Author : Category : Home Of Novels
samu sai itama ta yarda. Da danlelenta suka yanke shawara. Yana murna harda fadin " inna don Allah ki barta taje in an tara albashin inna kya saya min mashin" ta amsa masa da fadin " mai zai hana ubana, ai duk abinda kake so zan maka. Kuma ma dama me take yi min a gidan, dan kaye kaye ne kuma nayi abina. Ga kuma qaruwa da za'a samu. Inaga ma idan ta fara aikin adashe zan shiga. Domin a tara kudin babur din naka. Kaga har kayan daki na samu na tara mata". Amma dai inna sai an fara siya min mashin din tukunna ko". To tunda kaine babba ai dama ta kanka zan fara." Wai waya ganni da babur ai in na dinga zazu dashi a unguwar nan, dama ina jin haushin shitu dan gidan Alhaji Lawan wai kawai rannan daga na ari mashin dinsa tsautsayi yasa na fasa masa danja, ya ringa yimin bala'i. Ai kawai kyale shi nayi amma da sai nai masa rashin mutunci. Amma kinga inna idan na samu nawa habawa" Kai gandoki jira a fara aikin a samu kudin mashin din ko kafin ka rama abinda akayi maka. Nima ai bana son na rika ganin kana yawo a qafa. Nafi son kaima ka kece raini kamar sauran matasa ' yan uwanka" Allah ya barmin ke inna tawa" ya fada yana dariya Sani bashida masaniyar wannan shawara tasu, kasancewar baici abincin dare a cikin gida ba. Dakin dake tsakar gida Ta hada nasa ta kai masa shida baqonsa sa'idu da shima yazo hutun qarshen mako. Daga jami'ar maiduguri. Kafin yayan zaria ya koma makaranta sai da ya dubi littatafan ta ya kuma yaba da irin qoqarin da take.
.......****7****........... Komawarsa zaria ne ya bawa inna damar tura sadiya aikatau. Taja mata kunne matuqa kafin tamasar ta kaita gidan aikin nata. Sadiya tayi mutuqar baqin ciki da afkuwar hakan. Saboda sanin karatun ta yazo qarshe, amma bata da yadda zata yi. Tunda dai bata isa tace bazata je ba. Gidan da za a kaita tayi aiki yana cikin jerin manyan gidajen da suke bakin titin unguwarsu, sabanin nasu da suke a lungu. Misali tara na safiya tamasar tazo tafiya da ita. Tana jin sallamarta bata San sanda hawaye ya fara zubo mata ba. Ai kuwa yaya baba yana lura da ita ya fara zaginta yana fadin " ' yar baqin ciki watau ke baza'a qaru da keba." innarta ta amsa da cewa " qyaleta komai abin tsiyarta sai taje in kuma kika je kika qulla musu abin tsiya nida kene a gidan nan kinsan sauran. Har in suka koroki kin quntuka musu abin tsiya to talla zan dora miki. Ta dago idanuwanta da suka cika da hawaye tace mata " kalleni da kyau, kinsan zan iya. Tana bambamin fadanta suka fita daga gidan ita da tamasar. Ta lungunan unguwar tasu suka bille suka nufi bakin titi. Tamasar tana dada tausarta tare da kwadaita mata alherin dake tattare da gidan da zata kaita. Tace da ita " gidan dazan kaiki ba wani aiki ne mai wahala ba. Zaki ma samu ki huta. Matar gidan so take a nemo mata yarinya qarama da zata dinga taimaka mata da qananan ayyuka. Kuma dadin dadawa daga qasar waje suka dawo gidan 'yan gayu ne inda zakije. Tadan numfasa tajira taji ko sadiya zata furta wata magana taji bata ce komai ba. Taci gaba da fadin "keda zakije kici mai kyau nasan har kayan sawa sai ta baki. Kisaki ranki ai bazan kaiki inda za'a cuce kiba." sadiya ta amsa a zuciyarta "ni dai ai kin cuceni tunda kika raba ni da karatu na" sai kuma ta tuna da wa'azin da aka yi musu a islamiyya inda malamin yake fada musu cewar duk abinda suka ga ya same su Allah ne ya qaddara kuma su kasance masu neman taimako a wurin Allah kadai da kuma dogaro dashi. Insha Allahu zai isarwa duk wanda yayi tawakkali dashi. Wannan tunani da ya darsu a zuciyarta shiya sanya ta tayi ajiyar zuciya. Jin haka da tamasar tayi shiya bata qwarin gwiwar cigaba da nasihar da take yi mata a zaton ta sadiya taji hudubar da take yi mata ne. Taci gaba da fadin " idan kinje ba ruwanki da kowa aiki da aka sakaki shi zakiyi kar ki taba musu yara kuma duk abinda ba'a baki ba Karki dauka. A zuciyarta tace mai cin zalina ma a gida na qyale su balle wadanda naje aiki gidansu. Professor Abubakar Ibrahim da matar sa Hajiya mariya nan ne gidan da tamasar ta samowa sadiya aiki. Gidansu na daya daga cikin manyan gidaje masu furannin da suke burge sadiya anan babban titin unguwarsu. Asalinsu mutanen bichi ne. Amma aiki ya kaishi har qasar barno inda ya koyar a jami'ar maiduguri na tsawon shekaru takwas. Daga nan ya tafi America inda yayi tsawon shekaru hudu domin qaro ilimi. Yanzu haka yana daya daga malaman jami'ar bayaro ta kano. Mutane ne masu mutunci da sanin darajar dan Adam 'yan uwan juna ne dashi da matarsa har Allah ya hada su aure........****8****......... Sun tarar da matar gidan mace mai far'a da cikar kamala ta karbe su da murnarta. Gidan tsaf dashi ko ina sai qamshi ne yake tashi. Bayan sun gaisa da tamasar sadiya ta rusuna ta gaisheta Cike da ladabin data saba gaida mutane dashi. Matar tace " hajiyan masar ina kika samo yarinya kyakkyawa da ita.? Tamasar ta amsa mata da cewar "yarinyar da kika ce a samo miki da aiki ce. Nan da nan ta fadada far'arta tare da nuna farin cikinta ta kuma dora da fadin " kai maddala nagode amma kina ganin zata iya yin ayyukan dazan sakata. Kin ga Inason ta dinga taimaka min a kicin da kuma harkar yara domin na lura dadinsu baya son qabilun nan suke shiga harkar yaransa balle rannan da yaji amira ta fadi wata kalmatil daya tambaya aka sanar dashi fassararta daga yaren gwari. Suka tuntsire da dariya. Tamasar ta amsa da cewar wannan yarinyar nayi miki alqawarin ba abinda zai gagara. Sai kinyi mamakinta. Ai kin san bazan kawo miki mashiririciya ba. Tayi mata godiya ta shiga daki ta hado mata sabulai harda turmin atamfa ta kuma dauko kudi ta miqa mata. Tayi godiya ta sake tsayawa tayiwa sadiya fada sosai akan ta kiyaye ta tsaya tayi aikinta yadda ya kamata. Sannan tayi musu sallama ta tafi ta bar sadiya mai shekaru goma sha daya a baqon muhalli da bata San kowa ba sai dogaro ga Allah. Wanda ta haqiqance shine kawai gatanta. Sadiya ta fara aikinta a gidan mom mariya da kuma dadinsu mai suna Abubakar. Momi tayi mutuqar mamakin yadda sadiya ta iya aiki da kuma girki. Gata da far'a da son yara. Yaran gidan guda uku ne Amir dan shekaru tara shine babba sai qanwarsa Amira mai shekaru bakwai. Sai kuma babyn da Momi take goyo watau Khalifa. Gida ne na tsantsar 'yan boko masu dauke da kyakkyawar akida. Basa nuna mata wariya. Ita kuma bata yi musu shishigi a bisa lamuransu. Aikin sadiya a gidan ya hada da wankin uniform safa da kuma qananan kayan yaran gaba daya. Sai rainon Khalifa da kuma taimakawa Mominsu girki a kitchen. Kaf kaf dinta da kuma taftarta ya sanya Momi ta dada sakar mata wasu al'amura na gidan. Wata rana da la'asar momi tasa sadiya ta fere mata dankali a bayan harabar kicin ita kuma tana daga kicin sai taji amir ya tanbayi sadiya da harshen turanci wani lissafi da aka basu a makaranta. Ya gagara yi. Abin ya bata dariya a zuciyarta take fadin Amir da shirme. Sadiya tama san me kake fadi. Bata kai qarshen tunanin ta ba taji muryar sadiya a nutse tana bawa Amir amsar tambayarsa. Duk da turancin bai kama qafar nasu ba amma tayi masa bayanin daidai yadda zai gane. Bata gama wannan al'ajabin ba taji Amira ita kuma tayi mata tanbaya akan wani hadisi da ustaz da yake biya musu karatu ya saka tayi bitarsa itama sadiya ta amsa mata ta ta tambayar. Al'amarin sadiya bai qara daure mata kai ba saida taji ta dage tana gwama turanci suna hira da dariya dasu Amir. Ga wani qarin abin birgewa da Amir duk sanda tayi kuskure kamar yadda al'adar bature take baya yi maka dariya sai dai ya gyara maka. To haka Amir ya dage da gyarawa sadiya inda ta kuskure har kuma ya sata ta maimaita don ya tabbatar data gane gyaran da akayi mata. Momi abin har tsoro ya bata. Ta kira Amir ta tanbayeshi yaya akayi har sadiya ta iya turanci. Ya amsa da bai sani ba. Ta bar maganar a ranta. Sai bayan yaran duk sunyi bacci sai sadiya dake qoqarin karasa gyaran kicin. Momi tana tare da dadi a falonsa take mayar masa da abin data gani tsakanin yaransu da kuma sadiya. Dadi ya dan nisa sannan yace "any kuwa ba cutar yarinyar nan mukeyi ba. Amma kirawota muji amsar wasu tambayoyi daga bakinta. Momi ta leqa ta kwallawa sadiya kira ta leqo daga kicin da dan tsumman da take goge goge dashi 'gani momi inji ta. Kin Gama ne? "A'a ta amsa mata amma sauran kadan.". "Barshi kawai kinzo inji dadi.=======***9***======= A kan qofar kicin ta ajiye duster tabi bayan momi zuwa falon nasu. Ta shiga da sallama kamar yadda ta saba. Ta durqusa a gefen kujera, ta dada qasqantar da muryarta. Dadi barka da yamma" barka kadai ya amsa mata. Zauna mana da kyau" ta gyara zamanta maimakon durquson da da tayi. Dadi ya ajiye kofin shayin da yake kurba ya kalle ta tace, ina babanki yake Inason inyi magana dashi" nan da nan muryarta ta fara rawa ta amsa masa da cewa "babana ya rasu tun ina shekara biyar." Mamanki fa? Itama ta rasu tun ina baby. Banma santa ba sai dai labarinta da ake gaya min" Ya danyi jim sannan ya sake cewa " to yanzu a hannun wa kike da zama" "A hannun innata yayar babana ce". Ta amsa masa cikin rawar murya. Wadda ta tabbatar masa da cewar ya tado mata da wani tsohon miki na maraicin da tayi. Ya nisa yace " Allah yaji qansu. Dama kin fara makaranta ne?. "Ina makarantar boko da islamiyya. Momi ce wannan karon ta sako tata tambayar "ajinki nawa? A boko zamu zana common nazo nan a islamiyya kuma ina ajin 'yan sauka don munyi izifi arba'in da biyu kafin zuwa na gidan nan." tana magana muryarta na rawa alamar kuka na qoqarin qwace mata. Dadi ne ya fara magana. Yace "tashi kije ki kwanta". Ta miqe da sauri don kar suga qwallar da take qoqarin sharewa. Bayan fitar ta momi ce ta fara magana. " dadin amir yaya kake ganin za'ayi? Ya amsa mata da cewa"daurewa zakiyi kije gidansu gobe mu nemi yardar mariqiyarta mu maidata makaranta". "Nima dama tunanin danayi kenan. Karmu ajiye yarinyar mutane tana mana bauta bamu lura da cigabanta ba. Sai convenience dinmu kawai muka duba" " kin kyauta da wannan tunani naki. Ki tattala da kona waye baka san alherin da zai zamar maka ba. Sai yayi maka alherin da dan cikinka ba zai iya maka shi ba" Washe gari sadiya na qoqarin karasa hada abincin dasu Amir zasu tafi dashi makaranta. Momi ta leqo tace " yi sauri ki hada musu kije kiyi wanka fita zamuyi. Kai bari ma zan qarasa jeki ki shirya" Da qafa suka zagaya suka shiga lungun gidan su sadiya tun da ba wani nisa ne dashi ba. Ga kuma uwar dakin nata ba malalaciya bace. Sun sami inna a rumfarta tare da sarkin fadarta wato yaya baba. Da hanzari inna ta miqe tana maraba amma fa gabanta sai bugawa yake, dariyar yaqe kawai take yi. Amma zuciyarta fadi take Allah yasa yarinyar nan ba abin tsiya ta shuka a gidan da aka kaita aiki tayi ba suka dawo da ita ba. Gashi taji dadin kudinta na wata uku da tazo kwanaki da kanta ta kawo mata. Wanda dasu ta fara adashi don sayen babur din dan lelenta. Bayan musayar gaisuwa a tsakanin su, Sadiya ta miqe ta fice ta barsu domin bata san me zasu tattauna ba. Shi kuwa sarkin hankali yana zaune bashida niyyar tashi. Wai zazzabi ne yake damunsa. Inna dai tayi saqare tana jira taji ta inda labarin zai bullo mata. Harta fara tunanin irin azabar da zata ganawa sadiya in dai har tayi sanadin da aka koreta aiki. Momi tace "sai kika ganmu kwatsam" inna ta muskuta ta hadiye yawu da qyer tace "ai na rasa ma ta inda zan fara. Yaran yau ka haifesu baka haifi halinsu ba. Amma in banda haka wane irin Jan kunne ne ba'a yiwa yarinyar nan ba amma............ Momi tayi sauri ta katse ta tace "kinsan Allah sadiya tun da aka kaita ban taba samun matsala da ita ba. Da kyar ta maimaita kuskure. Kusan duk abinda akayi mata gyara a kansa to da kyar ta sake maimaita makamancinsa". Sai a sannan inna taji hankalinta ya kwanta. Momi ta dora da cewa "alfarma muka zo nema. So muke idan har kun yadda zan maida sadiya makaranta taci gaba da karatunta. Tunda na fuskanci ta fara karatu da can" Wata munafukar gyaran murya yaya baba yayi. Nan da nan inna ta gane me yake nufi. Ya tashi ya shiga uwar daka. Ita kuma ta miqe tana fadin Hajiya bari na samo miki ruwa kisha. Momi na qoqarin nuna mata ta barshi ba komai amma duk da haka ta miqe ta shige dakinta da nufin dauko kwano. Tana shiga ya yafitota da hannu sannan ya rada mata "Karki yarda baki suka hada da ita sadiya. Da anfara za'ace miki kudin aikinta dashi za'a biya mata kudin makaranta". Itama ta rada masa "na gane wayonsu ai. Barin dani suke zancen" ta dauko kwano ta fito ta nufi randa, anan ne ta tarar da sadiya tana qoqarin karasa share mata tsakar gida. Ta harareta kawai ta wuce. Bayan ta shiga da ruwa. Tace to Hajiya anfa gode amma wani hanzari ba gudu ba zan so. Ita sadiya taje ta gayawa wan babanta idan ya amince shikenan. Nama san zai yadda wannan abin alheri haka".=====***10***====== Da wannan momi tayi musu sallama. Bayan tayi wa inna ihsani wanda taji dadinsa sosai. Ta dawo ta bari sadiya akan ta kwana taje ta nebo zini a wajen baffan nata. Tana fita kuwa yaya baba ya dire a kanta. Ta inda ya shiga bata nan yake fita ba. Har yana fadin munafuka ita taje tana fadin asirin gidansu. Inna kuwa fada takeyi tana fadin "kaga min annamimiyar yarinya. Zuwa kikayikina gayawa mutane magana ana ganin kamar ba'a kula dake, dama duk akanki an saka min ido kamar akanki na fara riqon maraya. Nima 'ya'yana duk marayu ne. Kuma haka na riqe su ba tare da kowa yaga gazawata ba. Ehe dan kiji in gaya miki. Ke baki isa kisa mutane su zage ni ba". Ta kuka take fadin " wallahi inna ban gaya mata komai ba. Kawai ji tayi muna karatu da yara shine ta tambayeni a ina na koyi karatu, shine na gaya mata na fara makaranta. Allah inna ban san komai ba bayan haka" "Idan bake kika fada ba wane shegen ne yaje ya gaya mata. Idan kikayi wasa sai in dawo dake daga gidan ki koma talla inga abinda zakiyi." A'a inna ki barta ta koma gida aikin. Amma in taje tace baffa bai yarda ta shiga makaranta ba. In an matsa kije da kanki kice yaqi. Amma ni yanzu inda aka samun rai zan mallaki mashin kuma azo ace an fasa. Ai gaskiya ni aka yiwa. Ta koma kawai taci gaba da aikinta" Da wannan sadiya ta koma gidan aikin nata ta kuma fada musu kamar yadda inna ta shirya mata. Momi bata yarda ba. Ta kuma ya qoqari ta bugi cikinta dan taji komai dalla- dalla. Amma hakan ma bai samu ba. Inda ta gano bakin zaren sai da ta tanbayeta " shi wannan da muka samu a dakin Innar taku waye shi.? Ta amsa mata da cewar yayanta ne. Ta sake tambayarta shi aiki yake ko makaranta. " baya komai shekara biyu kenan daya gama sakandire" "Allah mai iko. To shi bazai fita aiki ba sai ke da kike mace za'a tura neman kudi". Ita dai bata amsa ba. Ta nisa tace ku nawa ne a gidan ta lissafa mata tun daga yaya kulu har zuwa kan Salisu. Ta sake tambayarta. Kowa abinda yake yi. Sadiya ta gaya mata. Momi ta sake cewa. Amma ai naga yayarki Dija tayi makaranta. Ita dai shiru tayi bata ce komai ba. "Ba komai duk abinda ya samu bawa shiryayye ne daga Allah" inji momi. Da dai ya dawo momi ta gaya masa duk abinda ya faru a zuwanta gidan su sadiya da kuma abinda ta gani hadi da kuma bayanan da ita sadiyan tai mata. Ya nuna mamakinsa yace "Karki damu inaga abinda zai faru ta rubuta jarrabawa a makarantar su Amir zanyi magana da principal din sai taci gaba da home study a wajen lesson teacher su Amiran. Haka Inason duk sanda ustaz yazo ki tabbatar taje itama ta dauki karatu" Haka kuwa akayi. Da wannan taimako dasu dadi suka yi mata ta zana jarrabawar common entrance ta kuma cigaba da daukar karatu a wajen lesson da kuma ustaz. Duk gidansu babu wanda yasan da wannan shirin ko yayanta. Yayan zaria. Farko daya kawo ziyara gida aka gaya masa sadiya tana aiki a wani gida yayi baqin ciki matuqa. Saboda ya tabbatar wannan zai zama sanadin tsayawar karatunta gaba daya. Da kansa ya nemi tamasar tayi masa kwatancen gidan da sadiya take aiki. Da la'asar ya shirya ya nufi gidan. Yana isa bakin gate din gidan ya rusuna ya gaida magadin wanda ya kasance dattijo ne. Bayan sun gaisa yace "baba don Allah so nake yi naga sadiya, ni yayanta ne. Baba maigadi ya amsa da cewa "anya zaka ganta yanzu kuwa domin maigida ya hana in dai yara suna karatu a katse musu. Amma bari in yiwa Hajiya bayani" Ya shige cikin gidan yabar