Chapter 9 Reading WACE CE UWA Complete Hausa Novels.txt Arewa Novels

WACE CE UWA Complete Hausa Novels.txt

Author :  Category :  Home Of Novels

Chapter   9 / 15

24K to 27K   out of 42.5K words

wata macen sai dai ta koya a wajensa. Ita kuwa wannan zance shine mafi dadin ji a wajenta. Ta dade da burin Sani ya bara da kansa. Ya nuna yana sonta. A kansa ne taji zata iya canja ra'ayinta na kin son auren mai mata ta aure shi. To kuma gashi taji daga bakin da take zaton ba zai mata karya ba. Dan uwa shakkiki kuwa ai a zaton ta ba zai taba yiwa dan uwansa karya ba. Ai nan Asma'u ta hau kan wannan zance ta zauna. Taji dadin wadan nan maganganu na yaya baba. Kudi ta dunkulo daga jakarta bata san ko nawa bane ta rusuna alamar girmamawa ta mika masa "don Allah yaya yi hakuri ka karbi wannan a sayawa madam turare ban san da ita ba sai yau da muka gaisa da ita a dakin inna. Dana taho mata da tsarabar ta dabam. Kasan kuma halin kaninka zurfin ciki gareshi bashi da yawan magana.====***36***==== Hannunsa har rawa yake yi saboda murnar kudin daya samu daga gun asma'u inji wa yana da magana. Mu anan idan ya tsinke da labarin ki ba har sai mun gaji daji ba. Ko rannan daya zauna yana kuranta ki inna har tausayinsa ta ringa ji tace nidai Allah yasa yadda kake kaunar yarinyar nan ita tayi maka koda ravinta ne. Ya fada yana dariya. "Kai yaya inaga dai zolayata kake yi. Amma duk da haka naji dadin zancen ka. Kuma idan sani ya dawo ka fada mishi nazo nemansa baya nan. Sai kuma ka sanar dashi sakon Abbana na batun damam din idan yana da ra'ayi sai ya kawo credentials din nasa da sauri. Ta fada tana kokarin shiga matar data kawota. "Ina wane mutum. Inji auwalu ai kema kin san ba zai kiba. Yana dawowa zan gaya masa. Dana san inda yaje ma da can zan bishi in kirawoshi " karka damu ai ba abin sauri bane. Idan ya shigo din ka gaya masa. Direba yaja mota suka tafi. Har suka kule bai daina daga musu hannu ba. Tun daga soro yake kwallawa inna kira. Ta fito tana gyara daurin zaninta. Inna fito kiga abin data bani. Kudi ne masu yawan gaske. Mai iya cewa tunda yake bai taba rike irinsu ba. Suka zauna suna al'ajabi dama akwai masu kudi irin wannan. Shiya katse tunanin inna. Amma inna in kina son wannan daular ta dore to sai kinyi da gaske yarinyar nan auren sani take son yi amma shi yana gocewa saboda yaji tace bata son mai mata shine yayi saurin sanar da ita. Cewar yana da aure. "Yo in banda abinsa auren mace mai arziki irin wannan ai yana da dadi. Dubi fa alherinta yau dinnan kawai. Wannan in tazo cikinmu aimun warke. Kuma ma ince har addini an halarta auren mace don dukiyarta. "Inna cemun tayi fa babanta zai samar masa aiki a can saudiya in har zai yadda ya aureta. Allah inna ki dage kar wannan arzikin ya wuce mu. In har ya matsa ba zai yi ba kawai ki sashi ya saki waccan yarinyar tun da ai dama ke kika ga dama kika aura masa ita. "Saki a'a bazai yiwu ba ai kaga ga yara da take fama dasu. Inna yara ba sai in kula dasu ba. "Kai da Allah tafi can naka ma inace kwana biyu ne Amma kun kasa dasu saboda tsabar lalar matarka. Nifa bana son ana shiga harkar gidan. Kawai dai kinsan yadda zakiyi da wannan batun. Ya mike yana kunkuni. Baza ka ban komai a kudin da ka samu ba. A'a inna kowa ya rike nasa amma dai ki aika min da kayan shayin tunda naga suna da yawa. "To naji jeka zan aika maka. Ai wannan kaya masu yawa haka har Dija sai na aikawa. Labarin sani da Asma'u taji a wajen yayansa shita labartawa umminta. Ita kuma ta fadawa abbanta da kansa ya koma gidan su sani ya sami inna suka tattauna ya kuma nuna mata shi ba abinda zai hana shi aurawa sani 'yarsa in har suna son juna. Haka kuma ya dada jaddada mata batun sani ya kawo takardunsa domin a fara nemar masa aikin da ya alkawarta masa. Wannan sako shi kadai inna ta sanar wa da sani. Kansa tsaye ba tare da tunanin komai a ransa ba ya kai takardunsa gidan ambassador. Asma'u tazo sun gaisa. Har ma da mamanta shi dai yaga karrama wa ta ban mamaki. Abba sai fadi yake ai mun gama tattauna komai da innarka. Allah dai ya tabbatar da alheri. Da murnarsa ya isa gidansa sadiya na shanyar kayan wankin yaranta a tsakar gida taji kawai anyi sallama kafin ta amsa taji anyi sama da ita. Sani da tsananin murna ta koro shi ya dagata yana juyi da ita a tsakar gidan. "Yi hakuri yaya karka kada ni. Ya ajiyeta yace kyale shanyar nan kizo kiji abinda ya samemu Nan ya zayyane mata duk irin alkawarin da ambassador yayi masa. Ta daga hannun ta sama ta godewa Allah. "Allah ya tabbatar da alheri ashe ka kusan zama Alhajin saudiya. "Ni kadai banda ke ai wadan nan kyawawan yaran naki dake kanki in muka je saudiya sajewa zakuyi a dauka larabawa ne. Tayi masa hararar wasa. "Kaima ai kamar balaraben kake dame muka fita. Dazu ma sa'idu yazo yayi maka sallama shima batun tafiyarsa zaije legas gobe saboda shirye shiryen tafiyar. Ashe shima American zai tafi? "Eh can zai tafi. Bari inje in same shi kinsan Muna shirye shiryen auren sa dan kinsan abbansa yace bazai tafi ba sai da matarsa takardun tafiyar ma nata ake processing ba nasa ne ba. Nasa ai sun dade da haduwa. Itama amaryar makaranta ya samo mata. "Allah ya samu a danshinta. Wani irin kallo yayi mata "danshi wane iri na aure da kika zarta ta ko kuma na haihuwa da da kyar ta kamoki" "Na karatu ta bashi amsa a gajerce. Ajiyar zuciya kawai yayi domin yana tararrabin ranar da duk zata dago zancen makaranta. "Ai karatu Muna zuwa saudiya makaranta zan maida ke " "Allah yasa. "Baki yarda ba kenan. Ni na isa ai dai kana ji addu'a nayi. Bari in tashi in sami sa'idun na San ba zai wuce yana shagon auliya'u ba. Bari inje muyi sallama nima in sanar dashi alherin daya samemu. .=====***37***===== Inna tana yawan takura masa daya kai ziyara gidan su asma'u. Yana zuwa bai san neman aure inna ke tura shi ba. Baifi wata biyu da kai takardunsa wajen ambassador ba. Da kansa yazo har gidan ya kawo masa takardun shaidar samun makaranta da kuma aiki a jami'ar damam. Kuma nan da sati biyu suke nemansa. Ya juya wajen inna yace inaga sai a gaggauta daura musu aure kawai su tafi da matarsa. Domin itama ta samu cigaba da karatunta a can. Kafin sani yayi magana inna tai sauri ta cafe da cewa "Alhaji auren baiyi wuri ba. Karki damu bana bukatar komai sai sadakin kawai. Ai sani yanzu dana ne. Sani wani gami ne yake tsiyaya ta ko ina a jikinsa. Sai yanzu ya gane fassarar karramawar da akeyi masa a gidansu Asma'u kafin ya gama hadiye maganar auren da ake kokarin kaka ba masa sai jin sallamar ambassador yayi inna kuwa tana ta faman zuba godiyar dattijantakar da aka yi musu. Har soro ta raka shi. Ta dawo ta tarar sani zaune kamar babu jini a jikinsa tafin da tayi a kansa ne ya dawo dashi duniyar da inna ta saka shi a ciki mai rudarwa. Muryarsa na rawa "inna don Allah kiyi min rai na hakura da aikin indai sai na auri 'yarsu. Kuma inna yaya zanyi da sadiya don Allah inna ki bar wannan zancen zan nemi aiki anan ko ina arzikin mutum yana tare dashi" "Ka gama ubana" shiru bai bata amsa ba "nace ka gama jira nake ka tashi ka rufeni da duka. Tunda kaine ka haifeni ba nice na haifeka ba. Sadiya kuma da kake tambaya ta yaya zakayi da ita. Saika hadiye ta ka maida ita ciki shi zai tabbatar min da irin son da kake yi mata. Ina kokarin yi maka gata kana neman kayi mana sawarwara. To wallahi ka saurare ni da kyau wannan aure kamar anyi an gama. Kuma baba ya gaya mata karya kake da kace kana da aure baka da kowa baka da komai suma kuma wannan magana suka sani. Ya dago da hanzari ya kalleta. "Kalleni da kyau kuma ka furta mata cewa zancen iyalinka akwai su to ranka sai yayi mummunan baci. Idan an samu daukakar akwai wanda zai fita mora. Ba ita da 'ya'yanta ne zasu fi kowa cin gajiyar duk abinda ka samu ba. "Amma inna an taba boye wuta da hayakinta?" Wannan kuwa zata boyu lokacin da hayakin zai bulla kuma an samu ruwan kashe ta. Nan kuma ta sassauta muryarta kuma sani in banda abinka ni so nake in ta riga ta shigo gidan akayi auren kai kuma kafin nan ka kama aikinka ga kuma karin ilimi da zaka samu. Sai tasan da sadiyar da nata 'ya'yan. A lokacin kaga itama da nata 'ya'yan nasan babu yadda zata yi. Kuma irin son dana ga tana yi maka tsaf zata hakura ku zauna lafiya. To ai inna saboda hakan ne bana son na yaudare ta. Yo yaudarar 'yan mata a kanka aka fara ai inda sabo an saba. Kuma ban taba ganin inda auren ya lalace don an gane yaudara yaron yayi ba. Amma nasha ganin an fasa aure saboda yaro ya fadi gaskiyar lamarinsa. Mutane da kake ganinsu yanzu ba son gaskiya suke ba. Kuma in ba tsananin rabo ba duka-duka nawa kake. Ai babu ma mai yarda kana da yawan iyali haka. Na tabbata ka fada musu ba yarda zasuyi ba zasuga kawai baka son auren 'yarsu ne yasa ka fadi haka. Sai kuma ta fara sharar majina alamar kuka "in ka tona zancen nan sani ni ka ciwa mutunci " "Amma inna randa duk zancen ya fito mutuncin mu ba zai zube ba" " kai dai kyale ni dasu na San yadda zan bullo musu. Ai tana shigowa gidan nan na San lokacin da zan bullo da zancen. Zanyi kokarin nuna mata. Tsananin son da kake mata yasa kayi mata karya. Kuma kaga iyayenta dattijai ne ba zasu goya mata baya a wannan maganar ba. Tunda dama ita da baba sukayi maganar su. Ai sai ta fito a zancen yara kuma in banda kai da abinka ita da zata ji ka ajiye mace da yara ka dauketa ai ta san karshen so kenan. Ai mace ba abinda take so irin a fifita ta sama da wata shikenan ka gama da ita.**38***===== Shi dai kansa yana sunkuye bai samu damar bata amsa ba. Ya san indai fadi in fada ne ba zai taba kure innarsa ba. Saboda ita mutum ce mai son ganin abinda take son gani. Wanda kuwa bata son gani duk kokarin mutum bai isa ya sanya ta ganshi ba. Sai dai su dawwama musu amma ba zata taba daukar ra'ayin da ba nata ba. Ya san duk ta inda zai bullo mata ba zaiyi nasara akanta ba. Wani jiri yake ji yana dibansa. Idanuwansa na masa dishi dishi addu'a kawai yake ja a cikin ransa ba tare da yasan wacce yake karantawa ba. Saboda yawan karanta addu'o'in ne yasa kawai suke zuwa zuciyarsa ba tare da kwakwalwarsa ta san me yake karantawa ba. Ta sake cewa "ahaf zancen kake so kai yanzu kana fara aiki a saudiya akwai kuma wanda zai turkeka ai kaima daga nan ka zama babban mutum. Babu wanda zai sake titsiyeka. Sama -sama yake jin sauran maganar tata. Tunda ya riga ya gane cewa bazai iya canja mata ra'ayi ba ya daina fahimtar me take fada. Jikinsa a sanyaye ya mike ya fice daga gidan. Wannan karan kam har yaya kulu sai da sani ya roka akan ta rokar masa inna ta janye batun auren sa da Asma'u. Amma ta nuna masa yayi hakuri bazata kara shiga harkarsa da inna ba. Anan take bashi labarin irin artabun da suka yi lokacin data nuna son ya auri uwar kamalu. Data nuna rashin goyon bayanta ta zage ta tas ta kuma ce mata duk randa ta kara shiga maganar ta da danta to sai ta tsine mata. Har tana gaya mata ba wani ne ya haifar mata shi ba. Da za'a hana ta iko da abinta. Sani bai hakura ba ya sake nufar 'yan uwan babansa amma nan ma bai sami goyon baya ba. Baffan shi laminu ne ya zaunar dashi yayi masa nasiha akan biyayya ga uwa in har abinda ta saka kayi bai kaucewa shari'a ba. Tunda aure take so yayi ya hakura yayin don samun ladan biyayya a gareta. Sani yasan tsakanin innarsa da tsakuwa tsakaninta da dangin babansa. Sai ya kasa sanar dasu karyar data sashi yayiwa asma'u na rashin iyali a tare dashi kwata - kwata. Ya so su dai daita ita dashi kar kowa yasan zancen don gudun zubewar mutuncinta amma hakan ya faskara. Gidan sa ya nufa ba tare da ya san kalaman da zai gaya wa sadiya ba. Tun daga soro yake jin hayaniya alamar ba ita kadai bace a gidan. Ya shiga tare da sallama. Abokinsa ne sa'idu tare da amaryarsa zuwaira suka kawo masa ziyara. Shaf ya manta sun yi dashi zasu shigo yau domin ya kawo amarya gurin sadiya sannan kuma yayi musu sallama saboda tafiyar su America. A Washe garin ranar. Sadiya kallo daya tayiwa mijinta ta gane cewar nutsuwar sa da sauki. Ga wata zuvewa da yayi ta farat daya kamar ya kwanta rashin lafiya. Sa'idu ma yana mika masa hannu domin su gaisa gaisuwar ta tsaya a bakinsa. " malam baka da lafiya ne? "Lafiya ta kalau me ka gani? "Kai Haba ko dai zazzabi kake yi a tsatsaye. Amma baka ga yadda fuskarka ta fada ba. Kuma naga jiya har kusan magriba Muna tare baka gaya min baka da lafiya ba ". "Ka bari kawai inaga shirye shiryen tafiyar nan ne duk ya hargitsa ni. Ya juya inda zuwaira take zaune amarya sannu da zuwa. Kuyi hakuri kun shigo baku same niba. Na dan fita ne. Suka gaisa ya tashi ya shiga bandaki ya dan watsa ruwa a jikinsa tare da dauro alwala duk domin ya samu nutsuwa. Yana dawowa ya tarar da garar da sadiya ta shirya musu duk da rashin sanar da ita zuwan su da yayi. Gurasa ce ta mu ta hausa ta tirara ta amma maimakon taushe da aka saba ci da ita sai tayi miyar nikakken nama wanda ta nika shi a injin nika nama. Yana danyen sa sannan tayi jar miya dashi ta kuma kawo dankalin bature wanda ta fere ta yanka shi manya manya ta zuba a cikin miyar suka karasa dahuwa tare sai lemon citta data hada musu ga kuma yankakken lemo da aka jera musu akan filet.**39****====== Da irin wannan hidima da hikimar sarrafa dan abin da Allah ya hore mata take burge sani tare da fitar dashi kunyar bakinsa. Babu yadda za'ayi ka shiga gidanta bata baka wani abu da zaka sanya a bakinka ya burge kava. Koda kuwa lemon tsami ne da takan fere ta zuba a blander ta nika tasa sugar ta tace. Gashi dai duk da ya manta bai sanar da ita zuwan bakin ba amma tayi kokarin yin sabon abinci. Dukkansu sunci abincin sun kuma yaba mata. Duk da ita kam yaranta basu batta ta nutsu taci yadda ya kamata ba. Wannan kam inda sabo ta saba kusan kullum sai dare idan ta samu sunyi barci take samu taci abinci sosai da kuma nafilfilun ta sa'arta daya hatta kamal bai cika tashi cikin dare ba. Baifi ya tashi sau daya ba shima kuma ruwa kawai zata bashi ta dora shi a foo ta kuma saka sauran yaran suma suyi fitsari shi kenan shida tashi saida asuba. Amma fa da asubar da kyar take idar da sallah bai tashi ba amma shima da yasa nono zai koma to kuma ba zai kara tashi ba sai tara na safe. Hakan ke bata damar ta kammala hidimar yayyensa da kuma ayyukanta na gida. Bayan nan kuwa idan ya tashi to sai da daddare zai sake bacci saboda kazarniyarsa. Bayan baki sun mata sallama sun tafi ta kammala da yaranta da kuma sauran ayyukan gidan ta. Sannan ta dumfari maigidan nata da son jin abinda yake damunsa. Ba tare da murna a tare da shi ba ya sanar mata da fitowar takardun aikinsa da kuma na karatu. Harma da batun tafiyar nan da sati biyu Shiru baiyi magana ba. Ta daure tace "karasa min sauran maganar data saka bacin rai da tashin hankali" a dan firgice ya dago da kansa daga inda yake kwance tare da sarkewar murya yake magana "me aka zo aka gaya miki kuma me aka ce miki. " ba wanda yazo ya gaya mini komai fuskarka ce ta nuna min akwai matsala a tattare da tafiyar taka. Kuma na San dole ba zata rasa nasaba dani ba. Ta saura ra taji ko zaiyi magana taji shiru. Nan da nan kwakwalwarta ta hada mata 2da 2 suka bata 4 take ta gano inda matsalar take. "Inna tace ba zaka dani ba ko kuma inaga kamar zaka samu gata kamar wanda ka samu lokacin tafiyarka Sudan? " Kamar daga nesa yake jiyo muryarta tana gaya masa abinda ya kasa gaya mata. Shiru bai bata amsa ba ta danyi ajiyar zuciya. "Wacece ka samu kuma bana" shiru ya kasa bata amsa Ganin ta dan jima da masa tambayar amma ya gaza bata amsa ta mike da niyyar ficewa daga dakin domin itama ranta ya fara baci "Sunanta asma'u " taji muryarsa na fadi lokacin data tura kofar dakin tana kokarin ficewa daga dakin "Allah ya sanya alheri " ya tashi ya karasa bakin kofar ya kama hannuwanta ya dawo da ita cikin dakin sannan ya zaunar da ita a bakin gadon shi kuma ya tsuguna a bakin gadon har lokacin yana rike da hannuwanta bai sake suba. Ya kwantar da murya yace " Kiyi hakuri karatu

9 / 15