Author : Category : Home Of Novels
WACE CE UWA?
Hadarin daya taso shiya sanya yarinyar kara sauri. Tana hanzarin ta karasa gidansu kafin ruwa ya sauko. Yara ne 'yan makaranta, kuma daga dukkan alamu daga makarantar aka taso su. 'yan matan sanye suke da kayan makaranta na shudiyar Riga iya gwiwa da kuma wando har kasa, sai farin hijabin daya tsaya iya gwiwarsu. Mazan kuwa Riga ce da wando kala daya Dana 'yan matan sai kuma farar hula a kawunansu. Gungu gungu suke kowa da 'yan group dinsa. Daga gani 'yan makaranta ne tasowar su kenan daga islamiyyar dake kan babban titin unguwar. Wasu sun tsaya suna tattaunawa, wasu suna 'yan kokaye kokayen su na yara. Ita kuwa sai qara sauri take yi. Sauran yaran da suke tare da ita suka dan kwana mata kira ganin tayi musu nisa " sadiya saurin me kike yine"? Inji daya daga cikin su. Ta amsa " sauri nake kar ruwa ya jika min itacen dazan dora abincin dare". Dukkan su suka kwashe mata da dariya "Au ashe fa umma mai tuwo ce sai kikara sauri sai munzo cin dumame inji wata daga cikinsu". Murmushi kawai tayi musu domin ta dade da sabawa da wannan tsokanar tasu. Sai kuma akayi dace ta kasance yarinya mara fushi. Kusan duk abinda akayi mata da kyar ne fuskarta ta nuna bare har takai ga maida martani. Ita ko irin 'yan group dinnan bata dasu. Bata da wata shaqiqiyar kawa kamar yadda yara suke, saboda rashin samun damar hakan. Ta tsallako babban titin unguwar su wadda ke jere da manyan gidaje masu kyau da tsari, kamar ba a kasar nan ba. Gidajene na masu hannu da shuni. Kowanne sakaye yake cikin katuwar katanga sai kuma hanyar shigarsa masu dauke da tangama tangaman kofofi. Da yawansu harabarsu kewaye take da furanni da suka dada kawata gidajen wadanda Idan an bude gate din za'a hango su, yayinda wasu suka kere suka fito ta saman katangar gidajen. Sannan daga waje sukan sanya 'yar gajerar katanga Ko kuma waya su kewaye wata haraba da bata shiga cikin katangar gidan ba. Anan kallon yake domin nan aka fi kawata wa da furanni, da kuma bishiyoyi da suke karawa wajen sanyi da ni' ima. Idan mutum yana wucewa sai yaji wajen yana da sanyi na mussaman ga kuma kamshin shuke-shuke dake fitowa. Sau da yawa in har tazo wucewa takan ringa tafiya a hankali tana nazarinsu. Ita dai yadda suke a jere ga kaloli daban- daban wasu koraye wasu ruwan dorawa wasu jajaye wasu kuma farare yana buge ta. Amma yau bata tsaya kallon furannin yadda ta saba ba. Racing gaba da tafiya kanta a sunkuye tana sauri ta isa gida ko dan ta gujewa fadan innarta tasallah wacce ta kasance Yaya a wurin mahaifinta. Inna tasallah kamar yadda 'ya'yanta suke kiranta dashi itace uwar goyon sadiya. Ita ta budi ido ta gani a matsayin mahaifiyarta saboda kasance war mahaifiyarta ta asali Allah yayi mata rasuwa a lokacin haihuwarta. Ta tashi marainiyarda babu uwa babu uba saboda tsiran iyayenta shekaru biyar ne kacal shima babanta ya rasu a sanadiyyarhatsarin daya rutsa dashi Akan hanyarsata dawowa daga kamfanin da yake aiki a unguwar sharada. Bayan rasuwar mahaifiyarta mahaifinta mai suna isiyaku ya sake aure inda ya auri kanwar abokinsa mai suna ramatu. A dan zaman da sukayi da sadiya tayi mata riko na gaskiya, amma ita allah bai bata haihuwa ba harta allah ta kasance a kansa. Bayan rasuwar sa ta koma kauyensu inda ta sake aure kuma anan ne Allah ya azurtata da 'ya'ya maza da mata. Inna tasallah. Wadda sunanta na asali karimatu kuwa sun kasance su uku a wajen iyayensu. Itace Babba sai labaran sannan mahaifin sadiya isiyaku. Ya kasance autansu. Tana da fada bana wasa ba, saboda haka kowa a 'yan uwan shayinta yake yi.2............... Kawu labaran wanda yara suka fi kira da kawun maririmutum ne mai karamin karfi, amma fa mutum ne mai mutuqar San zumunci sai dai shima abubuwan sun sha masa kai. yana so ya taimaka. Amma nauyin gidan sama da qyar yake kaiwa. Yaransa duk qanana ne kuma wani na bin wani kamar bene. Dawainiyar su kadai Tasha kansa. Lokacin da mahaifin sadiya yana da rai shi yana taimaka masa. Hatta gonar da yake nomawa anan mariri isiyaku ne ya saya masa hadi da gidan da yake ciki. Kafin rasuwar isiyaku Allah ya rufa masa asiri inda ya mallaki katuwar gona a wajen hanyar titin farm center. Hatta gidan daya mutu a ciki mallakarsa ne da kuma wasu qananan kadarori. Ita kuwa inna tasallah yaranta guda biyar ne. Maza uku mata biyu. Yaya kulu duk itace babba mace ce mai tsananin yakana da wadatar zuci. Tana aure a unguwar kurna. Da yaranta dukkan su maza guda shida. Mijinta malam sunusi mai karamin karfine. Wannan yasa take sana'ointa na cikin gida don taimaka masa. Yaranta suna da da'a sosai kuma duk da rashin abin hannunsu bai hana su sanya yaransu a makaranta ba. Suna zuwa boko da safe da yamma islamiyya. Kamar yadda sadiya take yi, babban danta mai suna Ibrahim shine sa'an sadiya tsiran su kwana Talatin da biyu ne. Kusan lokaci daya sukai aure da kawunta isiyaku, kuma tasu tazo daya da matar sa wato mahaifiyar sadiya mai suna Maryam. Tana tausayawa sadiya da janta a jikinta kamar yadda uwa zata yiwa danta. Taso tadau riqon sadiya tasallah ta hana ta. Auwalu wanda akewa laqabi da baba saboda sunan kakansa ne na wajen uwa, shine yake bin yaya kulu. Wannan sunan shiya bashi dammar yin sangarta San ransa, dan ma babansa mai dan tsanani ne, da lamarin nasa ya zarce hankali. Da farko ya fara shiri rita ta zaman karta da makamantan su, mahaifinsa ya nuna bazai dauki wannan iya shegen ba. Ya taka masa birki ganin idonsa yasa ya rage wasu abubuwan. Mafi muni a lamarinsa baisan neman na kansa ba. Sai dai duk abinda mahaifiyar sa ta samu ya lallabata ya karbe. Ita kuma wannan bai taba damunta ba. Sai ya kasa.ce indai kana son kaga ta yaba da al'amarinka to kayiwa babanta alheri. Yafi ita kayi mata. Sani ke bin yaya baba. 'yan gida daya masu hali bambam. Yayin da auwalu yake mai tsaurin ido. Rashin kunya. Malalaci. Son kai. Da tsageranci. Sai Sani ya kasance mai kunya ladabi. Biyayya. Mai kawaici haziqi kuma jarumi. Tun yana dan yaro yasan yayi qwadago kodan ya dau wasu daga cikin larurorinsa. Hali sak na mahaifinsa ne sai dai shi yana da sanyin hali ba kamar mahaifinsa ba. Da indai kayi ba dai dai ba zai nuna maka kuskuren ka. Yana da hazaqa da basira, wadda ya bashi damar dai daita ajin karatunsa dana yayansa. Amma a karatun addini saida Sani yayi sauka yana da shekara goma sha hudu, auwalu mai shekara sha shida da qyar ya hada izifi biyar. Shigarsa jami'ar Ahmadu bello ta zariya yasa sadiya ta maida masa suna yayan zaria. Dija ita ke bin Sani. Itace mai kama har hali babu abinda ta bari na babarta tasallah. Halayenta tsaf ta dauke su. Banbancinsu daya ita inna tasallah Mijinta tsayayyene. Ita kuwa na Dija sai dai a slow inji yara. Bata da nisa dasu tana aure a gwammaja. Mijinta malam usman yana koyarwa ne a makarantar 'yan mata ta dala. Karatunta a makarantar shine sanadin haduwarsu,,har takai ga auratayya. Ba laifi suna zaune lafiya indai yayi mata abinda take so. Indai ya dan kuskure ne tofah sai a hankali. Sa'arta daya wajen 'yan uwanshi bata shiga harkar su. Amma karka ta bata domin Komai girmanka bazata saurara maka ba. Salisu shine autan inna ya girmi sadiya da shekara daya da 'yan watanni. Akwai tazara ta shekara shida tsakanisa da Dija. Saboda barin da inna tayi har sau biyu kafin a haifeshi. Bashida wata illa sai shagwaba da tayi masa katutu. Har yakai shekara bakwai bai daina kuka da shure shure ba irin na qananan yara ba. Dalilin da yasa yara basu cika son wasa dashi ba. Yayi rashin kunya ko tsokana ana taba shi ya cillo muku inna. Daidai gwargwado yana da dan qoqarinsa a makaranta. Gaba daya 'ya'yan inna tasallah kamarta sukayi fararen fulani masu kyawun fuska da jiki gami da tsayi da santsin gashi. Dogaye ne daga matan har mazan. Yaya kulu ce ma take dan dibi da fuskar mahaifinta. Amma ita jikinta irin na innan ne. Suka mahaifinsu malam kabiru ya rasu bada dadewa ba domin sadiya nada shekaru bakwai ya rasu. Tsayayyen mutum ne mai zuciyar neman nasa da son wadata iyalinsa. Kafin rasuwar sa babu abinda suka nema suka rasa. Kuma har bayan rasuwarsa 'yan uwan sa basu watsar da iyalinsa ba. Fadan tasallah nema yasa suka rage shiga harkar yaranta. Amma duk da haka basu daina kula dasu ta fannin abinci da sutura da kuma 'yan hidindimunsu ba. Dadin rufin asirin Allah gidan da suke ciki a unguwar Sani mainagge mai dauke da dakunan barci hudu biyu tare da runfa a ciki da kuma biyu a ware gefe guda. Sai kuma babban tsakar gida a tsakanin dakunan wanda shi ya raba gida kashi biyu. Ya kasance mallakarsu ne.3..........Dukkanin yaran gidan babu wanda bai girmi sadiya ba a shekaru amma ba a wahala ba. Tun tana shekaru tara take kwancala girki a gidan. Balle su shara da wanke wanke gami da wanki wannan duk nafila ne. Kasancewarta yarinya mai hanzari shiya dada assasa mata wahalhalun gidansu. Ga misali haihuwar Dija ita take zuwa kullum da safe gidan Mijinta tayi mata shara da wanke wanke hadi da wanki kayan jaririn sannan ta dawo gidansu ta dora da nata aikin gidan data saba. Saboda haka har maijego tayi arba'in sadiya ko makaranta bata samu taje ba. Dan ma Allah yai mata basira bata wasa ba. Ko yaya ta samu aka dora ta a karatu wala na islamiyya kona boko yanzun nan zai zauna mata daram. Da sallama ta iso soron gidansu tana sauri taje kar tayi laifi a wajen innarta. Ita dai ta kasa gane dalili amma sai taga kamar fadan innarta yafi yawa a kanta, ta kuma rasa Dalilin da yasa kullum ita ake yiwa fada duk da qoqarinta na son taga ta kiyaye faruwar haka. Ta karasa falon innarta ta shiga tare da sallama ta same ta ita da baquwa. Maqociyarsu ce nan bata da nisa dasu.mai suna tamasar. Mace ce mai harkoki iri iri, gata da shige shegen gidajen mutane. Domin ko alawar biki kake son a raba a unguwar baiwa tamasar yanzu zata zaga maka da ita. Haka nan inma mutuwa akayi kaji 'yan unguwa suna a wajen tamasar naji. Har gidajen babban layi ance tana zuwa. Takai musu talladega Kusan kowa a unguwar ya santa itama kuma tasan kowa.4..............Ta durqusa har qasa tare da gaisheta sannan ta juya wajen innarta tace "inna na dawo" kafin ta qara magana ta fadada Murmushi ta. Saboda hango yayanta wanda suka fi shiri dashi wato Sani. Da murnarta take fading "yayan zaria yaushe ka dawo? Shima da far'a ya amsa mata "ban dade da shigowa ba. Yaya makaranta? " "Lafiya qalau" ta amsa masa "inata murna ka dawo in fada maka mun ma shiga ajin 'yan sauka" zata cigaba da bayani innarta ta ta katse da cewa "ba kuma sai kiyi hanzari ki dora girki ba. Ai ba tsinkewa zakiyi da labari ba. In har baqo ya isa baqo ai abinci ake qoqarin tanadar masa." Ta miqe da hanzari tana fadin "yaya bari in gama in kawo maka books dina na makaranta ka gani" ya bita da Murmushi baice mata komai ba. Yarinyar tana burgeshi matuqa. Bai taba ganin yarinya mai qarancin shekaru amma da nutsuwa da kuma hakuri kamar sadiya ba. Duka duka yanzu ne ta shiga shekara ta goma sha daya amma kusan duk zuwan da zaiyi daga zaria inda yake karatu cikin hidima yake samunta. Shekararsa daya kenan a jami'ar Ahmadu bello dake zaria inda yake karantar shari'a wato law amma duk da haka kafin ya qara sadiya. A karatu dai dai na shekarunta yakan jima duk da 'yar fashin da takewa makaranta mussaman ta boko wadda saboda ayyukan dake tsareta a gida bata samun zuwa da wuri ko kuma zuwan ma ya gagareta gaba daya. Yayanta Sani ya kasance daya daga cikin malaman su na islamiyya kafin tafiyarsa A.B.U zaria domin hada digirinsa na farko. Tun yana dauke ido a makarantar islamiyya game da dukan makara da ake yi mata har ya kasa daurewa yayiwa malamai 'yan uwansa magana. Yayi qoqarin nuna musu bata da laifi amma bazai iya fada musu dalilin cewa mahaifiyarsa itace sanadi ba. Qorafinsa bai samu karbuwa ba, saboda da yawa daga cikinsu sai suke ganin kamar son kai kawai yake so yayi domin ita yar gidansu ce. Saboda haka hukunci ba sani ba sabo ya cigaba da haka kanta. Mafi yawan lokuta qwaqwalwarta ce take fansarta saboda bata cika bada itaba Yayin da duk aka tanbayeta hadda ko kuma bitar karatun na baya. Abokin yayanta sa'idu shine ya rangwanta mata yawan horon da take fuskanta ta hanyar fito da horon dalibi ya fanshi kansa da karatu maimakon duka da ake yawan yi musu. Wanda baya haifar da komai sai kangara yara da yake yi. A hankali sai wannan horo ya zama shine horon da makaranta take amfani dashi wajen horar da 'yan makara da kuma na fashi. Ai kuwa yara da suka gane hakan duk randa kayi fashi mafi sauqi a gareka ka nemi wanda kuke dasawa dashi ya biya maka karatun da aka wuce ka. Yayanta ne ya koyar da ita tilawar karatunta idan tana ayyukanta. Yakan ce da ita "hannu yayi aiki baki yayi karatu" A wajen Salisu autan inna take samu tana dora karatun data rasa a makaranta. Salisu ya girmeta da shekara daya amma tare yayan zaria ya sanya su a makaranta.5........ Da hanzari kamar yanda ta saba ta cire kayan makarantar dake jikinta tasa doguwar riga 'yar kanti ta fito daga uwar dakin inna zuwa rumfa inda ta sameta tare da baquwarta da kuma yayan nata. ta dan rusuna daga gefe cikin ladabi tace " inna me zan dora"? Innar ta juya ta kalli sani tace "tunda kaine baqo me kakeson ci. Nasan dai baka son cin tuwo da daddare. Duk dakin akasa dariya. Abinda inna bata fahimta ba sani ya lura da cewar duk ranar da sadiya tayi tuwo to da qyar take tsallake dukan inna, saboda zaiji ana fadin ta tuqashi yayi guda kokuma anaci yana wargajewa inna shinkafa ne. Bakin cikin haka ne yake sawa in aka bashi tuwon sai yace baya ci. A tunanin inna tuwon ne baya so. Bata saniba horon da ake yiwa kanwar sa ne yake fitar da tuwon daga ransa. "Ya amsa mata inna koma meye a dora mana". Sadiya Cike da doki tace "inna in dora taliya da busasshen kifi? Nason yaya da son taliya" kuma..... shigowar Awwalu tare da fito ne ya katse mata duk abinda tayi niyyar fada. Ita dai sadiya bata San meya saba jininta sam bai hadu dana yaya baba ba. Gashi dai ba abinda zai sakata batayi masa ba amma bata kaucewa zaginsa da hantararsa. Lokuta da yawa shine yake zama sanadin da inna take yi mata fada wani lokacin harda duka. Qarancin shekarunta ne suka hana ta gane inna bata iya son dan kowa sama da nata. Bata iya kyautatawa wani sama da 'ya'yanta. Sune wadanda ko laifi suka yi bata cika daurewa ta tsawatar musu ba. Ta kasa gane dalilin da Salisu zaiyi abin da yaga dama ya kwana lafiya. Ita kuwa koda kuskure ta gwada rabin-rabinsa jikinta zai gaya mata. Sadiya taso gwada abubuwan da Salisu yake yi kamar qin zuwa aike amma ita koda wasa tasan bazata wanye lafiya ba. A hankali ta gane ba so iri daya inna take mata da 'ya'yanta na cikinta ba. Tana qara wayo tana fahimtar yadda zata kaucewa dukan inna harta gane cewa yi nayi bari na bari ce mai fissheta. Da hanzarinta ta samu ta kammala daga dafadukan taliya 'yar hausa mai wadataccen busasshen kifi ga qamshin attaruhu da albasa yana tashi. Ta zuzzuba a kwanuka kamar yadda inna ta saba koya mata. Saboda indai ba baqi akayi ba ta koyi yadda zata raba abinci dai dai 'yan gidansu. Kafin kiran sallar magriba ta kammala. Ta kuma kaiwa kowa nasa. Bayan ta idar da sallah taci nata abincin sannan ta tattare dakin girkin ta kuma tattara kayan wanke-wanke wanda take yi cikin dare domin ta ragewa kanta aiki karta makara zuwa makarantar boko da safe. Zuwanta hutu gidan yaya kulu ta nuna mata dabaru na yin ayyukan gida a tsare da qoqarin rage aiki a duk sadda ta samu sarari. Fara yin hakan ta gane anfaninsa domin ya rage mata zuwan makara makaranta mussaman ta boko. Inna da 'yan mazanta guda biyu suna zaune suma abincin suke ci. Kowa yayi shiru sai loma suke zubawa. Shiru mugun santi inji 'yan magana. Can baquwar inna wato Tamasar ita ta fara magana tace "yanzu tasallah wannan 'yar taki iya tayi wannan girkin"? "Qwarai kuwa ita tayi shi"Inna ta amsa mata. Ta kuma cigaba da cewa "ai ba abinda bata iya ba kin sanni bana son sangarta yara. Nafi son yaro mai kazar kazar." Wannan kalami na inna son ransa kawai ta fada domin kuwa yaya baba ko mai jego bata kaishi zaman daki ba. Har a bada a daki zaka same shi. Baya zuwa ko'ina tun da ya samu ya qare makarantar sakandire bai ci gaba ba. Tare suka gama da yayan zaria amma shi takardun basuyi kyau ba. Inna tace malaman ne basa son sa sun tsane shi. Wannan abinci da tamasar taci shine ya janyo sanadin da tabawa inna shawara akan sadiya tunda ta yaba da yanda take gudanar da ayyukanta Like · Reply · Edit · 2 hours ago Fatima Binta .......****6****........ Tunda ta yaba da yadda take gudanar da ayyukanta. Take ta sanar da ita cewa wata mata da suka tare a babban layi ta bata cigiyar ta nemo mata yarinya qarama da zata taimaka mata da ayyukan gida da kuma renon yara. Inna taso taqi amma tamasar ta kwadaita mata kudin da za'a