Chapter 11 Reading WACE CE UWA Complete Hausa Novels.txt Arewa Novels

WACE CE UWA Complete Hausa Novels.txt

Author :  Category :  Home Of Novels

Chapter   11 / 15

30K to 33K   out of 42.5K words

na tayin kudi da sani yayi mata. Saida ya ajiye mata kudi masu yawan gaske. Abinda sani bai sani ba. Ba auren sa ne ya tunzura sadiya ba sai dai labarin da Dija ta gaya mata na cewa shi sanin da kansa yace su boye wa amaryarsa batun sadiya da kuma yaranta. Wannan shi yake koma mata rai fiye da komai. Bata so gaskata zancen Dija ba saida 'yan uwan amarya suka zo kawo kayan amarya suka gaisa da ita a matsayin kanwar sani. Saboda inna ta fada musu gidan sa kanwarsa da mijinta na zaune a ciki ko don su kula masa dashi tunda shi ba mazauni bane. Wannan dalili yasa sadiya taji fit sani ya fice mata daga ranta. Da farko ta hakura da auren sani amma ganin yadda ake lamarin auren ba ita a ciki yasa ta dada tabbatar da zancen Dija. Ta tattara shi ta watsar kamar Allah baiyi ruwan tsirarsa ba. Da farko hatta yara ji tayi ta tsane su saboda ganin kamar don su ne ake mata wannan wulakancin da kuma ganin bata da inda zata je. Amma da tayi tunani sai taga su meye laifin su. Yadda aka watsar da ita haka suma aka watsar dasu. Gwara ita aure ne ya hada su za'a iya kare shi. Wanda shine kadai abinda take jira daga gurin mijinta. Amma sufa da basu da wani uban sai shi.=====****44****===== Ta juya ta kalle su. Tafi tausaya wa kamal da bashi da uwa. Uban kuma ya yar dashi. Ta share hawayen da yake zuba daga idanunta. "In sha Allahu daga yau bazan kara zubar da hawaye na akan Sani da inna ba. Zanyi kokari in rike 'ya'yana in basu kulawar da bazasu taba maraicin rashin uwa ko uba ba. Allah ne ya hallicce mu ya kuma kaddara mana rayuwa ta kasance haka a wajensa kawai zamu nemi taimako. Ta numfasa taci gaba da tunaninta. "IYYAKA NA'ABUDU WA IYYAKA NASTA'IN. Ta fada har sau uku "insha Allahu yarana bazasu shiga walagigin rayuwa irin yadda na shiga ba. Zan zauna dasu muddin rai. In Allah ya yarda bazasu dandani madacin maraici ba. Kamar yadda ni na sanshi nake dandana har yanzu. Nasan banida gata sai na Allah. Kuma insha Allah dashi zan dogara. Wannan shine alkawarin da sadiya ta daukarwa kanta da kuma zuciyarta. Ta sawa ranta hakura da sani komai son da take masa. Da kuma duk yadda take kulafucin shinfida rayuwar aure da kuma ginawa 'ya'yansu ingantaciyar rayuwa sabanin irin wadda ta sami kanta a ciki. Ta dauka aurenta da Sani shine zai kawo mata karshen bacin rai da kuma kuncin rayuwa da take ciki. Amma sabanin haka Allah ya shirya mata. Duk da yaran da ta sami kanta a me tara su cikin dan kankanin lokaci. Wannan bai dame taba tunaninta 'ya'yanta. Mijinta kuma wadda Ada take wa kallon masoyi zai tallafe su. A yau ta tabbatar wannan damar ta kubuce mata. Bata kanta take ba ta yaranta take. Su kam ta kudurtawa ranta zata sadaukar da rayuwarta domin tasu ta inganta. Zata yi hakuri da duk wani jin dadi na rayuwa domin yaranta suji dadin da ita bata samu ba. Sani dai kam ta hakura dashi tasan bata da kowa sai yaranta sune madadin 'yan uwanta su kuma kadai take dasu da zata sadaukar da komai nata don su su sami kyakkyawar rayuwa.=====****45****===== Shirye shiryen aure sun kacame inna tasa Sani fito da duk wata ajiya tasa domin yin aure na fitar kunya in jita. Duk da hanawa da baban Asma'u yayi saida inna tasa Sani hada lefe na kece raini. Hatta kayan kunshi da lalle da ake sawa a kwalla shi nasa a kumbo tasa aka zuba. Akwai wani fegi da ta saya saida aka siyar ya shiga cikin hidimar auren. Wata rana sani ya kasa daurewa zuciyarsa ga dauke masa wuta da rabin ransa tayi ga kuma wasuwasin karyar da inna tasa shi ya shuka. Kawai sai yayi kundunbala ya nufi gidansu Asma'u da niyyar samun abbanta ya warware masa duk abinda yake ciki ko su bashi aure ko su hana shi duk daya ne a wajensa. Inna kuma ya shirya duk tashin hankalin da zata yi ya san ya fita gaskiya. Mai gadin gidan ne ya tare shi tunda ya sanshi farin sani. Bayan sun gaisa yace masa amma ka daki gurbi. Ai amaryar bata nan taje karaye sallama da kakanninta shi kuma Alhaji sunje umra shida hajiya sai nan da kwana goma zasu dawo. Sani ya lissafa yaga sai ana saura kwana hudu daurin aure zasu dawo. Asma'u kuwa baiga anfanin tattauna wannan maganar da ita ba. Haka nan ya hakura ya juya gwiwa a sanyaye ya koma gida. Abokinsa daya da yake ganin zai tattauna wannan matsalar dashi shine sa'idu sale shi kuma ya masa nisa. Tun zuwan da suka yi yi masa sallama shida amaryarsa yaso fada masa amma zatonsa zai iya shago kan matsalarsa. Addu'a kawai ya dage da yi akan Allah ya fito masa da mafita a wannan al'amari. Sanin na cikin wannan tashin hankalin har ranar daurin auren sa da Asma'u tazo anyi biki an gwangwaje. Su Dija kuwa sune 'yan kan gaba wajen halartar cocktail party. Fadi take yaya yayi aure a babban gida. Daki falle daya da yake gidan sani shi aka gyara wa amarya tunda ba zama zasu yi ba. Kayan ma sai jingine su kawai aka yi ba tare da an jera ba tunda a washe garin daurin auren zasu tashi. Da daddare ango yaci kwalliya da babbar rigarsa ta shadda wacce yaya baba ya dinka masa a matsayin gudun mawa tunda yasan auren jari ne a gare su. Kusan yafi angon dokin auren. Bayan ya shirya duk ya budewa uwargida hanci da kanshin turaren sa sai kuma kunya ta hana shi fitowa daga dakinsa. Yana jin ta shiga tolet yayi wuf ya fice daga gidan. Anyi party hadadde mai tsari. Ga amarya kyakkyawa ga ango kamar tauraro don haskaka wa da yake yi. Anyi hotuna nasu kyawun gaske da kuma video. Irin wanda ake yayi a wannan lokaci. A gidan inna akayi budar kai saboda jirgin dare zasu bi don tafiya saudiya. Inna da mukarrabanta basu gayyaci sadiya ba. Itama bata nuna sha'awar zuwa ba. Bayan an gama budar kai da kansa ya bukaci amaryar da ta fito zasu unguwa. Gidan yaya kulu suka je saboda bata samu halartar bikin ba. Ta aikowa inna da cewar danta bashi da lafiya amma shi Sani hankalinsa bai kwanta ba. Yasan yaya bata cikin harkar auren ko don wulakancin da inna tayi mata. Yaya ta karbe su da murnar ta bata bari amarya ta fahimci wani abu mummuna daga gareta ba. Harda tsara bar su kuka da daddawa da kuma yaji ta bata. A hanyar su ta dawowa gida Asma'u tace akwai wasu kaya da zata tafi dasu kuma suna gidansa da aka kai mata kayanta. Zuciyarsa na lugude suka nufi gidan sadiya. Tana durkushe tulin kayan wanki ne na yaranta a gabanta tana faman yi. Sallamar da Sani yayi ce taso taki amsa masa. Amma sai taji sallamar mace. Ta dago suka yi arba da ita. Kyakkyawa ce wankan tarwada shigar da ta gani ta alfarma a tare da ita shiya tabbatar mata da cewar wannan amaryar Sani ce. Nan da nan ta kauda bacin ran da ke kan fuskarta ta fa dada far'arta oyoyo oyoyo ga amaryar yaya" ta mike daga wankin da take yi. Da sauri ta dauraye hannunta tana musu sannu da zuwa. Ku shigo daga ciki. Ta fada tana mai shiga dasu cikin falon ta. A tsafta ce yake sai kanshin turaren wuta yake yi irin wanda ta koyi hadawa a gidan momi. "Bismillah ta fada tana mai nuna musu gurin zama. Kamal ya tako da son zuwa wajen babansa amma sai tayi hanzari ta dauke shi shi dai yana zaune kamar kurma. Don duk a tunaninsa da kuma ganin irin zaman da suke da sadiya sai yake zaton wani tanadin rashin mutunci take masa shine take masa shigo shigo ba zurfi. Sun gaisa a mutunce ta gabatar musu da lemon asir wanda take hadawa da lemon tsami da sugar Asma'u taji dadinsa sosai. Su walida suka shigo ta kalle su "kai wadan nan cute yaran fa amma triplets ne" kafin sani ya sake magana ta amsa da eh 'yan uku ne. Kamar da taga sadiya da Sani sunyi shiya dada tabbatar wa da Asma'u cewa ita din kanwarsa ce. Su biyu suke ta 'yan hirarrakisu kuma duk akan yaran da ta gani ne. Su walid da imam bata gansu ba sunje gidan malama umma. Ta mike tace bari na duba wasu kaya na kar muyi missing flight dinmu. Tana shiga sadiya ma ta mike ta shiga kicin kamar wani aiki zata yi saboda bama tason Sani ya sami kafar yi mata magana. Indai bazai iya magana da ita a gaban matarsa ba. To kuwa itama bata da lokacin sa a bayan idonta. Asma'u ta samu nasarar gano kayan da take nema ta fito daga dakin sukayi sallama da sadiya ita kuwa ta shiga daki gaba daya kudin da Sani ya ajiye mata kwanakin da suke rigima su ta dauko ta bawa Asma'u tana fadin "gashi na sayi bakin amarya. Ta. Rakota har soron gidan tana fadin "Allah ya kaiku lafiya. Ya fissheku hanya. Allah ya bada sa'ar abinda abaje nema. Tana amsawa sukayi sallama.**46****===== Ta dawo ta cigaba da wankin ta Sani ya tsaya kawai a tsakar gida yana kallonta. Bata dago ido ba. Duk da tasan yana tsaye. To ita in ta dago ma me zata ce masa. Magana tsakaninsu ai ta kare mema zasu ce da juna. Idan ma shi yana da abin cewa to ita kam bata da shi. Yana nan tsaye kimanin minti biyar tausayi nadama da kuma soyayyar tace take nukurkusar sa. Ya duba yaga yanzu haka wankin yaransa ne take ta fama dashi. Wanda kuma kullum haka take fama da irin wadan nan hidimomin yaran da ba duka ne nata ba. Amma shi kam bai taba ganin koda wasa ta nuna wani bambanci a tsakaninsu ba. Ko don yana namiji bai san cewar ba abinda yake kawo shakuwa tsakanin da da uwa ko ba ita ta haifeshi ba irin shayarwa. Ga misali irin karramawar da Annabi (S.A.W) yake yiwa sayyida halimatus-sadiya shakuwar shayarwa ce ta wanzar da haka. Yana cikin wannan tunani saiga salisu da saurin sa yana fadin "inna tace kuzo ku tafi wai ga motar da zata kaiku airport tazo jiki ba kwari haka yabi bayansa. Har ya fara tafiya ya sake juyowa ya kalli sadiya da tunanin ko zata dago ido ya kalleta amma wanki take kamar bata san da mutum a tsaye a wajenta ba. Haka nan ya hakura ya juya ya tafi ya barta da igiyar auren da bata San makomarta a kai ba. A airport suna zaune asma'u ta bude jakarta ta fito da ambulan din kudin da sadiya ta bata. Ita kanta duk da ta saba da rike kudi masu yawa amma wannan kyauta daga kanwar Sani ta bata mamaki. Ta mika masa "ga gift din sister ka ta bani. Ta mika masa ya karba. Tabbas kudin daya bawa sadiya ne ta maido masa da abinsa ta hanyar Asma'u bai mata magana ba ya karba yasa a aljihu can kuma ya mike "bari in canzo miki su zuwa riyal ko kya bani lada " dariya kawai tayi bayan ya dawo ta sake cewa "Amma Kuna kama da ita bata wasa ba. Inaga duk yaran gidanku kunfi kama da ita. Shi dai bai amsa mata ba ta sake cewa yanzu duk yaran tane wadan nan amma she is too young. Shekararta nawa ne yanzu. Twenty cif. Ya amsa mata a takaice. Ita kam ta yaba da sadiya sai yabon taftarta take yi da kuma kyawun da ta gani a tare da ita. Ta kara da cewa "Amma tana da baby face wama zai ce tafi sha shida. Gata kuma da kyan jiki ba wanda zai kalle ta ya dauka ta taba aure ma balle har ace ta haihu by the way ni ina mijinta be"? Kirjin sane ya bada ragaga yaso warware mata zancen sa da sadiya amma sai ya kasa bakinsa yake jin yayi masa nauyi. Harshen sa kamar an dora masa dutse akai bai san ya akayi ba sai jin bakinsa yayi yana cewa "yayi tafiya "Uhm lucky guy. Zan so in ganshi in gaya mishi yayi sa'ar mata. Ta kishingida a jikinsa cikin shagwaba take fadin "wash Allah gaskiya biki akwai gajiyar wa. Baka ji duk yadda jiki na yake ciwo ba. Tana kokarin jan Sani da hira shi kam hankalinsa baya tare da ita. Hankalinta a kwance ta samu abinda take so. Sabanin nasa da yake tashe. Saboda samun abinda take so wanda yai masa sanadin rasa abinda shi yake so. Kudin da sadiya ta bawa Asma'u shiya dada tabbatar masa da cewa sadiya sako ta bayar a kai masa wanda ya nuna masa cewar ita kam bata da muradin sa a rayuwarta. Ba abinda zuciyarsa ke hasko masa irin sallamar da suka yi. Har yanzu bai daina ganinta a durkushe tana wanke kayan yaranta ba. In dai wahala ce yasan shi take yiwa. Yaran nan da take dawainiya dasu duk shi ya tara mata su. In ya tuna kusan yini take tana fama da hidimar su duk domin ta inganta musu rayuwa ya juya ya kalli Asma'u da take baccinta lakadan ba abinda ya dameta. Ya sake wani tunanin a ransa Inama sadiyan shi ce zata samu wannan gatan. Tayi rayuwa koda ta kwana biyu ce ba tare da damuwar komai a ranta ba. Ya sake tuno kwazo da juriya irinta sadiya. Anya akwai mace ko kuma yarinya mai hazakar ta. Shi kansa inya tuna hidimar da take dashi ya kamata ace tafi karfin abinda yayi mata. Da rana ta yini hidimar gidansa da yaransa. Da daddare ta kashe kusan rabinsa shi kuma tana hidima dashi. Shi kansa yasan yana takura mata da bukatun sa. Amma kasa daurewa yake ya hakura indai tana tare dashi. Wai shin yaushe ma take samu ta huta ne ita kam a rayuwarta.=====****47****===== Ya sake juyawa ya kai kallonsa ga Asma'u a ransa yake fadin ke kam kinji dadinki. Allah ya hore miki abinda zaki sami biyan bukatar ranki a wannan zamani. Wato kudi da mulki. Inama yadda ya tsaro musu rayuwa shida sadiya haka ya same ta. Ubangiji Allah ka bawa sadiya juriya akan wannan jarrabawa data same ta. Ya sake nisawa ya tu.a tun da yarinyar nan ta tashi bata da kowa. Allah ne kawai gatanta. To shi din ma kusan abu daya ne dashi. Ya dade da fahimtar ba kauna iri daya inna take masa shida sauran 'yan uwansa ba domin da yaya baba ne ko Dija. Ko sama da kasa zasu hadu inna bata isa ta sasu abinda basuyi niyya ba. Ita ma kuma bazata taba tursasasu suyi mata abinda basa so ba. Koda kuwa hakan su zai anfana. Kamar dai misali yadda yaya baba yayi biris da karatu inna tace tunda bashi da ra'ayi a kyale shi ai ba kowa yake da nasibi a boko ba. Aka fara zancen sana'a kawu labaran ya nemo masa aiki a gidan biredi yace wuta zata dafar dashi. Inna kuma tace sabara take sawa. Aka ce yayi acaba yace yan daf su take shi ya mutu. Kawu labaran ya samo masa aiki a shagon wani abokinsa a kantin kwari yace bazai iya aiki a karkashin wani ba saboda shi ba zai dauki wulakanci ba. Yaya kulu ta bashi shawarar ya koyi dinki yace zama basir yake kawowa. A nan ne ma taji haushin sa tace ko wacce sana'a akace sai ka kawo kushenta. Idan zaman shagon tela bai saka basir ba ai zaman dakin inna ya saka basir din da kake gudu. Duk da rashin kunyarsa yana shayinta saboda kwarjininta. Gunguni kawai yayi a cikin ransa. Inna tace a kyale shi. Yana nan inda yake arzikin sa zaizo ya same shi. Ya dauka biyayya ce take sa a daukaka wani akan wani. Bai taba jin inda akai auren jari da namiji ba sai a kansa. Shida yake binta sauda kafa shita tursasa ta Zubar da nasa 'ya'yan yara kanana har guda shida tare da 'yar yarinyar matar sa wadda itama kulawarsa take bukata a girme asma'u ta girme mata da shekara daya tunda ita shekara ishirin da daya take ciki. Ya aure ta tana shekara sha biyar ta haifi walid da imam tana 16 sannan walida da rikon shukra da jidda daya sameta tana 'yar 17 shekara biyu tsakani aka sake kawo mata rikon kamal yana jariri. Danye sharaf ya sake jinjinawa ba domin tana da kyawun jiki ba da yaran nan sun tsofar da ita. Ko don shayar dasu da take yi. Murmushi ya subuce a fuskarsa daya tuno kyawun surarta hatta cikinta a shafe yake kamar bai dauki jego hawa biyu ba. Haka nan kirjinta kusan shine abinda yafi so a tare da ita. Ba yadda za'ai kace bana budurwa bane ko yaro zata shayar saidai ta tashi ta zauna saboda dasuwar su bazata iya shayar da yaro tana daga kwance ba. A dan zaman da sukayi na shekara biyar duk da dai a tsitsinke suka yishi. Amma sadiya ta dasu a ransa fiye da duk wani mutum daya taba mu'amala dashi. Ita ma kuma ya tabbatar da ta so shi duk da rigingimun. Aure auren sa daya ringa sakata a ciki. Ya san kwarai tayi hakuri dashi da irin rayuwar da ta samu a gidan sa. Ya san ta kauna ce shi yana yayan ta. Ta kuma so shi soyayya inganttaciya kuma tsaftataciya a lokutan da ya zamo miji a gareta. A yanzu ne dai bai san matsayin da ta ajiye shi ba. Bai kuma ga laifin ta ba. Kaddara ce ta datse wannan kyakkyawar danganta kar da suka faro ta shida ita tun tana karama. "Ya Allah " yayi addu'a a cikin zuciyarsa "Allah ka bani ikon farantawa inna da kuma kyautatawa sadiya da yarana sannan ka bani ikon sauke nauyin Asma'u

11 / 15