Author : Category : Home Of Novels
kona abinci ko kuma abin masarufi kai ko da goro ne sai ta kulle tace su kai mata. Ba dai zasu shiga hannu ba komai ba. Suna cin abinci da daddare sai jidda wadda duk tafi 'yan uwanta magana tace umma meye kwalamammu.? Tayi tsai da cin abincin da take yi wanda suka saba tare take zuba musu a tire suci. Suna ci tana koyar dasu ladduban cin abinci. Kamar su tauna da yadda zaka debe shi. Ta maida hankalinta kanta tace "a ina kika ji wannan kalmar.? Shukra ta amsa mata da cewa "Wai fa dazu ne muka shiga gidan inna suna cin kaza ita da anti huwaila. Shine ita antin tace ga kwalamammu nan sun zo. Shine ta fada miki. Maganar ta bata mata rai matuka. Taga indai kwalama ce to ita kam huwaila sai dai a bata certificate domin haka kawai zata nado zaninta ta shigo nan gidan tace tazo neman abin kwadayi. Kuma ko bata da shi sai tasan dabarar da tayi ta bata wani abu. Banda wannan ma fiye da rabin kayan jeren da aka yi mata mai kwalama tasa ta siyarwa suka ci nama da kudin ita da mijinta. Ta kalle su tace "Amma na hana ku idan kunya mutum yana cin abu ku kura masa ido kuna kallon sa ko kuma ku roke shi. Umma in kayi haka shine ka zama kwalamammu? Inji imam. "Eh ta amsa masa "kuma na gaya muku kwadayi bashi da kyau yana jawo wa mutum halaka. Ta cigaba da fada Imam ya sake cewa "Allah umma muba kwalamammu bane don bamu ga abinda take ciba sai da ta cewa inna ga kwalamammu nan sun zo sannan muka kalleta muka gane kaza take ci. Kuma ta bamu ma muka ce mun koshi. Tunda kince mu daina kwadayi " "To shi kenan mu bar zancen haka. Amma dai ku dinga dauke kanku idan kunga mutum yana cin abinci ko wani abu mai dadi. Idan kuka yi haka in kunzo gida in muna dashi ba sai muci ba. "Amma umma mu kince idan muna cin abu komai dadin sa kuma ko dan yaya yake in munga wani mu sammasa ko. Inji walida. Eh ku sammi shi. Ai rowa bata da kyau. "Kenan umma ita anti huwaila rowa tayi. "Ke kuma kina gulmarta kin san kuma gulma haramun ce. Ba kyau zancen mutum idan baya nan. Da wannan ta samu ta kashe zancen. Amma ta dauki matakin daina tura su gidan su kadai. Sai dai ta daure suje tare. Ko da minti kadan ne su shiga su fito. Bayan haka ma ta lura tarbiyyar yaran huwaila guda hudu da sauki. Zagin juna da kuma fada a tsakaninsu ba wani abu bane ba. Hatta ita inna zasu iya kallonta suce inna uwaki. Kuma duk sai ayi dariya wai duk nan yarinta ce. Alhamdulillahi ita kam bata da abin cewa sai godiya ga sarki Allah. Yadda duk ake gaya mata renon yara da wahala ita komai da sauki yake zuwa ma. Dadi da karawa kusan duk abubuwan data lissafa zata samar wa yaranta suna zuwa sannu kan hankali. Ita kam rayuwarta sai hamdala. ****************************** Alhamdulillahi muhadu a littafi na biyu na dauke da cigaban labarin.
H Inna 👨👨👦