanta ne ako ina suke*


*Ban cika qorafi kan readers ba koma ince ni ban taba ba saidai wani abu da yadan fara batan rai dasu shine insun ma magana kadan dauki time baka amsaba wani dan rashin kyautawa irin tasa sai yafara zagi ko faden maganganu marasa dadi hakan bayamin dadi danshi rubutun online sa kaine kawai bawai rashin abinyi ba sai sha'awaryi dan kawai ina rubutu online bashi yake nufin duk sanda kaso ko kika so zaki min magana in amsaba dan kuwa inada abubuwanyi da dama masu mahin manci arayuwata fiye da rubutun online*


*Readers kance writers basu da mutimci musanman na online sai dai kuma yawancin readers masu fadin haka asannu na gane sune marasa mutinci ta yadda suke zagewa su dinga cima mutun mutinci beji ba be gani ba.*


Ruwa Hajiya ta shafawa mahfuz a fuska ya farka a gigice yana fadin hajiya karki barta ta tafi dan Allah inban aureta ba bazan iya rayuwaba hankalinta yai matuqar tashi.


Malan ka ishemu da kuka da kasan kanasanta kai sana diyar barinta a gidan nan mansur ne ke fadin haka hajiya ce ta daka masa tsawa yai shiru yana dan qunquni.


Shiko nasir jin su muktasir sunce basuga su ummu ba hankalinsa ya tashi dan tazararsu da futarta beci ace har ta bacema ganinsu ba.


Miqewa yai zaiyi waje hajiya tace ina zaka mara san yan uwa dan uwanka na wani hali zaka fice yadawo jiki ba kwari ya zauna.


Mahfuz ne ya miqe hajiya bari kawai inje gidan da take in roqota hajiya ta zaunar dashi kayi haquri yanxu dare yayi gobe maje da sassafe inyaso sema mu tafi da masu daura muku aure inma acan zata zauna ita taji shidai Nasir abin duniya duk ya isheshi ji yake kamar qirjinsa zai tsage zuciyarsa ta fito tausayin ummu duk ya cika masa zuciya.


Gidan su Abbakar.


Gidan cike yake da farin ciki kana shiga zaka san tabbas yau suna cikin farin ciki shi kansa Abbakar wasai yake jin kansa bakamar kwanakin baya ba da zuciyarsa take cikin kunci duda farin cikin da suke ciki yanzu koya ya tuna da ummu da nahfuz sai gabansa ya fadi dan baijin zai iya rayuwa batare da ummu ba saidai baijin zai iya auren matar da Amininsa yake masifar so yanajin zai iya sadaukar da komi akan abokinsa ada duda zatonsa natana da aure yanajin wataran zai iya aurenta tunda yayi yayi ya cire santa ya kasa saidai tun lokacin da ya gano ita mahfuz yake so yasa ma ransa koda zai mutu ya haqura da ita.


Kamar kullin tun zuwan muktar hutu yau kwana hudu kenan gidan cika yake da yan zuwa sannu da zuwa dare yayi kowa ya miqe yai makwansa cikin shauqi da farin ciki haka shima Abbakar saidai yana tura qofar dakin ya nemi farin cikin ya rasa haka kullin yake dan da ya zauna shi daya shikenan tunanin ummu ne ke cika shi in bacci yake baccin cike yake da ummu ya rasa yadda zaiyi addu'a kullin yake kan Allah ya temake shi ya cire masa ita aransa anman kamar addu'a yake Allah ya qara masa santa.


Juyi kawai yake akan gadon hawaye na bin fuskarsa yama kasa rufe idansa dan ko rufewa yai ita yake gani tana masa murmushinta me ratsa zuciya.


Gidan su mahfuz da sassafe ya farka dan be niyar komawa ba bayan yin asuba saidai bacci barawo yai gaba dashi ko wanka be ba yai dakin hajiya dan dama ya dade da dawowa bangarenta.


Qofar a bude take ya tura ya shiga ko taisheta beba tana zaune tana lazimi yace haji pls taso mu tafi ina tace yadan zaro ido kin mance gidan ummu taja tsaki kabari sai anjima dan ita dan kawai tana san mahfuz ne sosai shi yasa take iya haqurin jin sunan ummun dan batasan ransa ya baci anman a haqiqanin gaskiya ta tsani yarinyar sosai.


Hajiya inbazaki ba ni zani ta miqe muje suka fice sai da suka biya gidan malan habu suka daukoshi shida almajiransa guda hudu masu jire masa dalibai dan daura auren.


Bakwai dedai a gidan ta musu sunsha bugu kafin Farida tazo ta bude tana murza ido alamar bacci tana fadin ummu badai yanxu kika dawo ba sai dai ba ummu ta gani ba tadan zaro ido tana ja da baya.


Hajiya da mahfuz da sauran mutanen suka shigo suka tsaya hajiya na bin gidan da kallo ba lefi yana da kyau sosai da kuma dan girmansa.


Mahfuz ne ya daure yace ina ummulkairi pls Farida tace wallahi tun jiya da ta tafi dauko danta a gidansu bata dawo ba what ya fada pls karki mana qarya ta ce sabida me zan muku qarya.


To me yasa baki nemeta ba taja tsaki kaji malan taya zaka zo ka isheni da tambayoyi.


Nasir Hajiya ta kira tace ya sameta gidan ummu gin tana gidan da sassafiyar nan ya daga masa hankali hakan yasa yashararo mota ya tawo Allah ne kawai ya kawoshi lafiya.


Koda yazo ake fada masa ai tun jiya bata dawo gidanga hankalinsa ya kuma tashi cikin tsoro da rawar murya yake tambayar Farida.


Farida dan Allah ki fadan gaskiya da gaske bata dawo ba ta gyada kai cikin kwalla dan itama yanzu hankalinta ya tashi wallahi yaya bata dawo ba ta kirani bayan wajen awa uku da tafiyarta tace ai an dai daita komi yanxu dan haka a gidan zata kwana salati ya saka Farida me yasa baki kirani ba tace ai saida ta bani kai a waya ka tabbatar min hakane batunta innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni kuma Farida wallahi muryarka naji.


Aikuwa mahfuz yai kansa ya shaqeshi yana fadin wallahi saika fito min da masoyita mugu kawai da sauri Nasir ya fuzfe wuyansa ya tankadashi baya kai malan bansan hauka kabarni inji da abinda ke damuna.


Ita kuwa Hajiya can kasan ranta dadi taji da batan Ummu dan gaskiya batasan ko kadan danta ya aureta dan kawai ta fuskanci in bai aureta ba komi zai iya faruwa zai iya mutuwa.


Wayarsa Nasir ya dauko ya fara kiran Aisha qawar ummu batare da la'akari da cewar ai safiya bace bugu uku ta dauka cikin muryar bacci tai sallama a gaggauce ya amsa bai jira tace komi ba yace Aisha ummu tazo gidanku kuwa ta gyada kai kamar tana gabansa tace a'a me ya faru fatan lafiya bai bata amsa ba ya katse ya fara kiran Fatima ita ma din haka ne duk wadda yake da number dinta ya kira ummu bataje ba.


Jiyai qafafunsa sun kasa daukansa ya tsugunna gami da dafe kai dan yadd yaji yana sara masa.


Duk inda suke saka ran ko ummu taje sunje ba ita ba dalilinta hankalinsu duk ya tashi sun rasa me zasuyi cigiya suka kai gidajen radio.


Hankalunsu bai qara tashi ba sai da police suka tsinci kayan Abbakar da wayarta a

7 / 20