Author : AXEEX Category : Romantic Story
dawo sir make up test in tawa yaja tsaki pls sir tace kafin yace wani abu jeki i will think about it dan Allah sir ta kuma fade yaja tsaki gami da fadin oppps kije during exam ki amsa all question in yaso se kisa C.A a biyun zan gane thank you sir ta fada tai saurin ficewa.
Wayarsa ya dauko ya danna recording din da yai nasu yana kuma sauraro at list yasamu evidence against ita da nasir dole yai wani abu he yas to expose them dan kare martabar abokinsa.
Miqewar dazaiyi wayar ta fadi jiyai har cikin ransa faduwar wayar yaisaurin daukowa yai yai ta kunnu taqi oh my goodness ya fada yana dan dukan goshinsa memory din ya ciro yasa ada wayar sedai ba recording shedar yana kan wayar ya Allah ya fada gami da komawa ya zauna wani hawayen baqin ciki ya gangaro masa ya rafka uban tagumi yana tunanin abinyi.........
Koda ummu ta fita daga office din kai tsaye ficewa tai daga sch din saida ta hau dan sahu sannan ta dauko wayarta tafara dialling din number din Aisha yafi sau hudu bata dauka va kawai sai ta kira Fatima ita ma same thing happen kawai sai ta zura wayarta a jaka.
Saida taje gida sannan kiran Aisha ya shigi lafiya dai irin wannan kira haka bata bata amsa ba ta kuma tambayarta kina ina ne ke muke jira fa.
Tun dazufa nake nemanku ban gankuba shine na tafi gida nakirama in ce muku na tafi gida se mun hadu gobe tsaki Aisha taja Fatima tai sautin karbar wayar cikin fada take magana anman wallahi ummu bakida muntuci inba rashin mutunci ba kinsan bazamu tafi ba sai mun jiraki kawai saikiyi tafiyarki ayi hakuri naga tun wajen fitowa ta banganku ba kofa office din ban shiga ba kutt bakishiga ba kika ce muna kallonki fa kika shiga munfi awa biyu baki fitoba.
Ganin yadda Fatima ke fada yasa Aisha karbar wayar haba ummu taya zaki mana hk tsaya ma naji fatima tana cewa wai kince ko office din baki shiga ba No bata fahince ni bane kinsan ta da fushi inta hau bata tsayawa cin ribar zance zata hau fada.
Cewa nayi ina shiga na fito fa baku dai kula bane ni kuma banyi zaton kuna nanba natafi masallaci nemanku da banganku ba na tafi gida anya ummu idanuna fa nakan office din kinsan dai karatu mukazo ko bataji komi kan maganar Aishan ba dan tasan ta da tsantseni da fadar gaskiya gama kowaye .
Ki yadda dani abinda yakaini kawai nayi banmayi make up dinba cewa yayi in answering all question 2 for test in yaso 3 for exam ok yayi kyau yanxu kina ina ina gida ki yadda ina gida bakomi ki shafan kan Abbakar zaiji insa Allah sukayi sallama.
Ta goge hawayen da ya zubo mata wani dacin rai na taso mata tarasa me ke mata dadi ji take inama batazo duniya ba ko inama ta mutu kafin a haifeta.
Gidansu mahfuz
Hajiya wai bakya ganin haqqin ummulkhairi ke dawainiya da dangin nan namu musanman nahfuz taja tsaki me muka mata da haqainta zai dawai niyada mu eyye mara mutunci.
Gani naifa yah mahfuz ya haukace gashi an kasa gano me ke damunsa Hajiya tai shiru kin tunan wani abu nasan tabbas da sahannun uwar yarinyar nan a abinda ya same shi sai yanzu na fuskanta aljanu suka turo masa suka masa farraqu da dan uwansa maza kiramin doctor yusif.
Yawwa Doctor so nake mahfuz ya dawo gida mu gwada ruqiyya tunda naga na asibitin ba sauqi kinsan nayi tunanin haka aqwada ruqiyya hakan za'ayi.
Kiramin musa ummi ta miqe saigata ta dawo da musa yana biye da ita ya russina ya gaida hajiya gami da cewa gani.
Yawwa musa so nake kaje kadauko min mahfuz a asibiti yadan fada da razana hajiya mahfuz eh shi so nake ya dawo gida mu masa na gida tunda na asibitin yaqi.
Hajiya ya warkene ya fada cikin rawar murya inda ya warke ai dabazance ma zamu masa maganin gargajiya ba ko.
Jikinsa ta hai kyatma anman hajiya taya zan iya tawo dashi cikin sauqi ina tuqi to me kake nufi yai zuru zuru da ido ummi yasa dariya wallahi hajiya da gaskiyarsa taya zai dauko mahaukaci a mota shi daya wanda yake cewa zai kashe mutane kawai ya shaqeshi.
Hajiya ta cilla mata daquwa ungonan dan uwan naki ne mahaukaci to hajiya aiba qarya akaiba ok to naji ku tafi tare sai ki riqe masa shi ta zaro ido hajiya ni eh ke inkuma bazaki ba to kinsan ba ke daya na haifa ba tasan indai hajiya ta fadi haka to taki qololuwar jin haushi.
Ta miqe muje ta hau sama ta dauko gyalenta hajiya mun tafi Allah ya kiyaye tace amin.
Tunda suka fara tafiya ba wanda yacewa kowa ci kanka kowa zulluminsa taya iya tafiya da mahaukaci cikin mota.
Koda suka isa sunje office din doctor usif sunyi cike cike kafina abasu mahfuz, yadda ummi ta ganshi ya daga mata hankali dan mahaukaci sak tagani ya tara uwar suma da gemu wanda dauda har tafara sawa ya koma jaja.
Koda ummi taje dab dashi amai ne kawai batai ba sabida wani tsamin dauda da yake tace yah mahfux ka gane ni ya kalleta ba ummi bace tadanyi ajiyar zuciya aqallah ya ganeta.
Lafiya me ya kawoki nazo mutafi ne nine nace miki inasan mu tafi yadda yake magana cikin fushi da fada ya tsorata ta a'a to ba inda zani pls yah kinga alamar wasa a idona.
Ni nariga na yanke shawar qare rayuwata anan dan haka zaki iya tafiya yah kayi haquri kazo mu tafi kowa na kewarka qarya kike kowa yafisan Nasir gashinan sabida shi kowa ya mance dani kowa ya tsaneni kowa ya gujeni.
Cikin sauri tace yah kayi haquri inkasa wa ranka kowa ya tsaneka ka cire hajiya tanasanka kullin burunta kasamu sauqi pls kazo mu tafi kodan hajiya.
Miqewa yai yabi bayansu ummi ta fara yadda da batun hajiya anwa mahfuz da Nasir farraqu tunda gashi har yasama ransa anfi san nasir duda yana cikin hauka.
Suna tafe tana kaf kaf dashi cikin mota dan tsoronta karya shaqo me tuqi ko ya bude ya fice yana fiskantar ta sosai kasantuwarsa bayan yai degree dinsa a fanni qere qere yaje yayi wani sabon degree din a psychology baisan sanda dariya ta kufce masa ba aikuwa gabaki dayansu ummi da musa hankalinsu ya qara tashi fuskantar haka ne yasa shi yin shiru.
Agida ma kowa kaf kaf yadingayi dashi har suka isa sashen hajiya sai asannan ummi ta saki sanyayyar ajiyar zuciya aqallah sunzo lafiya.
Baibi ta kan kowa ba ya shige
bangarensu toilet ya shige ruwa me dumi ya hada yai wanka ya wanje jikinsa yakai sau goma still bedana jin wani iri ba haqura yai ya daura towel ya hau shaving din gemun ya rarrage sumar kansa sannan ya sake wanka aqalla yadanji dadi.
Ya fito yana saka kaya ne hajiya ta shigo riqe da kofi ummi na biye da ita da flask gabaki daya sunyi mamaki mahfuz ya koma mutun sak hajiya tazauna gefen gadon ummi ta zauna gefen kujera.
Saida ya kammala sakayan yazo ya gaida hajiya aqallah ta danji dadin ganinsa yanzu va kamar dazu ba ga tea kasha ko zakaji dadin cikinka ga danwake kuma sekaci yunwa yakeji hakan yasa be musa ba ya amsa yasha.
Yanasan dan wake sosai hakan yasa ya karba da zumudi yahauci saidai taunar farko yaji ba dadi dan gabaki daya bakinsa ba dadi dagyar ya hadi a hankula ya furta Allah ya isa Nasir hankalin hajiya ya tashi tadai daure.
Ganin ya ijiye yaqi ci ne ta kalleshi kadaure ka ci hajiya wallahi ba test daurewa zakayi kaci se ahankula komi zai koma normal.
Ummi kije ki samo toka ki gasa masa nama da ita zai temakawa test din bakinsa to hajiya.
Da yamma agun cin abinci kowa ya hallara har mahfuz inka dauke Nasir mahfuz yakai lomar abinci baki kenan nasir yazo yaja kujera ya zauna kamar koyaushe kujerarsa kusata da ta mahfuz ya sha kansa qanina yajikin naka ya tankade hannunsa cema akayi banda lafiya ne ya miqe fuuu yabar gurin.
Koda Abbakar yabar office din gida ya wuce dan gabaki daya ransa ya baci yama rasa abinyi.
Da Amira qanwarsa ya ci karo zata fita tace lah yah sannu da zuwa ya amsa yawwa ina zuwa haka da yamma yah zani gidansu khairiyya ne zamu dan tattauna yai dariya zadai asha gulma tai dariya wallahi yah ba haka ne kyaji dashi se an dawo yai ciki be jira amsarta ba.
Gabaki daya mutan gidan na falo har masu aiki shima anan ya zauna bayan ya gaida hajiya yasa baki cikin firar da suke hakan ya rage masa kashi arba'in na bacin ran dake damunsa.
Kiran sallahr magariba ce ta tashi kowa dan kawo farilla ya kai kayansa samansa kafin ya daura alwala ya fice.
Daga masallaci gidansu mahfuz ya wuce baisan an dawo da mahfux dinba ganinsa ba qaramin dadi ya masa ba sun tattauna kafin suyi sallama har ya fita ya dawo.
Ban fada ma ba wani abin takaici nan ya zayyana masa komi cikin takaici Abbakar ke bashi labarin mahfuz ya goge hawayen da yazo masa ba komai Aminin Allah ya kawon mafita amin Abbakar yace.
Kasan me inji mahfuz sai kafada Abbakar ya fadi ni wallahi bawai gidan mahaukata da aka kaini ne matsalata va babbar matsalata itace San ummu da kullun ke qaruwa cikin raina ko nayi yunqurin cireta araina abu kamar.
Yana daya daga abinda yasa nake jin haushin yah nasir da ya aureta ni wallahi yanxu ji nake da rashin ummu gwanda abanni in dawwama gidan mahaukatan.
Abbakar ya dafa shi se haquri taka qaddarar ce a haka uhun ba qaddarata bace nasani haqqine ke bibiyata tunda Allah ba azzalumin sarki bane yana sakawa wanda aka zalunta kadena sa haka aranka ka ci gaba da qoqarin mancewa da ita ni zan wuce kar hajiya taga na jima.
Yana barin inda mahfuz din yake ya share hawayensa wanda tun dazu suke san fitowa yana jarumtar riqesu shi kadai yasan azabar da yake ji na san dalibar nan tasa dauriya kawai yafi amin nasa.
Ashan gida ma bayan yaci abinci yaje gurin motsa jikinsa jiyai duk jikinsa ba kwari dakinsa ya shige ya rasa abinyi wayarsa ya dauko ya hau kunnawa ko Allah zaisa ta kama amman ina tace batasan zance ba tsaki yaja yahau gado ko Allah zaisa yadan samu bacci.
Baccinma gabaki daya yaqi zuwa daya rufe idanunsa ummu yake gani tana masa murmushinta da yake qara mata kyau agunsa yarasa wace irin zuciya gareshi me nacin tsiya da take jawo masa masifa kala kala ace dik yan matan dake sansa takasa kallonsu sai matar wani.
Ganin da gaske idanunsa basu shirya yin bacci ba yasa ya miqe yashige toilet dinsa ya dauro alwala ya hau nafil filun.
Yau lahadi ba inda Abbakar zaije hakan yasa ya fito babban falo dan yin fira ko zai samu ya raje kewar da ke damunsa.
Hira suke sosai inka ganshi bazaka taba cewa yana cikin damuwa ba danshi din akwaishi da jarumtar boye damuwa duk girmanta shi yasa ko hajiyarsa take cewa yana da zurfin ciki.
Yau litinin yanada kula da masu jarrabawa qarfe biyu hakan yasa tun asuba da yasamu bacci ya debeshi yai me isarsa dan ya dade be yi me dadin sa sai goma ya farka yai wanka sannan ya sauka danyin breakfast dinsa.
Bakowa a falon sai kwanukan abinci dake kan dining da alamu nashi ne kawai saida yaci sannan yaje dan gaida hajiyarsu.
Tana kishin kide tana tasbihi suka gaisa kafin yace hajiya mu zamu fita tadan gyara zama to Allah ya kiyaye ya tsare ya amsa da amin cikin jin dadi.
Gidansu mahfuz ya wuce sun dan taba fira da hajiyar sakamakon mahfuz din na wanka a hankula ya fara sako mata da maganar ummu aikuwa nan danan ta hau wato mun samu ya mance da maganar shine zaka zo ka tayar mana da ita to ahir dinka.
Sin sin ya miqe yai dakin mahfuz din dan jiransa.
Wai mahfuz in tambayeka mana inajinka in har ka yadda ummulkhairi ba matar nasir bace me yasa sukayi qaryar aure mahfuz yai shiru na dan lokaci kafin yace waya fada maka ban yadda ba ni wallahi na yadda matarsa ce.
Kasan kawai meke ban mamaki seka fada inji Abbakar kawai ina mamakin me yasa yah nasir yakesan dole sai ya haukatani ta hanyar nunan bashi nake gani innaje gidan matar tasa.
Abbakar yai dariya ba dole ya haukata ka va fansa suke dauka shida matarsa mahfuz yai danshiru na wani lokaci yes u are right wallahi se yanxu na gano dalili wato ya zabi mace kan dan uwansa.
To wallahi tunda haka ya zabarma kansa ni nasan nafishi santa to zan nuna masa hauka sedai kowa ya rasa dan wallahi kashe shi zan yau bako gobe ba ya miqe ya zari wuqar dake kan kayan marmarin dake bed side drawer yai waje yana huci............
[12/31/2020, 5:51 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[12/31/2020, 5:52 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR*
*PAGE 60---70*
Da sauri Abbakar ya riqoshi yajawo shi zuwa ciki haba mahfuz kasan nasan da hankalinka pls act serious ma katsaya ka saurareni ya amshe wuqar.
Ni ban yadda ummu matarsa bace mahfuz ya zaro ido what bafa ka yadda ba kace eh ban yadda ba to sabida me sabida kawai ban yadda ba ayanzu banda hujja anman ina ji ajikina ba matarsa bace kawai suna maka haka be dan ka fita daga rayuwarta.
Ka yadda dani karka yi abinda zakayi danasani a hankula komai zai koma dedai haka yaita tausarsa har ya samu ya sauko.
Fatima ce riqe da paper din test dinsu tana faman mita wallahi dedai nayi mutumin nan zai kansilemin dan Allah Aisha kalli nan ba haka ake ba ta kalla to ba gwanda keba nida ba'amin recording bafa to ba inkin kai masa zai miki ba.
Pls ku rakani nai photocopy din paper dinnan suna tafe fatima na mita yayin da Aisha itama keyin tata kan rashin mata recording duda yake lefin tane na rashin saka reg. Number dinta.
Ita dai Amina ba abinda take fadi se maganar absent da aka saka mata a last exam yayin da ummu tai shiru ita kadai tasan abinda ke damunta gabaki daya ta dena jin dadin sch din kawai tana daurewa ne.
Kinsan Allah maidama mutumin nan zanyi jibi fa ko makamin nan beba yaushe zaki kaimasa ya shigar miki Fatiman ta tambayi Aisha ko yau ne sai muje inasan zuwa can chemistry lab ma ok se muje gabaki daya.
Sunyi rashin sa'ar samun me photocopy hakan yasa suka kira sauran frnd dinsu kan suzo su tafi daga nan zasu viya suyi ahanya.
Sun hadu a CIT inda student dinnan suke graduating se murna suke se anan ummu tadan ji sukuni aranta dan ita din mutunce me san taga mutane sun kanmala karatu musan man data ga yara qanana se taji dama ita ce.
Tuni qawayenta sunyi gaba ta tsaya sakato tana kallom masu bikin sunata selfie yau batazo da me rainonta ba bata da lafiya koda zasu shiga exam sai wata yar level 4 ta roqa ta riqe mata Abbakar shine ya matso alamar ya tashi tai saurin sakkoshi ta matsa gefe dan bashi abinci.
Da yake yafara shan kamu shi take bashi sha yake sosai alamun yunwa yakeji yadda yakesha da kuma tunanin da zuciyarta ta tafi yasa batasan sa'adda hawayen da suka cika mata idanu ya zuboba.
Jitai an dafata ta baya tai saurin jiyowa Hafsa ce kinsan tun dazu muke nemanki ina su fatima inji maryam assha kukan me kike haba ummu ki dinga ragema ranki damuwa pls inji maryam ke wallahi kina da matsala nasan duk bazai wuce kan exam din yauva kawai ki shateta exam luck ce kawai inji hafsa to Allah ya bamu sa'a su suna waje jen fais muje nace su jirani.
Suna tafe hafsat na selfie da dan surutanta intayi wani tauawo ummu tayi musu su biyu wani ta jawo maryam, yayin da maryam ke faman tambayar ummu wace amsa ta samo a questions din yau wasu ummun ta bata amsa wasu kuma tai shiru.
Sun yi photocopy din inda fatima da amina suka wuce toilet na CIT mosque basu jima ba suka dawo.
A bus stop suka hadu da halima da sauran frnds dinsu sun hau mota tare yan hanya sun sauka ahanya yayin da su suka sauka a old side din sch din tasu dan can ne gun da zasu.
Sinyi rashin sa'ar samun duk wanda sukaje nema hakan yasa kawai ko wannen su ya wuce gida kan zasu hadu ran alhamis.
A gida ummu ta rasa me ke mata dadi dan tun randa Abbakar ya titsiyeta batajin dadi ita ba abin ta fadawa Nasir ba tsoronta daya kar yaje ya ballo mata ruwa abinci ma ba koyaushe take ci ba ko tahajin yunwa data fara ci zataji ya fita aranta.
Ran alhamis da sassafe ummu ta shirya tai sch dan sunyi zasu hadu dasu hafsa 10 na safe.
Basu wani makara ba sukazo duda kuwa ta dade da zuwa Fatima ce last din zuwa suka dunguma sai math department sunyi rashin sa'ar samun wanda sukaje gunsa bayan sun tambayi maqocinsa ko zaizo ya basu tabbacin zuwansa suka koma qasa dan jiransa.
Zaune suke sina hira sama sama yayin da karatin paper din dazasuyi yau yafi qarfi maman humaira ce ta dauko wata paper suna dan tattaunawa akai dagowar da Aisha zatai taganshi yazo suka miqe dan bin bayansa.
Faduwar da Hafsa tai ne yasa har isarsu bakin office din basu bar dariya ba ganin office din abude yasa su shiga taitayinsu suka jira na ciki ya fito kan su shiga.
Bayan sun gaisa cikin hade rai ya ce lafiya me ya kawoku paper dinta Aisha ta nuna wadda ya rubuta not recorded ya amsa da Id dinta ya shigar yayin da fatima tace complain gareta ya karba yana dubawa.
Ya dago a fusace haka na koya muku tai tsuru tsuru ya miqo mata paper dinta