Author : Category : Home Of Novels
a ranta. Yanzu haka irin yaran nan ne da soyayya kan rufe musu ido. Su auri soyayya kawai su zo suna fama da wahalar rayuwa. Allahu akbar gaskiya malamai da suka ce 'IYYAKUM WAZZANNA' Wato na hane ku da zato domin zato shine mafi karyar zance. Sister Aisha dai ta gama tunaninta ta shiga falon ta. Ta bude firji ta dauko kwalbar septrin da ta ampiclox da kuma priton sai paracetamol duk na ruwa. Ta bata. Bayan ta nuna mata yadda zata bashi kowanne. Sannan ta umarceta da idan jikin baiyi sauki ba to lallai ta dawo suje ta kaita taga likita. Washegari kuwa sai gata da kanta 'yar malama umma hafsa ta rakota gidan. Ganin yara da yawa a gidan suna lesson da uwarsu ya bata mamaki. Take ta cire duk wani zato da take yi mata. Ta zauna suka gaisa ta tambayeta yaya mai jiki. Nan ta nuna mata shi yana ta wasan sa. Sadiya ta bude firji dinta ta dauko lemon data hada na matsatsatten lemon tsami da kuma danyar citta wato ginger drink ta kawo mata cikin jug ta doro akan tire da kuma kofinsa. Gaskiya sister irin mutanen nan ne masu tsantsani da kuma rashin ganin abin burgewa a tare da wani in basu ba. Amma tsaftar gidan sadiya yau kam ta kure ta. Ga yara fes fes dasu. Gida ko ina sai kamshin turaren wuta dan tsinke yake yi ga kuma lemo mai dan Karen dadi da bata taba shan irin saba. Kusan duk ginger da take gani zata ganta tayi duhu alamar bata kankaru ba. Amma wannan shar da ita. Ta yaba mata kwarai har ta bata shawarar data dinga yin na sayarwa. Ai kuwa tayi murna da wannan shawarar data bata. Dama ga fridge dinta da Sani ya sai musu lokacin daya dauki wani kudin sa a kumbotso. Tare ya hada musu da talabijin da kuma decoder ta ABG Da video. Wannan zuwa na sister gidan sadiya shiya sanya ta shiga cikin jerin masu kawo mata wanki. Ba domin Komai ba sai taftarta data yaba da ita. Kudin wankin da sister ta biya ta dashi ta saro kayan yin ginger. Da farko shagon mustafa ta fara kaiwa ai kafin kace meye wannan ya kare sai dai kudinta. Ga na gida da take bari shima in aka dinga sallama mussaman wata dabar samari da suke kusa da gidan. Da suka gane ba karamin ciniki suke mata ba.=====*****53*****===== Wani abin haushi kawai sai ga huwaila tazo wai ta koya mata yadda ake yi itama zata fara. A lokacin suna tare da hafsa. A gabanta ta hada komai ta nuna mata yadda zata yi. Hafsa dai nata kumbure kumburen jin haushi. Sai da ta fita tace. "Allah umman kamal mai yasa kika nuna mata. Kowa yaje ya koyi nasa. Mamaki ne ya kama sadiya na wannan magana da hafsa tayi. Ta rike baki tace "anya hafsa inace ni dake jiya da muka dauki karatu a wajen malama tayi mana bayanin hadisin da aka ce komai ya same ka bai kasance zai kuskure ka ba haka nan komai ya kuskure maka bai kasance zai same ka ba. Kowa da rabonsa a kasuwar nan. Ta tura bakinta tace. "Ai da ita ce baza ta koya miki ko da yake ma tayi wa zai sayi kayan wannan kazamar matar. "Uhm uhm hifzu lisaniy. Ki kiyaye harshen ki. "Wai astagfirullah ashe fa gulma ce nayi. Ta fada cikin dariya.=====*****53*****===== Wani abin haushi kawai sai ga huwaila tazo wai ta koya mata yadda ake yi itama zata fara. A lokacin suna tare da hafsa. A gabanta ta hada komai ta nuna mata yadda zata yi. Hafsa dai nata kumbure kumburen jin haushi. Sai da ta fita tace. "Allah umman kamal mai yasa kika nuna mata. Kowa yaje ya koyi nasa. Mamaki ne ya kama sadiya na wannan magana da hafsa tayi. Ta rike baki tace "anya hafsa inace ni dake jiya da muka dauki karatu a wajen malama tayi mana bayanin hadisin da aka ce komai ya same ka bai kasance zai kuskure ka ba haka nan komai ya kuskure maka bai kasance zai same ka ba. Kowa da rabonsa a kasuwar nan. Ta tura bakinta tace. "Ai da ita ce baza ta koya miki ko da yake ma tayi wa zai sayi kayan wannan kazamar matar. "Uhm uhm hifzu lisaniy. Ki kiyaye harshen ki. "Wai astagfirullah ashe fa gulma ce nayi. Ta fada cikin dariya.****54*****===== Da wannan wanki da kuma ginger drink dinta data kiyi. Ta rike yaranta a haka kuma kaga har alheri take yi. Kusan duk inda akayi haihuwa a makotansu ko kuma ana biki dai-dai abinda Allah ya hore mata zata baka. Ba kuma da niyyar biki don a rama mata kamar yadda mafi yawan mata kanyi ba. Ginger kam ai ta karbu. Tun da tun daga babban layi sai a zo a saya. Wasu ma in zasuyi biki ko suna. Sukan bata tayi mai yawa. Dan asusu ta samu take tara kudinta da niyyar ta saka su walid da imam makaranta. Wata rana taje ta gaida yaya kulu kamar yadda ta saba tanayi lokaci-lokaci ta sauka daga hayis. Taga signboard na wata makarantar koyon dinki da aka bude anan unguwarsu. Ba tare da bata lokaci ba. Ta shiga ta tambaya aka gaya mata nawa ake biya. Ta karbo form ta dawo gida. Ga koshi ga kwanan yunwa. Kudi dai da zata shiga makarantar nan tana dasu. Ga kuma su walid 'yan shekara biyar da taso su shiga makaranta wannan shekarar. Tunda karatun da ta koya musu a gida ba makarantar kudin da baza su iya shiga ba kuna radam su zauna. In ta gwamnati ce kuwa ko dan aji uku ba zai nuna musu komai ba. A dan lesson din da tayi dasu. Rashin sanin iya abinda ya kamata yara su koya a kowanne zangon karatu yasa ta tsallake ba tare da ta sani ba. Ga haddar da suke yi A wajen malam mai salati wadda kamal ne kawai bai fara zuwa ba. Ga kuma islamiyya da suke zuwa. Ai yara kam karatu radam ba Arabi ba ba boko ba. Kamar yadda ta saba bata cika shawara da kowa ba don gudun tonan asiri. Diary ta dauko ta rubuta matsalarta. Takan ji damuwa ta ragu a zuciyarta duk sanda ta rubuta ta a dan littafin nan. Da daddare kuwa istikhara tayi ta nemi zabi a wajen RABBIL IZZATI. Washegari da ta tashi kuwa sai taji hankalinta yafi kwanciya da ta shiga makarantar koyon dinkin nan. Tun da dai karin samun kudin shiga ne. Ta san Idan yara suka fara makaranta wanki da kuma lemon ginger bazai rike suba. Kuma ko banza ta huta da wankin nan mai azaba. Da wasu zasu kawo maka shi ba sabulun kirki sai kaya masu uwar dauda kayi ta dirza kafin su fita. Inka gama kuma ace za'a aiko ma da kudin. Wani haka zai mula bazai biya ba. Kowacce karuwa bata zuwa sai da matsala. Ita wadda ta hararo yaya zata yi da yara in ta fara zuwa makarantar. Har ta hakura saboda bata ga yadda zata yi da yaranta ba. A wannan jumma'ar taje gaida gwaggon Rahina kamar yadda ta saba. Lokaci-lokaci tana jin dadin hira da tsohuwar nan. Bayan sun gaisa labari ya kawo labari har take bata labarin makarantar data so shiga amma saboda yara ta hakura. "Wane irin hakura ba dadin ji. Gwaggo ta fada. Cikin murya mai nuna alamun rashin jin dadi. "Tattara su ki dinga kawo min su har shi wannan da kika mannewa kin ki rabuwa da wahalar sa sai anyi magana kice wai maraya ne. In ba iya shege ba ace yaro ya haura shekara biyu amma bai wuce goyo ba. Duk kawo su. Suma samu haddar ta dada nisa har shima wannan din. "Amma gwaggo baza su wahalar dake ba. Babu wata wahalar wa. Kuma wata uku kamar yaune. Yo ni duk wanda yayi min a cikinsu ramawa zanyi bazan yadda a ce ni babba bace. Dariya suka saka tare. Ta dan dada kaskantar da murya "Amma gwaggo banda kamal shi sai in dinga tafiya dashi. "Har shi zaki ajiye. Duk wannan makon nasa da kema naki ajiye shi zakiyi. Dama ina cike dashi rannan da kuka zo kika shiga bandaki ya tsaya a kofar bandakin duk sai da ya hada gidan nan. Malam tun daga soro ya taho yana tambayar meya same shi. Ni dan haushi ma kasa magana nayi sai murtala ne yake gaya masa abinda ya faru. "Kai gwaggo sa ido ne kawai irin na murtala kuma shi da yake kawu ai baya biye muku ba tunda ke bakya auren. Haka kuwa akayi da wannan shawara ta gwaggo taci gaba da zuwa koyon dinki. Da sauran kudin da kuma ciniki ginger na wannan zafin ta hada ta sai keken dinki ta ajiye a gida. Allah na taimakon duk wanda ya taimaki kansa. Sadiya wata iri ce. Duk abinda tasa kanta koyo to kuwa sai ta zarce makadi da rawa. Ai kan kace kwabo ta koyo yanka da taku. Kai ganin haka ma a maimakon wata uku da tai niyyar yi sai. Sai kawai ta biya ajin kos din wata shida. Kwalliya kuwa ta biya kudin sabulu. Sadiya ta fito a matsayin kwararriyar tela mai daraja ta farko wato fist class inji masu digiri. Kamar da wasa ta fara dinki. Da yake abin na Allah ne kafin karshen shekarar nan sai da aka santa da dinki a unguwarsu. Wata karin fasaha data samu daga gareta shine dinka kayan 'yan kanti abdulsalam dan wajen yaya kulu na uku ya kawo mata ziyara. Sai taga wani yadi mai kyau a jikinsa. Ta tambaye shi ina ya sayo ya gaya mata a nan kofar wambai ake kawo su a kayan gwanjo amma sababbi ne. Shiya rakata taje ta siyo domin ta dinka wa su walida 'yan riguna. Wani littafin mother care ta samu a wajen sister mai dauke da hotunan kayan yara masu mutukar kyau da kuma tsari tana dubawa ta samo kalolin riga da siket da kuma dogayen riguna iya gwiwa na yara masu kyau. Da yadin nan da ta sayo ta gwada dinka wa. Haba wai aida ta sa musu a jikinsu kai kace 'ya'yan turawa ne dan kyau da suka yi. Ai wannan shi ya zamo mata mai talla shi ke da riba. Malama umma ita ta fara tambayarta inda ta samo musu riguna masu kyau. Har tana fadin idan ba tsada in sayo wa 'yar kanwata. Ta gaya mata cewa dinka wa tayi. Tayi mamaki mutuka. Tace "dama har da kayan 'yan kanti aka koya muku a makarantar.? Ta amsa mata cewar karanbani kawai tayi ta dinka wa yaranta. Ta yaba da fasahar sadiya matuka. Itace kwastoma ta farko a wannan cinikin. 'yan unguwa suka yaba da kayan suma aka dinga zuwa saye. Da wannan ta fara. Shima kuma tana samun ciniki matuka da alheri akai. Wanda take sayen yadi a wajen sa kuwa da ya samu sababbin yadudduka zai turo yaronsa har gida ta zabi wadanda take so ya karbo masa kudinsa.****54*****===== Da wannan wanki da kuma ginger drink dinta data kiyi. Ta rike yaranta a haka kuma kaga har alheri take yi. Kusan duk inda akayi haihuwa a makotansu ko kuma ana biki dai-dai abinda Allah ya hore mata zata baka. Ba kuma da niyyar biki don a rama mata kamar yadda mafi yawan mata kanyi ba. Ginger kam ai ta karbu. Tun da tun daga babban layi sai a zo a saya. Wasu ma in zasuyi biki ko suna. Sukan bata tayi mai yawa. Dan asusu ta samu take tara kudinta da niyyar ta saka su walid da imam makaranta. Wata rana taje ta gaida yaya kulu kamar yadda ta saba tanayi lokaci-lokaci ta sauka daga hayis. Taga signboard na wata makarantar koyon dinki da aka bude anan unguwarsu. Ba tare da bata lokaci ba. Ta shiga ta tambaya aka gaya mata nawa ake biya. Ta karbo form ta dawo gida. Ga koshi ga kwanan yunwa. Kudi dai da zata shiga makarantar nan tana dasu. Ga kuma su walid 'yan shekara biyar da taso su shiga makaranta wannan shekarar. Tunda karatun da ta koya musu a gida ba makarantar kudin da baza su iya shiga ba kuna radam su zauna. In ta gwamnati ce kuwa ko dan aji uku ba zai nuna musu komai ba. A dan lesson din da tayi dasu. Rashin sanin iya abinda ya kamata yara su koya a kowanne zangon karatu yasa ta tsallake ba tare da ta sani ba. Ga haddar da suke yi A wajen malam mai salati wadda kamal ne kawai bai fara zuwa ba. Ga kuma islamiyya da suke zuwa. Ai yara kam karatu radam ba Arabi ba ba boko ba. Kamar yadda ta saba bata cika shawara da kowa ba don gudun tonan asiri. Diary ta dauko ta rubuta matsalarta. Takan ji damuwa ta ragu a zuciyarta duk sanda ta rubuta ta a dan littafin nan. Da daddare kuwa istikhara tayi ta nemi zabi a wajen RABBIL IZZATI. Washegari da ta tashi kuwa sai taji hankalinta yafi kwanciya da ta shiga makarantar koyon dinkin nan. Tun da dai karin samun kudin shiga ne. Ta san Idan yara suka fara makaranta wanki da kuma lemon ginger bazai rike suba. Kuma ko banza ta huta da wankin nan mai azaba. Da wasu zasu kawo maka shi ba sabulun kirki sai kaya masu uwar dauda kayi ta dirza kafin su fita. Inka gama kuma ace za'a aiko ma da kudin. Wani haka zai mula bazai biya ba. Kowacce karuwa bata zuwa sai da matsala. Ita wadda ta hararo yaya zata yi da yara in ta fara zuwa makarantar. Har ta hakura saboda bata ga yadda zata yi da yaranta ba. A wannan jumma'ar taje gaida gwaggon Rahina kamar yadda ta saba. Lokaci-lokaci tana jin dadin hira da tsohuwar nan. Bayan sun gaisa labari ya kawo labari har take bata labarin makarantar data so shiga amma saboda yara ta hakura. "Wane irin hakura ba dadin ji. Gwaggo ta fada. Cikin murya mai nuna alamun rashin jin dadi. "Tattara su ki dinga kawo min su har shi wannan da kika mannewa kin ki rabuwa da wahalar sa sai anyi magana kice wai maraya ne. In ba iya shege ba ace yaro ya haura shekara biyu amma bai wuce goyo ba. Duk kawo su. Suma samu haddar ta dada nisa har shima wannan din. "Amma gwaggo baza su wahalar dake ba. Babu wata wahalar wa. Kuma wata uku kamar yaune. Yo ni duk wanda yayi min a cikinsu ramawa zanyi bazan yadda a ce ni babba bace. Dariya suka saka tare. Ta dan dada kaskantar da murya "Amma gwaggo banda kamal shi sai in dinga tafiya dashi. "Har shi zaki ajiye. Duk wannan makon nasa da kema naki ajiye shi zakiyi. Dama ina cike dashi rannan da kuka zo kika shiga bandaki ya tsaya a kofar bandakin duk sai da ya hada gidan nan. Malam tun daga soro ya taho yana tambayar meya same shi. Ni dan haushi ma kasa magana nayi sai murtala ne yake gaya masa abinda ya faru. "Kai gwaggo sa ido ne kawai irin na murtala kuma shi da yake kawu ai baya biye muku ba tunda ke bakya auren. Haka kuwa akayi da wannan shawara ta gwaggo taci gaba da zuwa koyon dinki. Da sauran kudin da kuma ciniki ginger na wannan zafin ta hada ta sai keken dinki ta ajiye a gida. Allah na taimakon duk wanda ya taimaki kansa. Sadiya wata iri ce. Duk abinda tasa kanta koyo to kuwa sai ta zarce makadi da rawa. Ai kan kace kwabo ta koyo yanka da taku. Kai ganin haka ma a maimakon wata uku da tai niyyar yi sai. Sai kawai ta biya ajin kos din wata shida. Kwalliya kuwa ta biya kudin sabulu. Sadiya ta fito a matsayin kwararriyar tela mai daraja ta farko wato fist class inji masu digiri. Kamar da wasa ta fara dinki. Da yake abin na Allah ne kafin karshen shekarar nan sai da aka santa da dinki a unguwarsu. Wata karin fasaha data samu daga gareta shine dinka kayan 'yan kanti abdulsalam dan wajen yaya kulu na uku ya kawo mata ziyara. Sai taga wani yadi mai kyau a jikinsa. Ta tambaye shi ina ya sayo ya gaya mata a nan kofar wambai ake kawo su a kayan gwanjo amma sababbi ne. Shiya rakata taje ta siyo domin ta dinka wa su walida 'yan riguna. Wani littafin mother care ta samu a wajen sister mai dauke da hotunan kayan yara masu mutukar kyau da kuma tsari tana dubawa ta samo kalolin riga da siket da kuma dogayen riguna iya gwiwa na yara masu kyau. Da yadin nan da ta sayo ta gwada dinka wa. Haba wai aida ta sa musu a jikinsu kai kace 'ya'yan turawa ne dan kyau da suka yi. Ai wannan shi ya zamo mata mai talla shi ke da riba. Malama umma ita ta fara tambayarta inda ta samo musu riguna masu kyau. Har tana fadin idan ba tsada in sayo wa 'yar kanwata. Ta gaya mata cewa dinka wa tayi. Tayi mamaki mutuka. Tace "dama har da kayan 'yan kanti aka koya muku a makarantar.? Ta amsa mata cewar karanbani kawai tayi ta dinka wa yaranta. Ta yaba da fasahar sadiya matuka. Itace kwastoma ta farko a wannan cinikin. 'yan unguwa suka yaba da kayan suma aka dinga zuwa saye. Da wannan ta fara. Shima kuma tana samun ciniki matuka da alheri akai. Wanda take sayen yadi a wajen sa kuwa da ya samu sababbin yadudduka zai turo yaronsa har gida ta zabi wadanda take so ya karbo masa kudinsa.****54*****===== Da wannan wanki da kuma ginger drink dinta data kiyi. Ta rike yaranta a haka kuma kaga har alheri take yi. Kusan duk inda akayi haihuwa a makotansu ko kuma ana biki dai-dai abinda Allah ya hore mata zata baka. Ba kuma da niyyar biki don a rama mata kamar yadda mafi yawan mata kanyi ba. Ginger kam ai ta karbu. Tun da tun