Author : Category : Home Of Novels
sani da dumbin mamaki a fuskarsa. Ko dai ba gidan yazo bane. Mistake yayi bai gane ba. Nida nazo neman mai aiki ana min zancen yaran gida. Kai bari in bar wajen nan inajin ban gane kwatancen da tamasar tai min ba. Yana shirin juyawa ya bar wajen ya hango baba maigadi da saurinsa yana dawowa. Kamar ya gudu sai kuma yaji tsoro kar ya jawa kansa mummunan zato ya dai daure ya tsaya. Mamaki ya sake kamashi da yaji baba maigadi yana fadin ance ka shiga daga ciki.======***11***====== Da jan qafa ya bishi suka shiga harabar gidan. Amma fa a tsorace yake. Wani hadadden falo babba ya shiga dashi. Da sallama ya shiga ya tarar da dadi zaune yana karatu. Shiya fara miqa masa hannu sukayi musabaha. Duk da sani yaso ya noqe. Bayan sun gaisa dadin da kansa ya shiga ya kirawo momi. Fitar sa ce ta bawa sani dammar qarewa falon kallo. Hotunan su daya gani shiya tabbatar masa da cewa shine maigidan. Yana zaune daga qasa duk da tayin kujera da dadin yayi masa. Yaji sallamar momi. Mace mai cikar kamala ta shigo. Bayan sun gaisa. Suka shiga yi masa tambayoyi har suka gano shine yayanta na zaria. Suna nan zaune suna 'yar hira sama-sama mafi yawa akan karatun sani ne. Har suka jiyo hayaniyar yaran alamar sun tashi karatu. Sadiya hanyar kicin ta nufa don ta fara shirin abincin dare. Amma sai ga Amira da gudu tana cewa momi is calling you" sadiya ta amsa I am coming " haka su momi suka hore su da su riqa yi a tsakanin su. Su yawaita yin magana da turanci don ya zauna musu a baki. Hatta ita sadiyan da batai wata hudu dasu ba. Bakinta ya fara murjewa. Haka zalika ita kuma da yake suna muhaddasa a islamiyyar su sai take qoqarin su riqa wasu maganganun da larabci. Inda suka kakare sai ustaz ya gyara musu. Tare suka shigo falon inda take zaton ko wani aiki momi zata sakata. Bata kula da baqon dake zaune kusa da qofa ba. Wanda mamaki da kuma farin ciki suka cika fuskarsa saboda ganin kyakkyawan yanayin da take ciki. Da ganinta kasan bata tare da takura. Ta durqusa gaban momi tace dadi Sannu da hutawa". Ya amsa mata sannan ta juya tace " momi gani" Momi tace "baqo kikayi" mamaki ya kamata tunda tasan tunda tazo gidan aiki ba wanda ya taba zuwa dubata kamar bata da kowa. Ta kuma san inna ce zata hana kowa zuwa. Ta dubi inda momi ta nuna mata. Ai kuwa tana area dashi. Bata San sanda hawaye ya fara zuba a fuskarta ga kuma dariyar farin ciki duk a lokaci daya. Amir yace "yeh tana kuka tana dariya" duk suka tuntsire da dariya. Bayan sun fice daga falon sani ya zuba mata ido. Yana mai jin dadin yanayin daya sameta a ciki. Ga dukkan alamu bata tare da wahala a gidan. Ta murje ta qara kyau. Kyawun ta ya dada fitowa. "Share hawayen mu gaisa sarkin kuka. Ai na dauka kin daina saurin kuka ashe har yanzu kina yi. Ta share hawayen da habar zaninta. Sannan ta gaida shi. A 'yar hirar da suka yine sani ya fahimci alherin daya sami sadiya na samun damar cigaba da karatu. Yayi murna mutuqa. Suna zaune Amir yai sallama dauke da tire mai dauke da lemo da kuma 'yan kayan tande tande ya ajiye yana fadin " momi says not to worry about dinner, she will take care of it". Gyada kanta ne ya bashi damar gane amsarta. Ya juya ya kalleta " har turanci kike ji haka?" tayi Murmushi kawai. Kafin ya tafi har littatafanta na boko da islamiyya saida ya duba. Kiran sallar magriba yasa yai sallama. Ya dauko'yan kudi daga aljihunsa ta bata. Taso taqi karba ganin gidan ba abinda suke saya komai sai dai su ganshi basu San fa akayi aka siyo ba. Amma sani ya dage sai da ta karba. Dadi ne ya fito ya jashi suka tafi massalaci tare dashi da Amir. Ya kuma matsa masa saida yaci abincin dare dasu. Da zai tafi kuma ya bashi kyautar shadda yadi goma da kuma kudi masu yawan gaske.***12***======= Karamcin dasu dadi suka yiwa sani da kuma kyakkyawan yanayin da yaga sadiya a ciki su suka kwantar masa da hankali, ya tabbatar da yardar ubangiji ta samu iyayen daki nagari masu kula da 'ya'ysn wasu tamkar nasu. Samun hutun 'yan makaranta da kuma rufe jami'a domin yin hutun sallah, ya sanya su momi shiryawa don ziyartar garinsu wato bichi. Kafin tafiyar su sai da Momi ta tabbatar kayan sallar sadiya guda hudu sunzo wajen mai shi. Lokacin data miqa mata kayan ba qaramar murna tayi ba. Ta daddagasu tana dubawa. Leshi marar nauyi guda daya. Atamfa sai kuma shadda. Da riga da siket 'yan kanti. Qarin dadi harda mayafai guda biyu kalar leshin da kuma shaddar. Sannan atamfar tata zannuwa biyu manya da riga dinki mai kyau. Dai dai da jikinta. Sai takalmi scholl da kuma wani mai qyalli da kuma dunduniya kamar ta gilas, suma dai dai ita. Tayi murna mutuqa, momi na gode Allah ya saka da alheri". Amin dai inji momi. Tace kinji abinda na gaya miki sati biyu zamuyi. Da mun dawo zan turo su Amir su gaya miki" ta kawo albashinta ta bata. Sannan ta sake debo wasu kudin daban ta miqa mata "ungo ki riqe wannan a hannunki ko zaki buqaci wani abu. Ga kuma kayan abincin can da sauran provision na hada miki". Tayi ta godiya. Momi tace "Karki damu ganinki nake kamar su Amir. Ki kuma kula da holiday assignment din da uncle ya baku. Kije kiyi sallama da Dadi direba ya ajiyeki. Yazo mu kama hanya kar muyi dare". Da tarin alherin da iyayen dakinta suka bata ta isa soron gidansu. Anan suka hade da yayan zaria shima yazo hutu. " ga 'yar gidan momi ya fada da murnar sa" itama da murnar ganinsa ta gaishe shi. Ya tayata suka shiga da kayanta dakin inna. Maganar suce ta fito da yaya baba daga dakinsa na wajen tsakar gidan. Yana fadin uban me kikazo yi nan gidan da sassafe. Ai daman nasan sai kinyi abinda za'a sallamoki daga gidan arziqin nan. 'yar baqin ciki wadda bata San 'yan uwanta da alheri. Babu shiri hawaye ya fara zuba daga idanuwanta. Inna ma tana ganinta fada ta fara yi. "Me ya kawoki gida da sassafe haka. Duk abinda na gaya miki ba kiji ba gani kike kamar bazan iya aiwatar da abinda nace zan aiwatar a kanki ba idan kika baro gidan nan ko?" ta dauko mafici ta wurgeta dashi. "Dena kallona da idanu kamar na mayya" cikin muryar kuka ta amsa Inna ba koroni suka yi ba. "Me kikazo yi gida da sassafe Inba tsiya kika tsula musu ba?" ta share hawayen da suke zubo mata "inna tafiya sukayi ganin gida shine nima sukace inzo gida in huta'. "Ai towoo. Kuma ba sai kiyi magana ba tun dazu" takai dubanta tarin kayan da suke zube a rumfar. "Wadan nan kuma fa mu gani" ta fara bubbudewa. Yaya baba yana tayata. Kayan abinci ne dangin su macaroni da taliya da kuma shinkafa takai rabin buhu. Sai kuma babban kwali mai dauke da kayan shayi da kuma su sabulun wanka dana wanki. Akwatin ma da aka bude kayan sawarta wanda momi ta dinka mata a zamanta a gidan. Da kuma kayan sallar ta. Shida sani yana tsaye yana kallon ikon Allah bai sa musu baki ba balle hannu a abinda suke yi. Da kanta ta kunto hannun zaninta ta miqa mata kudi. Inna da yaya baba har rige rigen karba suke yi. Inna dai tayi nasarar karbar kudin. Ta qirga taga sun haura albashin sadiya. Da sadiya taga ba magana zatayi ba. Balle ta tambayeta bayani akan kudin da taga sun haura sai tayi hanzari tace mata "inna kuma ta qara min wadannana da kika gani a daban. Tace in dinga kashe wa kafin su dawo. Kafin ta amsa mata yaya baba ya cafe da cewar "shi kenan inna sai ki bani in karbi dinkina ki kuma bani kudin hular danace miki ina son saya." "Kaifa dadina dakai kenan. Ka bari mana idan na zuba dashin muga abinda yai saura. Kuma kaga Dija ma kasan mijin nata an dakatar dashi aiki. Saboda haka sai na tsakurar mata. "Amma dai inna ni ina ruwana da wata Dija. Mijinta aikin me yakeyi daba zai kula da gidan sa ba" inna ta amsa baka ganin halin da suke cikine kai me yasa kake abu kamar ba kaine babba ba"? "Hular nan dai kinsan duk samari ita zasuyi yayi. Kuma ni sai ace bani da ita. Kuma baga kayan sallar wannan yarinyar ba. A bata mana ta qara girman su. Kuma ga shinkafa da kayan abinci ba sai ki bata ba. Kawai dai inna ni in bazaki baniba ki fada min. Kuma wallahi idan ba'a bani ba kowa sai ya sani a gidan nan. Yayi qwafa. "Kai dadina dakai rashin hakuri " ta qirgo kudin ta miqa masa. "Gashi inceko shikenan " yasa hannu cikin kwalin yadau sabulai da kuma wani turaren sadiya da Momi take siya mata. Ita ta saba mata amfani dashi. Har ya kasance ko yaushe sukaje sayen kayan amfanin gida sai an sai mata. Harda su man gashi da sauran kayan kwalliya.=======***13***======== Sani ya sunkuyar da kansa kamar yai kuka don takaicin wannan son kai da ake a gidansu. Wani da shan duka wani da karbe kaya. Inna na cikin ware kaya saiga Dija tayi sallama. Suka shigo ita da danta Al amin wanda baifi shekara daya ba. Firgai-firgai dasu daga gani ko wanka basuyi ba suka fito. "Ke kuma daga ina haka da sassafe" Tashi mukayi gidan ba abinda zamu karya shine yace in taho gida. Shima ya tafi gidansu" Idonta akan kwalin da sadiya tazo dashi. Tana bude wa taci karo da qaton gwangwanin Nido irin gugan nan. " kai-kai-kai Inna wannan gara fa daga ina? Sadiya na qoqarin ta gaisheta ta kasa amsawa saboda zalama. Inna tayi mata bayani duk kayan da sadiya tazo dasu. Nan dai ta samu rabon leshin da shaddar sadiyan na sallah. Duk sunyi mata kadan haka ta turmutsa su a jikinta tana fadin akwai alawus. Na bayar a buda min. Itama inna Dija tasa ta dauki atamfar tana fadin ai zani biyu ne sai kikai a gyara miki rigar da dayan zanin. Haka dai suka rabe kayan suna fadin ai nata da aka dinka mata a gidan momi ba abinda suka yi. Saboda haka ta iya sakasu a sallah. Shigarsu daki ya bawa sadiya damar dauke turare guda biyu a qarqashin a kwatin da basu kula da suba da kuma wani man gashi. Da kuma wani silifas mai kyau data siyo shi a dalilin wani Abokin Dadi yazo ya basu kudi aka raba harda ita. Qawar momi ta kawo tallan takalma ta nunawa momi tana sha'awar ta saiwa yayanta. Tayi wuf tashige daya dakin ba tare da sun ganta ba. Ta sake dawowa babu kowa a dakin ta sake daukar sinqin sabulun joy tashige dashi dakin ta hada ta boye. Bayan an idar da sallar tarawi ta iske yayan zaria a dakinsa ta bashi takalmin da kuma turare guda daya. Yayi murna mutuqa ya kuma sa mata albarka. Ranar sallah sadiya bata samu kanta ba sai bayan la'asar lis. Saboda duk aikin abincin sallah ita tayi shi. Hatta da Dija a gidan aka data mata abincin da zatayi rabo dashi. Aka dorawa almajirai suka kai mata shi a kwalla. Mijinta ko banza yana jin dadin wannan bajinta. Ballantana a yanzu da bashida shi. Sai yake ganin sauqi ne ya samu. Baya hangen rainin dake dada shiga tsakaninsa da matarsa. Ta hada musu lemon citta wanda ta koya a wajen momi. Washe garin sallah tai kwalliyarta da riga da siket din yan kanti. Ita da yayanta suka nufi gidan yaya kulu. Takai mata tsarabar turare man kitso da kuma sabulu. Taji dadin ganinsu mussaman yanayin data ga sadiya a ciki. Anan ne sani yake mata qorafin abinda su inna sukayi da kayan sadiya. Ita kuwa tai saurin dakatar dasu tare da cewa "Allah yaya ba komai dama ai su na kawowa" "Amma kayan sallar ki fa, da ko sudin sun bar miki." "Shima din ba komai ba gashi nayi kwalliyata da wadan nan ba". Hakurin sadiya shiya ke sa yaya kulu take dada kaunarta. Sai kuma amincin da sukayi da innarta kafin rasuwarta. Sun fara tattauna wasu batutuwa sadiya ta fice daga dakin ta barsu. Kamar ko yaushe yaya sani yana qorafin halin auwalu na lalaci. Yaqi karatu kuma shi baya aikin komai. Kullum yana gida. Anan suka wuni saida la'asar lis sannan suka kama hanyar komawa gida. Sadiya ta samu ta zaga dangi harda gidan baba labaran da yake zaune a mariri saida taje ta kwana biyu. Shi kam baima San sadiya tana aiki ba saida tazo wannan hutun. Halin yayarsa yasa sai ya shekara bai leqa inda take ba. Shima ganin da yayiwa sadiyan ta samu jin dadi a gidan da take sai hankalinsa ya kwanta da aikin nata.
=======***14***====== Kamar yadda su momi suka yi mata alqawari. Sati biyu na cika saiga Amir harda baby Khalifa. Ta dauka ma bazai ganeta ba. Amma yana ganinta ya fara miqo hannu ta dauke shi. Su amira ana tayi mata rakadi a haka suka koma gida. Suna bata labarin da maman Dadi suka zo zata ga likita. A wajen Hajiyar bichi sadiya ta gano inda su momi suka koyi martaba dan adam. Koda ba matsayinsa daya dasu ba. Duk wani kyautatawa da su momi suke yi mata sai taga nafila ne akan na Hajiyar bichi. Ta kuma samu sadiya irin yaran da take so watau yaro ba kyuiya ga kuma biyan buqata. Duk irin aikin da zata sa sadiya da hanzari take mata shi. Sauqin kanta da kuma hakurinta ya dada sa Hajiyar bichi ta jata a jiki. Har ta gama da likitan qashi da take gani a asibitin dala. Sadiya bata taba kosawa da hidimarta ba. Hazaqarta a karatun qur'ani shike dada sa mata farin jini a wajen Hajiyar bichi. Zaune suke a falo suna hirarrakin su. Sallamar anty salma ce qawar momi ta katse su. Daya bayan daya suka gaishe ta. Sadiya tayi dabara ta zame jikinta da zummar kawo abin sha. Ta gudu daga falon.=======***15***======= A gaskiya bata cika son zuwan anti salma gidan ba. Saboda kyararta da tsangwama da take yi mata. Ita a dole momi saita banbanta ta da 'ya'yanta. Watau ta nuna mata ita 'yar aiki ce. Amira ce ta fito da tiren da sadiya ta shirya. Tana jiyo anti salma tana mitar watau itama ta samu wuri har aiken 'ya'yan gida take yi. Bayan dauko ta akayi dan yara su huta. Momi dariya kawai tayi domin ta saba da wannan korafi na salma. Sun shiga dakin da Hajiyar bichi take ciki don su gaida ta. Tana taya momi zuzzuba turaren wutar da ta gama hadawa. Wanda take sanyawa a gidanta. Turaren wuta irin na 'yan maiduguri. "Lah Hajiya dama ke kike hadawa mariya turaren nan in munzo roqo ta ringa yi mana yanga"? Salma ta tambayeta. Hajiyar bichi tace" "ita take hada kayanta da kanta. Qarasa zuba mata a kwalba kawai nake. Kuma yadda naga tanayi kamar ma bashida wuya sosai. Sam bashida wuyar hadawa idan akwai kayan yi a garin nan. Ai gata nan ta iya hadawa zamanta a maiduguri saida ta koya a wurin wata qawarta. Sai dai in kiwa ce irin tata. Amma ba wanda bata iya hadawa ba. Harda turaren humra". Duk suka sa dariya. Salma tace "ai kuwa da zaki hada zan samo miki har masu saye. Kuma inaga kamar ana sayar da kayan turaren a kasuwar kurmi. Kinsan yanzu akwai kanuri mazauna kano da yawa". Bayan komawar Hajiyar bichi momi ta cigaba da sayen kayan turaren wuta tana hadawa masu qamshin gaske. Masu tsada da kuma masu sauqin kudi. Kuma duk salma ce tayi mata hanyar masu sayen. Sadiya kuwa kamar domin ita aka fara hada turaren wutan nan. Tun tana kama ma momi suna yi tare har saida takai sai dai momi tace mata hada turare kaza mai giredi kaza. Tas kuwa zata hada shi. Zamanta da Momi ta koyi abubuwa da yawa bama ya kwalliya da gyaran jiki. Su anti salma da suke kyararta an kuma dawo in zasuyi baqi ko miji yayi tafiya zai dawo a roqi momi ta basu aron sadiya ta taimaka musu da girki da gyaran gida. Wata umara da Momi da salma suka tafi tare nan gidan aka kawo yaran salma suka zauna daga su sai maigadi da kuma matar maigadin da take taimaka musu da wasu ayyuka. Har Allah ya dawo dasu lafiya suka tarar da yara fes dasu. Ba'a taba lattin makaranta ba ko qin zuwa islamiyya. Haka nan home work na makaranta duk sadiya na tsaye akai. Akwai wasu mutane da Allah kan hallita tun suna qanana sun iya kula da na kasa dasu da kuma tattali. To haka sadiya take. Tana da himma wajen tattala yara da kuma qoqarin gyara waje. Ko kiranta momi tayi indai ta durqusa a kasa sai ka ganta tana tsince-tsince akan carpet. Ko dan tsinke ta gani to saita dauke shi. Kullum momi in taga tana wannan abun sai ringa tsokanar ta tana fadin "sadiya karfa muje gidanki ki bamu tsintsiya kice mu share qafarmu kar mu shigar miki da datti". Dadi ne mai tare mata yace "gwara ace kayi tsafta da ace ka fiye datti." hausawa kance halin mutum jarinsa. Da wannan dabi'a tata sadiya ta shiga zuciyar jama'ar momi da dama. *********************** Sadiya nada shekara goma sha biyar wanda yayi dai dai da zamanta dasu shekaru hudu. Ta rubuta jarrabawar qaramar sakandire a makarantar su Amir. Wadda a wannan lokacin ana yinta ne domin tantance ajin da ya kamata yaro ya shiga. Ko dai ya shiga ajin koyon kimiyya watau science a ajinsa na hudu a sakandire. Ko kuma ya shiga na koyon kasuwanci watau commercial class. Ko kuma ya shiga