Author : Category : Home Of Novels
a 'yan kwanakin da ya shiga damuwa. Ita dai ta kasa gano dalilin damuwar sa. Jarrabawar su ta fito kuma sakamako yayi kyau. Posting dinsu tafiya bautar kasa yake jira. Makarantar da yake koyarwa suna biyansa albashi dai-dai misali tunda a ciki har hidimar inna yake dauka. Duk da dai ita kam yi mata yiwa yaya baba ne. Tunda shi yake daukewa. In kuma maganar karatun tane shima bata sake masa magana ba tun rigimarsu kafin ta haihu. Tayi ajiyar zuciya "Allah kayi mana maganin abinda yafi karfin mu" sallamar Salisu ce ta katse mata tunani. Suna gaisawa yayi but ya fito daga dakin a firgice yake magana "kai lafiya wani abu ne? A sakarce ya amsa "inna ce tace nazo na kiraka. " To to muje" ya fada kamar a rikice. Ita dai jikinta yayi sanyi Duk a tsorace take. Bayan kamar rabin awa saiga salisu ya shigo yace itama tazo inji inna. Tare suka juya suka koma. A falon ta tarar dasu harda Dija da ta zama day student a gidan saboda nan take yini sai dare ta koma gidanta. Nan zata ci na safe taci na rana ta kuma ci na dare ta dauka ta kaiwa mijinta. Kuma duk a aljihun sani. Ganin fuskokinsu ba alamar tashin hankali shiya dan rusunar da ita. Amma fa fuskar yayanta kamar zaiyi kuka. Ta tsuguna ta gaida su. Inna ce ta fara magana "duba ki gani" ta turo mata babban akwati da kuma mai binsa. Ita dai jikinta ba kwari ta daddaga kayan sama-sama. "Inna na gani kayan aure ne ko?" inna tace wannan lefen mijinki ne nan da sati biyu za'a daura masa aure da zainab. Naga shi yaki ya gaya miki shi yasa ni kuma nayi masa karanbani" sadiya ta dai daita nutsuwar ta bayan ta samu damar yin addu'a a cikin ranta. "Lallai yaya Allah ya sanya alheri " ta fada da alamar rikicewar murya wanda shi kadai ne da yake jiran yaji ta inda za'a fara ya lura da rudanin da take ciki. Jin kalamanta ya kwantar masa da hankali. Saboda ya tsammaci dubun haka daga wajenta. Tunanin tashin hankalin da yake tunanin zai fuskanta daga gareta ya sanya ya kasa gaya mata maganar aurensa da zainab. Shi dai yasan dalilin dawowar babar zainab da zancen auren su ya faru ne a dalilin wanda taso zainab din ta aura mai hali ne yana aiki a matatar mai ta kasa reshen su na portharcourt. Shi kuma baban ya dage da sani zai baiwa a dalilin tsohon alkawarin da suka yi da mahaifin sani. Wanna yasa yana rasuwa ta tana ballistic tun da dama ba tare suke ba sun dan jima da rabuwa. An hana shi aure. Mai kudi kuma daga portharcourt bai zo ba. Har an shekara daya. To shine mussababin zuwa ta bawa inna hakuri harda turo mata mutane. A gaskiya inna tana son a nuna mata ita wata abaje. Balle irin mutanen da aka dinga turowa daga gidansu zainab manyan mutane. Bayan Taja musu rai ta yadda da auren sani da zainab. Akwatin lefe da suka dawo dashi data hana sadiya shita dauko aka sa sani ya dan kara 'yan kayan da Dija ta tsince bayan da aka dawo da lefen da farko. "Yawwa haka nake son inji karuwar aure karuwar arziki ce. In kinking mijinki ya kara aure to alamar ce ta bakya son shi da arziki. Kuma bakin da yace so bazai taba cewa kiba"=====***29***===== Inji inna. Taci gaba da cewa "dama uwarta ce taso taki auren to itama tayi nadamar abinda tayi. Da kansu suka aiko suna bada hakuri. So nake ku zauna lafiya bana son fitina" "Haba inna nida aka dauke ni aka bashi yayi hakuri ya zauna dani sai kuma nice zance bazan zauna da wata ba. Allah ya kara buda masa ya rike mu dukka" Wata harara ya wurga mata yana mamakin kalamanta. Shin haukan kuruciya ne ke damunta ko kuma tsabar hakuri ne yayi mata yawa. Ko kuma bakar magana tayi niyyar yaba masa. Ya kasa tantance wanne ne daga ciki yake damunta. Inna ta miko mata wata leda tace buda ki gani kayan fadar kishiyarki ne." kai kuji dan Allah wadda bata samu lefe ba ita aka bi da kayan fadar kishiya. Shima ta duba atamfa ce kala biyu sai shadda guda daya da kuma leshi duk masu saukin kudi. Sai takalmi kafa daya da kuma mayafi. Ta fadada far'arta. Inna harda ni madalla nagode. Yaya ka gani " ta mika masa karba kawai yayi ba tare da yayi magana ba. Sai yanzu ya gane dalilin inna na hana shi bawa sadiya lefen da gidan su zainab suka dawo dashi. Watau dama bata hakura ba. Sai ta aura masa ita. Yayi kokarin nuna mata a hakura da auren nan tunda dai yana zaune da matarsa lafiya. Kuma shi ba wani kallafa rai yayi akan ita Zainab din ba. Har korafin rashin yadda zai rikesu su biyun yayi mata. Amma bata dauka ba. Tace masa kowacce mace da arzikinta take zuwa. Abinda sani bai fahimta ba. Kulawar da yake nunawa sadiya da soyayyar da yake nuna mata ita ta haddasa wannan karin auren nasa. A ganin inna sadiya zata maida shi sai yadda taga dama zatayi dashi. Abinda bata taba la'akari dashi ba. Shine irin kyautatawar da sadiyan take masa. A tsakar gida sadiya ta zube bisa gwiwarta su walid ta baro su gidan inna. Hannu ta dora aka ta fasa wani irin kuka mai ban tausayi. Tayi kukan ta ma ishi. Babu mai taimakon ta sai Allah. Ta hakikance inna bazata taba barinta ta sake ba. A rayuwarta. Ita a nata ganin inna ta yarda da aurenta da yaya sani domin kawai taci gaba da takura wa. Rayuwarta. "Kisa a ranki duk abinda ya same ki daga Allah ne kuma shi ya shirya miki hakan. Kuma karki nemi taimakon kowa sai Allah zai isar miki" karaf nasihar da Dadi yayi mata lokacin da zasuyi ban kwana ceta fado mata a rai. Ba shiri ta daura alwala ta dauki kur'aninta tana karantawa tana mai tawassali Allah ya maganta mata abinda duk yafi karfinta. Sani kuwa saboda kunya kasa shigowa yayi saida abokinsa sa'idu ya takura masa da suzo su bata baki tukunna. Ita da Dija ne lokacin da suka zo wajen la'asar tazo tana zolayarta. Fadi take "Kinsan kefa huce haushin muce tunda kuwa yanzu zamu kawo matar da muke so tafa ke hakuri ya kama ki" ta fadi haka da zummar wasan kanen miji da matar wa take mata. Sadiya ta amsa mata hakan ma da aka barni nagode. Zancen su karaf a kunnen su sani. Bayan sun shigo sun zauna sa'idu da kansa ya kira Dija. A siyasance ya nuna mata kuskuren kalaminta har yana ce mata "keda zaki kwantar mata da hankali ki kankare duk wani zargi dake zuciyar 'yar uwarki. Kuma sai ki zamo mai tunzurata". Ta basu hakuri ta nuna musu ita wasa takewa sadiya. Tana komawa gida baifi da minti biyar ba sai kuwa ga inna ta dora gidan da kanta ta kuwa wanke sadiya tas har tana ce mata munafuka zata hada mata 'ya'ya fada " fadi take indai kishi ne yake damunki kiyi da wanda yayi miki kishiyar bada ita ba. Kuma ke din nan baki isa ki raba min kan yarana ba " ta numfasa sannan taci gaba da cewa "kuma karya akayi miki ba hucen haushin akayi dake ba. Kaji min zancen banza. To baki isa ki hada min 'ya'ya fada ba" Sadiya na durkushe tana dama furar da zata mikawa su sa'idu. Bata daina abinda take yi ba hakan nan bata tankawa inna ba. Sai dai hawaye ma bai daina ambaliya a fuskarta ba. Sani kuwa yana daga cikin falon kansa kamar ya tsage domin tsabar takaicin innarsa. A yau kam duk abinda yake boyewa abokanansa dangane da takurar da take yiwa sadiya yau saida ta tona. Sa'idu ne yayi karfin hali ya fito daga falon. "Inna barka da yamma" ya katse mata fadan da take yi. Sai kuma kunya ta kamata "Au ashe Kuna ciki sannu yaya mutan gidan ina Fatan kowa lfya. Sai kuma ta wayence "Haba kaji ni ina ta fada ko. Wai ace kai da dan uwanka ba zaku zauna kalau ba. Yanzu inace Dija da sadiya duk abu daya yayi su" "Kwarai duk daya ne. Yaran ne sai hakuri kiyi hakuri dan Allah zancen ya wuce haka nan. Sa'idu ya fada mata "ai shikenan yaya wajen gwaggon ka kwanaki naje na duba ta da kafar nan ta matsa mata ". "Ai ta samu sauki ya amsa mata. Suka gama gaisawa ta juya tayi ficewarta. Idanuwanta kamar gauta tabi bayansa zuwa ciki. Furar data dama ta shiga cikin falon ta kai musu. Sani ya ko kasa daga fuska ga Kunyarta gata amininsa da yake ji. Sa'idu ne yace sannu madam munzo dan yin gyara kuma inaga kamar barna mukayi mun jawo miki fada ba gaira ba dalili " "Lah Haba ai babu ruwanku. Kuma ina laifin ma yaya Dija don ta tuna min matsayina wata kila gani tayi ina kokarin wuce inda aka ajiye ni" "A'a karki kara tunanin wai baki da matsayi a wajen sani. Duk yanda kike tunanin kanki a wajensa kin wuce haka" Dariya tayi "anya kuwa ina shakkun maganarka. Karfa ka ari baki kac albasa mai bakin yazo yace bai yarda ba. Amma tunda kace haka to shikenan mubar zancen komai ya wuce banda zuwan amaryar sani ". Ta fada tana mai kokarin kakalo murmushin dole. Amma muryarta har a wannan lokacin rawa take yi alamar tana kokari ne kawai kar kuka ya sake kubuce mata.=====***30***===== Shima dariya yasa "to kaji uwargida dai batai fushi ba yanda kake tsammani. Duk kabi ka daga hankalinka. Har kana tattago ni da inzo in taya maka bada hakuri" Ya dago kansa ya kura mata ido na dan karamin lokaci. Itama ta tsaida idonta bata dauke ba. Ba kamar lokutan baya ba da indai yayi mata irin wannan kallon ita bata iya maida masa martani sunkuyar da nata idon take yi. Ya girgiza kansa tare da murmushi mai nuna bacin rai amma ba murna ba "sani sak. Sa'idu tunda nake da sadiya bata taba fadar sunana ba sai yau. Kalamanta da tace an tunatar da ita matsayinta su suka tabbatar min da matsanancin fushin da takeyi dani. Kabar ganinta karamar yarinya. Dani dakai ba lallai mu kaita dabara ba. Zata yi magana. Yace karki katseni ina magana. Ya cigaba da maganar sa cikin bacin rai "ba kowa ne yake gane fushin sadiya ba sai wanda ya santa da gaske. Kai zan iya rantse maka duk gidanmu ba wanda zaice ya san fushin sadiya sai ko ni da yaya kulu ba karamar shock absover wannan yarinyar take da itaba. " kace haka mana tunda kaso inyi kuka inda za'ayi min dariya ban yi ba. Tunda ka rufe ni zancen auren ka. In zaka auri masoyiyyar ka ni na isa na hana ka ne amma sai ka nemi da insani ta hanyar da bazai min dadi ba. A cikin maganganu biyu dole in zaton daya. Ko dai kana shayi na kamar yanda ake fada ko kuma baka yarda dani ba a zatonka zan iya sanadin hana zuwan amaryarka." Sa'idu zaiyi magana da hannu Sani ya tsaida shi. Ta cigaba da magan cikin dan zafi kadan domin kuwa harda take magana cikin yanayi na bacin rai bata daga musu murya ba. Sautin maganarta a hankali yake fita. Shi mijinta da ya santa da kyau shine ya gane a cikin bacin rai take magana. Domin ita in ba ranta ne ya baci ba to bazata taba maida maka martani ba. "Nifa bana son inji kina maganar wai baki da matsayi da kuma rashin yarda da wani wai menene-menene. Kin san Allah Sani gudun bacin ranki ne yasa shi kasa furta miki zancen auren nan. "Amma kana ganin yaya yayi min adalci daya ki sanar dani. Kuma ace wai abin that concern me most sai kuma in zama the last to know. Kawai dai a bar maganar. Anan ta sake share hawayen daya zubo mata wanda take kokarin dannewa. "Kasan Allah ba auren shine ya bata min rai ba amma rashin gaya min na dauka yaya ko mutum ya kashe zai sanar dani domin mu taru mu rufawa juna asiri. Nima bashi ni akayi ya hakura ya zauna dani sai ni in ki amincewa wadda ta zamo dama ita yake muradi ta zo inda nake. Daga anyi min alfarma kuma ai bana zake ba. Kuma dama a rashin uwa akanyi uwar daki randa kuma uwar tazo sai a manta da uwar dakin. Shi dai sa'idu yayi kokarin dada bata hakuri duk da yunkurin da tayi na nuna musu ita komai ya wuce a wurinta. Sani ne ya tare shi da fadin "na fison ka barta ya gaya min maganganu masu zafi ta sauke abin dake cikin zuciyarta ko taji saukin bacin ran da take ganin na haddasa mata. "Wai ni sadiya kike ikirarin bani ke akayi zanyi auren wadda nake so. Naji ke ba zabina bace amma na tabbatar Allah zuciyata ya duba da kuma yawaita addu'a da nake yi na samun mata tagari ya mallaka min ke." ya kura mata ido ya tabbatar da maganganun sa sun ratsa zuciyarta kuma ga dukkan alamu ta yarda da zancen daya fada mata. Ya sake lankwashe murya duk da niyyar rarrashi yace "maganar bani ke da akayi da kike ta nanata wa tafi komai bata min rai amma idan fadar ta zai sanyaya ranki kiyi ta fadar ta. Bazanji haushi ba saboda nasan fada kikeyi kawai dan ranki yayi sanyi "**31***===== Ajiyar zuciya mai karfi tayi wanda shi ya tabbatar musu da saukowa daga fushin da tayi. Suma duka ajiyar zuciyar suka yi. Ta mike da niyyar komawa kicin dinta " yace mata ina zaki kuma bamu gama magana ba Ta sassauta muryarta ba kamar dazu ba tace "Allah yaya maganar ta wuce Allah ya sanya alheri a auren da zakayi. Bari in shiga kicin in samo muku abinci kar dare yayi" tana fita sa'idu yace "sani Allah yasa mu a danshinka. Kaga yarinya karama da kyakkyawan lafazi kamar wata babba. Wannan koda zance aka barta ta kwantarwa da mutum hankali." "Ba shi yasa kaga hankali na ya dada tashi da wannan auren ba. Ba zaka gane baiwar da Allah ya yiwa yarinyar nan ba saika zauna da ita. Ko kasan wancen lefen dana hada zan yi auren zainab din sallamar da uwar dakinta ta bata akan ta koma makaranta shita dunkule ta bani. Koda kunyar wannan aka barni ai ta ishe ni. Sa'idu sale kam ya nuna masa yabawarsa akan halin matar tasa duk da karancin shekarunta amma tana da tarin hankali juriya da kuma tunani. Amarya ta tare a gidan sani. Zamansu lafiya lau ita da sadiya. Itama saiwar sala ce ba sawa ba hanawa. Tafiyar Sani bautar kasa zuwa jihar legas ya sanya inna ta sashi daukar zainab su tafi tare. Yaso ya dan bijire a wannan karon. Amma sadiya da kanta ta nuna masa yafi dacewa ya tafi da ita Zainab din tunda inda yake bautar kasar sun bashi muhallin zama. Rayuwa irinta wancen lokacin ba yanzu ba da abubuwa suka tsananta. Da alawus na bautar kasa sani yake daukan nauyin iyalinsa. Harma dana mahaifiyar sa. Ya gama bautar kasa ya dawo gida a lokacin zainab tana dauke da cikinta ta kusa haihuwa. Ita kuma sadiya nata wata bakwai. Domin yaranta nada wata hudu ta sake samun wani cikin. Tayi bakin cikin faruwar hakan. Amma Sani shiya karfafa mata gwiwa da nuna mata ba'a fushi da kyautar Allah. Basu dade da dawowa kano ba wani yammaci zainab ta tashi da nakuda aka kaita asibiti amma haihuwa shiru daga baya likitoci suka bada shawarar ayi mata aiki. Allah gwani itama 'yan mata biyu aka fiddo mata kyawawa masu kama da ubansu. A wannan zaman ne kuma da akayi a asibiti na zaman jinyar zainab. Da inna da mahaifiyar zainab din suka samu sabani. Kowa a cikinsu dansa kamar ido yake. Abinda ya faru mahaifiyar zainab ce ta bada shawarar Sani ya sayo madara a fara bawa jarirai kafin jikin uwar yayi karfi. Inna kuwa tayi tsallen arziki tace ita fa danta ya gaji da wahala. Yarinya ta haihu da kanta ance aiki. Aka zo aka kashe makudan kudi. Karku dauka wasu kudi ne masu yawan gaske. A'a'a lokacin ba'a biyan kudin asibiti saidai mutum ya siyo kayan aiki. To wannan inna take yiwa mitar. Itama mahaifiyar zainab ta kule tace amma dai ai kinga wahalar da tasha kafin ace ayi aikin" "Yo wahala ai dole ce. An taba haihuwa ba nakuda ne kuma an taba nakuda ba wahala. Ai dole kafin a samu da a wahala. "Yawwa tunda kinsan da wahala kin gani nima ba rawa nayi na samo tawa ba. Nima wahala nayi na same ta. Kuma da baifi da ba. "Inna ta mike har tana cire mayafi. "Au haka kika ce. To ni kuma ba wanda ya isa ya juya min dana. Tunda dai nawa ne sai yadda naso dashi." "Kiyi duk yadda kike so ai na dade da lura dake ke mace ce mai kishin matan 'ya'yanta. Kuma duk tsiyar ki sai dai wata ta zauna dashi" anan ne inna ta saka kuka wai mahaifiyar zainab ta zage ta. Dai-dai nan sani ya shigo inda suke. "Indai nina haifeka ka rubuta musu takardar sakin 'yarta. Sai dai inka yarda ka zauna da mai zagin mahaifiyarka". Ta fadawa Sani tana share hawaye da hannun zaninta. Sani ya fara kokarin bata hakuri da kuma kokarin jin bahasin me ya faru har inna take maganar saki a auren da ita ta hada shi. Tana share hawaye take fadin "Nidai nina haifeka to yau kuwa na umarceka daka saki zainab. Saidai in zaka nuna min ta fini matsayi a wajenka. Ta fyace majina da gyautonta alamar kuka yaci karfinta. "Inna kiyi hakuri mu zauna mu tattauna wannan magana a nutse har mu samu maslaha " "Kasan Allah to wallahi tallahi a yanzu sai ka zaba ko ni ko