Chapter 12 Reading WACE CE UWA Complete Hausa Novels.txt Arewa Novels

WACE CE UWA Complete Hausa Novels.txt

Author :  Category :  Home Of Novels

Chapter   12 / 15

33K to 36K   out of 42.5K words

daya hau kaina" inna uwa ce ya san biyayyarsa tafi bukata zai kuma yita iya kacin karfinsa. Ita kuwa sadiya matarsa soyayyarta ta gama ginuwa a zuciyarsa. Kyautatawar sa take bukata sai asma'u da zai fara rayuwa da ita yanzu. Soyayya dai yasan babu sai dai a hankali bai sani ba ko zata ginu kamar zaman sa da zainab da kuma rahina. "Halimatu na yarinya mai kyawun asali kyawun kuma na zahiri dana badini Allah ya bani ikon kyautata miki da kuma fita daga hakkinki ina kuma fatan Allah ya sanyaya miki zuciya ki yafe min duk abinda nayi mik=====****48****===== Motsin Asma'u ne ya dawo dashi daga tunane tunanen da yake yi. Wanda ya fara tunda suka baro nigeria anan ya fahimci captain din jirgin yana mai sanarwa kowa daya daura belt din kujerarsa domin jirgi ya iso jedda inda zasu sauka. Bayan sun kammala da diban kayansu a airport din jedda suka sake hawa wani jirgin domin zuwa babban birnin saudiya wato riyadh inda ofishin jakadancin nigeria yake. Anan ma kwana daya kawai suka yi suka sake hawa wani jirgin domin isa dammam inda makarantar da zasu shiga don yin karatu shida sabuwar amaryarsa take. Basu samu damar fara amarci ba sai da Sani ya kammala da registration din karatunshi ya kuma yi reporting a wajen aiki. Itama ta kammala da nata. Gidansu dan madaidaici wanda hukumar makaranta ta basu. Daku nan bacci uku da falo biyu da kuma banda kuna guda uku sai katon kicin babu ce kawai babu a cikinsa. Haka nan dakunan kowanne da kayan gado set. Hatta da zannuwan gado an ajiye musu. Suma falukan guda biyu kowanne a tsare yake da kujeru carpet labilaye da kuma kayan kallo. Gidan nasu yana rukunin gidajen kananan malaman jami'ar dogon bene mai hawa ashirin. Su kuma suna hawa na goma sha biyu. Amarci dai kam an sha shi tsakanin asma'u da Sani. Ita kam duk yadda take tsammanin samun shi ya zarta mata haka. Ta kuma yaba masa kwarai. Ta tabbatar wa kanta batayi zaben tumun dare ba. Tsaftarsa da kuma yawan ibadarsa su suka fi birgeta dashi. Duk da bashi da yawan magana amma 'yar hirar da su kan yi da ita tana burgeta. Saboda ko banza tana karuwa dashi da kyar kaji magana marar amfani ta fito daga bakinsa. Asma'u bata gama sanin waye sani ba shiyasa ta gamsuwa da yadda ta same shi. Data taba katarin ganin irin sakankancewar da yake da sadiya da bata yi masa wannan yabo ba. In yana tare da sadiya yana bata dariya wani lokacin har rokonsa take yi daya daina kar cikinta ya kulle. Har rawa wani lokacin yake yi mata idan yaso. Labaran ban dariya kuwa har ta rasa ina yake samo mata su wasu ma sai taga kamar hada su yake da kansa. Sadiya ce kadai filin da yasan zai baje kolinsa ko wane iri ne. Na dadi ko kuma na rashin dadin. Ita kuma har abada tana da store da zata adana masa kayan da ya baje matan. Sati biyu yayi agida yana hutawa kafin ya fara karatu da karantarwa ka'in da na'in haka itama Asma'u lokaci daya suka shiga makaranta tare inda zata yi shekara biyu domin ta samo digirinta na biyu. Yayin da shi kuma zai shekara uku ne wajen hada nasa digirin. Allah ya bada sa'a.=====****49****====== A nan gida Nigeria sadiya ce kwance a doguwar kujerar dake falon ta. Walid da imam suna wasan su. Yayin da shukra da kuma walida suma sun tara 'yan tarkacen tukwanen su na kasa suna wasa. Ita kuwa jidda ta takarkare da biro da takarda wai nan ala dole rubutu take yi. Kamal kuwa dan gata sai ya hau kan ummansa ya sauka kamar ya sami doki. Tunani ne fal a zuciyarta. Dole ta san yadda zata tsara rayuwarta da kuma ta 'ya'yanta. Walid da imam sun isa shiga makarantar nursery amma babansu yayi mata romon baka yace ta bari sai sunje saudiya sai a saka su. Tuno sunan kasar kawai bata mata rai yake yi. Ballantana ta tuno da bakin da tuni sun sauka a kasar. Wannan su suka sani ta sake fadi a cikin ranta yanzu vita 'ya'yana nake yi. Wannan magana na fado mata a rai tayi zumbur ta mike daga kwanciyar da tayi. Kamal yasa kuka na rashin yarda da tashi da dokinsa yayi. "Yi shiru dan gidan ummansa. Bari mu tsara yadda zamu gudanar da rayuwarmu. Ai ni kuma kwanciya bata same niba. Duk da bai san abinda take fadi ba amma muryar rarrashin da tayi anfani da ita wajen tausarsa tasa shi yayi shirun. Biron hannun jidda ta karba tana fadin "yayata ara min biron ki. Umma kinga na rubuta A" ta fada yayinda ta isa wajenta tana nuna mata jagwalgwalon da tayi. Eye jiddan ba inaga dai ke malamar makaranta ce kullum cikin rubutu. To bani aron biron ki kuma dauko min littafi akan drawer gefen gado" ta mika mata ta kuma shiga dakin don dauko abinda aka aiketa. Sai da ta nutsu sannan ta nisa tayi tunani sannan ta dauki takarda ta fara rubutu kamar haka. ABUBUWAN DA 'YA'YANA SUKE BUKATA DAGA WAJENA Ta rubuta da manyan baki bayan jidda ta kawo mata littafin ta rubuta ta karanta abinda ta rubuta ta soke wannan ta rubuta waccan har ta kammala ta kuma gamsu da abinda ta rubuta din list din da tayi ya kasance kamar haka: Abinci Sutura Kiwon lafiya Ilimi Tarbiyya Ta dauki kowanne daya kamar mai yin note din makaranta. Misali da ta dau abinci. A kasan sa ta rubuta yaya zan samar wa yarana abinci. Haka nan tayi ta tsare tsaren ta a rubuce har ta gamsu ta yiwa kanta tanadi mai kyau. Anan kuma wani babban tunani yazo mata. Dame zan samar mana yadda zamu aiwatar da tsare tsaren rayuwarmu? Da biron ta rubuta ban sani ba amma Allah zai shige mana gaba. Wannan rubutu da tayi sai taji kamar da wani ta tattauna wannan damuwar tata har kuma taji kamar shawara wani ya bata. Hakan yayi mutukar taimakawa wajen rage damuwarta. Ta sake duba littafin. Diary da aka bawa yayanta ce ta makarantar da yayi koyarwa. Wato kumbotso. Sai yanzu ta gano hikimar Amir da kusan kullum sai ya rubuta abubuwan da yayi a diary dinsa. Wato ashe abokiyar hira ya samu su suna masa dariya da ganin wautarsa ita da Amira. Allah sarki su Amira ko suna ina? Da tasan inda zata gansu data neme su. A gaskiya bata taba jin tayi maraicin wani nata kamar yadda tayi maraicin su ba. Wannan tunani da tayi shi ta rubuta a kawar sirrinta kamar yadda tasa mata suna. Yanzu ta fahimci me suke bukata ita da yaranta. Sai kuma tayi tunanin yadda zata samar musu dashi. Abu na farko da suke bukata shine kudin da zasu tallafi rayuwarsu. Me akeyi a samu kudi? Zuciyarta ta tambayeta." Aiki ko sana'a "Ta bawa kanta amsa wanne ne ba wanne ne ba. Inji falsfa. Aiki dai bata da karatun da zata yishi. Sana'a kuma bata da jarin da zata fara. In kuma aikatau zata koma gidan mutane tasha jin kawayen momi in suna neman mai aiki sukan ce basa son mai yara. To ita kuwa yara harda yarori sun mata katutu. Ta kalli jerenta ta san da ta cire shi ta sayar yan unguwa zasu fahimci abinda take ciki. Wannan kuwa bashine burinta ba. Ta juya ta sake kallon yaranta "Allah ka kawo min mafita." Sallamar Dija ce ta katse mata tunanin da take yi. Bayan sun gaisa ta dan zolayeta "munje biki mun gwangwaje munsha party amma kinki zuwa. Inma kishi ke damunki gwanda ki sauke shi kin dai ga yayana me tsada ne masu so da yawa" I zuwa yanzu ta saba da bakaken maganar Dija har basa bata mata rai. To ita bayan abinda Sani yayi mata akwai wani abu da zai bata mata rai. Ai sai dai rabuwa da yaranta. Dariya kawai tayi. "Yaya Dija ba fa ki gayyace niba. Kuma kinsan ance haramun ne halartar biki ko walimar da ba'a gayyace kava. In kaje kaci wani abu to kaci haramun. Gudun haka yasa naki zuwa. Yayan ki kuma kinga ai na hakura na barwa mai so kinga babu sauran damuwa " "Gaskiyarki to kizo kiga gara inji inna." Dija ta gaya mata "Wai Allah na kinga ki bawa inna hakuri zan shigo anjima kinga yanzu ga ayyukan gida nan ban karasa ba. Kuma ga su walid yanzu zasu bukaci abinci kuyi hakuri dana gama zan shigo. Sadiya ta fada mata. "Hm inji Dija. "Ai ke dama har abada 'ya'ya ba zasu barki ki sake ba. Uwar 'ya'ya da anyi magana kice yara.***50*****====== Tana dariya ta bata amsa "kai yaya Dija ba haka bane zan shigo yanzun nan. "Ai dai an fita hakkinki tunda an gaya miki " ta fada mata yayin da take fita daga gidan. Murmushi kawai ta bita dashi. Sai bayan la'asar ta shiga gidan inna don tayi mata ban gajiya. A tsaitsaye suka gaisa da inna hankalinta na kan rabon kayan garar da aka cika musu tsakar gida dashi. Kayan abinci komai buhu goma tun daga shinkafa ta dafawa data tuwo. Sai kuma katan katan na su macaroni da taliya da kuma kus-kus suma goma- goma haka nan maimakon gero ko daya sai aka sa musu buhunhunan semovita masavita da kuma gyararren tsakin masara da akeyi a kamfanin fulawa na maiduguri. Kayan zaki ma su nakiya da alkaki dubulan bakilawa da kuma gireba suma gasu nan Bila adadin. Daga gefe kuma ga wasu akwatinan guda biyu daya shadda da boyel kowanne goma-goma da kuma huluna suma goma. Sai daya akwatin mai dauke da turamen atamfa suma guda goma. Duk 'yan holland sai kuma tarin samiru da dankwalaye na dangi. Ita dai da taga duk hankalinsu na kan kayan harda su huwaila sai tayi musu sallama ta wuce gidanta. Bata dade da shigowa ba saiga yara an doro musu buhun shinkafa da kuma macaroni da taliya gami da buhun semovita. Su kawo mata. Tayi musu godiya matuka ta kuma basu tukuici. Bata gaji ba da daddare ta sake koma wa gidan inna a tsaitsaye tayi mata godiya. Saboda gaba daya yaran suna gida. Sunyi bacci ta kulle su tazo. Anan din ma bata samu tarbar kirki ba saboda su yaya baba da suka gwagwafe ana ta daga shaddojin da aka kawo na kan gara. Ko wacce ya daga sai ya ajiye gefen sa yana fadin wannan ma ina sonta Dija ta gaji da hadamarsa tace to kai duka shaddojin zaka kwashe kowama yana so ai. Sai kace kaine angon" "Ke wallahi na babbalaki yanzun nan. Uban me zakiyi da shadda. Ko don ki kaiwa wannan mijin naki mara zuciya. Ya ki aiki ya zauna sai dai komai ai masa. "Marasa zuciya dai" ta amsa masa tare da murguda baki cikin fitsara ta cigaba da cewa "gwanda shi korarsa akayi daga aiki. Yafi wanda bai taba gwada aikin ba. Da kyar inna ta shiga tsakaninsu. Ita dai sallama tayi musu ta fita daga gidan. Washe gari ta tashi ta gama ayyukan ta kamar yadda ta saba. Jidda ce ta dauko takarda da biro tana fadin"rubuta min A" ai kuwa fadar haka taji wani kwan fitila akanta mai haske ya kunnu wani tunani mai dadi ya darsu a zuciyarta. Zuciyar tace take fadin mai zai hana ki yiwa yaranki home study kamar yadda Dadi da Momi suka yi miki kafin ki samu kudin sakasu a makaranta. Kamar wadda aka mintsina ta mike ta shiga daki purse dinta ta ciro kudi ta kuma karbi biron hannun jidda da kuma takarda ta rubuta list ta bawa walid tace " ungo yi sauri jeka shagon mustafa kace ya baka abubuwan dana rubuta. Walid da imam sun saba zuwa shagon bashi da nisa dasu. In abinda take so yana da yawa saita rubuta musu gudun shirme shi kuma mustafa idan ya karanta sai ya zubo musu a leda idan da sanji ya kulle musu a wata ledar don kar su zubar. Da saurin sa ya dawo ya kawowa ummansa sakon ta. Pencils ne guda biyar da cleaner itama biyar da kuma shapner sai kuma littatafan rubutu dana lissafi suma guda biyar-biyar. Anan tsakiyar falonsu akan teburin tsakiyar falon su ummansu ta bude ajinta na farko. Da 'ya'yanta a matsayin dalibanta. Ilimi ko wanne iri ne anfani ne dashi. Kullum kafin karfe tara na safe ta gama duk gyaran gidanta. Tana yi yaranta suna taya ta kaye kaye idan sun gama ta kulle kofar gidanta ta zauna tana koya musu karatu da rubutu da kuma lissafi dai-dai kwakwalwar su. Yara sun sha nonon hazikar uwa. Haba wa kan kace meye wannan sun dauke A-Z da 1-10. Duk suna gane su. Baza su tashi ba sai kusan sha daya na safe. Da la'asar kuwa kakan kamal ne malam mai salati zai turo daya daga cikin almajiran sa ya tafi dasu. Da kansa yake biya musu karatun Alqur'ani mai girma. Idan an tashi kuwa har da dan hasafinsu zaka ga yasa an dawo dasu.======*****51*****====== Wata rana da sadiya taje gaisheshi tace "kuma malam su kullum basa kawo kudin laraba sai dai su biyo su kwace maka naka" dariya ya saka sosai. "Yace kyale su ai dashi nake zubawa, ina nan ina rubutawa duk sai na karba har da riba" godiya tayi masa sosai shi kuma yana fadin halima mune da godiya. Dawainiyar da kike da kamal ba abinda zamu ce miki sai dai godiya. "Babu komai malam ni dai ku taya ni addu'a akan yaran nan gaba dayan su. Rayuwa yanzu tsoro take bani mussaman akan tarbiyyar yara." "Addu'a kullum a cikin yinta muke. Ke dai Allah yayi albarka. "Amin malam. Bari na shiga na gaida gwaggon rahina naji jiya su imam sunce bata da lafiya." "Ai dan zazzabi ne ya kama ta jiya tama ji sauki. Ya amsa mata. Ta mika masa kullin goro farare manya. "Malam gashi inji su walida. "Ke kam ba kya gajiya da dawainiya. Nagode Allah ya saka da alheri. Ta amsa sannan ta shige cikin gidan. Suma bayan sun gaisa sai da ta bata sabulun wanki guda uku. Wannan hali na sadiya duk da bata dashi amma hakan baya hanata alheri. Gwargwadon iyawarta. Takan tuna da fadin momi da takan ce musu kar kuce sai kun gama biyan bukatar kanku sannan za kuyi alheri. Dan adam bukatarsa bata taba karewa. Ku dinga kokarin bayar da abinda kuke so. Malam mai salati shine mahaifin Rahina ita kadai da kaninta suka haifa. Suma din saida girma ya fara kamasu suka same su. Bayan rasuwar rahina yayi musu saura murtala kawai kanin ita rahinan. Sadiya kuwa tana kokarin kyautata musu. Mussaman da Sani yana aiki a kumbotso. Tun da samun nasa ba laifi. Su kuma sun dau 'ya'yanta daya da jikansu kamal. Kasancewar sa mai almajirai ba makarantar islamiyya ba yasa yake koyar da yaranta karatun hadda. Duk ranar alhamis da jumma'a in suka tafi tun bayan azahar to sai la'asar lis zaisa murtala ko wani almajirin sa ya dawo dasu gida. Kasancewar shi gidansa yana bayan nasu layin Zuwan da su walid suke yi gidan malam mai salati shiya bata damar itama idan sun tafi ta shiga wajen malama umma daukar karatu. Takan biya mata littatafan fiqhu da hadisi da kuma karbar haddar qur'ani data cigaba dayi a wajenta. Kayan abincin da inna ta aika mata na garar mijinta zai dauke su lokaci mai dan dama amma babu kudin cefane balle na omo da sabulu. Suma kuma dole ne. Sadiya taga da karfinta da lafiyarta sai ta sanar wa su malama umma Makotanta duk wanda yake da wanki ya kawo har gida zata yi masa. Fita aiki kam ta san ba zai yiwu a wajenta ba.*52*****===== Ta fara karbar wanki tana yi kwandala- kwandala ko zanin gado ne kwandala ce. Haka kuma ko dankwali ne kwandala ce. Ita dai bata taba zuwa ta roki kowa ba. Balle su inna da suke zargin mijinta ya lafta mata dukiya kafin ya tafi. Kayan garar ma da kyar suka bata. Saboda handama da babakere na yaya baba. Duk sanda yaya kulu tazo taga gidanta cike da shanya sai tayi mata karyar makota ne suka yi shanya. Saboda tasan gaya mata daga mata hankali za tayi akan abinda bata da magani. Kuma tayi sa'a bata cika zuwa ba sai dai aike. Dama Abdurrahman ne mai zuwa akai-akai to shima ya sami shiga jami'ar Ahmadu bello dake zaria domin karatun medicine. Akwai wata ma'aikaciyar asibiti mai suna sister Aisha farkon haduwarsu ya faru ne wata rana da kamal ya kamu da wani irin zazzabi da kuma mura hankalinta ya tashi. Da saurin ta ta nufi gidan malama umma. Ita ta raka ta wajen sister Aisha. Ta duba shi ta sanar da ita kyanda ce amma bata kama shi sosai ba. Ta bata shawarar ta daure taje asibiti washe gari. Tayi shiru tana nazari kasancewar yanzu asibitocin sai a hankali indai zaka to kudi ne tsababa a kanka. "Sister indai zai yiwu ki taimaka ki rubuta min maganin ba sai naje asibiti ba. Ina maigidan ki? Ta tambayeta kafin malama umma tayi magana tayi saurin fadin "baya gari yayi tafiya. Ta kalle ta 'yar yarinya karama da ita da gani haihuwar fari ce amma ta fara haduwa da jula-jular namiji. In ba haka ba ya zaka tafi kabar mace da yaro ba ko abinda zasu sayi magani dashi. Yara kuma da ba wuya sun hadu da rashin lafiya ko kuma tsautsayi. "To ke ba kya komai da za ki taimaki kanki. "Sister ina yi. Wanki nake yi a gida kwandala - kwandala. "Wanki" ta fada tana mamakin wannan abu. Kyakkyawar yarinya irin wannan da ko beauty contest aka je tsaf zata lashe. Amma sai ta wahala zata rike kanta ita a nata tunanin kyakkyawar mace kam ai sai dai ta zauna taji dadi ba ruwanta da wahala. Tunda mafiya yawansu ma masu kudi ke aurensu. Ashe abun ba haka bane. Dace ne kawai. In ba haka ba wannan kam ai tafi karfin wulakanci akan namiji. Can kuma ta sake wani tunanin

12 / 15