Chapter 3 Reading ZABIN ABBANA Book Complet by Ummeey Muhammad Lawan .txt Arewa Novels

ZABIN ABBANA Book Complet by Ummeey Muhammad Lawan .txt

Author :  Ummeey  Muhammad  Lawan Category :  Romantic Books

Chapter   3 / 21

6K to 9K   out of 60.6K words

ya dawo baya.






Ummeey da ba tama lura da Abba ya 'karaso in da suke ba, ckin 'ba'cin rai Abba.






Ya ce"Keee! Ummeey me kike yi anan?"








Cikin firgici Ummeey, Ta ce"Abba sannu da dawo wa"






Dur'kusawa Haydar da Adam suka yi har 'kasa cikin girmamawa suka gaishe da Abba.






Amsawa Abba ya yi, y afara tambayar mai ya kawo su cikin jin kunya Haydar ya fara masa bayani.






"Abba ni ne Haydar. wanda ya ke xuwa gun Ummeey shekarun baya da su ka wuce"






Mamaki ne ya kama. Abba cikin sanyin jiki Ya ce"Ayya na gane ka mu shiga daga ciki"






Abba ya yi musu iso harxuwa cikin gida, haka su Haydar suka gaisa da Mama Ummeey ta kawo musu abinci da ruwan sha, sun ci abinci cikin farin ciki.




Shi dai Haydar duk in da Ummeey ta yi idonsa na kanta sai da suka gama cin abincin Abba ya shigo suka sake gaisawa cikin mutuntawa.






Jikin Abba ba 'karamin san yi ya yi ba, fuskarsa d'auke da damuwa ya rasa mai xai ce da Haydar domin shima shaida ne akan irin 'kaunar da su kewa junna su.






Cikin san yin jiki Abba, Ya ce"Haydar ina mai baka ha'kuri ka xo a 'kurarren lokaci domin kuwa kwana kakwai ya rage auren Ummeey na bata Muhammad d'an yayana Abdallah, ka yi ha'kuri Haydar hakan ta faru ba'a son rai na ba"






Ummeey dake gefe tana jin kalaman mahaifin nata take ta xube 'kasa a sume.










__By ummeey muhammad lawan (ummu Afnan)…✍🏻___Date:-_ 2022/11/09




*🤵🏻‍♂ZABIN ABBANA👳🏼‍♂️*




_NA_






_UMMEEY MUHAMMAD LAWAN ( UMMU AFNAN )_




_{YAR AUTAR DASHEN ALLAH}_






*DASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION*




*D.A.W.A*


https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783




__For inf...08140801885__






Page 19 & 20






_______________ Cikin tashin hankali Mama ta'karasa in da Ummeey take a yashe, jijjigata Mama ta fara yi taga babu alamar numfashi a tare da ita.





Fashewa ta yi da kuka tana fad'in, "Na shiga uku mai ya ke shirin faruwa dani, Ummeey ki tashi na yi miki al'kawari muddin ina raye sai burin ki ya cika"








'Karasowa Haydar ya yi in da take, dur'kusawa ya yi a gabanta idanun sa na xubar da hawaye.






Cikin kuka, Ya ce"Ummeey ki tashi zama dake babu mai hannani, idan kin ga ban aure ki ba to tabbas ruhi na ne ya bar jiki na"






Haka Haydar ya din ga kuka yana sambatu.






Tashi Mama ta yi ta nufi in da randar su take, ruwa ta d'ebo a kofin tanu fi in da Ummeey take ta yayya fa mata ruwa.






A hankalin Ummeey ta fara bud'e idanuta jin ruwa mai san yi na sauka akan fuskarta, ajiyar zuciya ta sauke mai 'karfi take abubuwan da suka faru suka fara mata yawo a 'kwa'kwalwarta.




Kallon Haydar d'in ta yi ta ga hawaye na xuba a fuskar shi take tausayin sa ya kara kamata.






Yun 'kurawa ta yi ta tashi ta nufi in da Abban nata yake zaune babu alamar fara'a a tare da shi murtuke fuska ya yi tsantsar 'bacin rai ne suka bayyana a fuskarsa.






Dur'kusawa ta yi a gaban shi, Ta ce"Ka yafe min Abbana bawai maganar da ka yi zan yi musu ba, Abbana bawai ina musu da kai bane akan za'binka na san ba xaka ta'ba za'ba min abin da xai cutar dani ba"




"Ka yafe min zuciyata ta kasa ha'kura da Haydar, Abba ka taimaka ka auran dani ga Haydar.


Abba idan baka aura min Haydar ba xan ha'kura da aure har abada!!






Kallonta Abba ya yi cikin 'barci rai, Ya ce"Keee! Kin ga nayi miki kama da wanda xai yi al'kawari ya kar ya, to wallahi kin ji na ratse muddin ina numfashi a duniya wannan aure babu fashi sai an yi shi ko da ko a ce idan an kai ki gidan xa a dawo min da gawarki ne"




Ummeey ba 'kara min firgici ta shiga ba,ta firgita kwarai da kalaman mahaifin nata ta san shi yadda yake da tsauri akan ra'ayin sa.






Shi dai Haydar bai ce komai ba ido kawai ya xubawa Abba.






Adam ne ya yi 'karfin hali, Ya ce"Abba kayi ha'kurin mu barwa Allah lamarin idan Allah ya 'kaddara Ummeey matar Haydar ce to babu mai hanawa, mu xamu wuce Allah ya xa'bar mana abimda yafi alkairi"






Mama Ta ce"Ameen ya Allah, amma dai ba Kano xaku wuce ba ko?"








Adam Ya ce"Eh da ke akwai kakata a nan d'in can xamu wuce mu kwana"






Adam ya kama hannun Haydar su ka yi ficewarsu daga gidan Mama tana yi musu Allah ya kiyaye.






Ummeey na ganin fitarsu fashewa da kuka tayi.








Abba ko ko kallonsu bai yi ba dan shi yanxu haushin suma ya ke ji dan gani yake xuwan su babu alkairi a ciki gashi sun jawo 'yar tasa tana son bijere masa.






**
Koda Haydar suka fito daga gidan motar su suka shige Adam ne mai tu'kin babu wanda yace uffan kai tsaye herwagana suka wuce…










_By YAR AUTAR DASHEN ALLAH......✍🏻_https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2192729347574173/?ref=share


_*FACEBOOK LINK*_
https://www.facebook.com/groups/2192729347574173/?ref=share_group_link




_*WHATSAPP LINK*_


https://chat.whatsapp.com/CnAupcS3i8c4y3JHVuXYXA


_*DASHEN🌲 ALLAH*_
_*WRITER'S ASSOCIATION📚📚*_
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_{ƙungiyar dashen allah ƙungiya ce ta jajurtattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, faɗakar daku.}_
*Alƙalami✍🏽 yafi takofi🗡️*


_*ZA6IN🤵🏻‍♂ABBANA👳🏼‍♂*_
_*NA*_
_*UMMEEY MUHAMMAD LAWAN*_
_*(UMMUH AFNAN)*_
_*"YAR AUTAR💃🏻DASHEN🌲 ALLAH*_








For inf...08140801885








*Page 21 &22*




______________Suna insowa gidan sallama sukayi inna ta Amasa sallam tare da fitowa daga dankin mamakine ya bayana karara akan fuskarta Inna


murmushi karfin halin Adam yayi yace sai Kuma kikaga nasake dawo wa ko toh wannan karon rakiya nayin ba gunki naxoba


Taɓe bakin Inna tayi tace to ai nima ban nemekaba toyaxu Mai yakawoka gidana ai saika koma gun wadanda kazo domin su


Tabarma Inna tashifiɗa musu zama sukayi suka gaisheta ta amsa


Cikin kulawa Inna tace Adamu ? aini dana ganka har gabana yafaɗi na ɗauka wanni abune yafaru naga jiya jiya kakoma Kano Kuma ance yau kadawo!




'Kallonta Adam yayi yace "kwantar da hankalinki Inna babu abuda yafaru


Wannan dakike gani abokina ne, yanuna Haydar dake zaune Inna ma kallon Haydar ɗin tayi tace " ayyah sannuko daƙyar Haydar ya iya buɗe baki ya amsa mata


Inna mushaƙu dashi sosai harta Kai ga bama iya boyyewa juna komai duk wanda yasani to yasan Haydar.

Inna ƙaddara tafaɗawa abokina wanda shine sanadi xuwan mu Gombe a yau


Take Adam ya kwashe duk abun dayafaru tun farko haɗuwar Haydar da Ummeey
Adam bai ɓoyewa Inna komai ba.


Kawai sai ganin Inna sukayi tana sharar kwalla domin Inna tsohuwar nan ce wacce tausayin abu 'kalilane yake sata zubar da Hawaye


Cikin tausayawa Inna tace sannu yaro hakika labarinka cike yake da abun tausayi


Shiko wannan mahaifin yariyar nan wanne irin mutu ne da zai nemin almakashi ya yanke ingiyar ƙaunar da Allah yadasata a zuciyar bayinsa


Wlh Ina tausayawa masoyan da sukeyin nisa cikin kogin ƙauna a zo ace rana tsaka za'a rabasu hakan yakan iya jawowa sanadiyar tar watsar zuciyoyinsu


Amma kayi haƙuri Haydar kada kamatsawa kanka, karasa kar sashin zuciyarka, kana lallashin zuciyar ka kabata hakuri Allah xai sauya maka da wadda tafita


Ɗago idanusa yayi wanda suka rine sukayi jaaa ya ɗaurasu a kan Inna yace "Inna bazan taɓa samun madadin Ummeey ba
barai har nayin tunani samu wace tafita, take tausayinsa yaƙara kama inna


A haka Inna taita rarashinsa Tana bashi labare daban-daban wanda suka shafi rayuwa duniya a haka harya ya ɗan samu nutsuwa a zuciyarsa kiran sallar magriba akafara suka ɗauki buta sukayi alwala suka wuce masalaci Basu dawo ba saida akayin isha'i ɗankin Inna suka wuce Inna takowo musu abinci


Amma Haydar yaƙi ci yace ya ƙoshi domin yarda zuciyar sa take masa ƙuna baiga alamar zai iya haɗiyar ruwa bama bare kuma har ya iya cin abinci


Babu yarda Adam baiyi da Haydar ba akan yacin abinci koda kaɗanne amma yaƙi


Inna ce tasa baki tace "haba Haydar kada kayin fushi da inkon Allah
kazamo mai karɓar ƙaddara a duk yarda taxomaka, ka godewa Allah domin shine ya jarabceka domin ya gwada karfin imaninka , dan Allah naroƙeka ka daure kacinye wannan jarabawar


Itafa jarabawa soyayyace daga mahalinci take, duk wanda baya samun jarabawa a rayuwa toh ya binciki kansa
maganganun Inna sunyi tasiri a kan Haydar take yaji zuciyarsa tayi sanyi godiya yayiwa ubangiji daya bashi inkon cin wanan jarabawar.


Yace "Inna nagode da tinatarwarki a gareni nagode da nuna kullawa da tausayawa da kikayi a gareni




Daɗi Inna taji dan gani ɓacin rai nasa ya ragu a zuciyarsa tace bakomai Haydar ai shi ɗa nakowa ne




Haka Haydar yasa hanu sukaci abinci ammafa yana cin abinci ne kamar wanda yake cin magani domin daurewa kawai yakeyi


Bawani cin abinci yayi da yawa ba yacire hannusa shima de Adam ɗin haka take a gurinsa ganin halin da abokin nasa yake cikin bakaramin tayar masa da hankali yayi ba sai yakejin jikinsa tankar wani marar lafiya




Tashi sukayi sukayiwa Inna sai da safe suka wuce ɗakin Adam, ɗakin tsaf yake an gyare dama Inna gwanace wajen tsafta ta gyara ɗakin tsaf kwanciya sukayi kowane su abu namasa yawo a zuciyarsa musamma ma Haydar dashi kaɗai yasan abunda yakeji a ransa
barci ɓarawo ne yayi awun gaba da Adam


Amma shi Haydar ko rintsawa baiyiba bai ankaraba saijin kiran sallar asuba yayi tashi yayi ya xauna sanan yatashi Adam


Sukayi alwala suka wuce masallaci basu dawo ba saida gari yayi Haske
Adam ya kalin Haydar yaga idanusa sun kunbura sunyi Jan


Yace "Haydar yaxu bazaka cire wannan abun aranka ba.


"Haydar ayau Ina mai baka shawara daka haƙura da Ummeey.




_*By. YAR AUTAR DASHEN ALLAH......✍🏻*_🤵🏻‍♂ZABIN ABBANA🎅🏻




NA




UMMEEY MUHAMMAD LAWAN
(UMMU AFNAN)
💃🏻YAR AUTAR 💃🏻DASHEN ALLAH






For more inf...08140801885






Page 23 & 24




________________ "Tunda har Mahaifinta yake in kirarin cewa Koda zata mutu baxai Aura mata kaiba"
kaduba irin Maganganun da yake fada Wanda kwata kwata bai dace ace uba yafadawa Yar'sa wannan magan ganu ba.


"Haydar Mahaifin Ummeey yayin fushi sosai Ummeey na cikin matsalla babba kaga baxamuyi nasara Akansa ba


Haydar inde har kaunar da kakewa ummeey ta gaskiyace toh ka kar'fafa mata gwuwa wajen ganin tabin ummurnin Abbanta


Ka rarashe ta wajan ganin takarbin zabin Abbanta'
Shide Haydar baice komai ba idon kawai ya xuba Masa.


"Ama kallamansa sunna Masa yawo a kwakwalwarsa


Zuciyarsa na tafar fasa kamar xata faso kirjinsa tafito waje idan akwai Abun da yafi tsana A duniya bai wuce ace yarabu da Ummeey ba


'To ama Kuma Yaya xaiyi kadadara tariga da tariga fatan mafita dayace shine ya yarda da shawaran da Adam din kebashi.


Haydar ya dau shawaran Abokinasa batare da son ransa ba wucewa yayin ya nufin inda suka anjiye motar su


budewa yayi ya dauko takada da bairo yafara rubutu kamar ha








Amincin Allah yatabata a garekin ya ke ma abociyar kyau da nutsuwa akullun burina na inso garekin nasamu yardarki na nuna mikin son dana zautu da muradin bengenki kece wace nake burin malaka Amatsanyin matar Aure Ama kash!!!!
Kaddara taringa da tariga fata mafarkina baxan tabba tabataba burina baxai taba ciki ba..


"Ummeey nah Ina son kixama jaruma Mai karbar kaddara komai girmar ta
Babu yarda muka inya yaxamo Mana dole murabu da juna.


Ki dau wanna abu a Amatsayi kaddara mu Wanda bamu insa mutsa laketa ba


Ina Mai Neman Alfarma a garekin ki daure ki karbin zabin da Abba yayin mikin domin Abba yafimu sanin daide
Duk Dan' nagari burinsa ya kyautatawa mahaifansa.


har yasasu cikin farin ciki
"Biyayyyah ga iyayyen dole ne baxan son ace ta dalilina Abba yayin fushi da keba


Ummeey xanjin dadin idan har Kika kasance daga cikin Yan"Yan da iyayyesu xasuyin alfahari dasu ummeey na sadaukar da soyayyata ne domin ganin ciga banki a rayuwa xan barki ne saboda farin cikin Abba fatana Dee Abba yayin Alfahari dake Ina yin mikin fatan alkairi da fatan nasara a rayuwa baxan tabba mantawa dake ba baxan manta halancinki gareni ba Ina Mai tabatar Miki dacewa da sonki xan koma ga mahalincina sonki yayimin tabo a zuciyata Wanda baxai taba gogewa ba nabarki lafiya ummeey sai watarana Allah ya hada fuskoki mu da alkarin Allah yabakin ikon cika wa Abba burinsa ga number Haydar idan kina bukatar temako daga gareni karkiji kuyanta yanxu naxama yayanki Kuma Dan uwanki najini bissallah ..




Dago kan daxaiyi suka hada indo da Adam


Mikawa Adam yayi yace Adam " gashi kaje gidasu ummeey ka aika yaro ya Kai mata Yana maganar jikin a sanyaye cikin tausayawa Adam ya karba wasikar budewa yayi yafara Karan tawa


Har karshe Adam ya karanta take yaji tausayin Abokin nasa ya Kara shigarsa.


kalonsa yayi yace kwantar da hankalin ka Haydar nasan da ciwo a Rai ama komai xai wuce xai xamo tarihi


Allah ubangijin ya shiga lamarinka Amsawa yayi da amiiiin


Zuwa sukayi sukayiwa Inna sallama Inna tarakosu har bakin mota tayi musu fatan alkairi


Da fatan sauka lafiya haka suka wuce suka bar Inna cikin alhenin da tausayin halin da Haydar din yake cikin
Koda suka inso kofar gidasu ummeey yara suka Taran sunna wasa


Adam ne ya fito daga cikin motar yakarasa inda yaran suke sallama ya musu yace " Kai xona aike ka gidanan ka kaiwa ummeey mikewa yaron yayi ya karbi sakon Adam ya ciro sabuwa dari biyar ya mikawa yaron


Yaron ya karba tare da godiya cikin farin cikin da jin dadi ya shiga gidan


Sallama yaron yayi ai ko ya cin sa.a Ummeey na tsakar gida Tana xaune ta kifa kanta a kan gwuwoyinta


Ta Amsa sallamar batare da ta dago kanta ba


Yaro yace Wai gashi ijin wasu muta ne suce abaki


Dago Kai Ummeey tayin da mamaki a fuskarta tace ni Kuma a kace kabawa


Yaro yace eh karbar ta karda tayin ta bude idanuwanta suka sauka a kan rubutun Haydar gabanta ne yafadin take xuciyarta tafara bugawa


Kamar xata fasa kirjinta tafiton waje fara karanta wa tayin Hawaye na kwarayan a idon ta


Cikin shashekar kuka tace shikenan narasa farin cikina na shiga uku na


Mama ce tafito jin kukan nata karasawa tayin da sauri ta fada jikin mama Tana cewa..












By YAR AUTAR DASHEN ALLAH...✍🏻🤵🏻‍♂ZABIN ABBANA🎅🏻






NA








UMMEEY MUHAMMAD LAWAN
( UMMU AFNAN)
💃🏻YAR AUTAR💃🏻 DASHEN 🌲ALLAH








For more inf...08140801885








Page 25 & 26








_______________" Mama Haydar ya barni barina har Abada shikena mafarkina ya rushe Kara fashewa tayin tayi da kuka Mai ban tausayi


' Rarashin ta Mama tafarayi tare da mata nasiha Mai ratsa zuciya


' Tadan samu sasauci dagane da radadin da zuciyarta take mata..


Share hawayen dake zuba a fuskarta tayin tace kiyin hakurin Mama zuciya tace take min zogi takasa jurewa a zabar radadin rabuwa da Haydar..


Tausayin tane ya Kara kama mama hawayen da take boyewa ne suka xubo a kan fuskarta..


Daga kan da Ummeey xatayi taga Hawaye naxirya akan kuncin Mama


Cikin tashin hankalin tace Mama kidaina xubar da hawayenki a kaina


Xubar hawayenki masifa ne a gareni


Hannu tasa tafara share mata Hawaye dake xuba a fuskarta..


Tace Mama hawayenki tsada gareshi a guna darajarsa yafin karfin zinare


Dan Allah mamana kada kibari hawayenki ya xubo Koda kuwa kan fuskar kine


Mama ki duba kingani inna murmushi Kuma hakan yasamo asalin ne tun daga kasan zuciyarta


Murmushi karfin halin Ummeey tafarayin Wai duk Dan taga ta kwantarwa da mama hankalin




***********


A bangaren Ango Kuma zaune yaken shida mahaifiyarsa


Yace momy gaskiya ya kamata ace kinyin wanni abun akan wanan Aure da Abba ya keson kaka bamin shi


Wai kamarni ace za.ayiwa Auren Dole
Kumama A rasa wace za a Auramin sai wacar kucakar


Nifa a duk family mu babu wacce natsana irinta


Kalonsa momy tayin tace bazaka gane irin bakin cikin da yake damu naba akan Wanan Dan iskar Aure da Akeson maka


Nayin inya yina a kan ganin Abbanka ya janye wannan maganar Ama Ina yakin saboda taurin Kai irin nasa waishi a dolle ga mai son kara kulla dankon zumuncisu!!


Nifa Ina tunanin baffa ka muhammadu asirin yayiwa Abbanka


Domin iban Asirin ba babu yarda za ayin ya nace yace Dole sai ya Auran maka wanan matsiyaciyar yarinyar


Kallon momy nasa yayi gamin da cije lebe cikin takaici


Yace Ai ko wlh sai baffa muhammadu yayi danasani cusa Yar,sa gareni
Saina nuna Masa cewa zaran ba kalan yadin bane Koda An dinka bazan taban yi kyau ba


Murmushi momy tayin hadin da sauke anjiyan zuciya tace My Son naci buri a kanka


Naci buri akan Aureka naso ace anyin bikin inrin Wanda ba taba yin irinshi ba a cikin wanna kasar Ama kash!!!


Sai gashi Muhammadu yazo Rana tsaka ya rusamin duk wani burina a kanka




Kalon momy nasa yayi yace kwantar da hankalinki momyna burinki bazai taba rushe waba


Zan Auro kalar matar da kike burin na Aura za ayin bikin irin Wanda kike buri za ayin watsi da Naira har sai kice ya Isa haka


Wanni dadine yaratsa zuciyar momy take tajin duk wani bacin dake ranta ya kau daga garenta


tace my Son a ranar zan kasance cikin

3 / 21