Author : Category : Home Of Novels
mukayi da ita a can Sudan babanta ya taimaka ya samo min aikin da muje zanyi kokarin sama miki wajen zama da kuma nema miki makaranta sai inzo mu tafi tare "Bana son kana daukarwa kanka alkawarin da na tabbatar ba zaka iya cika wa ba. Kuje kawai tunda dai ita tana da baban da zai sai mata miji ai tayi sa'a " itama ta bashi amsa kaima kasan batun wani tafiya da kake dani wannan duk zance ne. Mts" ta dan ja tsaki "Ina ma anfanin auren namiji mai kyau kowa idonsa na kansa. Ta fizge hannunta ta fice daga dakin. Komawa yayi ya kwanta akan gadon ya kurawa silin ido a fili yake furta "sadiya ki gafarceni na san na cutar dake" Dakin da ta ware ita da 'ya'yanta nan ta shiga ta cusa tsumma a bakinta don ya kare sautin kukan da take son kurmawa. Hakan da take a gidan inna ya sa ba wanda yake gane tana kuka ta dauka ta rabu da irin wannan kukan sai gashi yau ya dawo mata. Tayi abinta ya isheta ta rasa mai zatayi sai kawai ta tattara yaranta gaba daya ta rungume su ta tabbatar da cewa yanzu su kadai ne zata raba taji sanyi. Sani tunda ya gaya mata maganar aurensa shi kam ta fitar dashi a ranta. Ta hakurcewa ranta sa ran zata samu zaman lafiya dashi. Abinda yafi mata sauki shine ta cire shi daga mafarkinta na samun wata ingantaciya rayuwa. Saboda ganin duk sanda tasa ran samun farin ciki tare da shi sai wata kaddarar tazo ta gifta tsakaninsu. Ta tuna yaranta wadanda bata na sa a ranta akwai wani nata da ba nata ba ko a cikin ranta bata taba jin tafi son walid akan su shukra ba. Balle kamal da take jinsa a ranta sama da dukkan yaran da take reno. Bata san dalilin wannan kauna tasu ba. Ita dai tana ganin maraicinsa take tunawa dashi take dada tausaya masa. Tayi ajiyar zuciya sai da sannu ta samu addu'a tazo bakinta tana farawa taji ranta ya fara sanyi ta sake rungume yaranta tare da kudurtawa a ranta zata rungumi yaranta tunda ta hakikance su kam baza su taba butulce mata ba.======****40****====== Tunani ta cigaba da yi zuciyarta ta fara raya mata kema kinsan inna ce zata sashi yayi. Me tayiwa inna ne haka da bata sonta da kwanciyar hankali. Can tayi tsaki. Ta sake raya wa a ranta zato zunubi koda ya zama gaskiya. Ba inna bace bama ruwanta. Inna da kwana biyu da suka wuce har aiken sabulai tayi mata wai a wanke kayan mazanta dana kawayenta. Inna kam ai babarta ce matsalar daga wurinsa take ci gabansa yake tunani. To ai dole yaso ci gaba zuciyarta ta sake tuna mata. Allah ya kyauta ina ma amfanin auren namiji kyakkyawa duk hankalin mata na kansa. Ta fada a fili da dai taga tunani bazai kai mata ba. Sai ta mike ta fito tsakar gida domin ta daura alwala tayi abinda tasan shine zai fissheta. Muryar sani ta jiyo yana karatun Alqur'ani mai girma itama abinda ta kwana yi kenan. Washe gari da suka tashi kowa ya gansu yasan basu yi baccin kirki ba. A sanyaye ta gaida shi. Ba dan ma hankalinsa na kanta ba ba zaiji abinda ta ke fada ba. Ta ajiye masa karin kummalonsa yace kefa naga kin ajiye kin tashi. "Azumi nake yi. Ta amsa masa a takaice. Bai ja maganar da nisa ba saboda ya lura kusan duk sanda ranta ya baci to washe gari da azumi zata tashi. Shima shayin daya hada kadan yasha ya ture sauran ta fito daga daki goye da kamal a bayanta. Zanje wajen yaya kulu in gaisheta. "Kije gaisheta ko kuma karata zaki kai mata " ta juyo ta kalle shi da alamar harara a fuskarta. Shi kam hararar tafi dauke masa kan da take yi. Ko ba komai ya samu sanadin kallon idanuwanta ko don yayi kokarin gano halin da zuciyarta take ciki. Anan kuwa ya fahimci fuskarta ta dan saki ba kamar jiya ba. "Allah ya sawwake kawai don zaka yi aure sai kuma in ringa yawo ina fada. Ni ina ruwana ma da aurenka wanda kayi a baya ma basu dada ni da kasa ba balle wannan. In ma kana tunanin wani abu to ni kam zuciya ta ma har ta saba. "Dame ta saba? Ya tambayeta yafi bukatar su cigaba da magana ko don ta samu ta rage wa zuciyarta nauyin abinda yake damunta. Sanin kansa ne tun farko bata da wanda zata gaya wa damuwarta. Dama shine take dan iya fadawa idan wani abu ya dame ta. To yanzu kuma ya dawo ya zama shine mai haddasa damuwar. " da komai ma ta amsa masa a takaice. Inma kana tunanin wai zan gayawa yaya kulu ta hana ka aure ne sa ranka a inuwa ni tawa ce zata kaini. Kuma da da nake zuwa kara nake kaiwa. Ko dan kawai yanzu ka tsaneni sai ka dinga yi min sharri." "Allah ya baki hakuri ba nufi naba kenan. A zuciyarsa kuwa fadi yake ni da da inda zaki kaini kara ma a hanani wannan auren ai da ba karamin gata kika yimin ba. A fili ya furta mata "jeki kice ina gaisheta. Nima zan shigo wajenta da yamma. Amma ki bar min su walid don karsu dame ki. "Ka taba jin randa nace suna damu na. Dama can basu dameni da komai ba bare yanzu da nake jin su kadai ne............." "Su kadai ne me? Ya katse ta. Shiru taki bashi amsa "shike nan muje na sakaki a tasi. Amma komai dare karki dawo ki bari zan zo mu taho tare. Shiya tayata da rikon 'yan mazan da kuma shukura ita kuma ta rike walida da kuma jidda. Suka nufi bakin titi. Har kofar gidan yaya kulun mai tasi ya ajiyeta kamar yadda sani ya umarceshi. Ta shiga da sallama. Yaya na tsakar gida suka shigo ta amsa musu da murnarta fadi take ga babana ga baffa na ga uwata ga kuma aminiyata ga kuma tawan gaba daya. Ni 'yar gata duk yau ni kadai nake da wadan nan manyan bakin. Tana kunce kamal daga bayanta take cewa yaya kamal zaiyi fushi dake tunda shi ba naki bane ba "ni na isa ince haka. Dan gaban goshin sadiya ince bana maraba dashi. Ku shigo daga ciki. Cikin rumfarta suka shiga aka gaggaisa yaran gidan suka shigo suka gaisheta. Duk da kayan makaranta a jikinsu zasu je tahfiz da suke zuwa asabar da lahadi da safe. "Yaya ina Abdurrahman " yana dakinsa inaga bai tashi bacci ba. Kin san tun da ya dawo daga share fagen shiga jami'ar nan a zaria kamar da bashin bacci ya dawo. "Halan karatun nasu da wuya " To waya sani haka dai yace. Yace sai suyi kwana biyu basu runtsa ba. Suna karatu "Allah ya bada sa'a har yanzu likitanci yake so ya karanta"? Shi din yake son yi in har Allah ya sa yaci yanda ya kamata" "Ai yaya shi kam nasan insha Allahu zaici kinsan yana da kwazo bana wasa ba " "Duba cikin tukunyar nan akwai dumamen tuwo ki sako muku kuci keda yaran. "Yayan tace da ita. "Sai dai su in zuba musu ni azumi nake yi. Kinsan mutumin naki kamal inya samu tuwo baya masa da wasa. Ta fada tana mai buda tukunyar da yayan ta nuna mata. "Ke kuma mai ya kaiki yin azumi da wannan barden goyon naki ga wahalar yara" Dariya ta saka kinsan Allah yaya yaran nan basu da rigima sam. Shi kuma kamal yanzu idan yaci tuwo yakan dade bai nemi nono ba" "Ki yaye shi mana ki huta tunda yana tafiya. Ba inace ya cika shekara daya ba harda wata biyu" ta dan langwabe kanta "Wai da yaya yayi ko da shekara da rabi ne sai in yaye shi" "Ke kam ai akan kamal baki da dauriya. Duk suka sa dariya. Nan ta kama wa yaya ayyukanta har suka karasa. Bayan tagama bawa yaran abinci su walid Abdurrahman yazo ya fita dasu. Su walida suna wasan su. Shi kuwa kamal saboda tashin sa da akayi yau da sassafe barci ya koma.=======****41****======== Tana hankalce da sadiya kamar tana tafe da magana a ranta amma itama tana tararrabin yadda zata tari sadiya da zancen da tazo mata dashi. Itama zancen auren nan yana damunta amma ta rasa yadda zata fara yi mata magana. Sadiya ta gyara kishingidar data yi ta nutsu ta kalli yaya kulu tace "mh yaya nace ba. Don Allah ki bani tarihin mama na tunda kin santa sosai. Yaya taji zancen ba inda ta tsammace shiba. A tunaninta zancen auren sani sadiya zata yi mata. Amma sai taji sabanin haka. "Me yasa kike son jin tarihin mamanki? "Yaya haka kawai naji Inason in sani tunda nake ban taba ganin wani nata yazo wajena ba" Tayi ajiyar zuciya "ba haka kawai suka ki zuwa inda kike ba. Akwai dalili. Asalin maman ki mutuniyar jihar katsina ce sunan kauyensu tsakuwa a cikin karamar hukumar dutsimma. Wata rana sunje biki ita da kakarta kauyen kwari dake nan kusa dasu. Kwanansu hudu da tafiya annobar cutar amai da gudawa ta sauka a garin. Mutane da yawa sun mutu a ciki kuwa harda iyaye da dangin mahaifiyarki. Kinsan zaman kauye ba kamar nan ba zaki ga duk dangi ana zaune gida guda ne kowa da matar sa da 'ya'yansa. To su kuma gidansu Maryam duk maza ne ita kadai ce mace a cikinsu. Da annobar nan ta shiga yau a fita da gawa goma daga nan gidan gobe a fitar da biyar sai da jama'ar kauyen nan suka kusa karewa. Wanda suka rayu ma kaura suka yi suka bar garin. Ita ma kakar Maryam ganin basu da kowa ta kulle dan abinda yai musu saura suka yi kudin mota suka nufo kano. Da farko da tazo mai unguwa ne ya basu gida dan karami mai daki biyu yace su zauna a ciki. Furar kakar Maryam take yi tana sayar wa shi yasa duk muke kiranta baba mai fura. Makarantar allo daya mukayi da ita wanda shine ya zamo silar kawancenmu da ita. Kinga hazakar karatun ki to Maryam tace baki iya komai ba. Zuwa wurina da take yi shi kuma kawu isiyaku yazo wajen inna ya ganta ya kuma nuna son aurenta. Inna taso taki a dalilin wai su baba mai fura kararren dangi ne dasu. Basu da kowa. Amma babanmu yaki yarda da wannan ra'ayi nata. Mai unguwa shiya daura mata aure. Mace ce mai tsananin hakuri da kuma mutunta mutane. A dan zaman da mukayi shakuwa ce ba ta wasa ba a tsakanina da ita ba'a dade da aurenta ba itama baba mai fura ta rasu. Mamanki Maryam ce ta roki babanki da yasa miki sunan baba mai fura na asali wato halimatus-sadiya. Idan har mace ta haifa. Kusan ince tunda baba mai fura ta rasu Maryam bata kara cikakkiyar lafiya ba. Saboda tashin hankalin data shiga. Tana ganin ita kadai tayi mata saura. To itama mutuwa ta raba su. Itama Maryam lokacin haihuwarki Allah ya saukar mata da nata ajalin a dalilin hawan jini da ya same ta. Nan asibitin murtala aka kaita kwananta biyu a dakin duhu Allah yayi mata rasuwa. Bata san mai ta haifa ba. Allah ya jikansu da rahama. Sadiya ta share hawayen da ke sauka kan kuncinta tace "Amin. Amma don Allah in kina da hoton ta ki bani in gani"=====****42****===== Ta tashi ta shiga cikin dakinta ta dauko wata leda mai dauke da hotuna da yawa a ciki ta cigaba da duba su daya bayan daya har tazo kan wani mai dauke da mutum biyu dattijuwa da kuma 'yar matashiyar budurwa hoton mai baki da fari ne. Ta mika mata "gashi ranar aurenta akayi mata wannan hoton. Kinga wannan "ta nuna mata dattijuwar wacce suke mutukar kama da dayar itace takwararki watau baba mai fura ga kuma mahaifiyar ki Maryam. Shi kadai ne hoton ta da nake dashi" Ta kurawa hoton ido na tsawon wani lokaci. Kamar tana nazarin wani abu. Can ta nisa tace "Allah ya jikansu. Amma dan Allah ki bani shi zansa a dada daukar min shi sai na dawo miki da wannan din." "Babu komai ki tafi dashi. Ina shi sanin" ta dada tambayarta bayan ta farko da tayi mata dazu da suka gaisa. "Yana gida " ta amsa mata a takaice "yanzu kenan ni bani da kowa "? Yaya taji maganar kamar saukar duka a kanta. Ban gane maganar baki da kowa ba "? "Wai ina nufin bani da inda zan nufa idan wani waje yayi min zafi" karaf wannan kalami nata a kunnen Sani wanda hankalinsa ya kasa kwanciya da ziyararta gidan yayarsa. Ta sanya shi ya biyo sawunta. Sallamar sa ce ta hana yaya bata amsar tambayarta. Tana jin muryarsa wuf tayi ta shige daki. Ya girgiza kansa kawai ba tare da yayi mata magana ba. Tunda ya lura hakan ne bata so. Sun gaisa da yaya kafin ta kira ta ta kawo masa abinci. Ganinsa a falon sai kawai ta shige kicin din yayan da sunan gyara. Ta gama ta kama aikin abincin rana duk don kar ta zauna wuri daya dashi yaje massalaci sallar azahar ya dawo ya ritsa ta a dakin babu hanyar sake guduwa. Amma wani abin takaici duk yanda yaso su tattauna maganar ko don ya samu ya bata hakuri taki. Da yaya ta takura mata ne tace itafa a wajenta komai ya wuce Allah ya basu zaman lafiya da matar shi. Allah kuma ya bada sa'ar karatu. Yayan ce ma tace "Amma itama da ka dai daita zaman ka a can sai kazo ku tafi." dama shine nufina" ya amsa mata. Ita dai uffan bata ce masa ba.=====****42****===== Ta tashi ta shiga cikin dakinta ta dauko wata leda mai dauke da hotuna da yawa a ciki ta cigaba da duba su daya bayan daya har tazo kan wani mai dauke da mutum biyu dattijuwa da kuma 'yar matashiyar budurwa hoton mai baki da fari ne. Ta mika mata "gashi ranar aurenta akayi mata wannan hoton. Kinga wannan "ta nuna mata dattijuwar wacce suke mutukar kama da dayar itace takwararki watau baba mai fura ga kuma mahaifiyar ki Maryam. Shi kadai ne hoton ta da nake dashi" Ta kurawa hoton ido na tsawon wani lokaci. Kamar tana nazarin wani abu. Can ta nisa tace "Allah ya jikansu. Amma dan Allah ki bani shi zansa a dada daukar min shi sai na dawo miki da wannan din." "Babu komai ki tafi dashi. Ina shi sanin" ta dada tambayarta bayan ta farko da tayi mata dazu da suka gaisa. "Yana gida " ta amsa mata a takaice "yanzu kenan ni bani da kowa "? Yaya taji maganar kamar saukar duka a kanta. Ban gane maganar baki da kowa ba "? "Wai ina nufin bani da inda zan nufa idan wani waje yayi min zafi" karaf wannan kalami nata a kunnen Sani wanda hankalinsa ya kasa kwanciya da ziyararta gidan yayarsa. Ta sanya shi ya biyo sawunta. Sallamar sa ce ta hana yaya bata amsar tambayarta. Tana jin muryarsa wuf tayi ta shige daki. Ya girgiza kansa kawai ba tare da yayi mata magana ba. Tunda ya lura hakan ne bata so. Sun gaisa da yaya kafin ta kira ta ta kawo masa abinci. Ganinsa a falon sai kawai ta shige kicin din yayan da sunan gyara. Ta gama ta kama aikin abincin rana duk don kar ta zauna wuri daya dashi yaje massalaci sallar azahar ya dawo ya ritsa ta a dakin babu hanyar sake guduwa. Amma wani abin takaici duk yanda yaso su tattauna maganar ko don ya samu ya bata hakuri taki. Da yaya ta takura mata ne tace itafa a wajenta komai ya wuce Allah ya basu zaman lafiya da matar shi. Allah kuma ya bada sa'ar karatu. Yayan ce ma tace "Amma itama da ka dai daita zaman ka a can sai kazo ku tafi." dama shine nufina" ya amsa mata. Ita dai uffan bata ce masa ba.======****43****====== Haka suka gama yinin su a gidan yaya suka koma amma fa zama ba sauki. Ita dai bata ce masa ci kanka. Amma duk abinda ya sata zatai masa. Magana ce dai take azumin ta. A rana ta uku da ya gaji da zaman kuramen da suke. Yace mata "ai dai Annabi. Cewa yayi in anyi maka laifi ka nuna bacin ranka amma kar ya wuce kwana uku. Kuma in an baka hakuri ka hakura gudun kar ka zama abokin shaidan" Me nayi kuma. Me nace anyi min da har ake dangana ni da shaidan? Abinda Sani yake so kenan ta buda baki tayi magana ko da baka ce ta gaya masa. Kai shi ko zaginsa ne tayi yafi wannan shariyar da take masa. "Rashin maganar kine nake magana akai ya kamata ki hakura ki zauna mu tattauna matsalar mu ". "Ni kam bani da wata matsala da zan tattauna. Rashin magana kuma ina anfani da hadisin da Annabi (s.a.w) ya fadi cewar ka fadi alheri ko kai shiru" Girgiza kansa yayi "Allah ya kyauta" bata bashi amsa ba shima bai sa ran samun amsar taba. "Yanzu so nake yi ki rubuta min abubuwan da kike so keda yara duka in baki kudin ko kuma muje mu sayo ni da ke" "Ai ni zuciyata ta dade da hakura da samun abinda take so tafi raja'a akan abinda ta samu. Haka zalika ta koyi yin hakuri da abinda ta samu din" ya gane magana take son gaya mishi. Naji amma kin san da haka shine kike tambayar yaya inda dangin mama Maryam suke don ki gudu wajen su. Ko shi ba son zuciyar ki kika so biba" "Au dama labe kake mana. Kuma shima inda kake ikirarin zanje din ai zargi ne kake min. Kuma shima dana ga ba samu zanba ai na hakura. Ta mike zata fita "yanzu kenan ba abinda kike bukata. A takaice tace babu "yara fa? Tambayesu ai gasu ban " ta mike da niyyar ficewa. Duk da rashin nuna sha'awarta