Author : AXEEX Category : Romantic Story
dan Allah ki fadan meke damunki ko addu'a ce na tayaki ba komi ummi kawai na tuna da baya ne.
Ummi tace anti kan Yaya Abbakar ne ko ummu tai saurin kallonta da mama ki ummi ta qara da cewa insha Allah bazasu rabaku ba anti.
Ummu cike take fal da mamaki wato tana ma ummi kallon yarinya, bata qara shiga mamaku ga seda taji ummin na fadin anman anti kince musu kina sansa ta kalleta sororo alamar me kike nufi.
Anti kema se kinyi wani abu ni inaji ajiki na bawai sunasan rabaku ba ne suna son ji daga gare ki ne sunasan suji kince karsu rabaku da bakinki.
Ummu tace to inba san rabamu suke ba me yasa gobe zasu fara zaman court narasa me yasa suke san rabamu na rasa me ya musu.
Ummi tace anti kiyi haquri ki daure kije kice musu kinasansa ina cewa sukai zasu rabaku dan suna zaton auren dole ya miki dan baki da gata yanzu inya sakeki se wanda kike so zasu baki indai haka ne kenan ko shi din kika ce kinaso zasu baki.
Mamaki fal ran ummu me yasa dani banyi tunanin haka ba da ita kallon yarinya qarama takema ummi ashe duk tana sane da abinda ke faruwa agidan nace "ummu kenan daman yawancin iyaye kan ma yaransu kallon yara qanana irin basu san komi bacin da wasu yaran sunfi wani babban fahinta da iya zance"
Ruqo hannunta ummi tai anti ki daure kije ki fada musu har bakin falon baba mahfud ummin ta rakota seda taga tashiga sannan ta juya zuwa gurinsu.
Da baba Bashir ummu taci karo yace ummulkairi ba yanzu kika bar nan bane tai saurin cewa eh Daman magana nakesan muyi to to yace ai se mu koma cikin tabi bayansa.
Sauran da suma suka miqe da zummar fita suka dawo suka zauna ganin ya zauna itama ta zauna yace tace zata fadi magana ne.
Baba mahmud yace munajinki ummulkairi tai ta maza gami da nemo duk nutsuwarta kamin tace daman roqarku zanyi dan Allah karku rabamu da shi wallahi inasansa.
Gabaki daya suka kalli juna gami da sakin murmushi kamin Baba mahmud ya dora kika ce kinasansa tai shiro da kinsan haka kikai shiru ai da bata kai ga haka ba ma.
Yanzu kije maganar shiga kotu anbarta zan nemeshi dan shirya yadda tarewar zata kasance jitai kamar tasa ihu dan murna ta miqe tana sun sun dakai yayin da fuskarta ke dauke da murmushin farin ciki.
Hartakai bakin qofa Baba mahmud yace ummulkairi tai saurin kintsa kanta dan niyarta tana fita tasa tsalle ta juyo inda wata matsala zaki iya samun ko wanne cikinmu kinji to tace tai waje.
Alhamdulillah take ta fade gami da dansa gudu tai bangarenta tana shiga ta rungume ummi tana murna.
Seda ta nutsu ta fara tunanin ko ta ya zata ma Abbakar albishir tunda yanzu bata da waya tun kwanan Babyn ta arba'in da rasuwa aka kwace wayar duk dan karsuyi waya da abin sonta.
Ummi kije gidansu Takwararki kice tazo inji ni ta tawo da wayarta to anti tace ta miqe tai waje.
Afalo ta taddasu sunata fira ta gaida hajiya dasu Abbakar dinma kamin tace anti takwara daman mum(da yake wani zubin haka take cewa ummun) ce tace kizo kuma ki tawo da wayarki in kina wani abun kiban wayarki kawai in kai mata.
Ta6 wa ni rufan asiri muje inkai da kaina haka kawai a bunciken waya suka saka dariya gabaki daya ta ware mayafin abatar dake daure kanta ta yafa dan daman ashirye take sukai waje.
Abbakar ne ya biyo su yace yar mu zonan ta qarasa na'am yaya ya dan hade rai wato ita mum ni yaya to da ita dani waye ma yafi kama da wanda ya haife ki tasa dariya ita mana yadan hade rai alamar serious magana zaiyi itama ta nutsu.
Me mamar taki zatai da waya tadan kalleshi ko bajiki ni bane tace ai kai zata kira yai saurin cewa ni kuma eh yaya to me zata fadan a'a yaya kadai bari ta kirakan tukunna.
Pls ki fadan bazan ma nuna kin fadan ba yo daman cewa zatai anfasa zaman kotun yanzu su Baba sun yadda da aurenku da gaske kike eh mana yai dariya kije tukwicinki nanan tafe ya ja ya tsaya gami da tsurama wayarsa idanu jiran kiran ummu.
Ummi na shiga falon ummu ta amshe wayarta gami da yin daki ummi tace haba anti kofa gaisawa bamuyi ba bakuna ki fadan me zakiyi da waya ba ta juyo kindai san cikin samarinki ba wanda yakai matsayin in snatching dinsa ko tasa dariya waya sani ko kin hango wani ne da an raba auren ki maqale masa tsaki taja gami da fadin wushe nan yarinya ummi ta qara da inji dan fillo ba.
Tana shiga daki ta hau kiran Abbakar dan ko number dinsa bata tsaya nema ba takanta ta saka dan ta haddace number dinsa.
Bugu daya ya daga duda yasan komi abinka da namijin duniya se mazewa yai a'a ummi lafiya kika kirani bacun kinsan ina gida shiru tai can yace wai bazakiyi magana bane.
Daurewa tai tace Barka da safiya barka dai ya fada cikin sanyin murya dan tuni jin muryarta ya rage masa kuzari a'a ummulkairi kece lafiya dai ko tai shiru kamin tace daman kirawo ka nai mu gaisa yadanyi shiru aransa yace nikam zanso ganin randa yarinyar nan zata sake dani da yawa" nace araina kamar yau ne".
Daman kan zaman kotunnan ne yai saurin cewa gobe ko tace eh karkiji komi ki dena damuwa kinji insha Allah baza'a rabamu ba tai murmushi yai yace kinji dadi ko nace bazamu rabu ba ko tai dariya eh mana.
Kan yace wani abu ta kuma magana daman fada ma zanyi anfasa zaman kotun yanzu su baba sun yadda da aurenmu bata jura cewarsa ba ta kashe wayar gami da yowa waje.
Ummi ta miqama wayarta tace gashi nan nagode tasa dariya anti irin wannan dadewa ana duben waya tai dariya se gashi duk ba number ko hoton wanda ya burgeni ciki kai anti har yayan nawa tasa dariya to shi saurayinki ne ummi tace dadina dake anti kwai iya baqa.
Kiransa ne ya kuma shigowa wayar ummi ta miqo mata wayar anti yaya a'a bazan daga ba pls anti wallahi bazan daga ba kice masa na shiga toilet .
Ummi ta daga wayar yaya tace bazata kar6a ba kuma wai tace ince tana toilet yai dariya to inta fito kice nace to tace kai yaya cewa fa nai ta fadan bawai tana ciki da gaske ba ya kuma yin dariya hoo ummi sarkin hada husuma to batai lefi ba inkin wasa kece ma zakiyi tasa qara ni kuma eh ke ya kashe wayar.
Ta kalli ummu cike da barkwanci tace eyye angama da yaya na tasa dariya to ance miki nidin wasa ce.
Shi kuwa yana kashe wayar yai cikin falo besan sanda farin ciki yasashi sakin qara ba irinta farin ciki hajiya tace kai kuma mene haka nan ya fada mata komi da ya faru itama tai murna sosai.
Tun wayarsu da ummu yake faman baza idanu dan ganin kiransu Baban ummu anman shiru yai sati guda kenan duda an aiko musu an janye batun zaman kotun anman ba'a musu bayanin komi ba duk ranshi babu dadi shi ya qagu yaganta a gidansa.
Zaune yake a office dinsa yana duba takardun da yama dalibai test kira ya shigo wayarsa kamar karya daga yana dubawa yaga Baba mahmud ne yai saurin karawa a kunne gami da sallama cikin girmamawa ya gaidashi kafin baba mahmud din yace yau kazo gida inasan ganinka bai jira yace to bama ya kashe wayar.
Murna ce ta cika masa rai agonsa ya duba yaga yanxu warfe biyu ne yanma batai ba yace ya ninke takardun da yake dubawa yai inda yake da koyarwa yau.
Biyar dedai agidansu mahfuz din ta masa kai tsaye gurin baba mahmud yai dan rabonsa da mahfuz tun mutuwar ko ya kirashi baya dagawa se yaga dama duda bayasan haka sedai babu yadda ya iya.
Cikin mutunci sika gaisa kafin baba mahmud ya dora da bakomi yasa na kiraka ba sedan in sanar da kai ko kuma mu tatttauna kan batun auranku da ummu.
Abbakar yadan muskuta cike da farin ciki Baba mahmud ya dora inasan in fada ma ada bawai qiyayya yasa muka tilasta seka saketa ba bakuma qi bane yasa muka takura se anje kotu ba duda daman ba xuwan zamuyi ha sedan munasan samun tabbaci daga gareta na tana sanka dan bamasan za6a mata wanda bata so.
Yanzu zamuso muji a ina kake ganin zata zauna seka fada mana dan kai mata kayan daki kuma inasan in fada maka mu agaskiya bamu yadda da kunyi aure ba Abbakar yai saurin kallonsa eh bamu yadda ba gaskiya.
Hakan yasa muka yanke nanda wata guda zamu daura muku sabon aure sannan doke ka kuma bata sadaki danmu bamusan ka bata ba kuma inasan kasani yarinyarmu kamar ko wacce mace take dan haka dole ka kawo lefe kamar yadda ake a al'adance dan bama san barin wani sarari da za'a mata gori a rayuwarta duda abaya mun riga munyi sake.
Dan haka kaje ka turo wakilanka kamar yadda kowa yake inyaso semuyi magana dashi.
Wakilan Abbakar sunzo anyi maganar komi wata daya kacal aka saka dan gudanar da bikin nasu.
Amarya ummu se gyara takesha kowa da irin tasa gudun mawar sedai Baba mahmud ya hana Hajiyar Mahfuz kawo komi indai naci ne kosha ko shafawa da sunan abaima ummu dan gyaran amar sabida yace ba'a sake da maqiyi.
Taji ba dadi sedai tasan ita taja ma kanta ummu duk batasan sunyi haka ba duda haka Hajiyar batai fushi ba komi da ita ake.
Ummu tai kyau tai wani fresh gashi daman sunyi hutun mid semester tai wata yar qiba.
Yau take juma'a yau kuma aka saka dan daurin auren nasu a masallacin old campus na BUK za'a daura bayan sallar juma'a.
Zaune take cikin qawayenta su Aisha sunata tsokanarta wayar Aisha tai qara ganin sunan da ke yawo kan screen din wayar yasata miqawa ummu.
Abinda ya ziyarci kunnenta ne yasata sakin ajiyar zuciya wani farin ciki ya ziyarce ta ba komi bane face lasifiqa da taji ana fadin Alhamdulillah an daura auren ummulkairi Yasir Mahmud da Abbakar Fahad kan sadaki dubu Hansin.
Yace Baby kinji me naji tai dan dariya a'a my Habu yai dariya kema ko Habun nanfa Hajiya kawai ke fade tadan miqe to aini nace My a'a kinadai san muyi fada kenan tai dariya wato nayi lefi tun ba'aje ko ina ba to kuwa anya amaryar ce ni yai dariya kan yace wani abu ta kashe wayar.
Aiko tana kashewa su Hafsa na shigowa wato har an fara soyewar ko tace to da tsayawa kallonku zan.
Yau asabar ita ce yini shagali kawai ake sha gidan ya dinke ba masaka tsinke abu daya ke damun ummu rashin ganin ko mutun daya daga ummanta itakam agaskiya bata ga anfanin mutun ya aure wanda ba yar garinsu ba.
Goma dedai masu kai amarya suka kai ummu gidanta dake Nan waje jen state road gida ne na alfarma da ya kunshi duk wani abin more rayuwa da jin dadin dan adam.
Anan da yawa suka kwana yayin da wasu suka tafi.
Washe gari da rana masu gyara inda za'ai walima suka hallara kan yanma sun gama komi guri ya fito tas kai kace gurin yin biki ne na taskeba ba gida ba.
Itama ummu masu kwalliya sunzo sun shiryata sun mata kwalliya irin wadda ake yayi yanzu su Aisha ma duk anan suka kwana sune qirgin biki dasu ake ta hidima.
Wajen hudu gida ya fara daukan harama mutane sun fara hallara ango ma kamar amarya dinne yai kyau sosai komai irin na amarya yasa shima milk shadda yasa mai dinkin kofi da golding kamar dai Amar yar tasa.
Sunyi kyau sosai atare suka futi bayansu qawayenta ne se nasa suma biye dasu fadin kyan dasukai bata lokaci ne kaidai kana kallonsu kasan dansu akayi junansu.
Ba'abinda yaima ummu dadi se ganin innar Ummi tazo harda gwaggo da qawarta Ta Niger aikam tai murna sosai.
Aisha ce ta bude taro da addu'a gami dayin taqaitaccen yarihin amarya da turanci sannan mahfuz yai na ango Abbakar yai mamaki dan be ta6a zaton Mahfux zaizo gurinba balle har yamayi jawabi kowa zazzaune yake sai music me sanyi dake tashi awajen.
Kamar ance ummu ta dago ta hangi ummanta da qannenta sun fito a mota da sauri ta miqe tai gunsu cike da farin ciki bama tasan sa'adda kuka ya kufce mata ba dagyar suka lallasheta Fadya qanwarta ta gyara mata kwalliyarta suka tawo gurin tare.
Kana ganinsu kaga jini daya koda yake ummu tama fisu kyau kawai dai ita baqa ce nasan da ita tayo farin su kyau ba'a magana.
Ummanta itama tai bayani cikin harshen larabci gami da saka musu albarka.
Kowa yaci yasha ya gyatse kowa se saka musu albarka yake se isha kowa ya watse anman duk yadda ummanta tai kan su tafi can main house ummu taqi dole anan suka kwan.
Satinsu daya suka shirya se jordan bayan karamci da suka sha gurin dangin ummu mijinta da yan uwansa.
Rayuwar gidan ummu rayuwa gwanin sha'awa komi atsare suke yinsa shi yake kaita makaranta in ta tashi lokacin ya tashi su tawo tare in be tashi ba ta tawo ita kadai tun yan sch din na gulmarta har sun fara gajiya.
Wasu ma daga wata department din ko faculty dinma har zuwa ganin wace me sa'ar ce tai nasarar auren Mutun mafi farinjini da burge yan mata.
Wasu yan matan ma in sunzo da niyar kusheta se su raina kansu dan gani suke tafisu komi wasu ma sekaji sun koma fadin ai shine ma yai sa'a ba ita ba nace "Hmm students se abarmu"
Bayan shekara uku da auren ummu da Abbakar zaune take suna fira dan basu da wata damu inka dauke rashin haihuwar da suke fama dashi anman in ba haka ba kam rayuwarsu fal take da farin ciki.
Abotar Abbakar da mahfuz ta koma kamar da sedai gidan Abbakar din ne baya zuwa daqyar ya fara zuwa shi kome Abbakar zemsai bazai shiga ciki ba iyakarsa farfajiya.
Aure kam mahfux yaqiyi sunyi sunyi yaqi inma kai masa maganar aure yanzu zakuyi fada
Cikin sa ne ya motsa masa duda ya dade be motsa ba tun yana daurewa har yafara kasawa ta dube shi ganin yana yamutsa fuska tace my me ke damunka kan yafe wani abu cikin ya kuma murdawa tuni ya zubo daga kan kujetar tai saurin yin gurin sa ganin kamar baya nunfashi yasa qoqarin daga shi sedai banbancin halitta wato raunin mace yasa ta kasa.
Waje tai ta kira me gadi driver baya nan su biyu da ita dashi suka daukeshi sukai mota hijabi kawai ta dauka da key din mota tai waje me gadi ya ja mata falon dan yaga bata hayyacinta.
Hajiya ki jira Bala yazo seku tafi No buden qofa kawai ya bude gate din ta ja motar da gudu tai waje dan tuni ta koyi mota.
Kai kawo kawai take aqofar dakin da aka shigar dashi doctor ya fito gami da fadin madan abin ya zama worse ki kira namiji muna buqatar sa hannun wani namiji dan mu masa aiki qodarsa ce ta ta6u sosai kasantuwarta jaruma sosai yasata kasa fashewa da kuka.
Doctor pls ban aron wayarka yadan kalleta kamin yace ok biyo ni office tabi shi yana bata tahau kiran Yah nasir dan ta haddace number dinsa.
Yana dagawa tace yah ummu ce muna asibitin malan Yaya ne ba lafiya pls kazo da wuri ka biya ka fadawa hajiyarsa bata jira cewarsa ba ta katse wayar.
Hankali tashe ya kira ummi qanwar Abbakar ya fada mata ya kira mahfuz kan ya fada agida shi kuma yai asibitin seda yace ya tambayi inda suke ta fada masa.
Mahfuz dinma hankali tashe yai asibitin hajiya kam se kuka take har sukazo asibitin.
Duk suna tsai tsaye gefensa dan ansamu yadan farfado ido kawai yake binsu dashi har yakai kan ummu ya miqa mata hannu tai saurin zuwa cikin dashasshiyar murya irin ta mara lafiya yake magana.
Ummulkairi na yafe miki kema ki yafe min inaso ki sani ni Abbakar me sanki ne har abada sedai inaji a jikina ba'a yomu dan mu rayu tare har abada ba inaji ajiki na bazan tashi ba tai saurin rufe masa baki tana girgiza kai hawayen da tun dazu take qarfin halin boyesu suka kwaranyo kan fuskarta yasa hannu ya goge mata su.
Ya ce ummu ki dena kuka banasan ko bayan raina ki shiga damuwa pls kinji ko ta gyada kai gami da fadin bazaka mutu kaji yai murmushi kawai ummu mutuwa nakan kowa intazo ba yadda za'ai eh tace anman insha Allahu ba yanzu zaka mutu ba.
Ya ruqo hannunta yace inaso in roqeki alfarma dan Allah bayan bana raye karki auri ko wa inba mahfuz ba dan Allah alfarma zaki mun danni badan