Author : Category : Home Of Novels
damar kara magana ba ta dora mata gidan sarkar akan cinyarta ta mike ta fice daga dakin. A sanyaye sani ya bita da kallo har saida ta fice daga dakin. Ga kyau ga nutsuwa wanda aka dada kawatawa da kyawun hali mai nagarta. Mai kuma namiji yake bukata a zaman aure. Gyaran muryar yayan ne ya dawo dashi daga duniyar yabon matar da Allah ya mallaka masa badon halinsa ba sai don shi mai kyauta n izuwa bayinsa koda kuwa basu cancanci wannan kyautar daga gare shi ba. Yadda yayan ta kama shi yana kallon sadiya sai kuma kunya ta kama shi. Ya sunkuyar da kansa yana murmushin jin kunya. Ita kuwa tai kamar ma bata lura da halin shaukin daya shiga ba. Amma fa da za'a tona zuciyarta murna ce fal a ciki. Bayan fitarta ne sani yake gaya wa yaya yanda aka yi ya samu kudin da yayi hidimar aurensa wato wanda sadiya ta bashi. "To ka daiga irin hallacin da yarinyar nan tai maka. Ka rike ta amana." "Kinsan Allah yaya gwanda fa da haka ta kasance. Ni inaga kamar hakan ma yafi." tare duk suka sa dariya.
=====***24***===== Daga gidansu yaya kasuwa ta wuce ta sayar da sarka. Donma karta dawo gida inna ta canja mata ra'ayi. Daga sabon gari ta dawo goron dutse ta sai musu saitin gado harda sif da divider na zamani. Ga saitin kujeru mai guda dai-dai guda hudu da kuma doguwa guda daya. Hade da teburin tsakiyar falo. Sarka tai albarka. Ba sai ga yaya ta hado harda labule da zannuwan gado masu kyau ba. Dan canjin da yayi saura dashi ta sai musu kayan masarufi. Ta isa gidan da kaya cikin akori kura. Tayi sa'a inna bata yi mata fada ba. Saboda ko banza zata so a gyara wa danta muhalli. Kuma sadiya ta fitar dasu zargin mutane da zasu ce ba'ayi mata kayan daki ba 'yar gudun mawar da ta tara ta kara bawa yayan tace "gashi koma bakin asibiti ki samo mata kayan jere " sai kuwa gata ta dawo da mai Ross guda shida da saitin samiru masu biyar guda goma. Gidan amarya yayi shar dashi. Inna sai washe baki tana gaya wa 'yan jere donma ba'a shiri akayi ba da sai yafi haka. Sani da sadiya ansha amarci. Ya samu sadiya fiye da duk yanda yake zaton zai sameta. Duk wani dadin dake cikin aure saida sadiya ta samar masa da mafiyinsa. Ladabi. Biyayya. Tsafta. Ga girki. Abin sai wanda ya gani. Dan kayan abincin da Kawu labaran ya hada musu a matsayin kayan gara sun taimaka musu kwarai da gaske. Ga kuma gwana wajen iya girki da aka samu. Wata ziyara da Abokanan sani suka kai musu har suka tsaya suka ci abincin dare a gidan. Wani daga cikin su fadi yake "kai da da wannan a gidan ku sakarci ya kaika neman aure a waje"? "Kyale shi mana inji wani cikin abokan nasa. Da yayi sanya sa ba Karamar asara zaiyi ba" Sani ya cigaba da zuwa makarantar sa zaria. Amma shaukin San zama da sadiya ya sanya shi safa da marwa tsakanin zaria da kano. Wani lokacin da yamma zai shigo ya koma da sassafe. Ko inna baya bari tasan da irin wannan zuwan nashi tunda tana korafin zuwa sati bibbiyun da yakeyi. Allah mai taimakon bawa a duk sanda yaso. Nauyin iyali daya hau kan sani sai kuma ya zamar masa sanadin samun wani rufin asiri. Wani mai sukani ne yake kokarin kammala digirinsa na biyu a kulliyar su sani. Ya bawa da yayi da kokarin sani mussaman fannin Arabic sai ya dauke shi aiki yana masa fassarar binciken da yayi na karatun da zai rubuta project din sa akai. Sani yayi anfani da wannan damar shima ya rinka rubuta nasa project din a lokaci guda da yakan taya wannan dalibin. Dan abinda yake bashi da kuma tallafin da gwamnati take bawa dalibai dasu yake biyan bukatun iyalinsa. Har ya samu ya kammala karatunsa. Auren sa nada wata biyar a wani hutu da yazo wa sadiya wanda daga shi inya koma to ya gama hada digirinsa. Yaga ya dace ya fara maganar karatunta so yake ya bata surprise tunda ya lura tana son tayi maganar karatun amma tana kawaici. Da kansa ya samo mata komawa makarantar su Amir inda ta rubuta jarrabawa. Aka bashi list din littatafai da kudaden da zai kashe na kudin makaranta da kuma kayan sawa na makaranta. Duk yayi kundunbala ya biya mata da dan abinda ke aljihunsa. Yasan dai ikon Allah ne
zai kaisu karshen wata
=====***25***===== Kafin ya karbi dan albashinsa sai kuma tallafin local government da akayi musu alkawarin basu a cikin wannan satin. Da kayan makarantar sadiya duka ya nufi gidan su domin ya sanar da inna. Bayan sun gaisa take masa mitar wahalar zuwa da yake akai akai ya fada mata ai hutu suke yi. Tayi dai mitar ta gama. Da kansa ya fara yi mata bayanin makarantar da zai maida matarsa. Ai kuwa ina wuta inna ta saka shi. Ta zage shi Tas tace bazata dauki yahudanci ba in aure sadiya zatayi tayi. In kuma karatu karatu. Har tana fadin ga dan uwanka nan uwa daya uba daya shi baka kaishi makarantar kudi ba sai matarka ko. Watau aure yafi dan uwa. To kuwa makwafinta zai hau shi zai shiga wannan makaranta" Gaba daya zufa ta karyo masa baya tuna komai sai alkawarin sa da sadiya ranar sayen bakinta. Haka nan jikinsa ba kwari ya tashi ya karasa gidansa. A falo ya ajiye kaya ya shiga bandaki ko ya rage zafin da inna ta hado masa. Sallamar sa ce ta fito da sadiya daga dakin. Bata ga mutum ba sai kaya a falon. Jin karar ruwa ya tabbatar mata da yana cikin bandaki. Ta fara bubbude kaya ai kuwa tana arba da kayan makaranta. Bata san sanda murna ta kwace mata ta saki shewa ba. Ya fito daga bandaki yana kokarin goge jikinsa. Ta saki kayan ta rike hannuwansa tana fadin nagode nagode Allah ya kara budi. Shi dai ya kasa yi mata magana. Ta daga wannan ta ajiye ta bude jakar littatafai ta futo dasu tana dubawa. Habawa da dadi ya kamata duk da kunya irin tata sai gata ta zubar da komai ta kaiwa sani wata irin runguma. Badan yana da karfi ba to da kuwa saita kada su gaba daya. Kuruciya ce ko kuma tsananin murna ce ta kasa gane halin da yayanta yake ciki. Ita dai sai nanata godiya take yi. Tana godiyar hawaye da kuma dariya duk gaba daya. Washe gari da sassafe ta kammala komai na gidan hatta abincin karyawa ta kammala tsaf. Kafin bakwai na safe kayan makaranta sun hau jikin sabuwar daliba. Ya kalleta tayi mutukar kyau sai ta dada koma masa wata 'yar yarinya ya tuna ko a jiya daddare saida ya kara kokarin rokon inna akan ta barshi ya maidata makaranta. Amma taki da ya isheta da mariya sai tasa masa kuka tana fadin iya zaman ta dashi bai taba yi mata musu ba amma yau akan sadiya yana neman ya bijirewa umarninta. A haka ya bata hakuri ya fito daga gidan. To yanzu kuma ga sadiya yarinyar da yake jinta a ransa kamar yayi mata numfashi. Irin son da yake mata badan tana da hankali ba. Babu abinda bazatai masa ba. Ya daure ya dauke fuskarsa daga kallonta "yaya na shirya muje ka karya kar kasa na makara" hannunsa ya miko yana daga kwance ta kama ta dauka taya shi zatayi ya mike daga kwanciyar. Sai ji tayi ya jawota jikinsa ta fada gadon. "Dan Allah yaya ka bari karka sa mu makara daure ka tashi ka shirya " zaton ta irin wasan daya saba yi mata ne. Don wani lokacin hakan yake mata. Ya juyo da fuskarsa idonsa a cikin nata yai mata kallon ido cikin ido ya daure yace "ni waye gare ki?" ta amsa "yayana" "Bayan haka fa? Mijina ta amsa masa. "Wace dama Allah ya bani a kanki? Shiru bata amsa ba. Nasan kinsan ina da damar baki izini ko in hana mutukar bai kaucewa addini ba. Dan Allah ka daina irin wadan nan maganganun ta fada muryarta na rawa. Dake nuna alamun karaya da maganganun sa. Tausayinta ya kama shi amma yasan dole ne ya zartar da hukuncin da bashida ra'ayi domin cika umarnin mahaifiyarsa. Ya daure ya dai daita muryarsa ya kuma kara daure fuska. Wanda Gaskiyar magana karfin hali kawai yake yi. Amma a zuciyarsa kamar shima ya fashe da kuka. Yace "indai na isa na fada ki ji to maganar karatu na soke ta. " Ai wallahi baka isa ba tab! Ina bama zan taba yarda ba" sadiya ta fada cikin wata murya mai nuna zafin rai da bai taba jin tayi magana da ita ba. "Nidai iyakar maganata kenan. Guda daya ce bata kai biyu ba. Ko kibi ko ki kauce wannan ya rage naki. Idan naki bi sai me" itama ta fada a gadarance. "Gwada wa zakiyi sai kiga abinda zai faru. Shima ya fada da dan zafin rai. A zuciyar sa kuwa fadi yake Allah taimaka min in samu in kubuta daga fushin mahaifiyata.
H Inna ======***26***====== Bata tsaya taji abin da zai kara fada ba ta figi hijabin ta a saman kofa ta zura ta fice daga gidan. LAHAULAWALA WALA KUWWATA ILLA BILLAH. Ita kadai sani yake furtawa. Tashi yayi ya dauro alwala ya fara jera nafila yana mai neman dauki a wajen ubangiji. Sadiya data fita daga gida bata san inda zata nufa ba tafiya kawai take bata ganin hanya. Jefa kafarta kawai take bata san inda take wurgata ba. Idanuwanta sai zafi suke ta kasa zubda hawaye. Ga wani kullutu da yazo ya tokare mata kirjinta. Bata ko ganin gabanta. Karo data ci da dutse shiya sata dakatawa. Tana daga ido taga inda take kawai sai taji kuka ya balle mata. Ta zauna kan abinda taci karo dashi. Ta kuma kudundune kanta cikin hijabin ta tana wani irin gunjin kuka. Tun bayan fitarta sani ya dan jira ko zata dawo. Yaji shiru. Yaje makarantar da yai niyyar kai sadiya bata je ba. A wayence ya shiga gidan su ko can ta nufa babu ita. Ya fito ya shiga hayis ya nufi gidan yaya kulu amma itama bayan sun gaisa yaji tana tambayarsa sadiya ya tabbatar ba nan ta tafi ba. Daga nan ya nufi mariri gidan gidan kawu shima ya wayence da zummar yazo gaishe shi. Babu sadiya a gidan. Tabbatar hakan ma sai kayan kadi irin su kuka gwaggo lami matar kawun ta bashi wai ya kaiwa sadiya. Tofa tashin hankali ba'a sa maka rana. Yanzu kam hankalinsa ya jirkita domin bai san inda zai je nemanta ba. Haka gwiwa a salube ya juyo ya nufo gidansa. Tunda safe ya fita gashi har ana kokarin kiran sallar azahar. Kafin a karasa kwanar lungunsu inda zai sauka. Wanda kuma nan ne gidan dasu momi mariya suka zauna ya hango kamar kalar hijabinta. Da hanzari ya tsaida bus din ya sauka. Da gudu ya karasa wajen don ya tabbatar da waye ke zaune akan kwalbatin. Yana isa kusa da wurin ya tabbatar da sadiya ce je zaune akan kwalbatin gidan da su momi suka tashi. Gefenta ya zauna ya kira sunanta a hankali "daure ki tashi muje gida" jin muryarsa ya dada sata ta saki wani gunjin kukan. YA SALAM -YA SALAM" yake ta nanata wa. Har yaji kukan sadiya ya fara komawa shessheka. "Kiyi hakuri mu koma gida koma meye sai mu tattauna a can" " ba inda zani macuci mayaudari azzalumi mai saba alkawari" "Duk naji na yadda duk nine wannan din da kika lissafo. Amma nasan inada sauran sunaye a wajenki. Daure muje gida sai ki karasa lissafo min su. Shiru taki kula shi. Ya dade da sanin ita ba mutum ce mai yawan magana ba. Balle har ta fada maka bakar magana. To yau ma data fada yasan ta kure malejin zaginta kenan da kuma bakar magana. Da kyar da ban baki ya jata kamar rakumi da akala har suka isa gidansu. Da kansa ya cire mata kayan jikinta ita kam bata da kuzari ko kadan. Jin zafin da jikinta yayi ya tabbatar masa da cewar ta dade a zaune a kan kwalbatin nan. Tausayinta ya dada rufe shi. Inama da yadda zaiyi yayi mata abinda take so. Da yayi. Amma dukkansu basu da abin yi sai hakuri saboda bukatarta tafi karfinsu dukka su biyun.======***27***====== Da kansa yayi mata wanka sannan ya umarceta data daura alwala. Ita dai binsa kawai take yi amma har yanzu hawaye basu daina zuba daga idanunta ba. Tsayuwarta akan sallayarta ne ya taimaka wajen dawo da nutsuwar ta. Sani bai samu shiga massalaci ba saboda sanda yayi alwala an idar da sallah a massalacin da yake zuwa. Shiya ja musu sallar azahar da kuma nafila. Ba tare da yayi magana ba ya mikawa sadiya Qur'ani shima ya dauki daya fara karatunsa bada jimawa ba itama ta bishi suka yi tayi saida sukayi la'asar sannan yayi musu addu'a suka shafa. Izuwa wannan lokaci sadiya zuciyarta ta rage zafi. Shaidan dai kam sunyi kokarin sallamarsa daga gidansu yinin ranar ko ruwa baiga bakinsu ba. Saida magriba ne ya tilasta ta tasha tea da biredi yanka biyu. Ganin ta karbi shayin ya sanya da bayan isha'i ya balla maganin barci ya saka mata a shayi ya sake tilasta mata tasha. Ta samu barci wanda ya ragewa sani damuwa amma fa washe gari sai ta koma kurman karfi da yaji inma magana ta dace ta bashi amsa eh ce ko a'a. Sani ya daure amma fa shima kusan abinda takeji. A ranta to shi kam ya fita jinsa. Ganin bata ci komai bane ya sashi tambayarta. Ta amsa masa da ta tashi da azumin kaffarar rantsuwar da tayi. Ya sunkuyar da kansa kawai ya danyi jim sannan yace "zo ki zauna ki karya Allah baya kamaka da rantsuwa ko alkawarin da ka kasa cika wa. Sai dai wanda kaki cikawa da gan gan. Inma kaffarar ce to ni ki bari ta koma kaina. Ina kallonki fa tun jiya banda ruwan shayi babu komai a cikin ki. Kuma ki azumin zaki dauka ai kya tambayi izinina. Tunda dai na nafila ne " A cikin kun kuni tayi magana "ai dama mulki aka iya akan mace amma baza'a fita hakkinta ba" "Me kike cewa ne nafi son duk maganar da take ranki ki fade ta sak. Amma kinsani tun muna gida bana son yaro yai min magana a ciki. Ya dada daure fuskarsa danma kar magana ta dada tsayi ya sake ballowa kansa ruwan tiga dam. Ya kuma san bashida abinda zai tare shi dashi. Saboda haka ya kyale maganar kar ta kara tsayi. Bai gama da wannan matsalar ba saiga Salisu inna ta turo shi wai ya karbi kayan makaranta da kuma littatafai inji inna. Ba tare da yayi magana ba ya nuna masa inda jakar da kuma books din da ya sayo wa sadiya suke. "Yaya uniform din fa da kuma resit din biyan kudin makarantar. "Shima ba tare da yayi magana ba yasa hannu a aljihu ya dauko ya mika masa. "Yaya uniform din fa ". Adan kufule yayi magana muje makarantar gani nan zuwa. Sadiya taso ta fahimci abinda ke faruwa amma shekarunta suka hanata ganeta cewa mijinta umarni kawai yake bi. Shima zuciyarta data raya mata bambanci kawai yake nunawa tsakaninta da Salisu. Tunda da ai komai tare yake yi musu amma yanzu ya nuna mata wariyar launin fata. Suna cikin wannan zama na doya da manja sai kuma wata sabuwa ta bullo. Zazzabi ne mai zafi ya rufe ta. Kwana daya biyu har zuwa uku jiki yaki dadi haka ya tilasta ta suka tafi asibiti. Suna zuwa ciki ya tabbata a jikin sadiya na wata uku. Sani yayi mutukar farin ciki da rarrashi da wayo irin na wanda ya girme ka ya samu sadiya ta hakura da rigimar su. Suka dukufa rainon cikin da Allah ya basu.***28***===== Bayan dawowar sa daga karatu. Makarantar su Amir suka dauke shi aiki. Kafin jarrabawar su ta fito ya tafi bautar kasa. Dan wannan albashin da yake samu ya fara tattalin haihuwar matar sa. Cikin na cika wata tara ta haifo yaranta maza guda biyu. Kamar su daya da babansu aka sanya musu sunan baban sa da baban ta. Wato kabiru da isiyaku. Aka yi musu lakabi da walid da imam. Kusan lokaci daya suka haihu da huwaila matar yaya baba inda ita kuma ta samu zakiyya. Ita dai an hada mata kayan barka an kai mata. Ita kuwa sadiya ta samu sabulun salo da turmin atamfa da 'yan rigunan jarirai guda biyu. Dan inna duk karfinta a matar auwalu ya tafi. Da sunan wai ita bare ce dole a fita kunya. Ita kuwa sadiya ta gida ce ba sai anyi wahala ba tunda duk abin daya ne. Sani shi kadai yayi hidimar matar sa da yaransa. Saiko yaya data taimaka masa. Ita ta taimaka mata kwarai da zaman jego tunda ita ba inda zata wankan gida. Bayan suna kuwa da yaya ta koma shi ya cigaba da kula da ita har tayi arba'in. Su walid nada wata uku sunyi kyau gwanin ban sha'awa dasu. Ga kuma uwar goyon mai tsafta da kuma kula yadda ya kamata. Kullum cikin tsafta zaka gansu. Kiran yayanta ne yasa ta ajiye tsintsiyar da take shara da ita ta nufi daki wajen sa. Har ta shiga baisan ta shiga ba. Saida tayi tafi a kansa. Sannan ya dago a firgice ya kalleta. Fuskarsa ta nuna alamun damuwa Kwana uku kenan tana lura dashi kamar yana boye mata wani abu. Ta kuma so taji abinda yake damunsa a dan kwanakin nan amma ya nuna mata ba komai. Ita dai addu'a ta dinga yi a kwanakin koma menene Allah ya kawo musu shi da sauki. "Yaya gani" ta tsuguna gabansa. Ya daga kansa ya kalleta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Yace "jeki kawai" jikinta a sanyaye ta mike ta fice daga dakin. Ta lura haka yake yawan yi mata