Author : Category : Home Of Novels
daga babban layi sai a zo a saya. Wasu ma in zasuyi biki ko suna. Sukan bata tayi mai yawa. Dan asusu ta samu take tara kudinta da niyyar ta saka su walid da imam makaranta. Wata rana taje ta gaida yaya kulu kamar yadda ta saba tanayi lokaci-lokaci ta sauka daga hayis. Taga signboard na wata makarantar koyon dinki da aka bude anan unguwarsu. Ba tare da bata lokaci ba. Ta shiga ta tambaya aka gaya mata nawa ake biya. Ta karbo form ta dawo gida. Ga koshi ga kwanan yunwa. Kudi dai da zata shiga makarantar nan tana dasu. Ga kuma su walid 'yan shekara biyar da taso su shiga makaranta wannan shekarar. Tunda karatun da ta koya musu a gida ba makarantar kudin da baza su iya shiga ba kuna radam su zauna. In ta gwamnati ce kuwa ko dan aji uku ba zai nuna musu komai ba. A dan lesson din da tayi dasu. Rashin sanin iya abinda ya kamata yara su koya a kowanne zangon karatu yasa ta tsallake ba tare da ta sani ba. Ga haddar da suke yi A wajen malam mai salati wadda kamal ne kawai bai fara zuwa ba. Ga kuma islamiyya da suke zuwa. Ai yara kam karatu radam ba Arabi ba ba boko ba. Kamar yadda ta saba bata cika shawara da kowa ba don gudun tonan asiri. Diary ta dauko ta rubuta matsalarta. Takan ji damuwa ta ragu a zuciyarta duk sanda ta rubuta ta a dan littafin nan. Da daddare kuwa istikhara tayi ta nemi zabi a wajen RABBIL IZZATI. Washegari da ta tashi kuwa sai taji hankalinta yafi kwanciya da ta shiga makarantar koyon dinkin nan. Tun da dai karin samun kudin shiga ne. Ta san Idan yara suka fara makaranta wanki da kuma lemon ginger bazai rike suba. Kuma ko banza ta huta da wankin nan mai azaba. Da wasu zasu kawo maka shi ba sabulun kirki sai kaya masu uwar dauda kayi ta dirza kafin su fita. Inka gama kuma ace za'a aiko ma da kudin. Wani haka zai mula bazai biya ba. Kowacce karuwa bata zuwa sai da matsala. Ita wadda ta hararo yaya zata yi da yara in ta fara zuwa makarantar. Har ta hakura saboda bata ga yadda zata yi da yaranta ba. A wannan jumma'ar taje gaida gwaggon Rahina kamar yadda ta saba. Lokaci-lokaci tana jin dadin hira da tsohuwar nan. Bayan sun gaisa labari ya kawo labari har take bata labarin makarantar data so shiga amma saboda yara ta hakura. "Wane irin hakura ba dadin ji. Gwaggo ta fada. Cikin murya mai nuna alamun rashin jin dadi. "Tattara su ki dinga kawo min su har shi wannan da kika mannewa kin ki rabuwa da wahalar sa sai anyi magana kice wai maraya ne. In ba iya shege ba ace yaro ya haura shekara biyu amma bai wuce goyo ba. Duk kawo su. Suma samu haddar ta dada nisa har shima wannan din. "Amma gwaggo baza su wahalar dake ba. Babu wata wahalar wa. Kuma wata uku kamar yaune. Yo ni duk wanda yayi min a cikinsu ramawa zanyi bazan yadda a ce ni babba bace. Dariya suka saka tare. Ta dan dada kaskantar da murya "Amma gwaggo banda kamal shi sai in dinga tafiya dashi. "Har shi zaki ajiye. Duk wannan makon nasa da kema naki ajiye shi zakiyi. Dama ina cike dashi rannan da kuka zo kika shiga bandaki ya tsaya a kofar bandakin duk sai da ya hada gidan nan. Malam tun daga soro ya taho yana tambayar meya same shi. Ni dan haushi ma kasa magana nayi sai murtala ne yake gaya masa abinda ya faru. "Kai gwaggo sa ido ne kawai irin na murtala kuma shi da yake kawu ai baya biye muku ba tunda ke bakya auren. Haka kuwa akayi da wannan shawara ta gwaggo taci gaba da zuwa koyon dinki. Da sauran kudin da kuma ciniki ginger na wannan zafin ta hada ta sai keken dinki ta ajiye a gida. Allah na taimakon duk wanda ya taimaki kansa. Sadiya wata iri ce. Duk abinda tasa kanta koyo to kuwa sai ta zarce makadi da rawa. Ai kan kace kwabo ta koyo yanka da taku. Kai ganin haka ma a maimakon wata uku da tai niyyar yi sai. Sai kawai ta biya ajin kos din wata shida. Kwalliya kuwa ta biya kudin sabulu. Sadiya ta fito a matsayin kwararriyar tela mai daraja ta farko wato fist class inji masu digiri. Kamar da wasa ta fara dinki. Da yake abin na Allah ne kafin karshen shekarar nan sai da aka santa da dinki a unguwarsu. Wata karin fasaha data samu daga gareta shine dinka kayan 'yan kanti abdulsalam dan wajen yaya kulu na uku ya kawo mata ziyara. Sai taga wani yadi mai kyau a jikinsa. Ta tambaye shi ina ya sayo ya gaya mata a nan kofar wambai ake kawo su a kayan gwanjo amma sababbi ne. Shiya rakata taje ta siyo domin ta dinka wa su walida 'yan riguna. Wani littafin mother care ta samu a wajen sister mai dauke da hotunan kayan yara masu mutukar kyau da kuma tsari tana dubawa ta samo kalolin riga da siket da kuma dogayen riguna iya gwiwa na yara masu kyau. Da yadin nan da ta sayo ta gwada dinka wa. Haba wai aida ta sa musu a jikinsu kai kace 'ya'yan turawa ne dan kyau da suka yi. Ai wannan shi ya zamo mata mai talla shi ke da riba. Malama umma ita ta fara tambayarta inda ta samo musu riguna masu kyau. Har tana fadin idan ba tsada in sayo wa 'yar kanwata. Ta gaya mata cewa dinka wa tayi. Tayi mamaki mutuka. Tace "dama har da kayan 'yan kanti aka koya muku a makarantar.? Ta amsa mata cewar karanbani kawai tayi ta dinka wa yaranta. Ta yaba da fasahar sadiya matuka. Itace kwastoma ta farko a wannan cinikin. 'yan unguwa suka yaba da kayan suma aka dinga zuwa saye. Da wannan ta fara. Shima kuma tana samun ciniki matuka da alheri akai. Wanda take sayen yadi a wajen sa kuwa da ya samu sababbin yadudduka zai turo yaronsa har gida ta zabi wadanda take so ya karbo masa kudinsa.=====*****55*****===== Bata tsaya akan kayan mata ba kawai. Ta gwada yanka kayan kanti na maza. Anan ne ma ta dan sha wahala kafin ta gano yan kansu. Suma sai gasu sun shiga jerin kayan sayar warta. Ganin ta samu 'yan kudi masu dama sai tasa yaranta zuwa makarantar dasu Amir suka yi. Wacce kuma itama nan ta rubuta jarrabawar ta. Makarantar ta dada kyau an kawatata. Mai makarantar balarabiya ce amma sun dade a Nigeria ita da mijinta. Makarantar nada kwazo matuka da kuma sababbin hikimomi da dabarun koyarwa hadi da kayan karatu masu inganci. Ta shiga cikin makarantar tana nan kamar yadda ta santa sai dai an dada kawata ta an kuma kara wasu ajujuwan da kuma ofis na malamai. Wajen shugabar makarantar suka shiga ita da kyawawan yaranta guda biyar masu kyakkyawar sutura. Sun gaisa kuma har madam ayush ta gane ta. Tayi mamaki kwarai data ganta da yara ta kuma gaya mata duk nata ne. Ta janyo hannun walida da shukra tana fadin "beauty I like your dress " murmushi kawai suka yi. A zatonta ma basu ji me tace ba. Cikin turanci ta Tambayesu sunayen su da shekarun su suka gaya mata. Taji dadin ganin yaran suna jin turanci tasan matsalarsu zata zamo karama wajen fahimtar karatu. "Who bought this dress for you? Ta sake tambayarsu ga mamakinta sai taji shukra ta amsa mata "our mummy made it her self. "You did? Ta juya akalar tambayarta zuwa wajen sadiya. Dariya tayi ta bata amsa. Madam Ayush ta yaba da yanda rigar ta tsaru. Simple da ita amma dinkin ya dinku matuka. Bashi da wata tawaya kai kace dizaina ne. A lokacin su walid da imam shekararsu bakwai. Shukra da jidda da kuma walida shekararsu shida sai kamal me shekara uku da rabi. An yi musu jarrabawa ai kuwa taga amfanin koyarwar da tayi musu a gida. Aka gwada su aikin 'yan aji daya suka cinye. Kamar wasa aka ce bari a gwada su na 'yan aji biyu shima tas suka cinye. Aka sake basu na 'yan aji uku shima tsaf suka lashe. Aka bada ta 'yan aji hudu shima suka ci fiye da rabi. Tofa madam Ayush ta yaba da kokarin yaran matuka da kuma wannan sakamako nasu. Ita dai sadiya ta nuna tafi son a saka mazan aji uku matan kuma aji biyu. Haka kuwa aka yi. Aka bata lissafin kudin makaranta na littatafai da kuma kayan makaranta. Tofah ba hawan ba saukar inji madugun fulani. Ba samun makaranta mai kyau bace matsalar. Kudin da za'a biya mata shine babbar magana. Kudi kam sun shallake tunanin sadiya. Dan abin data tanada ba zai samata yara biyar a wannan makarantar ba. Ta dan yi jim sannan tace da madam ayush "inaga in saka manyan in yaso ko badi sai in saka matan. Da wannan shawarar taje ta biya kudin a wajen biya. Amma da taje karbar litattafai sai aka gaya mata idan ta gama madam tace ta same ta a ofis. Ta koma ofis din ta same ta. Madam tace "da gaske ke kika dinka rigar jikin yaranki.? Ta amsa da cewar ita ta dinka Harma data jikin yaran maza. "In that case I know how you can pay your children 's school fees. Tana fada tare da murmushi a fuskarta. Kije ki kawo min sanfur ns kayan makaranta a dinke in gani. Sai in baki kwangilar dinka mana uniform. Dama muna son mu canja uniform din makaranta. Da murnar ta tayi godiya sosai. Duk maganganun da suka yi da turanci suka yi su. Daga nan kuwa kasuwar sabon gari ta wuce. Ta shiga inda ake sayar da yadukan dinka wando na maza da kuma yadin shirt. Tayi ta dubawa har daga baya ta tsaida ra'ayin ta akan wani yadi mai dan kauri kadan ruwan toka da kuma yadin shirt fari mai layi layin ruwan toka a jiki. Ta sayo ta hada ta dawo gida. A daren kuwa ta dauko littafin nan na mother care da take daukar samfur -samfur na dinki a ciki. Ta duba har dai ta tsaya akan wata riga da siket da ta gani. Rigar shirt ce amma sikert din ya zarce gwiwa mai manyan tattara. Wadda aka dinka ta iya gwiwa daga nan kuma aka barta. Hakan yasa siket din ya baje daga kasa. Bayan riga da sikert din sai ta hada da wata yar falmaran kalar siket din wadda za'a dora akan shirt din. A jikin falmaran din ta baya aka yi belt wanda za'a ja ya bada shep mai kyau ba tare da ya kama jiki ba. Ta hada da wani samfurin neek tie wanda ba daura shi ake yi ba. Za'a dinka kamar wanda ake daurawa. Amma shi sai ta dasa roba a ramin wuyan yadda yaro zura shi kawai zaiyi. Mazan kuma wando da riga ta dinka musu. Shirt mai dogon hannu da kuma wandonta suma hadi da neek tie din. Da kuma falmaran irinta 'yan matan. Washegari da hanzarinta ta isa makarantar madam ayush tayi mamakin ganinta da wurwur haka. Sannan kuma ta yaba da samfurin kayan data kawo mata kai har ma kalar ta yaba kwarai. Nan akayi lissafin yawan kayan da za'a dinka da kuma farashin kowanne. A gaskiya sadiya bata taba alfahari da kanta irin wannan rana ba. Ranar ta dada yarda da indai ka tashi nema to kuwa allah zai taimake ka. Kudin da aka biya ta a wannan lokaci ba kadan bane. A yadin ma sai da ta sami riba. Sannan kuma ga kudin dinki da aka biya ta. Kudin makaranta tsaf suka fito daga hannun mai makaranta abin da ta biya kuwa sai dawo mata dasu akai. Nan ta biya kasuwar sabon gari ta saro yadin da zata yi amfani dashi da kuma sauran kayan dinki. Ganin ta sami dan canji tayi niyyar yi musu 'yan saye- sayen bukatun gida da suke da bukata. Washegari mota ta hau ta wuce kasuwar rims. Dai dai inda aka sauke shagon wani mutum ne da yake saida kayan turaren wuta dan maiduguri. Nan take wata idea ta fado mata ta yanda zata dada samun kudin da zata yi hidimar gidanta. Ta san dinkin uniform ba zata kuma samun mai yawan na yau ba. Tunda wannan karon uniform din aka canza gaba daya. Saboda haka gaba daya makarantar kowa zai saya. Nan gaba kuwa sai dai masu bukatar canza nasu ko kuma sababbin dauka. Fiye da rabin kudin nan ta zaftare ta sari kayan hada turaren wuta irin su hwi marshush sandal gab-gab. Aya da kuma kayan turaren humra. Dan canjin dashi tayi musu dan cefane da ba zai haura musu sati ba.=====*****56*****===== Makarantar da su walid zasu shiga cikin hutu suke. Amma saura sati biyar su bude. Haka nan ta kama dinki ka'in da na'in. Dan gajiya kam taji jiki. Amma tunanin irin nauyin 'ya'yan dake kanta da kuma nauyin alkawarin data dauka. Shiya ke dada karfafa mata zuciya abisa aikin nata. Ta dau hutu a wajen malama umma wacce ke mata karin litattafan fiqhu hadisi da kuma tilawar alkur'ani. Hatta da nafilolinta bata samu damar yinsu ba a wannan lokaci. Malama umma tace wannan sana'ar ma da take ibada ce domin ba dan ta tara a bin duniya take ba. Ko domin ta sayi kaya na alfarma. A'a tana yi ne don kulawarta akan yara. Farilla ce dai ta nuna mata komai ayyukan da suka sata a gaba ta tabbatar ta gabatar akan lokaci. Ana gobe za'a bude makaranta bata runtsa ba. Amma Allah cikin ikonsa da kaya seti dari biyar ta nufi makarantar. Kowanne dalibi set biyu haka ta kwana hada su guri guda. Madam Ayush kam ta yaba kwarai da ganin kayan da bata tsammace su yanzu ba. Ga wani abin burgewa a gefen siket din 'yan matan sai tasa roba a gefe da gefe wacce ta boye ta a cikin kalmasar siket din. Wadda idan yayi kadan ba sai an bude ba robar zata bude da kanta. Haka shima wandon mazan tasa roba daga bayan wandon. Yadda koda yayi yawa ba sai an nemi belt ba. Rigar kuwa sai tayi kalmasa hawa biyu. Idan tayi kadan farkewa kawai za'ayi ta karu. Ta matan kuma wato manya yan sakandire sai ta dan take ta daga wajen kirji zuwa ciki inda ta bada shep mai kyau ba kuma tare da ta dame ba. Kaya dai kam sun yi kyau da tsari. Mai dinki kuma ta cafki kudinta. Yara sun fara zuwa makaranta saboda haka hayaniya ta ragu sosai a gidanta. Bata koma ta zauna ba. Bayan sun tafi da safe zata gyara gidanta tsaf sai kuma ta hada lemon ginger ta mika wa mustafa mai shago. Malam mai salati a cikin almajiran sa ya samo mata wani almajiri mai hankali da yake shigowa yana taya ta da wasu ayyukan kamar wankin yara da kuma wanke- wanke da aka kwana ta yaba da tsaftar sa sai ya zama na har wanke cittar lemo shi yake mata ya kuma dura a robobi. Samun karin lokaci sai ta fara sana'ar turaren wuta Haba wa unguwa ta dauki kamshi makotanta har cewa suke su ko basu saya ba. Kamshin data bada musu ya ishe su. Amma shima fa tana farawa kamar an buga tambari ko da yake shi hafsa ce 'yar wajen malama umma ta dauka ta shiga gida-gida tana talla tana kuma gaya musu gidan da ake sayarwa. Har kuwa gidajen babban layi sai da takai. Cinikin ma yafi yawa a can. Su walid da 'yan uwansa karatu kawai suke yi. Ga kwakwalwa ga kudin biyan makaranta mai kyau ai shikenan sai himma kawai. Kullum basa tasowa daga makarantar bokon nan sai biyar da rabi na yamma Zasu shiga aji karfe takwas na safe su fito break tara da kwata. Sai goma su koma su fito karamin break sha daya da kwata su koma sha daya da rabi. Sai kuma su tashi karfe daya da rabi suyi sallar azahar a jam'i daga wannan lokacin har karfe uku kowa za'a kawo masa abinci daga gida suci su kuma yi wasa. Uku dai dai za'a koma aji masu home work suyi wanda basu dashi suyi karatu. Hudu saura kwata zasu fito suyi sallar la'asar bayan nan kuwa sai a shiga karatun islamiyya a tashi biyar da rabi. Wani kuma abin birgewa kullum da safe period ta farko karatun qur'ani ake a kowanne aji. Saboda haka da yamma muraja'ar na safen za'ayi sai a dora da karatun sauran litattafai.=====*****57*****===== Babu abinda ke burge sadiya da makarantar irin yadda taji su walid sun kuke suna larabci da kuma turanci saboda su kadai ne yarukan da aka yarda suyi magana dasu a harabar makaranta koda kuwa ba acikin aji kake ba. Ganin haka itama sai ta dauki sarar in sun dawo gidan ma da larabcin ko kuma turancin za'a yi magan hakan ya bata damar muraja'ar nata su kuma suna dada rainon nasu. Daga litinin har alhamis haka rayuwar makarantar su take. Ranar jumma'a ne kawai suke tashi sha biyu na rana. Duk da haka ummansu bata daina tura su wajen malam mai salati daukar hadda ba. Duk ranar asabar da lahadi tun tara na safe idan suka tafi sai azahar suke dawowa. Gida dai ya dawo daga umma sai dan lelenta wanda 'yan unguwa suke mata lakabi da sunansa wato suke kiranta umman kamal. Shi ma yadda ta taso da 'yan uwansa haka ta fara biya masa karatu. Tana dinkinta ko hada lemo ko kuma hada turaren wuta. Zaka jita tana biya masa karatu idan kuwa ka shigo kajita tana hira dashi sai ka dauka da wani babban mutum take magana. A haka rayuwarsu take tafiya. Wata rana ne bayan sun dawo daga ziyarar da suke kaiwa inna duk jumma'a. Wadda sadiya ta maida ta ka'ida ko ita baza ta je ba. Zata yiwa yaran kwalliya ta basu dan abin da ya sawwaqa