Chapter 17 Reading ZABIN ABBANA Book Complet by Ummeey Muhammad Lawan .txt Arewa Novels

ZABIN ABBANA Book Complet by Ummeey Muhammad Lawan .txt

Author :  Ummeey  Muhammad  Lawan Category :  Romantic Books

Chapter   17 / 21

48K to 51K   out of 60.6K words

Habiba tafara gani Ameenah tadauki karar tsana tadaurawa Mata Kuma hakan yasamo asaline sakamako iri kyau da Allah ya horewa Ameenah shine take hasada


A haka mukaci gaba da rayuwa har mukasamu kimani shekara biyar nida Ameenah Allah baibamu haihuwaba


Muna cikin Wana haline Abokina Usman yabani shawara dana shigo garin Kano naci gaba da sana ,ata tadinki Dan acan anfin samu kasuwa


Nasanar da Baba da yayana dakar suka Amince Muna shirye shirye tafiya Kano Allah yayiwa Innarmu rasuwa




BAYAN WATA UKU DA RASUWAR INNARMU


Muka tarkato kayamu muka dawo Kano da Zama Kuma cikin ikon Allah munasamu dinki sosai


Haka mukaci gaba da rayuwa a Kano cikin rufin asiri inazuwa Gombe akai akai haka zansaya kaya masu tsada natafiwa da Muhammad dasu Dan jin yaro nake har cikin raina Kuma kusan kullu saimuyi waya da yayana haka zai hadani da Muhammad a waya yanta min shirme nikuma sai naita jin dadi






Shakaramu goma da Aure Ama Allah bai bamu haihuwaba






Nida Ameenah mukasace Muna fama da radadin rashin Haihuwa sakamoko shekarun da muka kwashe Allah bai bamu haihuba


Mumika lamuramu ga Allah kullun cikin Adu,ah muke Allah yabamu Yan,Yan nagari wada Al,umar musulmai zasuyi Alfahari dasu




Haka rayuwarmu taci gaba da tafiya kullun cikin Kai kukamu ga mahalincimu


Allah majin rokon bawansa Allah ya Amsa Adu,armu Ameenah tasamu ciki cikin ikon Allah batare da Tasha wahalar laulayiba
Nakira yayana nasanar dashi sanar nakira K'anena su Asabe da Halima yayana Kuma yasanar da Babamu gaba daya Yan uwana suyi farin ciki da samu cikin Ameenah suka diga tayani murna.._*ZAƁIN🤵🏻‍♂ABBANA👳🏼‍♂*_






_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD




LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_




https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share


_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link




_*WHATSAPP LINK*_


https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA


_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*







For more information
08140801885




Page. 95 & 96




_____________Rayuwamu tacigaba da gudana cikin fariciki da kwanciyar hankali


Ameenah Tana samu kullawa daga gareni nakan tayata duk wasu aikace aikace gida hata wanki bana Bari tayi dakanta


Haka mukaci gaba da kasancewa kullu cikin tausaya Mata nake musamama gani yada take Zama da k'ar tashi da k'ar Dan a lokaci cikin nata ya tsufa


Tashiga watanin haihuwarta wata Ranar talatace da bazan taba manta Wana Ranaba a cikin tarihin Rayuwata a Ranar Saida nagama duk wasu aiyukan gida hata girki Saida namata sana nanufi shagona Dan akwai dinkuna Mutane a guna Kuma a Ranar mukayi dasu zasuzo sukarba


Ina insa shagona bantsaya bata lokaciba nafara gudanar da a yunkan dake gabana


Kiran sallah azahar ya tadani daga kan kekena nayi Alwala nanufin Masallacin

Ina dawowa daga Masalaci natar da wata Mata zaune a bakin kofar shagona da wata bakar jaka iri tahanu a gefenta


Bankawo komai a Raina ba nayi shigewata shago naci gaba da a yukana


Koda nafito yin sallah La,asar nasake tarda ita zaune a gun




Ina dawowa daga Masalaci Naga Bata gun Ashe Tana rakube a gefen shagona da Alamu itama sallah takeyi


Shigewa shago nayi Ina mamaki a Raina ko ita Kuma Mai ya kawota naguri Tana Mace ohh to Allah dai yasa lafiya


Cigaba nayi da aikina har Lokacin tashina yayi fitowa nayi narufe shagona daniyar tafiya gida


Har nafara tafiya nayi nisa zuciyata tafara rayamin akan nakoma naje nasamu Wana barwar Allah kotana bukatar temakona


Juyawa nayi nakoma bakin shagona natar da ita zaune a idan nabarta sai a Lokacin nalura Ashe tsohon cikine gareta


Take tausayita ya kamani Dan a zahiri Ina Tausayawa duk wata Mace Mai juna biyu


Karasawa nayin gareta tare da fadin baiwar Allah lafiya kuwa Naga tukafin azahar kike zaune a nan da Alama Kuma Kamar ke bakuwace a garina



Dago Kai tayi takaleni Hawaye nazuba akan fuskarta cikin wata iriyar murya tace Dan Allah Mallam kateemakeni Kamar yada Allah ya temakeka Koda da gurin kwanane zuwa safiya inacikin mawuyacin halin gashi bansa kowaba a cikin garina kuka tasa wada hakan yasa jikina yin sanyi




Kallonta nayi cike da tausayawa musamama gani iri halin da take ciki
Nace da ita bakomai baiwar Allah Zan taimakeki da gurin kwana kitashi mutafi gidana




Dak'ar ta inya mikewa saboda da cikinata ya tsufa gashi alamun Kamar a gajiye take


Godiya tadingamin sosai sana muka dauki hanyar gida


Koda muka inso gida Ameenah tatarbeta cikin Mutunci da girmamawa duk da batasan kowacece itaba batasan daga Ida tafitoba Abinci takawo Mata da ruwan shaa


Sana nasanar da ita bakuwar kwana zatayi Ameenah batayimin musuba sana Bata tanbayeni daga Ina Wana baiwar Allah takeba saima kokarin mikewa da takeyi da nufin gyara dakin da bakuwar zata sauka dakatar da ita nayi


Saboda nasan Me takeson ai katawa nace da ita tabari zanje nagyara dakin kallona tayi cike da tausayawa tace Dan Allah Mallam kabari nagyara dakinan dakaina ai wahalar zatama yawa kadawo daga kasuwa ko hutawa bakayiba gashi Kuma kakwason gajiya sana na kyaleka kayin wani aiki batare da kahutaba ai Abu akwai tausayawa





Hakan da Ameenah tayi ya Kara Mata girma da daraja a idanuna


Dakar Ameenah tayarda tabarni

Nashiga daki nagyarasa tsaf sana namata shufudin nafito natar dasu suna hira




Nikuma nayi shigewata daki Koda nashiga tausayin Wana baiwar Allah ce ya cikamin zuciya


Ameenah ce tashigo daki tasameni Kallonta nayi nace Ina Kuma Kika bar bakuwar

Kallona tayi cikin gimamawa tace narakata d'aki ama de Mallam Wana bakuwar tamu daga gani Tana cikin damuwa


Ama daga Ina tazo Naga bataba ganita a cikin dagikuba kode dangisu innace shiyasa bansataba


Kallonta nayi ciken da kullawa nace badangi mubace hasalima bataba ganitaba nide naganta a bakin shagonane shine Naga Tana bukatar temako Kuma Naga Muna da halin da zamu temaketa




Ameenah tace Allah sarki Mallam ai gyara daka temaka Mata daga gani Tana cikin damuwa gata da tsohon cikin garenta komai ya rabata da gida a cikin iri Wana halin da take cikin






WASHE GARI


Washe gari da safe bayan mun karya fitowa tayi tagashemu a lokacin inashiri fita shago


Amsawa nayi cikin kullawa sukuyar da kanta tayi kasa tare da fadin Mallam nagode da temakon da kamin Allah ya sakamaka da gidan aljannah


Zantafi bazan taba mantawa da iri temoko da kulaniba Kai da matarka tabbas samu iriku a Wana lokacin Abune Mai wuya


Ameenah tace to yazu idan kitafi daga nan Ina Zaki gashi ko sunaki baki fada manaba


Take idanuwata suka ciko da kwalla cikin murya kuka tace sunana Aysha Kuma daga nan basan Ida zaniba


Bani da kowa sai d'an uwana guda daya shima naje gidansa ance ya dade dabari gidan gashi basamu wada yasa Ida ya komaba Dan shin nashigo gari Kano



Kukane ya cin karfinta rarashinta Ameenah tafarayi tare da fadin kidena kuka baiwar Allah


Kikwantar da hankalinki kisanar damu Asalin Labarinki mudin kikasance daga cikin wadada suke bukatar temako to nayi mikin Alkawari zamu temakeki zamu zauna tare dake a cikin gidana har zuwa lokacin da Allah zaisa agano Ida d'an uwanaki yake


Hawayen dake zuba akan fuskatar tashare cikin dasheshiyar Murya tace



SUNANA AYSHA UMAR




Mahaifina Alhaji Umar ya kasance Dan kasuwane wada sunasa ya shahara a a cikin garin Bauchi


Mahaifiyarmu Hajiya zainab tumuna yara Allah ya Mata rasuwa bayan rasuwar Umma mu da shekara biyar


Abbamu ya. Auro wata Mata Yar katsina tuda Abba ya Auro Anty Fatima tabi tadaura Mana Kara tsana nida yayana Dan Bata kaunar tabude idon tagamu a cikin gidan






Mu biyu ne mukakasance Yan Yan a gurin Mahaifimu Yaya Musa shine babba saini nice Yar Auta mukasance muna samu kullawa daga gun Mahaifimu duk wani gata Yana nuna Mana soyayyah da Abba kemana tadabance Abba baya kaunar duk wani abu da zaibata Mana Rai


Shigowar Anty Fatima rayuwar Abba shine yazama sanadin tarwatsewar fari cikimu


Gani iri soyayyah da shakuwa dake tsakanimu da Abba baya samu nutsuwa idan Bai gamu kusa dashiba


Wana Abu bakaramin bakatawa Anty fatima Rai yayiba haka tadiga yiwa Yaya Musa makirci takasa kasa


duk dantaga tabatasa a idon Abba

Baban abuda kedamuta baiwuce gani duk wani makircita baya tasiri a gun Abbamu


Abba namana wani irin son wada baki bazai inya furtawaba


gata Babu iri wada Abba baya nuna mana komai namu nadabane




lokacin da Yaya Musa ya kamalla karatusa wani Abokin Abba ne yasama masa aiki a campany su dake Kono


Yaya Musa ya bar Bauchi ya dawo Kano da Zama Abokin Abba najin dadi aiki da Yaya Musa ya Aurawa Masa Yar,sa Ramlat






BAYAN SHEKARU GOMA SHA BIYU DA AURE YAYA MUSA








Abba ya yanke shawara hadani Aure da yaro Abokisa Alhaji Sadiq Koda Abba yasanar Dani hukunci da yayanke ban inya musamasaba saboda nasan Alhaji Sadiq mutumin kirkine saide inajin tsoro Matarsa Hajiya Saratu






AN DAURA AURE NA DA ALHAJI SADIQ




Dauri Auren da ya jefa duka ilahirin dangina cikin farin ciki ama bada Anty Fatima data karajin tsanata tanuku a cikin zuciyarta




A Ranar da nashiga gidan Alhaji Sadiq a Ranar nafara fuskatar barazana daga gun Saratu




Ina zaune akan katafare gadona na Alfarma fuskata lulube da mayafina Mai daukar idanu sai jinayi anshigo dakin a zatona nadauka ango nane jinayi ankaraso kusa dani anshakemin wuya har Saida nagagara yin nufashi


Duka akafara kaimin tako Ina kuka nake Ina Neman dauki Saida Saratu tamin duka lilis sana takaleni


Tahada damin gargadi cikin kakausar murya gamin da fadin saita lalatamin rayuwa sai nayi danasini shigowa gidanta saita maidani Abu tausayi yada kowa bazai son ya rabeniba


Nide bace da ita komaiba saima kuka danacin gaba dayin a Raina Ina tunani wace iri rayuwa zanyi a cikin gidana




Koda Alhaji Sadiq ya shigo dakina yaga irin abuda Saratu tamin Rashi ya baci sosai yabani hakuri sana yamin Alkawari zai dau mataki a kanta




Tudaga Wana Rana Saratu tasani a gaba bani da ikon yin wani Abu a gidana nide kullu Ina daki ban Isa nafito wajeba


Gashi sai tsoronta ya da'su a Raina duk abuda zatamin bazan tab'a iya ramawaba gashi nakasa sanar da Abba halin da nake ciki


Wani sabon Al,amari da nalura dashi shikansa Alhaji Sadiq tsorota yakeji a yazu bashi da ra ayin kansa Umarnitane kawai yake aiki a gidan




BAYAN WATA UKU


Da Aure Alhaji Sadiq natashi da Rashi lafiya zazabi gashi bana inya cin Abinci danaci Zan Amar dashi


Alhaji Sadiq dakansa ya kaini hospital likita yasanar dashi cewa Ida dauke da juna biyu har natsawo wata biyu


A Ranar Alhaji Sadiq yayi murna har kyauta Saida yayiwa likita


Muna dawowa gida Alhaji yasanar da Saratu cewa ina dauke da juna biyu aiko a Ranar Naga tashin hankalin Dan Saratu cewa tayi ban Insa nahaihu a gidataba shekarata Sha biyar a gidan Bata taba samun cikiba saini daga zuwana Shiko Alhaji Sadiq ya gagara Mata magana Dan shima tsorota yakeji






Cikina nada wata biyar Abbana yayi hadari Motar a kan hayansa tazuwa Abuja take ya Amsa Kiran mahalincisa




A Wana Rana naci kuka rabuwa da Abba sau biyu Ina Suma dan shikaide nake gani naji sanyi a Raina shikasa Yaya Musa kasa jurewa yayi kuka yakeyi tankar mace


Anyi sadakar bakwai Yaya Musa ya min nasiha sosai akan nakwatar da hankalina rasa Abba da mukayi bawai Yana nufin narasa komai narayutaba yamin Alkawari zai kula Dani zai sani cikin fari cikin maran yankewa


sana yace nakoma gida tuda har anyi sadakar bakwai


Tudaga Rasuwar Abba Yaya Musa shine ya dawo madadin Abba duk wata kullawa da Abba kenunamin Yaya Musa Yana nunamin kullu sai yakirani dan yaji lafiyata

Hata gini dayakeyi nasabo gida dazai koma Saida yasanar dani nima nake sanar dashi da Zara nahaihu zazo Kano


Anty Fatima Tubayan rasuwar Abba tamike kafarta a gidamu takecin duniyarta da tsike duk da Bata Gama takababa





Naci gaba da fuskarta barazana kalla kalla daga gun Saratu bata da buri da yawuce taga cikin dake jikina ya zube Tasha samin magani a cikin lemo


Haka nadena Shan lemo gidan hata Abinci gida nadaina cin saboda gudun kada tacutar dani




Cikina nada wata Tara a Ranar Yaya Musa ya kirani yake sanar dani ya tare a sabon gidansa natayashi Muna sosai sana mukayi hira tare da Kara jadada Masa cewa idan Allah ya saukeni lafiya nima zanzo Kano shide Yaya Musa yanajin a jikinsa banajin dadi Zaman Aure haka zaita tabayata ama sai nakasa fada Masa komai Koda nayi niyar fada Masa sai bakina yamin nauyi haka Zan hakura nayi shuru




Muna Gama waya da Yaya Musa nafito zani dakin Alhaji sai naji Saratu tanawaya tanacewa kadafa a samu Matsala a Wana aiki sonake kukashemi. Ita a yau sana kufarka cikinta ku kashemin harda Dan dake cikita


Kuzo yazu zuwa anjima Alhaji zai dawo banaso takara Koda mitin gomane a Raiye natsani Aysha mutuwarta kawai nake bukata


Jirine naji Yana dibata kuka nasaka nayi sauri toshe bakina kada tajiniyo


Dakina nawuce cikin sauri nadauki jakar nazuba Gwalagwlene a ciki da Dan saura kudadena fitowa nayi daga cikin gidan


a dare nanufin tashar mota acan nakwana da safe nahau motar Kano Saida nashigo cikin Kano natina da nabar wayata a can gashi bani da number Yaya Musa akaina


Nayanke shawara zuwa tsoho gidansa kozasamu wada yasa Ida ya koma


Koda naje gidan Suma cewa sukayi basusan Ida ya komaba haka naita yawo a cikin garin Kano


Duk wada nabukaci ya teemakeni sai yakin wasu har guduna sukeyi


To kaji dalilin zamana a bakin shagonka saka makon gajiya da nayi da bulayin Neman yayana


Dagani har Ameenah Tsitar kamu mukayi cikin tausayin Wana baiwar Allah


Kamar yarda Ameenah tayi Mata alkawari zamu temaketa


Haka nasanar da ita tacigaba da Zama harzu lokaci da Allah zaiyi ikonsa




A RANAR DA AYSHA TA CIKA KWANAN BIYAR A GIDAMU






A Ranar ne Nakuda tatasowa Ameenah misalin karfe 1:30 nadare nafito Neman Abu hawa domin kaita Asibiti

17 / 21