Author : Category : Home Of Novels
cikin aljihunsa ya dauko kudi daga ciki "ungo ya mika mata. Hannunta na rawa tasa hannu ta karba. "Kirga mu gani " ta kama kigawa Amma ba a nutse ba. Kawu yace nera dari biyar ne kuma kudin sadakin kine. An daura miki aure da yayanki sani. Ya dakata yaji ko zatayi magana yaji tayi shiru. Ya cigaba da yi mata nasiha. "Munsan ko a inane ke mai rufawa dan uwanki asirice. Kuma kowa ya lura da hankalinki munsan bazaki watsa mana kasa a ido ba. An daura miki aure da sani! An daura miki aure da sani! An daura miki aure da sani! Shi kadaine abinda kwakwalwarta take iya wassafa mata duk sauran zancen kawu sama sama take jinsu ta kasa ko kwakwaran numfashi. Shi kuwa ko ya kula da halin da take ciki ko bai kula ba. Sai nasiha yake ta tsaro mata. Yana dada nuna mata falalar yin hakuri da kama yadda da kaddara mai kyau ko mara kyau. Inna tace balle wannan ai kowa yasan kaddara ce mai kyau. Auren miji irin sani ai sai wanda bai samu ba. Magori kenan wasa kanka da kanka inna dai tana son son 'ya'yanta. Kuma a ganinta sunfi na kowa.======***20***====== Shigowar yaya kulu ne wanda yai dai-dai da fitar kawu da inna daga dakin wanda kuma ya bata damar hadiye wani abu daya tokare mata wuya. Sai a lokacin taji hawaye ya ya zubo mata. Ta fada jikin yaya kulu tana fadin INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN. Yaya kulu ta rungumeta tana fadin yi hakuri bari kuka. Duk abinda ya sami bawa da sanin Allah. Amma ni inaga hadin aurenki da sani Insha Allahu alheri ne. Cikin muryar kuka tace yaya baya sona nima bana son shi kuma yaya karatu nafa? Yaya kulu tace karatun ba inace kin dade da barinsa ba. Ba tare da sanin Dija na tsaye ba duk ta fayyace wa yaya kulu yadda duk akayi tun zuwan momi tambayar ta da tayi akan ta barta ta sata a makaranta har jarrabawar data zata. Take zaman jiran sakamako. Harda shirin da tayi na komawa gidan sanin da zama domin ta samu damar komawa makaranta duk ta fada mata. Zancen kudin da tabawa sanin ne kawai bata fada ba. Yaya kulu tayi Murmushi tace "to in banda abinki keda zaki gida matar gida tadan sammiki guri ki zauna in bataga dama ba ta kore ki. Allah ya musanya kece da gidan gaba daya me kuma yafi haka? Ni nasan Sani yana sonki koda kuwa kauna ce ta jini amma nasan duk wani buri naki zai taimaka miki dashi. To kuma ke matar malamin makaranta har a gaya miki karatu. Karatu ai sai kinfi Mongo park " maganar yaya kulu ta sanya ta murmushi ganin hakan ya sanyaya ran yayan. Ta dora da cewa "kuma ki kalli kanki a mudubi shi sanin inba don darajar zumunci ba ya isa a bashi ke?" Muryarta a dan raunane wadda ke nuna alamun kukan da tayi ya dan sa zuciyarta tayi sanyi fiye da sanda taji maganar tatsuniyar aurenta. Cikin sanyin murya tace " kai yaya to dame na fishi? "Kaji min shakkiyya ina kushe shi kina kare shi. Kuma kina kukan an aura miki shi. Itama yayan ta amsa mata. Amma duk da haka zaka gane farin cikin da ke tattare da kalamin nata. Saboda ganin canjin da tayi a tare da sadiya wanda yake nuna alamun ba zata sha wahala wajen rarrashinta ba. "Kai yaya ba haka nake nufi bafa. Ta fada tana mai jin kunya. Dija ta juya da baya ba tare da sun ganta ba. Ta samu inna a waje daya ta zayyane mata labarin karatun da sadiya tayi a gidan aikin da aka kaita. Inna ta tabe baki tace "duk ya zama na banza tunda dai sai yadda naso za'ayi" Yinin biki ya kacame a gidan amarya huwaila da angwaye auwalu da sani duk wannan badakala da akeyi sani baida masaniya. Shi dai daga daurin auren auwalu wucewa yayi shagon abokinsa sa'idu tare suke koyarwa a makarantar islamiyya. Dake unguwarsu. Shima yazo hutu daga inda yake nasa karatun a jami'ar maiduguri. Samun dakin da yayi a bude ya shige ya cire babbar rigarsa ta angwanci yayi kwanciyarsa. Da yaga tunanin abinda mahaifiyar zainab tayi masa yana neman ya haddasa masa ciwo. Sai ya mike ya dauro alwala yayi nafila. Bayan ya sallame ya dora da karatun kur'ani mai girma. Ya gama baqara ya fara ali'imrana yaji himma ta dame shi ya ajiye Alqur'anin son ya dan kishingida barci mai nauyi yayi awon gaba dashi. Rabon da ya samu barci tunda aka fara rigimar aurensa da zainab. Duk da dai daki bai koma gwauro ba amma yaji ba dadi da wulakancin da akayi masa. Yana kwance yayi mafarkin abokansa sunzo suna ta neman sa wai don su gaya masa an daura masa aure amma basu ganshi ba. Hayaniya ce ta tashe shi yaji ana gashi nan. Mafarkinsa mai dadi suka katse masa. Sa'idu sale ne ya daka masa duka yace "tashi duk mun hada gari Muna yawon nemanka ashe kai kana nan. Jin dadi ma kake harda barci " "Yo mai zai hana shi barci yasan abinda ya taka banda takalmin kafarsa. Inba haka ba ace an hana mutum aure amma har ya samu sararin yin barci" inji wani daga cikin mutanen da suka shigo dakin "ka tashi muje muyi gaisuwar surukai mu kuma fara shirin saida fura. Shi dai inda kasan rakumi da akala. Haka ya dinga biye musu. Hatta babbar rigarsa sai daya daga cikin abokan ne ya saka masa. Tunanin sa daya in ya tuno irin cin mutuncin da mahaifiyar zainab tayi masa kwana uku daya wuce yasan ba dattijuwa bace wannan ya sanya masa tsoron zama da 'yarta yasan bazai samu zaman lafiya da ita ba. Yana cikin wannan tunani har suka iso gida. Gaba dayan su suka dunguma cikin gidan inna. Suna shiga cikin gidan mata suka lullube shi da guda "ga Ango ga ango" wata mata ta daddage ta rangada masa guda a kansa. Shi dai dariyar yake kawai yake yi "ga angon sadiya" inji wata abokiyar wasansa data fito daga cikin rumfar inna. "Sadiya kuma wasu daga cikin abokansa suka fada wani daga cikinsu yace na dauka sunanta zainab. Shi kam ogan angwaye tsananin mamaki ya hana shi magana. Kansa gaba daya ya dauki caji. Ya kasa tuna wacece sadiyan da inna ta aura masa fitowar yaya kulu ita ta warware masa duk abinda ya faru. Farin ciki da kuma mamaki su suka taru suka cika masa zuciya wanda kuma zuciyarsa ta gaza boyewa har saida ya nuna a fuskarsa. Ya kasa yiwa yaya kulu magana. Fahimtar halin da yake ciki ya sata basu umarnin shida abokansa suje su cigaba da zaman angwancinsu. Masu taya shi murna da masu taya shi mamaki a cikin abokansa suka rankaya suka fita zuwa shagon sa'idu don cigaba da zamansu na angwanci.=====***21***====== Kawu labaran yaso ya daga tarewar sadiya koda zuwa sati na sama don a shiryawa sadiya kayan daki. Amma inna ta dage a tare kawai a Washe gari. A zaton kawun tunda kudin aikinta na hannun ta dasu zata hada mata kayan dakin. Tunda shi kam sadakin daya biyawa angwaye da kyar ya hada shi. Inna kuwa tayi haka ne dan kar kawu ya fahimci kudin sadiya dai babu su duk da tana da bakin da zata kwaci kanta. Amma duk da haka bata son a daga maganar. Sabuwar katifar da yaya kulu ta daure ta siya zata gyara dakinta ita aka dauko aka sa mata a dakinta ko arzikin zanin gado bata samu ba. Kudin sadakin ta dashi yayan ta kukuta tasai mata ledar tsakar daki da kuma 'yan kayan girki dana anfanin tsakar gida. Bayan ta gama da wannan ita ta daddage tana ta faman tattausar sadiya don ma tayi sa'a ita yarinya ce mai jin rarrashi da kuma saurin karbar nasiha. Aure kamar na 'yar tsana haka aka tattara sadiya aka mikata gidan da sani ya tanada domin rayuwarsa da zainab sai dai cikin hukuncin ubangiji ya zama nasa da kanwar sa sadiya. Amarya huwaila ta tare a sashen ta na cikin gidan inna da jerenta kamar zai zuba a kasa don yawansu. Ga kuma tarin gara kamar ta 'yar sarki. Saboda mahaifiyar ta irin matan nan ne masu nema don su huce takaicin su. Ga kuma mahaifinta shima yana da abin hannunsa. Wannan dukiya da aka nannago mata ita ta kara mata farin jini a wajen inna da Dija. Sadiya zaune a tsakar dakinta wanda yafi kama da zaure saboda rashin komai a cikinsa. Kan ledar tsakar dakin take zaune inda su yaya kulu suka tafi suka barta da tarin nasihohi da kuma ban baki da sukaita zubawa kamar sa ari baki. Ita da wasu makotansu da da dangin mahaifinsu. Har yanzu bata daina mamakin wai itace matar sani ba. Murna zatayi ko bakin ciki bata tantance wanne zatayi ba. Bata fita daga wannan alhininba taji muryar maza sunai mata sallama. Dada kudundune kanta tayi ta kuma amsa musu a ciki. Su hudu ne ta cikin mayafinta ta shaida su. Dukkaninsu sadiya ta sansu. Abokanan sani ne tun wanda sukai primary tare. Daya daga cikinsu tare suke koyarwa a islamiyyar nan unguwarsu. Gaba dayan su suka zauna a tsakar dakin suna masu fuskantar inda ta zauna. "Amarya bude fuskar mana mu ganki kema kiga angon naki " inji daya daga cikin aboka nansa. Ita dai tayi shiru bata matsa ba. Wani daga cikinsu ya bada umarnin a bude taro da addu'a ta cikin mayafinta ta daga hannu sukayi addu'o'i masu nagarta suka kuma nemawa ango da amarya zaman lafiya. Tare da ita suka shafa. Aka fara barkwanci irin na angwaye da amare duk da dai ita kam babu kowa a tare da ita sai wata 'yar yar mijin yaya kulu. Da suka zo bikin tare kusan sa'ace ga sadiya shine dalilin da aka barta ta tayata zama kafin a gama sayen baki. Amarya taki magana balle ta bude fuska. Abokan ango sun taya da kudi amma batayi magana ba. Ko nawa suka fada saita girgiza musu kai har suka gaji suka mika biro da takarda wai ta rubuta musu ko nawa ne bakin nata. A wasance wani daga cikinsu ya aikata hakan. Amma ga mamakin su sai suka ga ta mika hannu ta karba. Tayi rubutu a ciki ta mika musu. Sani yayi bismilla ya bude ya karanta sakon amarya kamar haka "na saida bakina in har yaya sani yayi min alkawarin ci gaba da karatu na" tofah kai sani wannan amsa a wajenka take Duk suka tuntsire da dariya. Sani ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa duk sunai masa dariya. Fadi yake aiki babba ya same ni ku dariya ma kuke yi.
***22***======= In za'ayi magana da gimbiya mutum nutsuwa yake yi. Ya dai-daita zaman hular kansa ya ajiye babbar rigar tasa a kan cinyarta "ungo wannan rike mu gani rigar girma ce. Kinsan sai girma ya hau kanka kake mallakarta " ya juya inda abokansa suke suna ta tintsira dariyar wannan drama da ango ya gwagwafe yana yiwa amarya. "Kalle su duka wa kika gani da shiga irin tawa. Ai sai ni da Allah ya martaba yau dinnan. " ita dai da kyar ta kunshe dariyar da take cikinta. Mamakin yayanta take dama yana sake wa da mutane har ya ringa abin dariya irin haka. Suma abokan mamakinsa sukeyi domin basu taba ganin kalar wannan sanin da suka gani yau ba. Wani irin tsugunno yayi a gaban sadiya wanda yai kama da mai yinsa yana gaban principal ko kuma gaban mahukuntan sa a lokacin da yayi laifi. Saboda nutsuwar da yayi. Ya kamo hannuwanta guda biyu ya rike cikin nasa. Ya dai-daita muryarsa ta hanyar gyara ta sannan yace " ni sani mijin Kanwata sadiya nayi alkawarin zan bar mata ta Kanwata kuma masoyiyata tayi karatu har iya son ranta. Mutukar yin hakan bai kaucewa shari'ar musulunci ba. So help me ALLAH. Dukkan ku ina son ku shaida wannan alkawari da nayi mata." "Amin kuma mun shaida " duk suka amsa cikin dariya. Bayan an shafa sadiya ta dan janye mayafin data lulluba har ya sauka daga kanta gaba daya saida sukayi tasbihi saboda kyawun hallitar sadiya da suka gani. Dakin ya dauki shiru na dan wani lokaci. Mamakinsa suke yi da ya tsaya wai har saida innarsa ta gano masa sadiya shi bai ganta da kansa ba. Shi kansa sani sai yaga kamar bai taba ganinta ba sai yau. Wani irin kyau ya lura tayi da bai taba tsammanin akwai mai irinsa ba. Bai San sanda ya jawo mayafinta ya dada rufe mata fuska ba. Gaba daya suka tuntsire da dariya domin sun fahimce shi kar a kalle masa mata ne ya sanya shi yin hakan. Sa'idu sale ya fara mikewa yana fadin "inaga kamar an sallamemu kar ango ya fara kora da kara tunda dai yayi da hali mun gani" duk suka mike suna yi mata sallama. Dayaje raka sune kuma suka bashi kudin da suka tanada wanda abokanai ke tabawa domin sallamar 'yan mata wajen saida fura da kuma alibidi. Banda na sayen bakin. Shi wannan hadashi sukai suka ajiyewa sadiya. Sannan suka yi mata sallama suka fita. Ya fita raka su bai dawo ba sai bayan kimanin awa daya. Saboda sai da Abokanan sa suka sake hada kudi suka sai masa kayan shayi da biredi da kuma kazar amarya.
=====***23***===== Ya shiga ya sameta zaune inda suka fita suka barta. Sani ya jima tsaye a kanta yana kallonta kafin daga bisani ya daure yayi magana da muryar da shi kansa baisan yana da itaba. "Tashi kiji magana zamu yi Kanwata. " ta gyara zamanta sosai ta fuskance shi ba tare da tace komai ba. Ya sake yin gyaran murya yace mata "Muna da tarin maganganu dani dake. Ga kuma gajiya da kike tattare da ita. Na kuma san harda yinwa. Saboda haka zaba mana wanda zamu fara yi " Muryarta adan dashe ta nuna alamun ta dade batayi magana ba tace " mu fara maganar da kake son muyi". Ta rasa dalili da yau kadai taji kunyarsa ta mutukar kamata "anya ayi haka inaga mu fara da sauke nauyin dake kanmu. Kinyi sallar isha'i? Daka ta amsa masa. "Very good yanzu je kiyi alwala kizo" A famfon tsakar gidan ta daura alwala yaja su sukayi sallar nafila. Tare da addu'o'in da suka kamata ango mai ilimi ya gabatar. Da wayo da dabara irin na wanda ya girme maka sani yaja hankalin sadiya taci abincin da ya shigo dashi. Ganin ta fara hamma yasa shi ya kwantar da katifar da take jingine a bangon dakin yayi mata matashi da babbar rigarsa ya sata ta kwanta. Kusan kwana sani yayi yana nafila yana godewa Allah na wannan canji da yayi masa. A gaskiya yaji hankalinsa yafi kwanciya da auren sadiya sama dana zainab. Washe gari su yaya kulu ne suka kawo mata akwatin kayanta na gida. Ita kam ganin akwatinta na gidan momi lafiya kalau tunda ta kulle shi da lambasted. Yafi faranta mata rai saboda kayan cikin sunfi kayan lefen da aka hadawa zainab yawa da kuma daraja. Ga kuma sarkarta full set mai dauke da abin hannu zobe sarka da dankunne. Gami da dankunnenta idon bazawara da sarkarta coka. Wannan duk alherin momi ne da kuma kudin da Dadi ya bayar a saya musu gwal ita da Amira a wani zuwa umra da suka yi. Yaya kulu tana dada tausarta take cewa kiyi hakuri yanzu zan koma gida akwai tumakin Abdurrahman da yake kawo a sayar aga koda gadon ne a saya miki da kudin" Ta numfasa Allah ya kyauta halin son zuciya. Yanzu haka na baro su suna ta rubibin raba garar huwaila bama wanda yake ko zancen naki kayan dakin. Wai ace abin duniya ya rufe wa dan adam ido har ya manta da darajar zumunci " sadiya dai batayi magana ba ta sake nisawa. "Kiyi hakuri kinji kawu ma yace bari yake gida ko anfanin gonarsa ne ya sayar ya dan hado miki gara kodan a taimakawa shi sanin" anan ma batayi magana ba. "Inna ce ta takura masa yayi auren nan amma ko ficika bata taimaka masa da ita ba sai ta auwalu take yi. In anyi magana tace ai yana koyarwa. To albashin islamiyya har wani abu ne da zai taimaka ma harkar aure. Kuma ma ince tana sane da cewa tunda ya koma makaranta scholarship ce take a gaza masa. Islamiyyar ba sai yazo hutu ne yake dan s............... shigowar sani dakin ce ta katse mata magana. Ya durkusa har kasa suka gaisa tana bashi baki akan yadda auren ya kasance. Da Murmushi a fuskarsa ya dan saci kallon sadiya yace "anya yaya ba gara da haka ta kasance ba. Nifa hankalina yafi kwanciya da hakan ta faru" "Kai ka ganmu da shakiyan yara ko dai dama da wata a tsakaninku ita jiya bayan daurin aure har kare ka takeyi a gaba na. Yanzu kai kuma kawo kana murna da auren dole da aka yi maka" dariya ya saka Yayin da sadiya ta rufe fuskarta don kunya. Yaya tayi murna tace Alhamdulillahi wannan matsalar ta kau sai muji da ta gaba. Tunda dai ma'aurata suna son juna ai shikenan " "Kai yaya Allah ni ba ruwana shine fa" "Eh na yarda ni din ne" sani ya bata amsa. "Nidai bari kuka inje inga yadda za'ayi a samo muku 'yan kayan amfanin gida" "Mh yaya ina zuwa bari na baki sako". Ta jawo akwatinta na gidan momi wanda ke gefenta sarkarta full set ta dauko ta mikawa yaya kulu "Gashi yaya ki sayar sai kiyi duk abinda zakiyi dasu" " anya kuwa ayi haka ke kuma ba zakiyi kwalliya da kayan ki ba. Kuma ba inace sarkar da Hajiya mariya ta saya miki ce ba."? "A'a ta bata amsa wannan wadda Dadi ya saya mana ce nida Amira. Ita momi kinga wadda ta saya min kuma yaya wannan din ta ishe ni sawa. Kuma ma kar inzo ban mora ba gwal da bashida wuyar faduwa". Sadiya bata bata