Author : AXEEX Category : Romantic Story
hutu nai missing din yaran nan tai dariya se bayan wata uku yai dan tsaki kamin yace.
Kai duniya ba komi bace ada mu biyu muke zaune muka haifi yaranmu sun tafi se jikoki suma tanzu sun tafi ta shafo gefen fuskarsa haka ne my D qarshe ma mutun shi daya zai dawwama akabari to Allah yasa mu cika da imani tace Amin ya kuma riqeta sosai ajikinsa sukai dan shiru na mintina kamin ummun tace my D yace na'am tace nagode.
Me akayi u support me alot yai dariya duty nane matsayin miji no need ki godemin tai dariya inasanka mijina shima yai dariya inasanki nima Allah yasa mu rayu a aljannah tare amin my D.
Alhamdullah nan nakawo qarshen littafin Abbakar.
*Abin lura*
_*Arayuwa muna buqatar yafiya gami da mantuwa kamar yadda ummulkairi ta mance da abinda mahfuz yai mata suka ci gaba da rqyuwarsu cikin jin dadi_
_*Mutun baya taba wuce rabonsa duk rintsi seka ci abinda Allah ya tsaga shine naka sannan zaka mutu inka nema baka samu ba to abinnan tabbas ba raboknka bane kamar yadda Abbakar har ansashi a kabari sedai kasantuwar rabonsa aduniya be qareba ya dawo ya ci gaba da rayuwa._
_*mutane da dama suna fadin me yasa bansama littafin suna Nasir ko ummulkairi ba sedai ni ina ganin Sunan Abbakar yafi dacewa da littafin Abbakar mutun ne me sadaukarwa kamar yadda yake ganin zai iya sadaukar da sosayyarsa ga aminsa._
_Abbakar mutun ne me iya tankwara zuciyarsa kamar yadda lokacin da zuciyarsa ta amince kan yin masha'a da ummu ya tankwarata yaqi yi duda alokacin tanada dama anman be hakanba se yazama mutumin kamsa kuma ni aguri hakan ya kamata mu zama masu danne san zuciyarmu in ba dedai bane._
_Abbakar mutunne me haquri da sanin ya.kamata duda kasantuwar rashin mutuncin mahfuz gareshi lokacin da mahfuz din ya shiga matsalar asiri shi ya shiga ya fita seda yaga yazama normal._
_Duda kasantuwar ummul kairi nada yaro bashi yai cikin ba bakuma da aure ta haifeshi ba anman hakan besa da sukai aure ya wulaqanta ta ba sannan kasantuwar yaron ba nasa ba baisa ya tsani yaronba yaso yaron tun kan yai nasa dan._
_Tabbas da zansa sunan wani ba Abbakar ba to kuwa na Nasir ne dan akoyaushe muna muqatar tausayi da san yan uwa muna buqatar muzamto jarumai alokacin da yazamto mana na baqin ciki._
_Nasir mutunne me san yan uwansa kulawa dasu ako wanne hali duda kasan tuwar farida yakeso da yaga auren ummu zak iya sauqaqa mata lamarinta ya akiye buqatar zuciyarsa dan ceto yar uwarsa._
_Nasir mutun ne da duk girman matsala yakan iya tattara nutsuwarsa guri guda kamin ya tunkareta kamar lokacin mutuwar baby Abbakar da shi kansa Habu din wanda kuna kowa anso yazamto mutun mai jarimtar nutsuwa a kowa ne hali._
_Miqama Allah lammuranmu akoyaushe shi yafi dan babu me maka abinda be ma ba zuwa gurin bokaye ba namu bane musanman mu mata komi kike buqata tashi cikin darw ki nema Allah na kowa ne zai baki duk girman buqata in kuwa kika riqi wani sa zaki qare cikin nadama kamar yadda Hajiya Batul tai._
_Kishi da yassada ba namu bane musanman kan yara inba haka ba zasu kaimu su baro kamar yadda suka kai Hajiyar mahfuz da shi kansa Mahfuz din danshi sharri dan aike ne in yaje ya dawo kan ka ke koma._
_Duk girman matsala in mukai haquri akwai sauqi kamar yadda ummu da tai haquri komi ya zamto labari_
*Godiya me tarin yawa ga duk wata ko wani da suka karanta fatan kukkuren da ke ciki za'a min afuwa ajizanci ne na dan adam.*
[1/13, 4:32 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚