Author : AXEEX Category : Romantic Story
au bakiji ba eh tace ok kiban amsa tace ai banji me kace ba dan Allah ka maimaita, kinga malama inzaki ban amsa kiban mamaki ne ya kamata lallai mutumin da nuna isa yake.
To taya zan baka amsa banji me kace ba to koma mene nidai amsa kawai nake jira kiban dan Allah ka maimaita wallahi bazan maimaita ba.
To dagaske ne zaka auren ya dago karaf suka hada ido wani yar yaji har cikin kansa yai saurin kau da kai au ashe kinji me nace ta sunkuyar da kai.
To tunda muke dake na taba miki wasa eyye tai shiru kawai kiban amsa zaki aureni to aini na kasa yadda ko da gaske kake yai dan murmushi da bako yaushe yake ba kin taba ganin anyi maganar aure da wasa.
Tai shiru kamin tace ai naga nidin bakowa zai yadda ya auren ba ya dago ido ya kalleta sabida me ya ta nuna masa Abbakar dake hannunsa yanata wasa yai murmushi kamin yace to ai ni babansa ne kin taba ganin inda mutun yaqi uwaddansa tai shiru can tace to family dinka fa yai dariya kice dama can su kike tsoro kawai ta sun kuyar da kai basu da matsala yace inma suna da ita ai dani zaki zauna bada suba ko.
Kin amince zaki aureni shiru tai kamin ta miqe tai ciki kawai.
Duk yadda sukai dashi ta fadawa inna ita kuma tace zata fadawa mijinta.
Kwanansu biyu da yin maganar ummu bata ce masa komi ba hankalinsa duk yabi ya tashi to ko bata yadda bane hakan yasa yau yai niyar saminta intaqi amincewa ya koma gida ya kawo Hajiyarsa ta roqar masa ita.
Yana zaune yana cin tuwon da gwaggo tamai dan baya iya shan koko suna ta fira dan sun saba sosai malan musa tazo ya zauna aka ci gaba da firar dashi.
Sai da Abbakar ya kammala kafin malan musa ya fara magana jiya Halima tamin bayani kan kanaso in zama waliyin matarka kan amaida muku da armenku haka ne.
Abbakar yai saurin cewa eh haka ne sabida inasan kawai mukoma Nigeria da aurenmu yai murmushi hakanma yayi kyau Abbakar ya ciro kudi ya baima malan musa ya amshe yana godiya.
Da Azahar malan musa yama liman bayanin komi aka sanar a masallaci kan da la'asar za'a daura auren.
Ilai ana yin la'asar mutane da dama suka shaida daurin auren ummulkairi da mijinta Abbakar aiko angon sai washe baki yake duda ba kowa yasani a garin ba yaci kwalliyarsa takwaransa ma ammasa wanka yana zaune dashi a qofar gida.
Kwana uku da daurin auren Abbakar da qyar yasha kan ummu ta amince ta biyoshi Nigeria sai da suka biya maradi ya dauko kayansa acanma sun kwana biyu kamin su mamo hanya da yaso yima su ummu visa abin yaci tura dole suka biyo mota bawai dan yaso ba.
Sun iso kano lafiya yakan yasa suka dauki taxi har gida.
Hankalin ummu bai tashi ba saida ta gansu a unguwarsu wato gidansu babanta gidan da ta girma bata qara shiga rudani ba saida ta gansu a lokon cikin tsoro ta kalli Abbakar ya daga mata gira ganin a farkon layin suka tsaya yasa ta gane ba can gidansu suka zo ba sai alokacin tadanji dadi kadan.
A gidan su Abbakar hajiyarsa ta amshi ummu sosai da mutunci ummu taji dadi sosai sai dai can qasan ranta fal tsoro ne dan tanjin kamar in hajiyar taji Abbakar ya aureta zata tsaneta ganin har dare yayi an nuna mata inda zata kwanta ita da danta Abbakar baicema hajiya ita matarsa bace yasa ta fara tunanin kenan shima yana tsoron abinda zata ce ne.
Sai da ummu ta hau sama yaje ya tabbatar tayi bacci sannan ya sauko yai gun hajiyarsa da tun tashin ummu ta wani hade rai ta fara cika tana batsewa.
Yana saukowa ta haushi da fada ta inda ta shiga bata nan take fita ba yanxu Abbakar yaushe ka koyi qarya haka shi dai hakuri yaita bata hartayi shiru.
Saida tayi shiru kafin ya dora Hajiya wannan ita ce wadda naje nema din kuma na aureta miqewa tayi tana tafa hannaye wato Abbakar harkayi girman da zakai aure bada sani na bako aqallah yaji dan sanyi cikin ransa dan baiyi zaton abinda zata ce kenan ba ya dauka cewa zatai me yasa ya auri ummu nan yaita qaqalo bayani dan shawo kan hajiyar har ya samu ta dan sakko kamin tace shikenan alasa albarka ka tashi kaje anman kasani ni bazan ma kawunnanka bayani ba kasan me zaka fada musu ya sunkuya yana godiya yai bangarensa.
Washe gari gidansu mahfuz yaje da yah Nasir suka fara haduwa sun dan taba fira kafin Nasir din kwana biyu bana ganinka a sch na jejje faculty dinku office dinka arufe.
Abbakar ya sosa qeya na dauki hutu ne nakuma yi tafiya towo ina kaje haka kai da nasani indai ba abu me mahinmanci ba kana baima aikinka time inka eh wallahi yah naje neman ummulkairi ne.
Nasir ya zaro ido wacce ummu ya sosa qeya ummu dai taka kuma ma naganta Nasir ya miqe tana ina a'ina ka ganta.
Naganta a Niger kuma kamin mu tawo an dauran aure da ita yanzu tana gidanmu shaqo Abbakar da akaine ta baya yasa Nasir saurin juyawa Mahfuz ne ashe duk yana sauraronsu.
Cikin fada da masifa yake zagin Abbakar kan yaci Amanarsa yaci amanar abota kan mene zai auri wadda yake so da qyar Nasir ya fincike Abbakar yace ya tafi kamin haniyarsu ta fito da sauri Abbakar ya bar gidan.
Shima kwace kansa yai yabi Abbakar din kan yaje har yashige gida shima gidansu Abbakar din yai dan ba baqonsa bane me gadi yasanshi bai bi ba'asin zuwansa ba.
Yana shiga ya fara kwalawa Abbakar din kira kai Abbakar kana ina ne kafito munafi maci amanar abota ka bani matata Hajita ta fito tace lafiya kake mana ihuu haka yace ni mamata nazo karba.
Hajiya tace wace mata ai matar Habu ce sai dai ko kazo kwace masa matana kawai wallahi Hajiya ummu tawa ce ni daya dan da take goyo nawane in ba tawa bace taya zata haifar min yaro tsawa hajiya ta daka masa futarmin a gida in qwayar ta sakeka ka dawo.
Ya juya zai fuce dan yanajin nauyin hajiyar Abbakar sosai sai dai jirin da ya debeshi yasa shi dawowa da baya luuuu ya fadi.
Da sauri Abbakar da tun da mahfuz ya shigo yake tsaye ya kasa magana yazo yana dagashi yana kiran sunansa sai dak kamar babu hakan yasa ya miqe ya kira me gadi ya temaka masa suka kaishi mota baibi takan hajiyarsa ba ya asibiti.
Sai da ya tabbatar likitoci sun duqufa kan mahfuz ya koma gida ya dauko Hajiyarsa da ummu shi kadaj yasan me yake rayawa aransa.
Ya bugawa Nasir abinda ake ciki kan ya fadawa hajiyarsu kafin wani lokaci sun iso Asibiti hajiyar mahfuz sai bala'i take.
Sai yanma liqis mahfuz ya koma normal yana ganin hajiyarsa yasa mata kuka Abbakar na shigowa dakin ya fincikd drip din da aka saka masa ya daga drip stand din ya wulla masa fita mugu kawai yana kuka da badan Abbakar ya sunkuya ba da sai yaji masa ciwo.
Da sauri Abbakar yazo ya riqe hannun mahfuz yana kuka haba aminin mene haka yazaka bari mace ta shiga tsakaninmu ya miqe yai inda ummu ke tsaye ya shigo da ita dakin gurin mahfuz ya nufo.
Kamo hannunsa yai yasa na ummu ana mahfux kamin ya share hawayen da ya tawo masa yace ni inasan abokina bakuma zan bari soyayyar mace ta bata mana abotarmu in dai ummu ce ni Abbakar nasaketa saki daya daman ban dora mata idda ba ko yanzu ne a daura muku aure yana kai nan yai hanyar fita yabar ummu tsaye kamar gunki yayin da mahfux ke bin hannunsu da kallo........
Zan cigaba insha Allah
[1/13, 4:19 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[1/13, 4:20 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR*
*140---150*
Fun cike hannunta ummu tayi cikin kuka take magana wallahi banasansa ba kuma zan aureshi ba ko gawata bazata zauna dashi ba yayin da Abbakar cikin qunar rai yai waje danshi kadai yasan mai yakeji aransa ji yake kamar girjinsa ya tsage zuciyarsa ta fado.
Hajiyarsa ce ta matsa inda ummu take dan tun dazu da Abbakar in ya kamo ummu ta biyosu dakin takuma ji komi.
Dafa ummun tai tace ki dena kuka kimki indai ina raye ba zaki kuma maraicin uwaba indai ina raye ba wanda ya isa ya aura miki mahfux duda shima dana ne anman kema yatace.
Tace cikin murya mai kaushi Habu dakata yaja ya tsaya taje ta juyo dashi yana kallonta tana kallonsa tace indai ni na haifeka inaso yanzu ka maida ummu amatsayin matarka ya kalleta zai yi magana tace karka cemin komi wannan umarni ne nake baka bawai shawara ba dan haka kayi abinda nace.
Cikin rawar murya yake magana na maida mata ta ummu hajiya ta saki ajiyar zuciya kamin tace kuma wallahi ko bayan raina kasaki ummulkairi kan Mahfuz bazan yafe maka ba zan iya maka afuwa in kan wani dalili ne.
Ta juya ta kalli hajiyar mahfuz kamar zatai magana kawai taja hannun Abbakar da ummu sukai waje sai kace qananun yara.
Suna fita Mahfuz ya muqe zai bisu hajiyarsa ta gyada masa kai alamar a'a kar yaje ya dawo ya zauna gami da rushewa da kuka yana fadin wannan wacce irin jarrabar so ne nake miki ummu hajiya ki temaka ki ko ragen santa ne dan Allah ta dora kansa a qirjinta tana lallashi kamar wani yaro.
Sai da su Abbakar suka isa gida hajiya ta ja ummu sukai daki suka bar Abbakar nan tsaye yana kallonsu sai yanzu ya gane kuskurensa lallai ya tafka kuskure yasan ko zai hadiyi laya ummu bazata yadda yanasanta ba zatayi zaton tafi san abokinsa kanta bacin ba haka bane yasan duniya bayan hajiyaraa it yakeso bema san me yasa ya ce yabarma mahfuz din ita ba can wani bari na zuciyarsa yace sabida kaima kanasan kyautatama aboki ka koda sau daya ne.
An sallami mahfuz dan ba wani serious abu bane, agida mahfuz mahfux duk yabi ya tashi hankalinsa ji yake kamar ya kashe kansa ya wuta dan dai kawai yana tsoron jahannama ne ya daure anman ji yake gabaki daya duniyar ta masa zafi.
Kwance yake akan gadonsa yana kallon fanka da take ta faman kadawa idanunsa na zubda kwalla ji yake kamar yaje ya sato ummu ayanzu ma azuciyarsa tunani yake tayi inda zai satota ina zai kaita santa ne ita da danta keta ruruwa aransa.
Hajiyaraa ta shigo ganin yana kukan ne yasa tai saurin yin gurin tana fadin subhanallahi haba mahfuz mene haka karka kashe kanka kan wata banza dan Allah, ya dago a fusace hajiya ummu ba banza bace masoyiyata ce to naji me yasa ka kuka.
Cikin shessheqar kuka yake fadin hajiya yarona inasansa wallahi in na rasa ummu bazan iya jure rashin dana ba hajiya ta dafe qirji wane yaro kuma kaida ba mata ba.
Hajita dan gurin ummu wallahi yarona ne ni nayi cikinsa tai saurin rufe bakinsa kul yi shiru vaka da wani da Allah ya rufa mana asiri shine kakesan tonawa indai yaro kakeso zanma aure sai matar ta haifa maka wani abin da yasa hajiya bata damuba da jin kalaman Mahfuz kan dan ummu sabida tasan halinsa tun futowar cikin tasan shi yayi da gaske din tsanar ummu da tai da san zuciya yasa taqi yadda.
Shiru yai kamin yace wallahi ni shi nakeso inasan dana nasan na cuce shi nasa an haifeshi bada aureba anman wallahi yanxu inasansa inasan riqeshi matsayin nawa.
Yace wallahi hajiya inasan yarona nasan ko yara dari zan haifa bazan dena sansa ba inasan amsoshi in nuna masa gata in sauya masa suna daga Abbakar zuwa mahfuz dan Allah ki yadda.
Da qyar tasha kansa ya yadda zai aure bawai san dagaske ya haqura da yaron nasa ba .
A can gidansu Abbakar na dai babu dadi sosai dan hajiya ta rage shiga sabgarsa zaman faloma ba cikayi tayo ba kusan ko yaushe tana daki ita da jikanta Abbakar qarami inyaje tayi kicin kicin tace me ya kawoshi, ummumma kullin idanunsa cikin sam ganinta suke sai dai baya ganinta inma yaganta daga ina kwana, barka da rana ko barka da dare shi kenan sai tayi dakinta.
Yakan kwan uku bai ma ganta ba abubuwa kawai yinsu yake babu dadi.
Yau Abbakar baya nan ya tafi aiki dan sun koma mid semister yanaso yai qoqari ya qarasa ma dalibai lectures insu da tunda ya tafi hutu malamin da aka sauya musu ba wani zuwa yake ba basuyi wani abin kirki ba.
Ummu na zaune suna kallo dan ita din ba me yawan magana bace hajiyan ma haka hakan yasa basu cika fira ba Abbakar qarami ne kan hajiya yanata dab dalarsa.
Su Aisha kabir ne suka shigo da gudu ummu ta miqe tai gunsu ta fada jikinsu Fatima ta tureta dalla ni mataa bakisan haushinki nakeji ba baki daukemu aminai ba lokacin da kika shirya guduwa kika daqa mana hankali tai gurin hajiya suma suka tureta sukai gun hajiya ta tatsaya tana kallonsu kawai kafin itama tai gurin.
Sun gaisa da Hajiya ummu ta mata bayaninsu kafin tajasu zuwa dakinta suna shiga ta shiga musu kuka dagar tai shiru sun rasa kukan me take.
Cikin kuka ta basu labarin komi har aurenta da Abbakar sukai ta murna to mene na kuka ai naga shi din mutumin kirki ne, kukan asarar sch dina danai nake yanzu fa sai na sake jamb fa na kuma jira, Aisha ta miqe af kin ganmu ko munata fira da baqo fa mukazo wakenan ba gurinki yazo ba tai waje ummu ta bita da kallo kawai.
Gurin Hajiya tai tace hajiya mun mance da baqo mukazo yanasan ganinki hajita tace towo baqo kuma waye kenan.
Eh muda Yah Nasir ne hajita tace Nasir kuma wanne Yah nasir dai na ummu na gidansu mahfuz........
Hajiya ta danyi shiru kamin ta nisa tace to me yasa be shigo ba banda a abin Nasiru da dayake shigowa ai ba wani ke masa iso ba kosan zainab mutuniyar tasa bata nan.
Wato zainab qanwar Abbakar duda kasancewar Abbakar ya girme mata anman tanasan yayan nata sosai fiye da kowa agidan dan haka duk girmanka in ka tabashi ka banu abinda ke hadata da Nasir kenan indai ya daki Abbakar sai tazo qofar gida ta labe indai nasir ya zo wucewa ta jefeshi ta gudu ya biyota har gida ya daddaketa.
Lokacin da ya qara girmane batafi shekaru goma ya dena dukanta sai dai in yaganta yace ke tsattsewala tasa kuka duda har yanxu in abu ya hadashi da Abbakar ya daddakeshi sai ta masa rashin kunya.
Data girma mutunci ya shiga tsakaninsu karatu ma da Abbakar ya tafi waje karatu shi yake koya mata dan basa shiri da mahfuz ko kadan dan ta ganshi yanashan taba ita kuma indai kanashan taba ta dena ganin girmanka yayin da mahfux mutun ne me dan banzan san girma.
Jeki kice ya shigo tai waje suka shigo tare Aisha ta dauki qaramin Abbakar sukai cikin dakin ummu Nasir ya zauna yana sun sun da kai.
Sun gaisa kafin hajiya tace yanxu Nasiru dan zaka shigo gidannan shi ne sai anma iso da wani kema yadan sosa qeya yana murmushi yayi kyau yanzu yaushe rabonka da gidannan ina zaton tin haihuwar zainab ta farko da tazo wankan gida ya sosa kanshi gami da sun kuyar da kai wallahi abubuwa sukamin yawa.
Eh haka ne shi yasa ai kake iya zuwa katsina ziyara yai dariya ni kuma ga hanci ga baki baka iya zuwa sabida abubuw sun maka yawa can dinma saifa aiki yakaini uhum tace ai shikenan. Tinda yanzu na dauko qanwarka ai dole in ganka Allah hajiya ba haka bane Nadiru kenan ta fada gami dayin shiru.
Daman magana nazo muyi to inajinka kan mene kan karatun ummulkairi ne ok inajinka.
Kinga tayi nisa yanzu ace saita sake jamb ta jira admission kamar abin beba shi ne naga tunda anyi sa'a ta dawo ba'ayi exam ba mai zaisa ta koma ko co tasamu ta gyara nan gaba.
Haka ne kayi magana zanma mijin nata magana yawwa yace wasuma sunyi test anman na roqesu zataje su mata inyaso inta koma sai taje din abinda bata ganeba sai shi Abbakar din ta koya mata bama sai ya koya mata ba in qawayenta sun kasa in yaso saita kiraka to yace gami da miqewa ya dire handouts din da ya shigo dasu gashi sai abata wadanda ta siya kan hutune sai wasu kuma wanda malamansu suka bada ne na sayo mata godiya hajita tai yai waje ransa fal farin ciki danshi daman burinsa ummu tasamu inda ake santa.
Sai yanma su Aisha suka tafi tunda ansan da zuwansu daga gidajensu.
Koda ummu taji batin komawarta makaranta tai ta murna tanama Yayanta addu'a nasir koma ince uba dan ita aranta jinsa take yafi qarfin matsayin yaya gareta saidai uwa da uba.
Washe gari sai gasu Hafsa ita da Ahmad Ahmad ummu tai murna sosai suka sha firarsu anan su ummu suka tafi suka barshi dan zai koya mata wasu abubuwan da bata ganeba cikin wanda taga yah nasir ya rubuta mata zatai test.
Ummi (me aikin ummu) dan tun dawowarsu Abbakar ya maida ita sch