Author : Category : Home Of Novels
zainab. Kuma bazan matsa ko nan da nan ba sai ka zabi daya daga cikin mu. "Eh in dai ka cika da na halal bani takardar 'yata nima na gaji da wannan auren na sa ido " inji maman zainab wannan kace nace nasu har sai da ya dauki hankalin wasu ma'aikatan asibitin da kuma majinyata aka taru ana basu hakuri. Amma inna ta dage itama maman zainab ta dage. Zainab dai daga asibitin gida aka wuce da ita. Sanadin rabuwar su da sani kenan. Da farko inna ta dau 'yan biyun zainab akan zata rike amma tun da sadiya ta haifi walida mai sunan mamanta Maryam. Sai inna ta dawo mata dasu akan ta hada da walida ta shayar dasu. Haka nan ta hada jarirai guda uku karima da akayi wa lakabi da shukra ga hauwa'u da suke kira da jidda sai kuma maSai kuma Maryam da ake kira da walida. Ga kuma yayayyun yaranta walid da imam. Duk wanda ya ganta yarinya 'yar shekara sha bakwai da yara biyar a gabanta sai ya tausaya mata. A wannan lokaci kam Sadiya taji jiki na renon yaran nan. Don Allah ya taimake ta mai kazar kazar ce ga jiki na kuruciya bashi da saurin gajiya sannan tayi sa'ar miji mai tausaya mata. Da fari yaso ya dauko mata mai aiki inna tace karfinsa bai kai ba amma fa za'a dora masa wahalar auwalu da iyalinsa. Haka nan yakan zage ya taimaka mata da ayyukan gidan. Kafin ya fita aiki. Haka indai yana gida yakan taimaka mata da hidimar yaran irinsu wanka da kuma canja napkin dinsu kai har ma da wankin kayansu. Suna wannan zaman ne Allah ya taimaka masa ya sami aiki da makarantar horar da malamai ta jihar kano wato kumbotso. Shekarassa daya dasu suka nemi tura shi karatu kasar Sudan domin karo ilimi. Anan inna ceta samo masa auren wata 'yar makotansa Rahina a dalilin Sani bazai zauna shi kadai a Sudan ba. Sadiya kuma ga yara a tare da ita. Rahina yarinya ce mai nutsuwa makarantar islamiyyar su daya da sadiya kafin komawarta gidan momi da aiki. Dija ita ta fara sanar da sadiya zancen auren sani da rahina. A wannan karon sadiya bata nuna bacin ranta ba ta dai sanar masa daya daure ya dinga sanar da ita lamuransa. Bata cika jin dadi ba idan wani ya sanar da ita kafin shi. Hakuri ya bata kamar yadda ya saba ya kuma yi kokarin kwantar mata da hankali tare da nusar da ita wasu dalilai da suka sanya shi yayi wannan aure. Duk da kokarin da yayi domin karta fahimci inna ceta sashi yayi auren. Amma saida ta fahimta. Ta dai yi masa shiru ganin har yanzu kallon karamar yarinya yake mata. Bai kuwa san yana mata kallon biri ne tana masa na ayaba. Duk da kokarin da yake yi na nunawa sadiya rashin hannun inna a aurensa saida ta dago su. Ko don yadda taga inna na nan-nan da auren. Har tana fadin ai shi namiji mijin mace hudu ne. Idan mutum ya dora wa kansa kishi shine zai sha wahala. Ita kam ta cire ran jin dadin zama a karkashin mulkin inna. Sai taga mafi sauki a gareta ta rungumi yaran da Allah ya bata da wanda ta haifa da wanda ta samu ko ta samu tudun dafawa. Duka-duka zaman sati biyu suka yi da rahina suka wuce Sudan ita da angonta. Bata tashi zuwa ba saida Sani yazo hutun karshen shekara yazo da ita da tsohon cikin ta. Ita kam ma zamansu baiyi nisa ba Allah yayi mata rasuwa a haihuwar danta mai suna kamal. Ya dawo da ita gida domin ta haihu anan Allah yai ikon sa a kanta. Gidan kakanin kamal bashi da nisa dasu. Sun so a bar musu shi amma shima inna ta karbe shi tace tafi son a hada shi da 'yan uwansa. Su kam suna zuwa duba shi akai akai. Zainab ce dai wani abin mamaki bata taba zuwa taga yaranta data rabu dasu tun suna jarirai ba. Babu abinda ke faranta ran sadiya irin ta zauna da yaranta tana hidimar su. Allah daya tai make ta kamal ne kadai mai dan taba rigima a cikinsu. Shima idan ta bashi nono yasha ya koshi ta sanya shi a baya sai tayi ta aikinta dashi. Wani zuwa da yaya kulu tazo duba su saida tayi mata magana inda tace " anya zaiyiwu kuwa sadiya kullum da na goye a bayan ki. Dariya tayi "Allah yaya tausaya masa nake yi. Kinga shi maraya ne" "Akwai dan da zai same ki a matsayin uwa yayi kukan maraici sai dai kukan bai san uwar data haife shiba. Kulawar da kike bashi ko uwar da ta haifeshi bazai samu sama da haka ba. Kuma dukkaninsu nake magana bashi kadai ba. Ta gyara goyon kamal a bayan ta " yaya ku dinga taya ni da addu'a in kula da yaran nan yadda ya kamata"***32***===== "Addu'a kam kullum ne sadiya. Ke dai Allah ya baki lada ya kuma kara miki juriya da kuma kokari. Kula da yaro da kuma hakurin zama dashi sai an daure. Inda Allah ya taimake ki bakya iya jurewa kazanta kuma kina da jurewa al'alar su. Inba haka ba kalli huwaila mai 'ya'ya biyu sai yaron cikin data ke dauke dashi amma dakinta in banda karin fitsari ba abinda yake yi. Amma ke wazai shigo gidan kima yace da kananan yara inba ganin su yayi ba " dariya kawai tayi amma a zahiri taji dadin wannan yabo na yaya kulu. Ya kuma bata karfin halin zage dantse wajen kula da yaranta. Duk karancin shekarun sadiya ta kanyi kokarin tashi da daddare ta sanya yaranta suyi fitsari a food. Hatta kamalu da bai cika shekara ba ya fara sabawa da wannan al'ada. Idan har zaiyi fitsari ko bayan gida motsinsa ne yake fargar da sadiya. Kusan koda yaushe hankalinta na kan yaranta tana hankalce dasu. Taga ko suna da bukatar Kulawar ta. Makotanta sukan so su shigo hira wajenta. Amma korafinsu bai wuce na ita idan anzo ba'a samun yin hira da ita ba saboda bata rabo da hidimar 'ya'yanta. "Dariya kawai take musu tace "to ai ni inaga lokacin uwa mai yawansa ya kasance na 'ya'yanta mussaman in suna kanana. Saboda bukatar lokacin ta da sukeyi. Kusan ko yaushe in tana hidimar yaranta momi ce take fado mata a rai. Saboda kasan cewar ta irin iyayen nan masu kula da hidimar yaransu in suna kanana. Duk da tana da halin daukan mai reno amma abin da duk ya shafe su kamar wanka da cin abincin su ita take yi da kanta bata mikawa 'yan aiki. Tuna wannan hali na momi shike dada sanya sadiya rungumar hidimar yaranta. Taga mai kudin biya a taimaka mata tayi da kanta inaga ita kuma da sai dai tayi da kanta din. Ko gaishe da inna sadiya zata je sai ta tabbatar da ta kammala komai na gidanta da kuma larurar yaranta. Wata rana tana zaune a gidanta bayan ta kammala ayyukanta. Makociyarta malama umma wacce take koyarwa a islamiyyar matan aure na unguwar ta kawo mata ziyara. Allah ya hada jininsu saboda yabawa da hakurin sadiya da kuma juriyarta da take yawan yi. Data tashi tafiya ta bata wani Littafin addu'o'i da mutum zai dinga yiwa yaransa. Taji dadin littafin nan kwarai da gaske. Kullum kuwa ta idar da sallar asuba bayan ta gama lazimi ta na safiya da maraice wanda yayanta ya koyar da ita saita dora da addu'ar nan kamar haka: ALLAHUMMA BARIK LIY FIY AULADI WA WAFFIKU LIDA'ATIKA WAR ZUQNI BIRRUHU. ALLAHUMMA YA MU'ALLIMU MUSA ALLAMHU. WA YA MUFAHHIMU SULAIMANU FAHAMHU. WA YA MU'ITIY LUQMANUL HIKMA. ATIMHUL HIKMA WA FADHLAL KHIDAB. ALLAHUMMA ALLAMHU MAA JAHILUU WA ZAKKARHU MAA NASUU. WAFTAH ALAIHIM MIN BARAKATIS SAMA'I WAL ARDHA. INNA KA SAMI'UN MUJIB. Addu'a r nada yawa feji biyu ce bari mu barta haka. Allah ya sakawa wanda ya rubuta addu'ar nan da alheri. Domin kusan duk abinda za'a rokarwa yara 'yan gata na alherin duniya da lahira addu'ar nan ta kunshe shi. Tun tana yi da littafi har saida ta kasance ta iya ta saboda yawaita yinta da take. Ga addu'a ingantaciya da uwa ta gari take yawan yi ga kuma kula da yakana ai sai dai muguwar kaddara tasa yaro ya tashi a fandare. Mai makon yawan wake- wake da wasu iyayen suke yawan yi. Ita kam tana yawaita tasbihi da hailala ne. Wannan yasa su walid sa suke kwaba gwaranci suma suke kokarin kwaikwayonta. ***** A Sudan inda sani yake karatu akwai wata yarinya data ke karatun shari'a a jami'ar su mai suna asma'u ta hadu da Sani a dakin karatu inda take zaune a kujerar kusa dasu. Bayan nan da yake yiwa abokanan bitar karatunsa ne ya dauki hankalinta. Tattaunawar su ta shafi wani aiki da aka bawa ita asma'un. Kuma shine abinda ya kawo ta dakin karatu. Kamar ta kyale su sai taga zata cutu. Tunda dama bata gama gane bayanin da akayi musu a aji ba. Sanye cikin shigarta mai mutunci doguwar riga da hijabin ta tayi musu sallama. Bata yi sanya ba tayi tambaya game da abinda ya shige mata duh. Kasancewar fannin da Sani ya karanta ne ta samu yayi mata bayani dai-dai yadda zata gane. Harma da abinda bata tambaya ba ya sanar da ita saboda kasancewar sa mai yawan bincike a fannin shari'a da fiqhu. Tunda ga wannan rana ita kam ta samu free lesson teacher. Koda yaushe tana like dashi don ta anfana daga ilimin da Allah ya bashi.***33***===== Mahaifinta ya kasance jakadan Nigeria a nan Sudan kafin aiki ya mai dashi saudiya. Sun tafi sun bar Asma'u ta karasa karatunta kafin ta bisu. Yadda Sani yake Shekararsa ta karshe na kokarin hada digiri na biyu haka itama take shekararta ta karshe a kokarinta na hada digirinta na farko. A gaskiya kwakwalwar Sani ita ta fara jan hankalinta kafin kyawun sa. Allah ya sanya mata kaunar Sani a zuciyarta. Amma bata nuna masa ba ta danne ko don kunya da kawaici irin na mata da suka san darajar kansu. Wata rana bayan sun gama bitar karatunsu ta tanbayeshi. Kadan daga cikin tarihinsa. Ya bayyana mata. Amma daya fara gaya mata yana da mata sai kawai tayi dariya tace na dade da jin wannan a wajen wata yarinya. Amma tace don tace tana sonka ne yasa ka fadi haka. Amma ai duk mun san matar taka ta rasu wajen haihuwa. Allah ya jikanta. Kai dai ka gaya mana ko auren alkawari kukayi irin na wasu kabilu da idan daya daga cikin ma'aurata ya rasu dayan ba zai kara aure ba. Kaga kuwa in haka ne sai mu taru ayi maka ruqiyya don mun san ba kalau kake ba. Dariya kawai Sani yayi a zaton sa zolayar sa kawai take yi. Daya tara sani da Allah daya bayyana mata batun sadiya. To shi wani irin mutum ne bai cika son magana da yawa ba mussaman da 'yan mata. Sadiya ce kadai macen da yake sake wa yayi hira harda shirme kamar karamin yaro. Saiko yaya kulu. Domin kusan duk shawararsu saita shigo ciki. Suka bar zancen a haka. Bayan kammala karatun ta iyayenta suka zo bikin kammala karatun 'yar tasu. Ita ta nuna musu Sani ta kuma yi musu bayanin irin taimakon da yayi mata har ta kammala karatunta. Suka yi masa godiya mutuka. Jirgi daya suka shigo domin koma wa gida Nigeria direban sune ya dauke su a airport. Sani suka fara ajiye wa a gidan inna tunda yafi kusa da titi akan gidan nasa gidan. Kuma sanin hali yafi sanin kama. Ya tabbatar yana fara isa gidan sa sai yayi rigima da Innar sa. Iyayen Asma'u da ita kanta sun shiga sun gaisa inna. Da suka tashi tafiya alheri daloli ambassador yayi mata. Inna kam rude wa tayi har ta kasa magana. Ita bama tasan wane irin kudi ne yazo hannunta ba yau. Bayan tafiyar su yaya baba ya gaya mata irin kudin da kuma darajarsu wanda shima a zahiri kintata kawai yayi. Sani dai an ga gaisa ya karasa gidansa ya samu matarsa da 'ya'yansa a cikin kyakkyawan yanayi ga yaran shi guda shida gwanin sha'awa dasu. Walid da imam suna da shekara uku da rabi. Shukra da jidda suna da shekara biyu da waya bakwai. Maryam kuma shekara biyu da wata biyar. Sai kamal mai wata goma sha daya. Dukkansu basu San wata uwa ba sai ummansu sadiya. Ga kuma kyakkyawar matarsa wadda kullum kamar kara mata kyau ake yi. Dan digon da ke kowanne kumatu nata da kuma wushiryarta da idan tayi dariya take kara mata kyau. Farin ciki ya rufe Sani sai ya daga wannan ya ajiye ya dau wannan ya rungume. Daga baya gaba daya ya hada ya rungume fadi yake "wayyo Allah dadi gida" ita kuwa sai dariya take masa. Inna ce tasa yaya baba ya bude akwatunan da Sani yazo dasu ta raba tsaraba taba wa kowa. Amma fa ta yaya baba tafi ta kowa. Yana daga gefe duk abinda aka daga yace "inna ina son wannan" hatta kayan sawar Sani saida suka shiga rabo. Sadiya dai tayi godiya da doguwar riga da mayafi guda daya da aka kai mata. Yaranta kowa riga guda daya ya samu tayi ta godiya. Sani dai yayi shiru shida yayiwa iyalinsa akwati guda amma ga abinda suka bige dashi. Wannan baya gabansa samun iyalinsa cikin farin ciki da wadata yafi komai a gare shi. Wannan kuwa ya faru ne da taimakon amininsa Sa'idu da kuma sa idon yaya kulu.=====***34***===== 'yan kwanaki da dawowar sa. Asma'u ta kawo masa ziyara a gidan inna tunda nan ta sani. Bata same shiba baya nan. Sun gaisa da inna da kuma huwaila matar dan lelenta. Mai hali irin na mijinta. Nan take wuni ko yaushe. Ba kuma wani abu zata taimaka mata dashi ba. Zaman ma tana yinsa a dalilin inna tana da talabijin. Kuma kwanan nan ta tara kudi ta sayi video. Saboda haka nan take wuni tana kallo Tana iya shigowa wajen inna ko shara bata yi a gidanta ba. Amma inna kullum yabonta take yi. Ai tana zuwa tana debe mata kewa. Akwaita kam da iya hira mussaman abin dariya. Inda kasan 'yar drama haka take. Ko labarin mutum zata baka saita kwaikwayi yadda yayi abin da zata bada labarin akai. Sai dai babu cas babu as haka take. Amma duk da haka sadiya mai dafo abinci ta aikowa inna itace mutuniyar banza saboda bata shigowa akai-akai. Har inna kaji tana fadin bata fita sai kace mai konanniyar fuska. Inna bata la'akari da aure da sadiya take darajawa ta hanyar zama a dakinta. Ga kuma yara da take fama dasu. Sannan ita ba kusa take da inna kamar huwaila ba. Zamanta gidan momi ya dada sabar mata da son zaman gida. Momi bata yawo duk da tana da mota da direba. Hidimar gidanta ita tasa a gaba. Kusan koda yaushe jama'unta sunfi kawo mata ziyara fiye da ita yanda take kai musu. Kuma saboda kusan ansan duk sanda aka zo gidanta ana samunta. Baka raba gidan da baki. Da wannan dalilin ne sadiya ta koyi dabarun sarrafa abinda za'a sauki baki dashi cikin gaggawa kuma gwargwadon ikon mutum. Inna tafi son sadiya ma ta ringa zuwa tana zama ana mata bambadanci kamar yadda huwaila take mata. Asma'u ta kawo mata alheri mai yawan gaske wanda ya hada da turmin atamfa 'yar ingila mai ABC Guda biyu. Sabulai da kuma kayan shayi. Tunda inna take babu wanda ya taba mata alheri a dunkule. A lokaci guda kuma mai yawan wannan. Godiya take tana karawa. Ta dan zauna suka danyi hira da inna tana tambayarta mutanen gida ita kuma tana amsawa cikin jin kunya da nauyi. Bayan dan lokaci tayi mata sallama zata tafi yaya baba ya tashi domin yayi mata raki ya ko shima ya samu rabon sa. Sun fita wajen da direbanta yake jiranta yayinda shima yake dada yi mata godiya mai hade da maula. Har suka iso bakin motarta .=====***35***===== "Halan kema abokiyar karatun sani ce" "I to ta amsa masa. Amma ai shi senior na ne. Ya kuma taimaka min wajen karatuna sosai. Yanzu ma dana same shi Abba nane yace a tambaye shi ko yana da ra'ayin zuwa damam ta kasar saudiya ci gaba da digirinsa na uku in har yana so zasu dauke shi aiki a matsayin malamin jami'ar sai kuma yaci gaba da karatu dasu." Ikon Allah ai kuwa sani ba zaiki wannan alherin ba. To ke kuma fa ya dan fada a wasan ce? Ko tare zaku koma karatun? "Haba mu koma karatu kamar wasu mata da miji. "In Allah yayi ba sai a zama mata da mijin ba mai kaunarka ai daban yake." "Ai kuwa auren sani zai min wuya" ta fada tana sunkuyar da kanta" "Saboda me ko dan kinaga matsayinki yafi nasa. Ai shi karatu yakan kaika inda kudi ko mulki ba zasu kaika ba" "Kasan Allah maganar bata matsayi bace. Ni inada wani ra'ayi nawa bazan iya auren mai mata ba. Shi kuwa sani yace min yana da aure. "Inji wa karya yake miki ina ga dai zolayar ki yake yi. Ke kinga yayi kama da mai aure. Ko auren da aka yi masa na farko ai matar ta rasu inaga zancen yake yi miki. Ke kuma baki gane ba. Kuma bai sake wani auren ba. Duka-duka shekararsa nawa. Yanzu nefa zaiyi shekara ashirin da takwas. Inaga dai zolayar ki yake. Inba haka ba tunda yazo garin nan in banda labarin kirkinki ba'a binda yake yi. Don inna kam baki ga inda kika shiga ranta ba. Kullum addu'arta Allah yasa kar iyayenki su duba bambamcin matsayi su bari sani ya aure ki. Kuma duk don saboda yawan maganar ki da yakeyi. Ni naji kamar jiya yace gidanku zaije" Kunsan ance har abada karya dadin jine da ita. Gashi kuma akayi dacen samun magaji mafiyi. Indai shirya magana ne to auwalu ya dame inna ya zarce nan. Yawan zaman sa a cikin mata ya bashi damar koyar kinibibi da kissa yadda ko