Chapter 3 Reading ABBAKAR BOOK COMPLETE DOCUMENT by AXEEX.txt Arewa Novels

ABBAKAR BOOK COMPLETE DOCUMENT by AXEEX.txt

Author :  AXEEX Category :  Romantic Story

Chapter   3 / 20

6K to 9K   out of 57.6K words

qalau qanina yahau zubama kansa abincin.


Kusa da mahfuz din ya zauna yanaci yana nazarinsa saida yakai lomar qarshe kafin yace wai qanina meke damunka ne naga duk ka rame gashi ka rigani fitowa anman har na cinye na barka bakomi yaya kawai banajin dadi ne.


Ayya anman ai daurewa zakai kaci abincin seka sha maganin cuta da yunwa ai sai abin yai yawa to yaya zanci yawwa ko kaifa ya miqe zai bar wajen.


Yai saurin dawowa subhanallahi ciwon mene haka a qafarka mahfuz ya kalleshi da mamaki kamar bashine jiya ya ji masa shi ba.


Ina tambayarka ciwon me ne haka ta yaya ka jishi ya hqu sosa qeya gqnin yadda mutanen falon suka zuba masa na mujiya kowa nasan jin yadda akai faduwa nai jiya munje unguwa da Aminin sunan da mutanen gidan ke fadawa Abbakar Ayya to Allah ya kiyaye ya fuce.


Sama sama Abbakar yaci Abincin karinsa sauran ya faki Hajiyarsu yaje ya kaiwa kaji yana yo kwana daga gurin kajin nasu yaji dariyar maryam Allah ya kamaka wato kaji kake kawowa to abakun hajiya tai saurin juyawa zatai cikin gida.


Yabita da sauri yana roqonta haba yar qanwata ki tsaya kiji mana tai masa banza ganin tai falon hajiyar yasashi kai kwanon kitchen ya bita da sauri.


Haba qanwis bafa ma haka dake karaf kunnen hajiya zonan autana me yayi fadamin ta kalleshi duk yai wani kalar tausayi vashi bane nace ya temaka yaje yamin test yace ba inda zashi ya saukar da ajiyar zuciya dan yasan indai hajiya taji yaqi cin abinci ya gama yawo.


Hajiya tasa dariya kyaleshi kije kiyi abinki da kanki zaki ci fiye dashi kinji autana anman hajiya kedai kawai ki yadda dani zakici zan miki addu'a to hajiya ai shi kenan yawwa ko kefa Hajiya ni na tafi yace mata ok seka dawo Allah bada sa'a amin ya fice.


Yakai bakin gate a cikin motarsa yana shirin fita maryam ta fito da gudunta yaja ya tsaya ta tsaya bakin tagar me zaman banxa to sarkin rigima lafiya zaki tsaidani eh kace haka mana I save u today dole kabani tukwici ko in fada mata ai daman nasan da biyu ya ciro kudi ya miqa mata ta karba tana dariya shima ya kada kai yana dariya.


Inba dan dole ba da ba'abinda zai hanashi dena zuwa buk koyarwa tun da ya fara tuqin abinda ke faman kai kawo a ransa kenan har ya isa yai parking yai qofar office insa.


Kamar ance kalli gefe ya hango ummu riqe da babyn ta a hannu Fatima na gefenta suna ta dariyarsu cikin nishadi wani qululun takaici yazo masa wuya lallaima yarinyar nan ta rainashi wato shi ta gama raina masa hankali ita tana cikin farinciki da aurenta tana chat dashi tasa ya shaqu da ita rasa abinda ma zaiyi yai.


Jiyar Fatima na fadin lah Aminiyar yafazo dan bari ya dan jima da shiga kar yaga daga zuwansa min takura masa haka ne kuma.


Da sallama suka shiga office din ita da fatima suka gaisheshi a ciki ya amsa kafin yace lafiya me ya kawoku Daman make up din dakace zakamin kullin in nazo bakanan oh shine daga zuwana zakuzo ku takuran basu ce komi ba any way zan baki assignment kiyi submitting jibi but ki baima captain inku sai ya kawon ta amshi question in tana godiya suka fice.


Binsu yai da ido zuciyarsa na ayyana masa abu buwa da dama masu kyau da akasunsu yaja tsaki gami da diban kasan zuwa inda zaima wadanda yace suzo yau lecture.


Koda yaje ma ajin be iya tabuka komi ba ya rasa wannan wace irin masifa ce ya kawo lecture insa asabar dan duk sanin yan ajinsu ummu basa karatu week end akalla bazai ganta ba anman se ace yana shigowa ita zai fara gani.


Abu daya zakai zuciyarsa ke fada masa nigeria sa fadi take kawai ka nemi aiki a wani state in ka koma can wataqil ka huta da wannan takaicin jiyai yayi na'am da shararar ya miqe dan dauko paper a dara barin dan fara rubuta takardar neman aikin in ya tashi yakai amasa printing dan bezo da system inshi va bama yasan se yaje gida ya sauya ra'ayi......


Ko me ya tuna oho ya hau yayyaga paper din ya miqe yabar office din.


Abinda bai saba ba wato yawo cikin sch din shi yaji yana sha'awa tafe yake cikin nishadi ransa fes yakejinsa .


Daga nesa ya hango yarinyar da kema ummu raino haka kawai yaji yanasan ganin babyn ummun ya dan matso dab da inda yarinyar keta faman jijjiga yaron yace ki miqama mamanshi shi mana tana test ne ta fada ayya kawoshi to.


Tai saurin kuma ruqun qumeshi tace kar inbama kowa to ai ba guduwa zan dashi ba ta miqa masa shi sabida kwarjinin da yai mata bawai dan taso ba cikin ranta kuwa tsoron kar uwar dakin ta tazo tazo taga ta bawa wani ne.


Masha Allah ya fada a fili yayin da a ransa yake fatan inama ace yaronsa ne yaron kuwa ya bangale da dariya dimple insa me kyau ya bayyana yasunansa ya fada sunansa Mahfuz ya kuma mai maitawa mahfuh tace eh anman abbasa ke kiransa dashi ummansa tace sunan danta Abbakar wani abu ya ziyarci zuciyarsa yai saurin kawar da tunanin da fadin Allah ya raya shi tace amin ya miqa mata shi yabar gurin zuciyarsa cike da tunanin sunan yaron.


Abin duniya duk ya ishi mahfuz hakan yasashi shi yanke shawar zuwa yasamu yayansa nasir.


Yana zaune yana rubutu a system insa Mahfuz yashigo da sallamar Nasir ya amsa batare da ya dago kai ya kalleshi yaci gaba da abinda yake Yah gurinka nazo ok yace ya rufe system in ya maida hankalinsa gareshi.


Inajinka maganar me zamuyi akan matarka ne What ya fada mata ta kuma kai kamin auran yadda yawani hade gira yasa mahfuz shiga taitayinsa ina tambayarka kaikamin auran yai saurin cewa ba.....bame ba .


Daman kan ummu ne ta gidan baba yasir anganta ne ya fada a'a kwanaki ne daman mukaje gun wata nida Amin naga ashe tayi aure ta aureka.


Bai nuna wata razanaba ko tsoro yahau fada ni ta aura kuma sanin kanka ne banida aure bakuma ni da niyarsa ayan kwanakinnan se dai in har alhakinta ne yafara haukata ka kake zaton kowa ka gani ita ce yarinyar da ba'asan inda take ba ake zaton tabi uwatta shine zaka zo kana tunanun na aureta.


Wallahi yah ita nagani kuma wallahi yah kai nagani a matsayin mijinta ai ko na haukace naganka zan ganeka saukar marin da yaji yasashi saurin miqewa a firgice fitar min adaki da alamin ka haukace din da gaske sha_sha kawai.


Washe gari da sassafe yai dakin yayan nasa ya ganshi yana bacci yai sauri ya fice daga gidan sai gidan ummun.


Bugun da yake faman musu na hauka yasa gabaki daya suyo bakin gate in da abinda basu saba ji bane.


Daba dabaya ya fara ja ganin yayansa Nasir sanye da rigar bacci yana mittsika ido alamin baccin be isheba.


Shima mittsika idon ya fara kodai dagaske na haukace ne ya fadawa kansa no wallahi da hankali.


Malan lafiya mutumin ya fada nazo tafiya da qanwata ne abarsona what kanada hankali kuwa mata ta cefa ganin bazai bashi hanya ba yasa tankadashi ciki ya hau jan ummu tana tirjewa.


Mutumin ya dauko waya ya kira police sukai gaba da mahfux din yana faman kuru ruwar sai yadauki masoyiyarsa
[11/22/2017, 9:17 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*40-45*
Haka mahfuz yana ji yana gani police sukai gaba dashi yana faman ihuu tuni yan kallo suka cika gurin duda kasantuwar lokacin sassafe ne.


Saida mahfuz ya kwan ya yini a police station kafin asamu labari a gida dan hankalinsu gabaki daya ya gama tashi anata tunanin ko lafiya Nasir da hajiya ne suka fara zuwa aikuwa yana ganin nasir ya hau fada da zage zage mugu azzalumi wallahi saika saketa ya shaqe nasir dagyar aka fitar daga nasir din daga dakin.


Shine wallahi hajiya shine haka kawai yake fade.
Hajiya ta riqe mahfuz cikin kuka tana fadin shine mene yaci gaba da fade ta jijjagashi sosai kafin ya koma hayyacinsa ka nutsu kafadan me ya faru.


Hajiya tah nasir ne yai aure ta miqe a razane haba dannan ni na haifeku gabaki daya yaushe kuma nasir in yai aure ka fada min wallahi hajiya shine kuma Ummun baba yasir ya aura dan naganshi yasa aka daureni ka tabbatar da abinda kake fade eh umma.


Ta koma tazauna haba biri yai kama da mutun shi yasa yaronnan yake cewa haukacewa kayi muje ina zuwa ta fice tabar dan dakin da suke ganawar.


Tana zuwa ta share Nasir da mari ya dafe gurin cikin qwalla ya kalleta menayi hajiya bansaniba ashe kai shasha ne da har zakayi aure bamu sani ka rasa wa zaka aura se yarinyar nan wadda uwatta bata ganin kowa da qima.


Ya dafe qirji cikin kuka yake magana hajiya ke kin yadda ina da aure in inadashi ai da tuni na dena kwana agida aje gidan da yace yaganni inyaso se agani inni inne tadan yi jim kafin ta koma dakin.


Mahfuz ta tambaya kwatancen gidan ya mata.


Eh kam yarinyar kamarsu daya da Ummu sedaifa yarinya tace ita ina batasan wani nasir ko mahfux ba har gidan iyayanta ta nuna mijinta ma ko kama basu hada Nasir ba police ma sun tabbatar ba nasir ne ya kawo mahfuz ba wanda yakawo mahfuz daban.


Aikoda su hajiya suka dawo da labarin komi Mahfuz ya miqe yahau dukan Nasir wallahi saina kasheka wallahi shine.


Ala dole su hajia suka yadda tabbas Mahfux ya haukace hakan yada sukayi bail insa suka kaishi asibitin kula da kwa kwalwa.


Duk wani bincike anyi anman ba'agano komi ba wato kwakwalwarsa normal take.


Saidai yadda inyaga Nasir yake tuburan dole hajiya naji na kallo ta yadda ya haukace tasa hannu dan kaishi gidan kula damasu tabin kwakwalwa.


Duk halun da ake ciki Abbakar baya da labari sai yau hankalinsa ya tashi danshi be yadda Mahfuz dinsa ya haukace ba.


Kai tsaye asibutun ya wuce aikuwa mahfuz din naganinsa yahau kuka tausayinsa ya cika Abbakar yadda kwana biyu kawai yaga mahfuz din duk yai baqi ya rame kamar bashi ba.


Ya hau rarrashinsa dan Allah amin kaje kacewa hajiya wallahi da hankalina Allah van haukace ba kai nasan zaka yadda.


Yadda yake maganar yaqarama Abbakar kwarin gwiwa tabbas Amininsa da hankakinsa wata maqirqisa kawai aka shirya masa.


Naji nayadda da hankali anman garin yaya me yafaru har aka kawoka nan ya bashi kabarin komi tabvas raina musu hankakin da yarinyar nan take ya isheshi yau zai maganin komi dan yanasan abokinsa yanaji yana gani baza'a mayar masa da Amini mahaukaci ba.


Ya kwantarma da Mahfuz hankali kafin yq fito daga gidan masu rangwamen hankalin.


Kai tsaye gidan Su mahfuz ya wuce baibi ta ko inaba yai bangaren hajiya abinda yake ba sabonsa ba shiga cikin falon gidan kai tsaye.


Yai sa'a tana falo suka gaisa kafin ya mata jaje ya dora da fadin yanzu hajiya kina kallo za'a maida mahfuz mara hankali vazakiyi magana ba.


Tai dan murmushi Habu kenan ai ba maidashi akaiba ya haukace din ne wallahi hajiya be haukace ba da hankalinsa haba dannan taya zakace be haukace ba mutumin da yake iqirarin kashe dan uwansa agabana fa.


Yana ihuuu yana shine ajalunsa yace yai aure alhalin qarya yake masa yace yaganshi alhalin bamashi bane bakajin wannan duk ba alamomin hauka bane.


Wallahi hajiya shi yagani tare muka ganshi taja tsaki daman ai abokin barawo barawo ina yabonka ashe kaima ka fara shan qwayar da yake sha nasan itace ta fara tamvayarsa inzaka tashi katafi to inkuma ansn zaka kwana sekayi tayi tamiqe tai sama dan wallahi kaima ban yadda dakaiba kar inje a afkamin.


Ya miqe yabar gidan takaici fal cikinsa.


Gidan da sukaje da mahfuz yai inda sukaga Nasir da ummun.


Yaro ya aika amasa sallama da me gidan yaron ya fito wai baya nan can saigata tafito.


Wake nemansa yai saurin dagowa daga daddanna wayar da yake dan ko a ina yaji muryarta sai ta gane nine ta fada.


Tace oh baya nan sedai inzaka jira ok va matsala yace ta koma ciki.


Ya kusa minti goma sha biyar mutumin ya parkee motarsa qofar gidan ga mamakin Abbakar ba Nasir vane anman yadan daurewa mamakinsa barka sannu ko yawwa kai kake nema na eh nine ok muje daga ciki ko suka shige.


Bayan ya shiga ya fito riqe da yaronnan da kodaga bacci Abbakar ya tashi saiya ganeshi dan tabbatar da abinda ke masa yawo arai na shakku yasashi miqa hannu kawoshi.


Ya amsheshi dadinsa da yaron kwai fara'a ya sunansa nahfuz yace ataqaice Allah sarki Allah ya rayashi amin yace ya miqo hannu ya amshe abinsa.


Nikam Kamar nasanka wataqil kwanaki dai munzo da abokina mahfuz oh naganeku kune yan iskannan masu shigarwa matan aure gidako yadan cige lebe dan yaji zafin kiransu da yan iska dayayi yaidai basar ehto koma me kakiramu ni ba hayaniya nazo ba nazone dan inasan yin magana dakai da matarka.


Ya miqe a fusace what dan mene inbazaka iyayi dani kadaiba to mata tata haramin alaik no maganece ta fahinta nakeso muyi kan abokina da kuka haukatar.


Kaga nafiskanci haka daikinyi pls tashi kabar min gida tun kan kadaga hankalin matata pls give me a chance wai baka ji me nace maka bane ko sai na hadaka da police na sassauta maka ne dan kawai na fiskanci kafi abokinka kamala.


Abbakar ya miqe yabar falon but kasani zan dawo kuma time in da zan dawo dole in magana da matar taka hakan kuma shi zai kawo qarshen matsalar nan na fada ma to muza nidakai dan halak ka fasa inji mijin nata.


Tunda yahau titi tunanin muhawarsu da mutumin yake yasan babu ta yadda zai iya magana da matarnan indai mutumin nan nanan but za'a iya kamashi inyaje ya shigar musu gida suka masa ihuuu gabaki daya tunaninsa a cunkushe yake ya rasa mafita.


Sauri kawai yake ya tafi sch ko breakfast din kirki beba ya bar gida.


Ko a office ma jira yai kawai takwas tayi ya wuce inda zaiyi lecture dinsa ta morning bayan ya gama yace wadda aka kawon complain bata da lafiya tazo yau for her make up ya fice be jira amsar student dinsa ba.


Aikuwa kamar tare suke yana shiga ta shigo riqe da babyn ta yadan kalleta ya kalli babyn zaki iya zama tace taja tazauna yai saurin murda makullin office din gami da zareshi ya zura a aljihu jikinta ya dau rawa ta mike ta daka mata tsawa koma ki zauna kika ce tak kome ya faru dake ke kika jawo yado gabanta dab da ita tana kallonsa yana kalkonta yazauna har yana iya jiyo faduwar gabanta suka hada ido ya daka mata harara tai saurin kawai da kai..........
[12/31/2020, 5:50 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[12/31/2020, 5:51 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR*


*PAGE 45---60*


Cikin kuka take magana pls let me go I beg ur pardon dan Allah, mtss yaja tsaki au daman ke kinsan Allah ne da har zaki hada wani dashi munafuka kawai taisaurin dagowa hawayen da ya cika mata ido ya gangaro.


Inkinga kinbar office dinnan to Wallahi kin fadan ke wace taisaurin kallonsa yes kinmaji na rantse sir bangane ba all i know am ur student kawai nop ba wannan nake san sani ba ki fadan mene alaqarki da mahfuz, Ni dakuma Nasir ni bani da wata alaqa dakai balle su ok kin shirya ma kwana ananko.


Ya shige toilet ya dauro alwala gami da fitowa ya tada sallah bayan ya idarne yaci abinci ya miqo mata sauran inkinyi niya kyaci ya sa hannu ya amshe babyn hannunta ya koma inda sallayarsa ke shimfide ya kwanta gami da dora babyn kan cikinsa ya lumshe idonsa hankali ba qaramin tashi yaiba ganin la'asar na shirinyi dagaske bazai barta ta tafiba.


Wata irin yunwa takeji abinka da me jego but batasan cin abincinsa dan bata yadda dashi ba yadda ta fuskanci yau din kamar a buge yake dan dazu da ya daka mata tsawa ta kalleshi taga idanunsa sun wani sauya launi batasan duk bacin rai bane kawai.


Dole in samu mafita naji zan fada ma alaqata dasu inkamin alqawarin barina in tafi ok inajinki ya fada batare da ya bude ido ba balle nuna concern innaji bayaninki ya gamsar dani mai zai hana inbarki ki tafi.


Mahfuz cousin dinane what ya fada gami da saurin bude ido ta gyada kai alamar da gaske take eh causin dina ne so Nasir fa ya fada.


Tai shiru oh baki shirya tafiya ba kenan ta kada kai cikin hawaye mijina ne ya miqe a tsorace sauran qiris babyn ya fadi ya tallafeshi mijinki ya fada eh ta fada oh i see.


Shiyasa kuka hada kai kedashi zaku haukatan aboki ko dan kawai san zuciyarku dan zalunci pls kabarni in tafi na amsa naka duk tambayoyinka dan Allah.


Naji zaki tafi but baki gama amsan tambayoyina ba baki fadan alaqarmu ba sir ni bamu da wata alaqa da kai banma sanka va sai a Bayero.


Karfa ki rainan hankali nasan me nake am 30 so kinga na fice kizo ki rainan hankali inkasa gano wa taya zakice baki sanniba bacin kinsan frnd dina if i can recall ke kika fara turon frnd requires sai yanxu na gane hakan duk yana cikin shirinku ne keda Nasir.


Sir kayadda dani bansanka ba eh naji baki sanni ba anman taya za'ai da aurenki ki dinga chat da wani harki dinga baima mijinki ku gaisa da wanin inbaya shirinku.


Sir in zaka tuna time in four years back muna chat but inka tuna bama na nigeria muna waya da kai inka tuna na fada ma i never being to Nigeria even though my Father's relative gaba daya suna nigeria na turo ma frnd requires ne dan kawai inasan yan nigeria naga kai dan nigeria ne.


Yai dan tsai yana tunani yes yatuna ok yanxu zamuje ki fadama iyayen mahfuz abokina da hankalinsa kafin inbarki ki tafi ta zaro ido what eh.


Hawaye ya gangaro mata haba sir ba haka mukai dakai ba pls let me go kazamto me cika alqawari any way zaki iya tafiya yabude mata office din gami da bata baby ta wuce.


Harta fita ta

3 / 20