Chapter 11 Reading ABBAKAR BOOK COMPLETE DOCUMENT by AXEEX.txt Arewa Novels

ABBAKAR BOOK COMPLETE DOCUMENT by AXEEX.txt

Author :  AXEEX Category :  Romantic Story

Chapter   11 / 20

30K to 33K   out of 57.6K words

ya shimfida masa ya sauna kafin mutumin ya fito da kwanuka a hannu tuwone na gero da miyar kadi ba lefi tuwon da dadi gashi da zafinsa hakan yasa Abbakar yaci ya qoshi.


Adakin zaure inda qanin mutimin ke kwana anan aka sauki Abbakar din.


Kwanar Abbakar biyar agarin nan yaje dik inda zaije sai dai ya rasa gano ummu hankalinsa duk ya tashi sai yanzu yagane bawai zuwa niger dinne wahala ba face gano inda take gashi kusan kullin sai ya kira wayarta wadda Ahmad ya bashi anman akashe.


Sun saba sosai da muntari da kuma qaninsa Basiru yau suna zaune suna fira duk hirar ummu ce basiru yace anman me yasa baki zuwa zender nemanta tunda naga lokacin da zani fara zuwa nijeriya tacan mukabi ta magarya kuma abokina yace min duk yawanci masu zuwa Niger ta mota tacan suke bi.


Miqewa Abbakar yai ai sai in tafi ma yanzu muntari ya ruqoshi ki bari gobe maje gyada kai kawai yai ya koma ya zauna.


Adaki kuwa ji yake kamar gari bazai waye ba shi ji yake kamar yaga ummu ya gama.


Da sassafe ya kintsa suka rakashi tasha ya hau motar maradi dan sai anje can kafin ya hau motar da zata sadashi da zender sai da ya shiga mota ya leqo yana qara musu godiya sai da motarsa ta tashi sannan suka bar tashar shi kuma muntari yai gurin sana'arsa wato saida fina finai danshi har kano yasani dan yana zuwa sayen fin qofar wanbai.


Kusan irin tafiyar da sukai kafun su zo niyame sukai yanzu ma sai dai yanzu awa goma sha daya sukai.


Nasaukinsa yai inda yabar kayansa dake maradi nan unguwar kawo dan yagaji sosai.


Washe gari ya hau haramar yin zender duk ya bi ya rame abinka da wanda bai saba wahala sosai ba.


Ita ko ummu sana'a ta karbu dan yawancin unguwanni dake nan magarya sun san da zamanta dan ita din kayanta da sauqi sosai ko akasuwa dake birni inkahe yadda take saidawa zaka samu dan ita ba ta riba take ba ta kawai juya kudin take.


Yanxu takai takawo daga unguwar
Ghana, Sabon gari , tudin wada , un franco,mayanka , gawo da gamdji, gawon kolliia, château, kai inma akace duk garin magarya ba'ai qarya ba..inka anbaci sunan gidan malan musa da ake sai da komi sai ankawoka har gidan.


Yau wasu kayayyakin sun qare hakan yasa mero da ummi zuwa zender sayowa inda ummu da ummi suka shirya dan zuwa can niyame sayen kaya dan inna tace niyame anfi samunsu da arha sai dai nisa kawai.


Gurin innar mero ummu tabar Abbakar dan yaba musu quya kuma komi yana ci.


Amaradi su ummu suka fara sauka anan tasha.


Abbakar yana cikin mota inda kwandasta ya shiga gami da bugun motar alamar muje fara tafiyar mota kamar ance ya dago ya hanqi wata kamar ummu ita dince ya fada sai dai cikin mota yagansu motarsu taja da gudu rasa abinda ke masa dadi yai shi ba abin yace asaukeshi ba anya kai ba ita bace abinda keta kai kawo aransa kenan.


Sunyi wajen awa bakwai a hanya kafin su isa zender nanma agajiye suka isa dagyar yasamu hotel yakama anan din yau kwanansa takwas gashi ko alamun ummu babu gashi sati biyu yacema hajiyarsa zaiyi kawai.


Sai da ya huta atashar da yake basu da nisa da kasuwar dole can ya nufa dan ko zai sami abinda zai ci dan wani irin hotel ya sauka basa baima mutun abinci.


Acan kasuwar ya rasa mai zaici can ya hango wani mai shayi yai gurin yana kurbar shayin da yake da zafi sosai.


Ya dago kenan suka zo wucewa ta gabansa indai ba gizo idansa ke masa ba wannan yarinyar itace mai ma ummu raino tabbas itace kenan yar niger ce kome ya fada gami da miqewa, buzun ya ruqoshi kudina malan ya ciro ya miqa masa.


Saurin shan gabansu yai har yana dan haki sukai saurin tsayawa cikin fada mero ke fadin malan lafiya ummi ce ta dan firgita dan tasanshi azatonta ma shine Mahfuz dan vatasan mahfuz din ba.


Yi haquri baiwar Allah ya fada gami da kallo ummi ina ummu take ta hade rai ni bansanta ba yadan kuma kallonta kafin ya basu hanya su shige.......


Zanci gaba insha Allah
[1/13, 4:18 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[1/13, 4:19 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR*


*PAGE 130---140*


Sai da sukai dan nisa ummi ta dubi mero wannan shine wanda antina ta baki labari ta gwalo ido to me yake anan bakiji yana cewa ina take ba nemanta yaso yi mun shiga uku mero tace kafin tace kinga zo muje mucewa dan bala ya kawo mana kayan gida zo mu tafi.


Abinda basu bani ba Abbakar buye yake dasu har sanda suka gama yima dan bala bayani sukayi hanyar futa daga kasuwar.


Gun dan bala ya koma suka gaisa kafin yace yanaso yakaishi inda zai kai musu kayan dan bala bai kawo komi aransa ba zatonsa ko irin masu sayen kayan da ummun ke sai dawa ne.


Suna tafe a mota dan bala na masa surutun kaima kaima kaji labarin sauqin hajiya ko shi dai eh kawai yake cemasa har suka iso qauyen magarya.


Su kuwa su ummu acan suka yanke kwana dan basu suka gama siyayya ba sai dare jafin su taso suzo maradi ma dare yayi sannan daga nan qara wata uwattafiyar zuwa zender dole sika yanke shawarar kwana gidan wani qanin malan habu mijin inna dake nan unguwar lazare dake nan niyame din.


An shisshigar da kayan dan bala yaja mota yai gaba ummi sin rigasu isowa tama dan jima agida dan harta dora girki danshi Abbakar kan su tawo saida Dan bala ya qarasa sayayyar.


Wata yarinya ce ta fito daga daya gidan dake kallon inda aka shisshigar da kayan riqe da Abbakar ahannunta duda magariba tayi sai da ya ganeshi dan akwai nefa saidai irin jan kwannance bakuma ta cika haske ba.


Zo yace mata tai sauri taje ya amshi yaron dan tabbatarwa ta miqa masa ba musu ya sunansa yace tace Abbakar yadan rungume taron yaiko lif ajikinsa ya miqa matashi jeki ki kiramin ummamsa tai dariya ai batanan tun safe suka tafi niyame sai gobe zata dawo.


Tausayin yaron ya cika shi ace yaro dan qarami haka babarsa ta tafi tabarshi harta iya kwana.


Ganin baice komi ba yasa yarinyar shiga gidan sai dagowa yai yaga bata nan yaci gaba da zamansa a qofar gidan har malan musu ya dawo.


Sai alokacin ya tsaidashi suka gaisa kafin Abbakar ya dora daman nine mahaifin Abbakar dan da suke zaune a gidanka malan musa yadan waro ido da gaske eh yace yajashi cikin gida to me yasa suka barka anan biyoni ciki ba musu ya bishi ciki suka shige.


Kai tsaye dakin inna malan musa yai ya fada mata komi itama ta hau murna ai wai tunda matarsa take da kudi ai sai yama fita kudi sukam karensu ne ya yanke sa'a.


Ummi najinsu ta kuma leqo ta ganshi hankalinta inyai dubu ya tashi ta rasa meke mata dadi ta kuma kasa fitowa duda futsarin da ya matseta.


Gwaggo ce ta je ta dauko Abbakar ta dangashi ahannun Abbakar babba tana fadin Allah sarki dan albarka ashe da uba nasa muke wadin shege ne dan kawai uwatasa nada kudi yasanya bamu wadi gabanata Abbakar yai dan yaqe kawai tausayin yaron da mahaifiyarsa na cikashi.


Washe gari wajen goma na safe gwaggo tai tabi gidaje tana cewa azo aga baban dan ummu aikuwa akaita zuwa.


Su kuwa su ummu basu suka dawo ba sai wajen biyar na yamma duk a gajiye suke daga ita har inna sai da aka gama shigo musu da kayan kafin su shigo gwaggo na zaune ummi a gefenta tana mata tsifa.


Anan suma suna zauna ummi da gwaggo na musu sannu da isowa sai da suka ci abinci sukayi la'asar kafin gwaggo tacewa ummu jiya mijinki yazo atsorace ummu ta ce mijina eh gwaggwo tace yanxu yana ina inji ummu yadan fita shi da dansa.


Dansa kuma eh danki mana ummu ta miqe badai Abbakar nawa ba eh shi kenan nashiga uku an gama dani hankakin inna ma ya tashi to wazaizo har yace shi ne mijin ummun harya dauke mata yaro komdai masu garkuwa da mutanene tunda kowa yasan uwar yaron nada kudi.


Sallamar da sukaji yasa ummu saurin juyawa danko mafarki take intaji muryannan tasan me ita zata kuma iya gane muryarsa cikin maza dari.


Shi dinne riqe da Abbakar dinta akafada da alamu ma yayi bacci tasaki ajiyar zuciya gami da fadin Malan kaine ya akai kazo nan waya fada ma ina Niger ya akai ka gano gidannan duk lokaci guda take maganar yayin da shi kuma ke binta kawai da kallo cike da mamaki.


Nigeria


Tun bayan bacewar da yan kwanaki mahfuz ya ware ya ciba da sabgoginsa inka dauke da daddare da yake kasa bacci dan ko ya rufe idanunsa ita kawai yake gani azahiri inka ganshi zakayi zaton ta ya mance da ita sai dai shi kadai yasan me yakeji aransa daurewa kawai yake yayin da yasaka ido sosai akan yayansa nasir dan yace yanxu ma shi ya boyeta.


Shiko bangaren Nasir hankalunsa yafi na kowa tashi har yau bai dena nemanta ba yabi ya rame yai baqi daman shi ba wani jikin qiba ke gareshi ba.


Gidansu Abbakar.



Ummi ce qanwar Abbakar wadda ita daya kawai tasan me yakai yayanta niger zaune take suna waya dashi yana fada mata irin wahalar da yasha tana ta jimami har ya fada mata ai yau yagano gidan da ummum take sai dai basa nan ta hau murna kai anman yaya nayi murna yaushe zaka dawo.


Ya nisa kinsam damuwata kenan jibi sati biyun da na fadawa hajiya zai cika gashi banma shawo kan ummum ba balle ta yadda ta biyoni.


Ummi tai dariya kai yaya kana ban mamaki kawai ka kira hajiya kace aiki zai iya kaiku irin wani satin yasaki dariya kai wannan yarinyar da wayo kike ta dan turo baki kamar tana gabansa kai yaya nidince yarinya ka manta shekaruna yai dariya kawai sukai sallama.


Gaban ummi ne ya fadi tai saurin miqewa tana fadin hajiya yaushe kika shigo ta watsa mata wani kallo bansani ba wato ummi harkinyi girman da zaki boyen wani abu ko inshi yayan naki yana ganin yai girman da zai boyen abu ke harkin san ki hada masa qarya ya fadan ko.


Wallahi hajiya ha haka bane ta fada wayar ta dauka ta hau kiran Abbakar gami da barin dakin ummi ta diro daga gadon gami da bin bayan ta.


Niger


Maganar Abbakar ce ta baima ummu mamaki wato murmushi yasaki gami da fadin haba tawan mene hakan daga mun sami yar matsala saiki baro gida ki tawo gari harya Niger kina ganin kin kyauta kenan kinsan yadda nakesan yaronmu jitai qafafunta basa son daukanta taja ta zauna.


Duban inna tayi taga itama din kallonta take alamun tana buqatar amsa tai saurin kawai da kai gami da miqewa ta suri danta dake cinyar Abbakar din tai dakinsu.


Inna ta miqe ta bita aba tana shiga tahau tambayarta ummu daman qarya kike min kinada miji ko ta ce wallahi inna ba miji na bane shine Abvakar dun da nake baki mamaki ni wallahi banmu ma taba maganar soyayya dashi ba gyada kai inna tayi tai waje kawai.


Washe gari masu siyayya sunata zuwa inna ta kira Abbakar dakinta yana riqe da takwaransa yana masa wasa.


Bawan Allah kadubi girman Allah ka fadan gaskiya ummu ta ban labarinta tas ni tacemin danta baida uba bata taba aure kai kuma kazo ka tubure kai mijinta ne ka fadan gaskiya.


Ya kalli yaron dake ta faman bangala masa dariya tausayinsa ya cika shi kafin ya fadawa inna gaskiyar komi ta gyada kai alamar yadda to kai yanzu da ka biyota nan me kake nufi kenan kazo ka dauketa ne ka kaima abokinka ya aura ko kuwa.


Ya karkada kai alamun a'a nazone nan inta yadda zata aureni adaura mana aure a matsayin ada na mata saki dayane aka maida mana da abunmu kodan ruwar mutuncinta anan garin naku da basu san komi game damu ba inna tai shiru shikenam kaje ka sameta kome tace inyaso se inji.


Ko da yaje tana ta hada hadar bada fulawa da za'a siya rasa me zaice mata yayi bama tasan yazo kusa da ita ba yadaure ya matsa kusa da ita dan da kunnenta yai maga ahankula wanda ita kadai zata ji yace ummulkairi inasanki da yawa zaki aureni......


Nigeria


Ita ko Hajiyar Abbakar ko da ta amshi wayar agurin ummi kiran Abbakar ta shiga yi sai dai taqi shiga hakan yasanya ta cillowa ummi wayarta harsai da ta fashe ummi bata bi takan wayar ba tai gun hajiyar.


Kuka tasa ma Hajiya sai tana roqonta tayi haquri daqyar ta haqura nan ta bata labarin ummun da yake hajiyan tasan ummun sai dai ba wanda yasan inda ta tafi ba dan dayawa suna zaton ko anmaidata gurin mum dinta ne.


Ta tausayama rayuwar ummu sosai sai dai vata nunama ummi sosai ba kawai dai ta haqura da mitar da take.


Muktar ne ya fito ganin idanun ummi ya kumbura yai jane yasa dariya towo ke kuma keda wa ta watsa masa harara ni sa'arka ce eyye shima harararta yai gami da zama kusa da hajiyarsu yakalli hajiya ummata dan Allah me yasa kika ce wannan yarinyar ce ta rigani zuwa duniya.


Hajiya tai dariya to shi kenan inka yadda to ita ta zama auta dun in dena cema auta ummi tasa dariya aikuwa na yadda ya miqe cab ni ban yadda ba wallahi yai waje hajiya ta miqe itama tana dariya tai dakinta.


Ummi ta dauko wayarta duk ta fashe wani hawaye ya zubo mata dan daqyar yah babba ta siya mata iPhone dinnan yanxu ko wata batayi ba ace ta yi raqa raqa haka haushi kamar me.


Yau muktar zai koma dagyar yasamu wayar yah Abbakar sukai salama daqyar Abbakar yasha kanshi ya haqura danshi cewa yai sai yazo sunyi sallama.


Yau ummi tana da test tun safe ta tafi taso sosai ace da ita za'ai rakiyar dan biyun nata har kuka tayi shi kuma sai dariya yake mata duda daurewa yake dan yanajin dadin zaman gidansu musanman rayuwarsu da yar biyun nasa.


Sai da ta tafi ya tuna da suprise din da yai niyar bata hakan yasanya ya faki idon hajiya da yayyensa da zasu rakashi yai makarantar su ummi din.


Sun shiga test gashi sai sunyi awa daya shi kuma qarfe goma zasu tashi ya rasa ya zaiyi kawai yai kasadar shiga ajin.


Cikin sa'a yaya yaya Nasir ne wato yayan mahduz ya kuma sanshi.


yana ganinsa ya danzo bakin qofa yace muktar lafiya ya gaisheshi gami da miqa masa ledar yace yah pls ka baima ummi ina sauri zamu tafi ne ok yace dashi gami da komawa ajin.



Muktar ya daga mata hannu tai murmushi kawai ta ci gaba da rubutunta.


Sauri tayi ta gama duk a burinta na taje taga tafiyar dan uwan nata.


Taxo fita Nasir yace ummi ki jirani anan waje ina zuwa yo tace masa taja ta tsaya kawayenta nata tsokanarta waiko dai ko dai dan ba tun yau sika fara ba tace musu yayanta ne shi yasa yake sakar mata fiska sunqi yadda dan shi din bama ko yaushe yake dariya ba.


Sai da ya gama karbar papers dinsa tas sannan ya fito haushi duk ya ishi ummi ya miqa mata ledar da muktar ya bashi gashi inji yayanki muktar ta turo baki kai yaya Nasir qanina dai yai dariya shima to gyanbo sarkin san girma yai gaba abinsa, zainab tace oh wow Allah ummi mutumin nan yayi naso nice muke wasa dashi haka tuni zansa masa sona suka saka mata dariya gabaki daya.


Niger


Ita ko ummu daki ta shige da sauri jin magan ganun Abbakar inna ta gani ta zube kan gado tana haki kai kace wadda tai wani uban gudu inna tace ummu lafiya kike irin wannan haki haka.


Cikin rawar murya take magana inna wai malan ne yace zan aureshi inna tai murmushi to me kika ce masa bakomi to kije ki tambaye shi ko dagaske yake inyace eh inaga ki yadda kawai.


Waje ta fice ta ci gaba da aikinta yana kallonta ganin bazata masa magana bane yasa yai waje abinsa riqe da takwaransa.


Sai da ta kammala komi itama tai waje yana can nesa da gidansu yana wasa da Abbakar dinta ta qarasa inda yake din tai sallama ya amsa a ciki ta jima tsaye baiko dago ya kalleta ba ya ci gaba da abinda yake.


Ganin tsaiwar bazata mata bane yasata zama dan nesa kadan dashi tace malan ina kwana bai amsa ba bakuma kalleta ba taji zafin abinda ya mata ta dai daure ta kuma cewa.


Yah dazu me kace ya dago ya kalleta

11 / 20