Chapter 4 Reading WACE CE UWA Complete Hausa Novels.txt Arewa Novels

WACE CE UWA Complete Hausa Novels.txt

Author :  Category :  Home Of Novels

Chapter   4 / 15

9K to 12K   out of 42.5K words

art class. Wanda zai bawa yaro damar karanta kwasa-kwasai irinsu law da makamantan su a jami'a Lesson da ake yi mata a gida ya wadatar da ita har takai wannan mataki. A kuma wannan lokaci ne suke qoqarin karasa yin saukar Alqur'ani ita da Amir
=======***15***======= A gaskiya bata cika son zuwan anti salma gidan ba. Saboda kyararta da tsangwama da take yi mata. Ita a dole momi saita banbanta ta da 'ya'yanta. Watau ta nuna mata ita 'yar aiki ce. Amira ce ta fito da tiren da sadiya ta shirya. Tana jiyo anti salma tana mitar watau itama ta samu wuri har aiken 'ya'yan gida take yi. Bayan dauko ta akayi dan yara su huta. Momi dariya kawai tayi domin ta saba da wannan korafi na salma. Sun shiga dakin da Hajiyar bichi take ciki don su gaida ta. Tana taya momi zuzzuba turaren wutar da ta gama hadawa. Wanda take sanyawa a gidanta. Turaren wuta irin na 'yan maiduguri. "Lah Hajiya dama ke kike hadawa mariya turaren nan in munzo roqo ta ringa yi mana yanga"? Salma ta tambayeta. Hajiyar bichi tace" "ita take hada kayanta da kanta. Qarasa zuba mata a kwalba kawai nake. Kuma yadda naga tanayi kamar ma bashida wuya sosai. Sam bashida wuyar hadawa idan akwai kayan yi a garin nan. Ai gata nan ta iya hadawa zamanta a maiduguri saida ta koya a wurin wata qawarta. Sai dai in kiwa ce irin tata. Amma ba wanda bata iya hadawa ba. Harda turaren humra". Duk suka sa dariya. Salma tace "ai kuwa da zaki hada zan samo miki har masu saye. Kuma inaga kamar ana sayar da kayan turaren a kasuwar kurmi. Kinsan yanzu akwai kanuri mazauna kano da yawa". Bayan komawar Hajiyar bichi momi ta cigaba da sayen kayan turaren wuta tana hadawa masu qamshin gaske. Masu tsada da kuma masu sauqin kudi. Kuma duk salma ce tayi mata hanyar masu sayen. Sadiya kuwa kamar domin ita aka fara hada turaren wutan nan. Tun tana kama ma momi suna yi tare har saida takai sai dai momi tace mata hada turare kaza mai giredi kaza. Tas kuwa zata hada shi. Zamanta da Momi ta koyi abubuwa da yawa bama ya kwalliya da gyaran jiki. Su anti salma da suke kyararta an kuma dawo in zasuyi baqi ko miji yayi tafiya zai dawo a roqi momi ta basu aron sadiya ta taimaka musu da girki da gyaran gida. Wata umara da Momi da salma suka tafi tare nan gidan aka kawo yaran salma suka zauna daga su sai maigadi da kuma matar maigadin da take taimaka musu da wasu ayyuka. Har Allah ya dawo dasu lafiya suka tarar da yara fes dasu. Ba'a taba lattin makaranta ba ko qin zuwa islamiyya. Haka nan home work na makaranta duk sadiya na tsaye akai. Akwai wasu mutane da Allah kan hallita tun suna qanana sun iya kula da na kasa dasu da kuma tattali. To haka sadiya take. Tana da himma wajen tattala yara da kuma qoqarin gyara waje. Ko kiranta momi tayi indai ta durqusa a kasa sai ka ganta tana tsince-tsince akan carpet. Ko dan tsinke ta gani to saita dauke shi. Kullum momi in taga tana wannan abun sai ringa tsokanar ta tana fadin "sadiya karfa muje gidanki ki bamu tsintsiya kice mu share qafarmu kar mu shigar miki da datti". Dadi ne mai tare mata yace "gwara ace kayi tsafta da ace ka fiye datti." hausawa kance halin mutum jarinsa. Da wannan dabi'a tata sadiya ta shiga zuciyar jama'ar momi da dama. *********************** Sadiya nada shekara goma sha biyar wanda yayi dai dai da zamanta dasu shekaru hudu. Ta rubuta jarrabawar qaramar sakandire a makarantar su Amir. Wadda a wannan lokacin ana yinta ne domin tantance ajin da ya kamata yaro ya shiga. Ko dai ya shiga ajin koyon kimiyya watau science a ajinsa na hudu a sakandire. Ko kuma ya shiga na koyon kasuwanci watau commercial class. Ko kuma ya shiga art class. Wanda zai bawa yaro damar karanta kwasa-kwasai irinsu law da makamantan su a jami'a Lesson da ake yi mata a gida ya wadatar da ita har takai wannan mataki. A kuma wannan lokaci ne suke qoqarin karasa yin saukar Alqur'ani ita da Amir=***16***====== A wannan shekarar ne kuma sadiya ta kasance makerin yan mata ya fara kerata. Duk da bata gama zama cikakkiyar budurwa ba. Amma kallo daya bazai ishi mutum a kanta ba. Tana da sura mai daukan hankali. Gata fara mai kyawun fata. Hausawa sukace kowa yayi tsaho yayi rabin kyau. A miqe take sambal ga yatsun hannu dana kafa dogaye masu tsari. Gashin kanta kuwa anan aka zuba kyau. Baki ne sidik ga tsaho da santsi. Fuskarta na dauke da dogon hanci wanda ya dada kawatar da 'yar doguwar fuskarta. Digon dake lotsawa a dukkan nin kumatunta Yayin da duk tayi Murmushi. Shike dada kawata fuskarta. Bakinta dan daidai misali mai dauke da wushirya da kuma jerarrun hakware masu tsari fari khal dasu kamar zata tallan makilin. Idanuwanta kuwa farare ne khal sai digon bakin ya dada kawata su. Ko a lokutan da take yawan zubar da hawaye. Watau sanda tana gidan inna to kuwa tana gama kukan zasu koma da haskensu kamar batayi ba. Tana mutukar kama da innarta sai dai tafi inna da duk 'ya'yanta kyau. Yayan zaria nema suka so suyi kunnen doki. Amma tunda ita mace ce saita tsere masa. Tafiyarta a nutse tare da kuma taftarta ita take dada daukar hankalin mutane a kanta. Da Momi ta lura samari suna neman su fara kawo mata har sai ta fara kalleta Inba da dalili ba bata barinta ta fita. Momi ta horeta da kwalliya da tsafta. Dokar gidan ce koba makaranta. To kana tashi da safe wanka zaka fara yi. In kuma kana da aikin yi to da ka gama sai wanka. Momi tana kokarin gyara amira da kuma sadiya. Koba inda zasuje cikin kwalliya zaka same su. Shiyasa da ance tashi muje mu. Sai dai daukan mayafi da takalmi. Babu wanda zaiga sadiya yace mai aiki ce a gidan momi. Yadda su amira zasu wataya haka itama. Irin fadan da za'ai musu in sunyi laifi. Shi za ai mata in tayi irin laifin.=====***17***===== Momi kuma irin matan nan ne masu wayon zama da yara da jansu a jiki. Duk abinda suke ciki ta sani saboda yawan hira da takeyi dasu. Da kyar kaji tana hargowa da sunan yiwa yaro fada. Sai dai nasiha da lallashi. Laifin da yafi jawo maka hukunci a gidan shine karya. Amma duk laifin da zakayi in dai ka fadi gaskiya to za'a sassauta maka hukunci. Haka baka isa kayi gulma ba ko ta waye to za'a titsiyeka a gaban sa. Ka maimaita abinda ka fada. Har abada dan adam yana tare da jarrabawa mussaman mumuni. A wannan lokacin sadiya ta hadu da tata jarrabawar ta farko. A dalilin karin girma da Dadi ya samu. Inda ya samu nasarar komawa jami'ar Wisconsin ta kasar america inda zai jagoranci bangaren kere-kere watau faculty of engineering. Wannan daukaka da Dadi ya samu shiya fara jefa sadiya cikin mawuya cin halin da ta shiga. Tunda aka fara maganar su momi zasu koma America. Kusan kullum sai sadiya ta kulle kanta a bandaki tayi kuka. Ga kukan rabuwa da wadanda ta saba ga kuma tararrabin rayuwar da zata koma a gidansu. Tasan dai karatu kam yasha ruwa. Momi ce ta kwalla mata kira amira ta amsa da tana bandaki. Momi ta sake kiranta akace bata fito ba. Amira tana dariya tace "momi yanzu kullum sadiya sai ta kulle kanta a bandaki bansan me take yiba kuma sai ta dade sosai bata fito ba." momi tasha jinin jikinta. Kasancewar ta mace mai lura tuni ta gano inda zancen Amira ya dosa. Domin itama ta lura da yanda sadiyan tai laushi kamar mara lafiya. Ga kuma dariyar yake data maye gurbin far'arta. Bayan bayanin da Momi tayiwa Dadi tare suka zaunar da ita sukai mata nasiha mai ratsa jiki. Dadi ya nuna mata cewar babu wani dan adam da zai isar wa wani inba Allah ba. Haka zalika ta kasance mai roko da kuma dogaro da Allah amma ba bawansa ba. Ya nuna mata addu'a ce kawai zata tsaya mata amma ba wani mahaluki ba. Momi tace nidai Dadi da iyayenta zasu yarda da sun bar mana ita. Idan ta isa aure sai mu dawo da ita. "A'a momin Amir karki dada karya mata zuciya akan abinda bazai yuwu ba. Wata kasa fa zamu tafi. Kinsan kuwa da wuya su yarda mu tafi musu da 'ya. Ba naga da kyar ma suka yarda take zama da muba. " Duk da wannan nasiha da suka yi mata ranar da zasu tafi kuka ba itaba ba momin baba kuma su Amir ba. Khalifa kuwa da ya budi ido ya ganta a gidansu. Ya dauka 'yar gidan ce. Duka duka baifi shekara ba tazo gidansu. Don haka shi a sanin da yayi mata itama 'yar gidan ce. Ko banza kuma dama tafi shiri dashi akan duk yaran. Tafi kowa tattalinsa da kuma daurewa al'alarsa. Da yaga kowa ya shiga mota. Sai kiranta yakeyi tazo su tafi kar a tafi a barta. Da kyar aka lallabeshi. Tafiyar su ita ta maida sadiya zaman gidan inna tare da tarin alherin da ta samu daga momi. Wanda ya hada da kudi da kuma tarin sutura. Wanda tasan ba ita zata mora ba. Sai kuma ilimi da kuma kyawawan dabi'u wanda su kam ta hakikance lahu suke a gareta. Babu me ara babu mai karbewa sai dai in mutum yaso ya koya. Ga kuma tarin nasihohin da Dadi da Momi suka yi mata.
======***18***====== Kudin aikinta dai babu wanda ya more su kamar yaya baba. Domin dasu aka sai masa mashin. Aka gyara masa dakunan da suke waje aka kara masa daki daya. Ga kuma lefen sa na aure. Duk daga wahalar ta ta shekaru hudu. Gidan kam yayi kyan tsari. Domin hatta dakunan inna da kuma rumfarta an shafe su tare da canja musu kyamare da kuma tagogi. Tsakar gidan ma an raba shi biyu. Aka ware wa yaya baba nasa. Aka fitar masa da bandaki da kicin. Dawowar sadiya ta tarar harda shirye-ahiryen auren yayan zaria akeyi. Tayi masa murna kwarai. Amma shi baisan dalili ba sai yaji yana jin kunyar sadiya yana ga kamar yayi mata laifi. Ganin inna ta auren yaya baba kawai take yi. Gashi kuma ta dage sai sani ya fito an hada da nasa. Yaso ta barshi ya karasa karatun sa tunda baifi saura wata tara ya kammala ba. Koda zai tafi bautar kasa ne sai ayi bikin amma ta dage ayi a haka. Fahimtar da sadiya tayi yayanta na cikin tashin hankali gashi ba zai iya ketare maganar inna ba. Ya sanya ta same shi a dakinsa na zaure. Inda suka koma shida Salisu kasancewar yaya baba zai zauna a wajensu nada. A hankali ta sudade ta same shi a dakinsa. Kunyarta yakeji sosai ya kasa ko hada ido da ita. Ita kam bata kula da wannan sabon canjin data gani ba. Kokarinta ta bashi abinda ta kawo masa. Makudan kudi ta kullo ta ciro daga cikin zaninta ta mika masa. Da sauri ya dago fuskarsa ya kalleta alamar neman bayani. "Kudin da Dadi ya bani ne akan inci gaba da biyan kudin makaranta ko kuma in nemi sana'ar da zan yi. To ni banga yiwuwar ko daya daga cikinsu ba. Kuma naga kamar zaka jawo min delay zuwan yayata. Kuma dama gaskiya kai nayi niyyar bawa koda ba aure zakayi ba. " Shidai ya kasa magana saboda mamaki. Ya rasa mai zaice mata. Kafin yayi magana. Ta sake cewa. "Amm Idan yayata tazo sai in koma inyi mata zaman daki. Kaga saika maida ni makaranta in samu in karasa. Nasan Insha Allahu inna bazata kiba. Tunda naga kamar yanzu muna shiri da ita ba kamar daba da take yimin fada. Abinda bata gane ba shirin inna da ita na ganin tana kawo mata abin duniya ne. Tunda zamanta a gidan momi yasa momi da kanta. Tana yawan yi mata alheri mussaman kayan sawa da abinci. Momi da Dadi Allah ne ya hada su dukkaninsu hannayensu a sake suke. Mutane ne masu son yin alheri mussaman ga mai karamin karfi. Kuma dadin dadawa Allah ya hore musu abinda zasuyi alherin dashi. Tana dariya ta mike da niyyar ficewa har ta fita ta dawo "don Allah karka gayawa kowa". Kafin ma yayi magana ta fice daga dakin. Ta kuma taki sa'a har taje ta dawo ba wanda yaga shigarta da fitarta. Washe gari gidan yaya kulu ya nufa da makudan kudin sa. Suka shiga kasuwa ta hada masa lefe Masha Allah. Su kansu su inna sunyi mutukar mamaki da kayan daya hado. Don har yafi na yaya baba da aka kai. Anan ne shi yaya baba ya ringa gunguni yana fadin "dama munafunci ne don karya taimaka min da komai. Anyi magana yace shi dan makaranta ne yanzu a gidan uban wa ya samo wadan nan iyayen kaya. Shi dai bai tanka masa ba. Yaya kulu cema ta cashe masa wannan karon ta nuna masa inzai mike ya mike don ba wanda zai rike masa mata in tazo. Shi kadai zaiji da kayansa. Ga mashin an saya masa saidai yayi wanka ya fice yawo cikin gari. Ba yadda bata yi da shiba akan ya dinga acaba. Yace yafi karfin haka. Inna kuma ta goya masa baya. A dalilin wai kwanaki ta samu labarin wani daya dauki fasinja zai kaishi wani waje. Saida sukaje inda ba mutane yayi masa duka ya kwace mashin din. A wajen gida ne sani yace zai nemi dakin haya anan unguwar. Amma sai inna tace ga gidan marigayi kawunku isiyaku ba sai ka gyara ka zauna ba kafin Allah ya baka naka. Da kansa ya tafi wajen kawunsu labaran don ya hana inna wannan kudiri nata wanda a ganinsa zalinci ne. Kawu labaran ke rike da gonakin sadiya na gado guda biyu da kuma hayar gidan data gada daga gun babanta. Hatta kudin hayar shiya ke karba da son ya sakata a makaranta. Amma ganin yadda inna ta ture maganar karatun shima sai yayi mata wani shirin da kudin hayar.======***19***====== Inna da Kawu labaran da kuma sani a tsakar gida suna tattauna batun gidan da sani yake so ya zauna. Inna ta matsa da sai sani ya zauna a gidan tunda basu da nisa. Nan ne baya da su kadan duka - duka tafiyar minti biyar ce zuwa bakwai daga gidan inna zuwa gidan. Dagewar da inna tayi yasa Kawu labaran yace a kira sadiya a tambayeta ra'ayinta in ta yarda dan uwanta ya zauna shike nan. Sani bai so haka ba don yasan sadiya bazata taba hana shi kayanta ba. Da aka kirata kuwa da murnarta tace "to ya zauna mana da wani ba gwara shi din ba" Kawu yace to "dole ya biya ki kudin haya" tana dariya tace to ya ringa biyan nera goma. Allah kuma daga hak baza'a kara ko kwabo ba. Kowa yasa dariya a wajen. A ranar sadiya taji kalmar da bata taba jin inna ta kira mata ba watau kalmar Allah yai mata albarka. Har ta mike zata tafi Kawu ya dakatar da ita ya zaro wasu takardu daga aljihunsa. Yace kinsan gonarki ta hanyar gaba da kasuwar tarauni (farm center a yanzu) to gwamnati ta yanka filaye a wajen wanda duk yake da gona an bukaci daya biya wasu kudade ayi masa takardun shaidar mallakar fuloti a madadin gonar. To nima nayi miki amfani da kudaden hayarki na biya. Wannan takardun ne. Inna dai murnar danta ya samu muhalli yasa sai murna take yi tana addu'ar Allah dai yabar zumunci. Cikin farin ciki wannan taro ya watse. An sanya bikin Auwalu da sani sati hudu masu zuwa. Wannan yaba sani damar kammala gyaran gidan da zai zauna mai dauke da dakunan barci biyu da falo a tsakiyar su. Sai dan karamin tsakar gida mai dauke da dan madai daicin bandaki da kuma kicin. Akwai soro da kuma karamin daki wanda za'a iya amfani dashi a matsayin daki ta cikin gida ko kuma shago ta waje. Ana saura sati daya daurin aure Allah yai ikon sa akan mahaifin Zainab watau yarinyar da sani zai aura. Ana tunanin daga biki su Kawu labaran suka ce a'a. A daura aure akai amare sai dai a rage bidi'a. Ana cikin wannan alhini sai ga sako daga mahaifiyar ita Zainab din akan ta fasa ita 'yarta bazata auri dan makaranta ba sai dai ya hakura da auren kafin nan itama tata 'yar ta fara makaranta sai ayi auren. Inna ma tai tsallen albarka tace itama danta bai isa daukar nauyin karatun wata ba tunda yanzu yake taso wa. Tashin hankali ba'a sa maka rana. Duk da auren hadi ne amma hankalin sani ba karamin tashi yayi ba. Su kawu labaran sunje domin a samu maslaha amma ta kekasa kasa taki ta kuma ce duk duniya ba wanda ya isa ya aurar mata da 'ya. Sai dai in sun yadda da wannan sharadi nata. Inna ta dage mahaifiyar zainab ta dage. Har ranar daurin aure babu wata sahihiyar magana. Ana zaune anyi jugum jugum harda su sadiya a zaune a falon inna sai ga wata kawar inna mai suna marka. Ta juya ta kalli inna wacce ke faman share kwalla tana takaicin wannan wulakancin da aka yiwa danta. Tace nifa tasallah da gangan kike wannan kuka. Ga magani a gonar yaro amma ciwo zai kashe shi. " Me kike nufi inji inna. "Zi muje daga ciki ai shawara ce gwara mu kebe. Sun dade suna tattaunawa. Inna ta fito tasa aka kira mata kawu labaran. A dakin zaure suka tsaya suka tattauna. Sannan ya fita waje. A kaje aka daura auren yaya baba da amaryarsa huwaila. Sannan aka dawo nan kofar gidansu aka daura na sani. Sadiya na zaune kawu labaran ya shigo gidan ya kirata cikin dakin inna. Itama Innar tabi bayansu. Cike da ladabinta na hallita ta durkusa. "Gani kawu " ya sanya hannu a

4 / 15