Author : AXEEX Category : Romantic Story
hadari kan hanyarsa ta dawo wa gida daga kaduna sai gawarsa aka kawo gida kuka gurinsu kamarme.
Kwana uku da rasuwar Hajiya Fiddausi ta haifi yaranta guda biyu macen ta fara haifa da kwana biyu wank ciwon ya taso dan agida ta haihu ko asibiti basu je ba ta kuma haihuwat namiji.
Abbakar ko kadan bayasan yayi medicine math yake so ko engineering hakan yasa da suka fara medicine aka tafi yajin aiki yasa kawonsa ya masa komi na tafiya japan karatu yai sa'a dagyar Hajiyarsu ta yadda.
Lokacin da ya samu mahfux da batu ya yadda shima zashi sai dai daya fadawa wani abokin shaye shayensa yace kar yaje haba Baba kaima kazama mutumin kanka mana ace kullin sai abinda guy dincan yace zakayi yaita zigashi har ya yadda....shi kuwa salim badan komi yake zugar ba dan sanin in Mahfuz ya tafi babu mai siya masa kota yar lasa ce wato kwaya.
Samun Abbakar yai ya fafada masa Hajiyarsa taqi yadda Abbakar yace zai sameta yace kar yaje nima inasan koda sau daya ne inma mahaifiyata biyayya Abbakar yaji dadi dan zatonsa shiriya tasamu abokin nasa.
Duda Abbakar basa tare da mahfuz anman komi yai sai ya fada masa lokacin Abbakar ya kirashi tayashi murnar kammala masters insa ne Yakr fada masa abinda yai ma ummu batare dajin komi ba zatonsa Abbakar ma bazaiji komi ba kamar su salim da sukai ta sara masa.
Saidai Abbakar fada yai ta masa har saida mahfuz yai danasanin fada masa.
Yaya Babba da zainab ke kula da Dukiyar mahaifinsu asibiti da makaranta sai dai lokacin da zainab ta samu miji tai aure a katsina abubuwa suka dawo kan yaya babba duka hakan yasa Hajiya tilastawa Muktar auta yin karatun likita tunda shi namiji ne tashi Abbakar yaqi.
Koda ya kammala secondary ya tafi india yin medicine ummi tagwai insa take law maryam pharmacy.
Ci gaban labari
Ranar da aka saka za'a zauna a kotu yazo ta kuwa cika ba lefi duda bakowa yasan da qarar ba.
Lauyoyi sun bayyana kansu inda maga takarda ya karanto bayanin qara kamin shari'a ta fara gudana.
Bayan bugawa da lauyoyi sukai tsakaninsu aka daga qara zuwa sati biyu ba tare da tabbacin wazai nasara ba cikinsu dan ko wanne kwararrene.
Yaya Babba ce tazo gida tana fadawa Hajiya abinda mijinta yace dole sai sun kai ummu kotu da ita da Nasir dan sune shaidun fyade ya mata dagyar hajiya ta aminta.
Bikin mahfux kam yai nisa dan gobe ake saka ran daurin aure yayin da shi tuni ya mance dan hankalinsa gabaki daya ya tashi ganin kamar bazasuyi nasara ba.
Yau akai za'ai zaman kotu dagyar Nasir ya yadda zaije sai da ummu da hajiya Hajiya da yaya babba sukai ta roqonsa ya yadda yaje.
Bayan saurarun shedu da DNA da akai aka tabbatar yaro na Mahfuz ne alqaliya tai gyaran murya kotu tai tsit kowa nasan jin me zata zartar.
Tace ina mahfux ya miqe ina yaron da ake qarar kansa shima ummu ta miqe gashi ranki ya dade ina uwattasa tace nice.
Miqa masa shi ummu ta kalli alqaliyar alamar in miqa masa kamar yaya tace nace ki miqa masa shi ko ummu ta qara qanqame yaronta police mace ce ta amshi yaron ta miqawa mahfuz dake faman washe baki ummu ta zube gurin tana kuka.......
[1/13, 4:21 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[1/13, 4:22 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR*
*PAGE 160---170*
Mahfuz yakai hannu ya amshi yaron tuni kotu ta hargitse da hayani kowa na fadin albarkacin bakinsa domin yau kotun ta cika sosai da yawa cikin mutanen kotun abu daya suke fade yake kuma basu mamaki wato wannan wace irin alqaliya ce wannan zalunci ne.
Maganar da alqaliyar ta fara ne yasanya kotun fara yin shuru kafin daga bisani kuma tai shiru.
Yanzu daman innace ka amshi yaron nan saika amsa ya kalli alqaliyar da mamaki, ina kai musulmi ne ko baka da labarin in mace ta haifi yaro a muslunci batare da aure ba yaron nata ne bana wanda yai cikinba.
Kai wane irin azzalumi ne da har zaka ma yarinya fyade ta haihu kakuma zo ka kawota qara ko dan ita batasan haqqinta ba ta gaza kawoka qara.
Wato kazo nan aqwace yaro abaka ko kai gaka uwa da uba na doka ko to abaka shi kamasa me ka kasheshi ko yai saurin kallonta da mamaki fiye da dazu eh mana kanasan karbar sa ka kasheshi dan karya girma ya zargeka da rashin kawoshi ta hanya dedai.
Mahfux cikin fishi yake magana Haba malama wannan ai bayi bane zaki dunga mun sharri kawai dan kina alqaliya tsawa ta daka masa kai malan kasan a inda kake kotu ba sa'ar wasan ka bace.
Sakamakon samun wanda yake qara da rashin ta ido da kotu saka makon haka kotu ta bada dama a sakaya shi nanda wata guda sannan yaro na mahaifiyarsa ne kotu ta masa katanga da yaron indai ba mahaifiyarsa ta yarje yaje gunsa ba.
Duk yadda yan uwan mahfuz sukaso kar yai firxin na wata guda abin yaci tura dan alqaliyar iya wuya yazo tace da a qyaleshi gwara ta bar aiki.
Har gida alqaliyar mai suna Salma tazo ta sami ummu tasamu karba ta mutunci sun gaisa da hajiya kamin ta fara bayaninta.
Indai kun amince ni zan tsawa ummulkairi ta kai yaroncan qara kan cin zarafinta da yai na keta mata haddi tunda duk wata shedu munadasu na zaman kotun da mukai.
Kafin hajiya tace wani abu ummu ta dora a'a ni zaman yarona agurina wallahi ya fiyemun komi na riga nakai shi qara gurin sarkin da baya zalinci nakuma san ko aduniya ko alahira zai saka min nagode sosai aunty sukai sallama ta tafi.
Hankalin hajiyar mahfuz yafi na kowa tashi gashi gobe daurin aurensa abin haushi dik gidajen radio da tv sun nuna shi sakamakon rashin mutuncin da yai akotu balle tace ko tafiya yai.
Ban garen gidansu amarya basu wani ji komi ba dansu burinsu kawai su aurar da salma gama ko wane ko sa samu su huta da halinta, itama bangaren Amarya bataji komi ba saima murna da tayi na rashin bashi shegen dansa dan mum dinta ta fada mata irin son da yake masa shi yasa tun kan tashiga gidan kishin duniya ta dora kan yaron, na biyu kuwa ta samu abinyi in ya mata gori zata rama da cewar ai gwara ita bata taba bursinba.
Mahfuz duniya ta masa zafi ba abinda yake tunawa sai sa'adda police suka saka masa ankwa Abbakar yasa hannu ya amshe takwaransa dake hanunsa ya miqawa ummu.
Gabaki daya yai baqi ya rame danshi mutunne da bai saba da wahala ba bakuma yasanta ji yake wata guda dinma taqi qarewa ji yake kamar shekara ce zaiyi ba wata ba.
Sanye taje cikin baqar abayarta mai adon ja ta nada mayafin abayar akanta sai yar jaka mai dauke da littafanta gudu uku kacal ita ma jace sai dan duwatsun baqi jikinsu takalminta mai sauqin nauyi tai kyau sosai.
Ummu kenan wadda ko wacce kwalliya tai tana mata kyau musanman a idan Abbakar wanda yanzunma tunda take saukowa ita da ummi qanwarsa yake binta da kallo gashidai shiga iri daya sukai anman gani yake ina ummu ai babu ya ita.
Ummu doguwa ce bacan ba komi nata me kyau ne ita din bata cikin fararen fata bakuma za'a kirata baqa can ba tanada dai duhu irin na yan Nigeria wato duhunta me kyaune fatarta ma me kyauce idanunta yan madai daita wanda hancinta da baqinta sun dace da yanayin fuskarta kana kallonta zaka san ta hada jinsi da larabawa ko ka kirata irin fulanin asalin nan kamarta daya sa babarta saidai ita batayo hasken babar tata ba.
Sai da suka zo dab ummi ta tabashi yah munata gaisheka bakaji ba ya dake irin karsu gane ita yake kallo yayin da tuni hajiya ta rafkoshi yace oh banji ba inadanjin bacci ne, ina zuwa haka zamu sch ne ok to ku jira in kaiku ya fada gami da miqewa.
Ajikin motar suka tsaya yazo ya bude duk suka shige baya shima yai zamansa agaban motar yaci gaba da daddana wayarsa yayinda lokaci lokaci yake satar kallon ummu.
Ganin bazai tafi bane yasa ummi qanwarsa cewa yaya muje ko ya juyo ya watsa musu harara baki dayansu muje ina? sch mana kai kace zaka kaimu ai, nace dai zan rage muku hanya ko suka kalli juna ita da ummu shi kuma ya ci gaba da danna wayarsa.
Ganin da gaske bazai tafiba yasa ummu daurewa tace pls sir karmu makara asanyaye tai maganar yadan kalleta watoma agidanma kallom wancan lecturer din nasu na thermodynamic take masa yace au ai nazaci baku shirya tafiya ba ummu aranta tace lallai mutumin nan dan rainin hankali ne bamu shirya tafiya inba zamu shiga mota ummi ta miqe daga bayan ta koma gaba.
Ko rufe qofar taiba ya tada mota ta jawota suka tafi, ummi ya fara saukewa a old campus dan zatai wani abu yaja yai tsawarsa ganin yana bata mata lokaci yasa tace pls dan Allah sir mu tafi.
Ya leqo gidan bayan ni direbanki ne ya fada yadda yai yamata kwarjini hakan yasa ta fito ta shiga gidan gaba yaja suka tafi.
Adai dai faculty insu ya paker ta bude kamin ta sauka ta juyo tace thank you sir ya ruqo hannunta da sauri ya juyo ta kalleshi ba sunana Sir ba, nakuma sanda kinsan da hakan dan haka akiyaye ya saketa tai waje dasauri.
Su Aisha ta gani can gefe suna sheqa dariya harda tafi iyye kaga masoya wato abin har yakaiga adinga kawoki inkuma ankawoki a zauna a mota a kwashi love ta turo baki to 'yan sa ido masu zuwa lahira da qoqom danbu anayi kuna irgawa to ya ranku.
Ahmad yace ransu fes birgesu kikai shi tasa suka kasa shiru Hafsat takai masa duka da littafinta kaifa dan is ne ah kinga yarinya dena iskantani da mutunci na har yanzu suka saka dariya baki daya.
Yau kwanan mahfuz uku kenan da fitowa duk yai baqi abinci ma ba wani da dinsa yakeji ba kawai dai yana daurewa ya cine dan kan abin ya masa yawa ga yunwa ga rashin dansa.
Ganin ya kwan uku ne bai maganar matarsa ba hajiyarsa ta sameshi adakinsa yana kwance da alamu tinani yake tace mahfuz magana nazo muyi ta Fahinta ya dago gami da jin gina da gadon to hajiya inajinki.
Maganar matarka ce Naga tunda ka dawo bakamin maganarta ba adan razane ya kalleta mata kuma hajiya eh matarka danshi a zahirin gaskiya yama mance dawai za'a daura masa aure balle yasan an daura.
Haba hajiya da wanne zanji da auramin wadda banaso ko kuwa da kwacen yarona da akai ta daga masa hannu kaga ni yimun shiru kai inbanda butulci naka yarinyar duda sanin kana da yaro shege ta yadda ta aureka kace aura maka ita tashin adalcine kai inbanda amincin dake tsakanina da uwatta aikasan kamin kasamu me aurenka saika shirya.
Dan haka ina baka umarni kayi maza ka hada naka yanaka ka koma gidanka na court road dan can nasa aka kaima ita idanunsa sunyi jawur rannan abace ya miqe ya hau dibar kayansa.
Ko sallama baima Hajiya ba ya fice daga gidan danshi yanzi haushinta yakeji gani yake ita ta cuceshi data sangarta shi ta nuna masa komi yayi dedai ne gashinan tasa yaje yai abinda sakayyarsa ke neman haukatashi.
Gidansu Abbakar
Yau shirye shirye suke sosai dan har su Nurat sunzo aunty zainab ce zatazo dan ganin amaryar yayan nata dan ita batasanta ba.
Lokacin da tazone aunty zee tasha mamaki qanwarmu ashe kece amaryar tamu ummu ma ta mamaki aunty zee daman ke yar nance eh aure yakaini katsina kowa yai mamakin sanin juna da sukai.
Aunty zee ta dubu Hajiya umma ai nasanta qanwar Yah Nasir ce kuma qawar Farida qanwar salma wato qannen mijinta Hajiya tace ikon Allah.
Da yake duk gida daya suka zauna da su salman yanzu ma tare suke ra Farida ummu tai dariya kawai Abbakar yace a'a yanzu ta dawo nan daiko suka saka masa dariya baki daya.
Zainab ta dubi ummu waiko in tambayeki ummu ta zuba mata ido alamar inajinki, Yah nasir kuwa ya fadawa Farida yana santa ummu tadan dubeta wato itama tasan yanasan Faridan a'a tace.
Kai yaya Nasir da zurfin ciki yake wallahi tun yarinyar nan fa na Jss yake fama da santa yasha fadan yadda yakejin santa aransa anman ya kasa fada ai shikenan nasan me zan masa.
Suna gama cin abinci ta kira Nasir din awaya Yaya na nafazo garin naku eyye watoma garinmu ko to ganinan zuwa gidan naku.
Sun sha fira kamin zainab tace daman jaje zanma bikin Farida ya gabato sauran wata uku what ya fada yana miqe ina wallahi bazai yiwuba farida tawa ce ni daya.
Yai waje zainab ta bishi a baya sedai kamin tazo ya fice a motarsa ita dai hankalinta duk atashe kar yaje yai wata baran baramar.
Kai tsaye gidan Farida ya wuce ya dade baije ba dan yanzu ita kadaice hakan yasa gudun shedan ya rage zuwa duda ta ce masa qannenta uku sunzo mata hutu baida niyar zuwa.
Kullin cikin kiransa take awaya ko a sch nunawa yake baisanta ba yama hanata zuwa office dinsa gabaki daya.
Kai tsaye gidan ya shige yana kwala mata kira Basira na shanya tasanshi hakan yasa bata tsorata ba se ce masa datai tana ciki.
Da gudu Farida ta fito yah lafiya kuwa cikin kwalla yake magana yanxu Farida kin kyauta min kenan kinsan da ke daya nakeso a duniya shine zakiyi aure ki barni ta kalleshi yah ban gane me kake magana akaiba yaushe muka taba maganar soyayya dakai.
Ko kuwa nace inasanka ne what eh bakice kinasona ba anman aikin nuna ta zaro ido ni wallahi a'a kawai irin kulawa da wa da qanwarsa ce .
Oho ke kika sani ni kawai abinda nasani ke din matata ce kuma dole koma wazaki aura a fasa ayi dani cikin dan murya me qarfi take magana wai yaya wane aure kake magana yaushe nace ma zanyi aure.
Wayarsa da tun dazu ke ringing ya daga bema duba ko waye ba ya amsa muryar zainab ce cikin muryar kuka take fadin yah wallahi da wasa nake tsokanar ka kawai fa nake ba wani aurenta da aka saka.
Kunya duk ta kamashi sun sun ya fice yabar gidan Farida na kiransa yai gaba ita dai tasan yaya nasir baya shaye shaye dasai tace ko ita ta fada masa qarya.
Gidansu zainab ya koma anman kin gama dani kinsa nayi abinda banniya ba tasa dariya to ai kaga na temakeka kaidinne inata ka tsaya katsaya kai gaba ummu tai dariya ke kuwa aunty zee yaji zuciyarsa zata tafi gidan wani yace eyye kema harda ke ko suka saka dariya Abbakar mamaki yake daman tana magana da dariya haka.
Gidan Mahfuz
Duk ransa abace ya shiga gidan sai dai me yana shiga yaji yamanta komi ba abinda yake sai burin ganin matarsa ko rufe murfin motar baiba yai ciki ita kuwa gwanar daman su suka tunzuro Hajiyarsa ta koroshi dan tuni ko wanne aiki da bokansu ya basu sun kammala.
A tsaye ya hangeta da wata arniyar shigarta suna hada ido wanda yaci kwallin boka yaji ya kasa koda motswa zuwa tai taja hannunsa sukai ciki gurin dinning area ta kaishi ta zuba masa lemon abarba da yasha magani ta miqa masa ya amsa ya hausha saida ya shanye ta zuba masa abinci yaci yai nak.
Komi ya tafi yadda suke so dan basu wani sha wuyaba asirunsu ya kama mahfuz dan shi din ba gwanin ibada bane .
Mahfuz ya zama kamar wani sauna sai abinda matarsa ta fada masa yake ta zama kamar itace mijin shi kuwa irin baiwar matarnan danma bazamu kirashi matarso ba.
Rabonsa da gidansu tun randa ya baro sati biyu kenan ko wayoyinsa matarsa ta kashe cewarta ita bata gama cin amarcinta da angonta ba aiki ma dan dole take bari ya fita shima sai yasha kashedin in ya dade ko ya kula wata shi da ita ne gabaki daya tsoronta ya gama rufe zuciyarsa.
Gidansu Abbakar
Zainab ce tsaye suna magana da Hajiyarsu umma wai yaushe ne Amaryar zata tare nama yaya magana yamin shiru Hajiya tace se randa ya shirya inkuma be wasa ba wallahi sawa zan yasakar min ita tunda naga baya santa inyaso na bata sulaiman kai hajiya kema kinsan yah nasanta sulaiman da tunda ya taso yake qasar waje ai bazai yadda da auren dole ba au haka kika ce zakusha mamaki tai dariya kawai sikai sallama suka tafi.
Soyayya tsakanin Farida da Nasir kamar sa hadiye junansu ko yaushe suna maqale awaya ko yana gidansu Abbakar dan tuni Farida ta dawo gidan da zama.
Magana tai nisa aure saura wata guda duda farida taso sai tana level five yace shikam ya gaji da yaquri tanaji tana kallo ya mata fun qarfi.
Rana bata qarya yau laraba ake kamun Farida su ummu ne manyan biki duda kuwa gogon nata baisan budirin da take ba dan ko ta kanta baya bi qarqari yazo ya dauki takwaransa girin hajiya su fice yawo dan yaron ya saba dashi sosai.
Yau zasu wuce kaduna dan acan za'ai bikin dagyar hajiya ta barsu sun fito da akwatu suna zubawa a bayan mota ya shigo da motarsa idanunsa kansu yai parking ya qaraso.
Ku ina zakune haka kuke jidar kaya cikin sauri ummi tace yah ka