Chapter 6 Reading ABBAKAR BOOK COMPLETE DOCUMENT by AXEEX.txt Arewa Novels

ABBAKAR BOOK COMPLETE DOCUMENT by AXEEX.txt

Author :  AXEEX Category :  Romantic Story

Chapter   6 / 20

15K to 18K   out of 57.6K words

ince mahfuz da ya rarrafo zuwa bakin qofa yana bin ball insa ya ko tsanyara kuka dan besan waya daukeshi ba Nasir yai saurin juyo da fuskarsa haba yaron babansa jin muryar nasir yasashi yinshiru yana ganowa a hannunsa yake ya bangale da dariya alamar farinciki.


Dan rigima wato da bani bane shikenan sai ayita kuka ko Ummi da ta zo daukansa tasa dariya itama lah yah nasir ashe zakazo yai dariya ce miki akai da nadena zuwa a'a nadai ga kwana biyu baka zuwa ne suka shiga falon gabaki daya har Farida.


Wallah yah nasir nayi missing inka da yawa eyye ko eh mana inji Farida duk ganina da kike a sch ta dan rausayar dakai bayan a sch din nuna wa kake baka san mutane ba Allah ko eh mn inka wani hade rai to shikenan maida wuqar zan dinga dariya sukai dariya baki daya.


Ta miqo masa littafi Allah tun jiya nake karanta nan nakasa pls koyan yakarba ya duba eyye wato duk lecture din da muku bakima gane ba tadan juyar da kai time inne inajin bacci to ynx ma ai inna miki cewa zakiyi bacci kike ji dan Allah yah nasir to shikenan bari sai anjima.


To wannan fa ta miqa masa paper a'a banda wannan ai assignment na baku pla yah inkika isheni ko sauran bazan koya miki ba wai ina Ummu ne ta dan fita ne nasan yanzu zata dawo.


What ina taje mene anfanin ummi da na kawo mata tace batasan aiken ummi bata rufe vaki ba Ummun ta shigo ya hade rai daga ina kike naje shago ne ko dan kinga kwana biyu bana zuwa shi yasa kika tsiri futa yawo.


Idonta yai rau rau kamar zatai kuka haba yah nasir kasan bana maka qarya to me yasa baki aiki ummi ba naga batasan zuwa ne what no bawai qi take ba aikenne kamarta dole taji kunyar zuwa wane irin aikene ta miqa masa always ya gani oh basai ki fadanba da wake sayo muku tadan turo baki to inama muka ganka bacin ka dena zuwa yadan sosa kai aishi kenan.


Farida ta miqe tai waje yah bari inje inci gaba da karatuna ummi tasa hannu zata dauki Abbakar yako sa qara Nasir ya ce jeki abinki kyaleshi tai ciki.


Ummu ta zauna yah ina kwana lafiya kalau yace ya dannawa ta kalli Abbakar ganinan ai.


Jiya sai naga saqo tai murmushi ashe ma shi ya kawoka yai dan murmuahi dadinsa da ita akwai bawa mutun amsa haka nace miki shi ya kawoni to yaya rabonka damu kwana nawa bakiga exam ake a sch ba bani da time inkuma nakai dare kinsan hajiya tai dan murmuahi batare da ta amsa ba.


To anman yah kana ganin family dinmu zasu yadda da aurenmu yai dariya gami da sauko da Abbakar to aiko basu yadda ba abinda nasani ni shine dolene su yadda tunda kin yadda ta kalleshi ya daga mata gira.


Fira sukai sosai sai da aka kira sallah ya miqe bari in sallah ya fice.


Haka kawai ummu kejin takaicinsa ya ragu aranta haka kawai takejin hirarsu ta mata dadi koda tana sallah lokaci kadan kadan take dan murmusawa kodan yadda nasir kesan Abbakar dinta ne oho dan rabon da taga yaron na kyakyata dariya yanata warkajaminsa tun dena zuwan nasir abu kadan ma aka masa sai kuka kodan farin cikin danta zata haqura ta takurama zuciyarta taso nasir .


Yana dawowa yace ni zan wuce sai kinjini yah mun gama abinci kazauna kaci inji ummi ok to kamar kinsan yunwa najeji tai dariya gami da komawa kitchen din.


Farida ta shigo yana cin abinci yanzu yaya da abinci be tsaidaka ba shikenan karatuna yasha ruwa yai murmushi sorry mangofa ynx zamuyi.


Sai da suka gama karatun Nasir ya musu sallama ya tafi cike da kewarsu ji yake kamar karya tafi.


Gidansu Abbakar


Wahidi ke ta faman kuka shi bazai tafi ba shi anan za'a barshi daqyar sai da yaga babansa yazo ya hau murna sannan ya yadda yabisu zainab sun tafi cike da kewar yan uwanta da ummanta.


Shi kansa Abbakar sai yaji gidan wani iri dan dan kwana biyun da sukai agidan gwanin dadi kullin cikin hayaniyar yara hakan yasa zainab suna tafiya yace ma hajiya zaije waje sai dare zai dawo sao kadawo tace ta koma ciki.

A teburin me gadinsu yazauna a qofar gida suka hau fira sai mangariba yabar nan din yai gidansu mahfuz dan ya kwan biyu bai ganshiba kamar yadda ya zata kamar koyaushe Mahfuz baya bangaren mazan gidan dole ya zayayo cikin gidan aikuwa abunda bayaso yan matan gidan sunata sha'aninsu waccan na zaune waccan na shanya ko wacce da abun da take bawai abubuwan da suke ke bashi haushi ba face shigarsu basa shigar kwarai indai sina gida duda kuwa abokan yaran gidan kowa shiga gidan yake haka mazan bakowa ne suke shaqiqaiba kawar da kai yai zai yi ciki.


Ya jiyo Aisha na fadin lah yah Abbakar sannu da zuwa yadan saki fuska yawwa qanwarmu ina kuwa mutumin naje dakinsa baya nan lah ai yadawo ban garen hajiya tun rashin lafiyarsa yana nan ma yanzu ok to bari inje.


Yana zaune a falon kansa kan cinyar hajiya Abbakar ya shigo ganinsa hajiya ta fada da murmushinta mahfuz ya miqe zaune a'a ai da kayi kwanciyarka dan gatan hajiya yai dariya zaka fara ko sun gaisa da hajiya ta miqo ai qwanda da kazo duk yabi ya damu kansa kan ummu ka masa nasiha nasan yafi jin maganarka akan ta kowa.


Sun taba fira Abbakar ya miqe sukai masallaci agidan yaci Abincin dare sannan mahfuz ya leqa dakin hajiya zai tafi zan rakashi shima ya leqa hajiyarmu sai da safe au ba'a nan zaka kwan ba eh hajiya ban fadama hajiyata ba to agaisheta sai da safe suka fita tare.


Sun dade a qarshen layi suna tattaunawa kan batun ummu kasan Allah Aminin in yau akace inada ciwon zuciya ba mamaki kullin cikin tinanin ummu nake bacci ma bayinsa nake sosai ba kai mahfuz kadaure ka cirema kanka damuwa kodan hajiya kasan yau in wani abun ya sameka tafi kowa tashin hankali haka ne shi yasa nake daurewa yawwa ka ci gaba hakuri kaji nawan sukai dariya gabaki daya gami da sallama suka rabu.


Hajiya daman so nake muyi magana inji Nasir ta maida hankalinta kansa inajinka akan nefa yadan sosa qeya eh daman ta miqe kaga inbaka shirya ba inka shirya sai ka same daman hajiya tada miki zanyi na samu matar aure tai saurin juyowa da fara'arta da gaske kake eh hajiya wace kuwa wannan Hajiya ummulkhairin baba yasir what ta fada eh Hajiya alamar faduwar da sukaji yasasu juyawa da sauri Mahfuz ne zube da alamun yaji maganarsu ne hajiya tai gunsa da gudu itama hippp ta fadi a sume.............
[12/31/2020, 5:52 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[12/31/2020, 5:53 PM] 🅰️ " AXEEX✌🏻 D'🅱️🅾️Y😎: *ABBAKAR*


*PAGE 80---90*


Rasa ma kan wazaiyi yayi ta maza yai yadauko ruwa yai kan Hajiya cikin sa'a ta farfado da tana bude ido ta tankade nasir tai kan mahfuz dake kwance tahau jijjigashi miqon ruwa mana ta fada cikin qaraji.


Dasauri ya miqa mata ruwan ta hau shafa masa bai far fado ba da sauri Nasir ya daukeshi sai mota hajiya na biye dashi ganin haka yasa sauran mutan gida dake farfajiya sukayo kansu suna tambayar lafiya basu basu amsa ba suka bar gidan hakan yasa suma suka biyosu amota sai kadan aka bari agidan.


Kai tsaye asibitin nasarawa suka wuce basu wani sha wuya ba dan babu marasa lafiya sosai a emergency din yau aka karbi mahfux din.


Tun wajen awa guda da'aka shiga dashi dakin bada temakon gaggawa hajiya keta faman kai kawo tana hawaye babu yanda ba'ai da ita tazauna ba taqi da nasirma ya mata magana saita haushi da fada daqyar tai shiru shima dan nurse ce tazo tace ta ishe su.


Ganin hajiya zata iya masa baki yasashi miqewa yabar gurin yai dan nesa kadan dasu dan yaga irin hararar da take sakar masa lokaci lokaci gami da tsaki da qwafa da take ja in suka hada ido.


Doctor yana fitowa sukai kansa bai kulasu ba yai gun Nasir dan yasanshi aikuwa hajiya na ganin haka tabi bayansa tana fada yau naga mara mutuncin likita ya jiyo zai yi magana Nasir ya dafoshi Am sorry Abdul mum dina ce yadan saki fuska kadan gami da cewa Hajiya bawai na share ku bane kunsan irin haka namiji yafi karfin rai.


Eyyye qarfin rai har yafi na cikin sa da nadauka nai naqudarsa ni nasan zafinsa dan haka zanfi kowa iya jure abinda ke damunsa dan in kula dashi ganin tadau zafi yasa Doctor din yace ai yamaji sauqi dan mun shawo kansa dakyar muka dai daita numfashinsa zaku iya shiga ku ganshi bata jira cewarsa ba tayi gaba.


Nasir ke biye da ita saida suka zo dedai dakin ta juyo ta watsa masa harara me kuma zaka shigo kayi masa bai ce komi ba ya koma baya ya tsaya.


Kwance yake idonsa a rufe da alamun bacci yake hajiya taja kujerar gefensa ta zauna gami da kamo hannunsa ta riqe yai saurin bude idanunsa zatonsa Nasir ne ganin hajiya yasashi fashewa da kuka ta hau rarrashinsa dakyar yai shiru.


Da sassafe nasir yabar asibitin saida ya biya ta gida sannan yai wanka ya shirya yai gidan ummu acan yakarya sun dan taba fira kafin ya miqe ni zan wuce yah tun yanzu eh ummu tadan shafa kan Abbakar Allah ji nake kamar karka tafi yai saurin kallonta da alamun har zuciyarta take magana anman bai fasa cewa da gaske kike tai dan murmushi Allah kuwa to banda abinki ai kwanan nan sai kinmace in fita ta rufe fuska anya kuwa yai dariya ina nan dake.


Har waje ta rakoshi ya miqo mata Abbakar yako sa kuka haba dan rigima yi shiru anjima zan dawo ya zura hannu a aljifu ya miqo masa alawa yako amshe yana kiciniyar budewa.


Har ta juya yace aff ban fada miki ba gobe ba lallai inzoba tadan juyo sororo sabida me yah eh mahfuz ne ba lafiya jiyama a asibiti ya kwan tadan tabe baki ayya Allah bashi lafiya gami dayin ciki abinta abinka da dan uwa sai gabaki daya baiji dadin abinda tai ba aqalla ta nuna tadan ramu ya gyada kai kawai yai gaba.


Ai kuwa da Nasir ya koma asibiti ya sha fada gun hajiya kan yasan dan uwansa ba lpy yai tafiyarsa yawonsa ba ita tai shiru ba sai da Mahfuz yace dan Allah hajiya kice ya fice daga dakinnan inna tanshi numfashina hadewa yake jin haka yasa yace ya fice.


Wajen qarfe uku na rana Abbakar yazo shida Hajiyarsa da qannensa biyu mata sukaita fira da hajiya inda shima sukaita fira da amininsa.


Kwanan Mahfux biyu ummusalma yayar Abbakar tazo dubashi aiko tasha qorafi dan sun saba sosai da Mahfux inma mutun ba sani yai ba zaiyi zaton Mahfuz ne qaninta ha Abbakar ba.


Bakowa adakin sai Mahfuz da ummu salma aikuwa mahfuz yasa mata kuka daqyar ta rarrasheshi yai shiru tahau tambayarsa mene yahau bayani kan ummu ne yar gidan baba yasir yah nasir yasan ita nake so anman yace shi zai aureta tahau masa nasiha haba nawan kabari zamuyi magana dashi nasan baisan kanasanta va inda yasani da tuni ya aura ma ita Allah yasani nace kabar min komi a hannu na zan mai magana ya riqo hannunta nagode yayarmu.


Sai dare ta bar asibitin shima saida Abbakar zai tafi ya tafi ita dan bada mota tazo ba.


Washe gari ta kira nasir a waya har gida yazo ya sameta ta mai bayanin komi yai dan murmushi kafam ummusalma kenan ai duniya ko hajiya bata isa tasa in fasa aurenta ba lokaci yayi da mahfuz zai dena abin da yaga dama lokaci yayi dazai gane vawai komi kake so kake samu ba arayuwa, tai sakato tana kallonsa eyye tunda hajiya ma bata isa ba inaga ni yar karoro yayi kyau ta miqe ta bar falon shima ya kade rigarsa ya bar gidan.


Kwanan Mahfuz hudu aka sallamesu sina zaune gabaki daya a falon mahfuz na kwance kujerar da Hajiya take Nasir ya shigo dauke da Abbakar dansa hajiya ta bishi da kallo gami da yaron wannan fa ya dubeshi dana ne what danka kuma eh hajiya dana ne da muka haifa da ummulkhairi ta miqe ashe nasiru haukan da kake cewa Mahfuz yayi ashe kai kayi yai dan murmushi hajiya aikinsan ba qarya nake ba kuma kinsan da hankalina.


Mahfuz ya miqe qarya yake hajiya dana ne wallahi qarya yake kumin shiru da Allah injita ta fada ra qarfi sukai shiru baki daya kafin nasir ya fara magana eh hajiya ki yadda dani gama kamarmu nan kina gani da yaronnan sabida shi na yanke shawarar auren mahaifiyars dan Allah ki yadda in aureta kodan kare mutuncin bawan Allahn nan tai shiru kawai tana kallon yaron da yaketa faman wasansa tabbas kamarsu nan sosai jitai tsanar yaron ta cika mata rai sosai tai kansa zata takeshi mahfuz da yake atsaye yai kasa asume tai saurin yin kan danta.


Sun samu ya farfado aikuwa ya hau kuka hajiya qarya Nasir yake yaronnan dana ne dan Allah karki yadda ya aure min mata wallahi inban aureta ba mutuwa zanyi Nasir dake zaune tun dazu ko motsi beba tun suman Mahfuz yana ta faman wasa da dansa yace aikuwa sai dai ka mutu Hajiya tahau rarrashinsa dagyar yai shiru tasa aka kai mata shi daki.


Adakin rokonta kawai yake kanta yadda adaura masa aure da ummu tai shiru kawai da ace wani ne cikin yaranta ke faman kiran suhan wannan yar maqiyarta ta da tuni ta yi maganinsa dan dai kawai mahfuz ne.


Haba mahfuz kayi tunani kwata kwata baku dace da ita ba ko kadan ya miqe haba hajiya inban dace da itaba da waxan dace zuciyata da gangar jikina ita suke so.


Nasir ya shigo dauke da yaron yanata faman dariya yace hajiya ni zan mayar dashi kuma gobe ne za'a daura mana auren kawu nazifi ne wakilinta ni kuma nazama wakilin kaina banasan ko kadan kosau daya yarona yai kukan rashin uba nasan ban kyauta miki ba anman nan gaba nasan zakiyi alfahari dani tai zuru tana kallonsa tama rasa ta cewa wai yau nasirun da ko uhum baiso yaji yace shi ke fada mata baqaqen maganganu haka.


Bai jira cewarta ba ya juya zai fita mahfuz yasa qara wallahi hajiya indai baki dakatar dashi ba ta auren masoyita wallahi yau zan kashe kaina tai saurin kiran sunan nasir yai gaba batare da ya tsaya ba tace nasiru wallahi ka qara taku daya Allah ya isa kuma sai ka biyani shayarwar da naima inyaso ka canja uwa yaja ya tsaya hawaye ya biyo idanunsa.


Juyo nan ka kalleni ya juyo ya kalleta kasani ni uwarka dana haifeka hai haqudarka na shayarda kai na haramtama auren yarinyar nan inko ka aurenta Allah ya isa bazan kuma yafe maba ka kuma sani koda bayan raina ne.


Jiyai kamar an sheqa masa ruwan zafi qafafunsa sunkasa daukansa yana qoqarin yada Abbakar a hannunsa zubewa yai qasa jabas hawaye na bun fuskarsa.


Ummu ce ta fito daga daki tana kwalama ummi kira da sauri ta qaraso gani aunty ina Abbakar tace sun fita tare da babansa tun yaushe wajen magariba ta gyada kai kawai ta koma daki.


Har kusan qarfe takwas bai dawo ba ummu ta kuma futowa wai ina yace zai jene farida tasa dariya Allah umma bakida kara indai akan wannan yaron naki ne tai kwafa gami da turo baki kuban amsa tukunna kafin afaramin qorafi ummi ce tace cewa yai zashi gidansu dashi zai nunama hajiya shi what ta fada tana zare ido mai yasa kuka kuka barshi baku fadanba ummi tace cewa yai bazai dadeba.


Kuka kawai ummu ta fashe dashi gami da fadin shikenan nasan hajiya bazata barmin shi da raiba kuka take sosai farida na bata haquri.


Zumbur ta miqe tai daki hijabi ta dauko da wayarta sai kudi dabatasan ko nawa bane ta zari jaka tai waje ummi taso muje tace bata jirata ba tai waje ummi tai saurin binta dan tunda tadan fara girma tadena cire hijabi ko ina dashi take shiga ko bacci zatai duk yadda su ummu sukai da ita taqi ita kunya takeji.


Farida ce tai saurin miqewa ta ruqo ummu haba ummu ina zaki cikin daren nan zani inga halin da yaro na yake ciki ta riqeta dan Allah ummu ki rufa mana asiri karkije dan farine fa tai dan murmushi daga gani na takaici ne tace farida sakeni koma dan mene bazan zauna inaji ina gani akashemin shi ba wai da sunan kunya.


Haba ummu aikin san babu ta yadda za'ai Yah Nasir yabari wani abun ya sami Abbakar kema kinsani ta gyada kai nasani Farida saidai nasan makircin mahaifiyarsa bata jira cewar Farida ba sukai waje ummi ta bi bayanta.


Adai daita sahu ta tara sai da suka fara tafiya yace haija ina zamu ne sunan unguwar ta fada masa.


Adai dai qofar gidan ya parker dan sahun yace hajiya mun iso ta

6 / 20