KURKUKUN KADDARA FINAL STEP BY HAFSAT BATURE BOSS.txt

Author :  Boss Barture Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 107

39K to 42K   out of 319.4K words

ba Owais, kayi duk abun da za ka yi..."


"meke faru ne? Yaya sharafuddeen? Owais! Me ya hada ku ne"?


Hajiya saratu ce ta yi maganar, bai ko kula ta ba, ya nufi baba Obie da ya gaza miƙewa agaban shi Ya wurgar da chief owais, gaba daya ya tafi zai kife ƙasa baba Obie yayi hanzarin ruko kafadunshi Ya janyo shi ya dawo kan laps dinsa.

Yana haki Yace"gayanan baba, ka tambayesa Uban me nayi masa! watakil kai ya iya faɗa maka"


ya faɗa yana nuna Owais da yatsan sa, Kafin Ya dubi yan uwansa cikin bacin rai yaci gaba da cewa"Owais Ya ɗaura min karan tsana, yau wata ɗaya kenan, rabon da in yi bacci cikin kwanciyar hankali saboda shi, gaba ya ke yi da ni! ya juya min baya, yana zargina akan laifin da ban aikata ba, ba yadda banyi da shi ba akan ya fadamin me nayi masa amma yaki ya faɗa...."

Daura hannu biyu hajiya saratu tayi akanta..

Uncles dinsa gaba daya sun rude da jin abunda ke faruwa tsakanin Owais da mahaifin sa.

Cikin sanyin murya Baba Yace"meyasa baka fadamin ba tun lokacin daya juya maka baya"?



"Saboda bana so na daga maku hankali, shiyasa nabar abun araina, yau ma dana fada maku naga abun nashi ya fara wuce gona da iri, nema yake ya daura min hawan jini, Baba Hakurina ya kare, Owais Ya kona min rai" ya fada idanunsa cike tab da kwalla.



Gaba daya basu ji dadin abun da Owais ya yi masa ba.


Senate lateef Yace'baka kyauta ba, owais, ka bani mamaki, ina hankalin ka ya ke? Da har ka bari mahaifinka Yana kwana da fushinka acikin zuciyar shi"?

Ya faɗa yana kallon chief wanda har lokacin bai ɗago ba, tunda Baba Obie ya daura kanshi asaman laps dinsa.



"Owais, ka tashi kayi mana bayani, wani laifi ne kake tuhumar mahaifin ka da shi? " His excellency abdul razak ne yayi maganar..



His excellency deen daya gama fusata da kakkausar murya yace"ba kaji ana magana bane? Ka tashi ka fada mana meya hada ka da shi"!


Cikin sanyin murya Hateem Yace"pls, Kubi shi a hankali, "

ya fada tare da kallon Owais"My son, pls, ka tashi kayi mana bayani, in sha Allah zamu fahimce ka,"



Pravin da ke ƙoƙarin shigowa falon har zai saci hanya ya nufi dakin hajjaty ganin abunda ke faruwa yasa shi cin burki Ya karya kwana ya nufi gurin su ya tsaya tare da ruke qugun shi da hannu daya ya kasa kunne Yana sauraron maganganun su.


A fusace Owais Ya miƙe tare da juyawa ya nufi daddynsa gadan gadan Kamar zai dokesa, lamarin ya daure masu kai owais bai taba basu mamaki irin na yau ba, har sun fara kokwanton anya ba Aljanu ba ne a jikin shi.



Hannu yasa Ya daki kirjin shi yana faman fitar da hucin bacin rai idanunsa sun kaɗa jawur tamkar an watsa barkono a cikin su, wlh a lokacin Sharafuddeen Yasha jinin jikin shi saboda bai taba ganin owais acikin bacin rai irin na yau ba, Batare da jin shakkarshi ba ya fuskance shi gaba da gaba.

Da farko yayi zaton Dukanshi zaiyi, ganin yadda Ya tsaya a gabansa Yana huci.

Gaba daya kawunnansa sun zubawa sarautar Allah ido, suna jira su ga iya gudun ruwan shi.

Dakyar ya haɗiyi ƙululun bakin cikin daya tokare Zuciyar shi..



Sautin muryarsa dakyar yake fita"ka za6i in tona maka asiri agaban su"?



Ya jefa mashi tambayar, muryar sharafuddeen tamkar zai fashe da kuka Yace"Sai me owais? Ka fada masu suji, wlh da Allah na dogara, ni nasan ban aikata komai ba..."



Gyaɗa kai Chief Owais yayi tare da cewa"kana ɗaya daga Cikin Elders na gidan KURKUKUN ƘADDARA❗...."


Aruɗe Sharafuddeen yace"bangane me kake nufi ba Owais, su wanene Elders? What Prison of Destiny are you talking about"?


Kallon kallo Uncles dinsa suka fara jefawa Junansu gaba daya sun rude da jin abunda Owais Ya faɗa! Su kansu sun kosa suji su wanene Elders? Kuma wani gidan kurkukun kaddara ne ya ke magana akansa?


Hateem har ya buɗe baki zaiyi magana baba obie ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu"kabarsu suyi magana atsakanin su, kada wanda ya sa masu baki"! ya umarta, batare daya motsa daga kan kujerar da ya ke ba.



Wani makirin murmushi Pravin ya saki tare da cizon leben shi saboda dadin da yaji.



"ka riga da kasan me nake magana akai, ina da tarin hujjoji akanka, kawai ka amsa min tambayata, Idan har baso kake In fallasa asirinka agaban su ba..."

bawan Allah Sharafudden Ya rasa Ina zai tsoma ranshi yaji dadi, murmushin takaici ya saki, tare da kai hannu Ya damƙi kwalar Chief yana huci yace"ka dade baka tona min asirin ba dan ubanka! ka fada kowa yaji Owais..."

"Haba yaya Sharafudeen pls Owais.."

Hajiya saratu da ta ɗauko maganar, bata kaiga dire ta ba, baba obie Ya daka mata tsawa tuni taja baki tayi shiru, da rudu take duban baban nasu ta razana ba kadan ba.



Kasa hakuri Hateem yayi don bazai juri kallon Dan uwansa Da dansa a yanayi irin wannan ba, Nufarsu yayi da niyar ya raba su, bai kai ga isa ba Baba Obie Ya ambaci sunan shi da kakkausar murya"Hateem!"

fuskarshi dauke da damuwa yace"baba pls kada ka hana ni! Bazan iya jure kallon dan uwana ahali irin wannan ba, ɗan sa fa ne, wannan ba abune da zamuja baki muyi shiru ba muna kallon uba da ɗa suna faɗa atsakanin su.."

fuskar baba Obie adaure Ya nuna masa sofa"ka koma ka zauna, Umarni nake baka"! Badan yaso ba ya nufi sofa din daya nuna masa ya zauna ransa abace.


Hajiya saratu data gama hasala juyawa tayi rai abace ta nufi part dinta don bazata juri kallon abunda ke faruwa ba.

"Ba zaka fada ba"? ya fada batare daya saki kwallar rigar shi ba..

Yaso Ya rufa mashi asiri saboda koba komai mahaifinsa ne shi, amma ganin yadda ya matsa ma shi akan ya fada ne yasa shi ya zuciya har baisan sa'adda Ya fara gaya masu irin miyagun ayyukan da Elders suke aikatawa..

Lokaci ɗaya yanayin fuskokinsu Ya canza zuwa tsantsar tashin hankali da rudani mara maisaltuwa hadi da tsantsar al'ajabi.

bai karasa maganar ba, Sakamakon Tsawar Da Hateem Ya doka masa, tamkar zai fasa dodon kunnansa.

wannan karon bai saurari baba Obie ba ya mike cikin fushi Ya nufi Owais yana fadin

"zaka tabka kuskuren da zakayi danasani arayuwarka! Idan ma zarginsa kakeyi to ka daina, Ka sake bincike akan wadanda kake zargi, amma mahaifinka baya daya daga cikinsu, sai dai idan kazafi aka yi masa...."

girgiza kai Chief yayi hawayen da suka taru acikin idanunsa tuni sun fara sauka kan kuncinsa.

"Uncle Ba zarginsa nakeyi ba, tabbaci nake da shi, Yana daya daga cikin Elders, saboda shine mutumin da ya janye ni daga fagen fama, Ya jefani acikin daki don kada a cutar dani, bayan haka aranar da zamuje kai farmaki, saida ya kira ni a resting home dinsa, Ya gargadeni akan kada inje kai farmakin, ashe ya saka min maganin bacci mai hadarin gaske acikin coffee din da ya bani nasha...." a takaice ya fayyace masu dalilan da sukasa ya ke zarginsa.

Maganganun Owais sun so suyi tasiri a cikin zuciyoyin su, har sun fara jifar sharafudeen da kallon tuhuma.


Dafe kai sharafuddeen yayi da tafin hannunsa, wani irin kululun bakin cikine ya tokare makoshinsa, sam ya kasa magana, dakyar yake iya furta Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..

"Baba dan Allah kasa baki a maganar nan! Kai kadaine zaka iya tsawatar masa..."

His excellency deen ne ya fada yana kallon Baba Obie, wani abun daure kai, kwata kwata fuskarsa babu alamun damuwa.

"Me ku keso ince? Sharafuddeen shi yakamata ya kare kansa agurin Owais, Ni banga laifin Owais ba, kubar yaro yayi aikinsa, ko kun manta cewa shi jami'en bincike ne"?


Cike da rudani suke kallon baba Obie, jin abunda yace, sun fahimci shi ko ajikin shi bai damu ba,



"Ba ku kai shi son mahaifin shi ba, Hakanan dai owais bazai tuhumi mahaifinsa batare da yana da kwakkwarar hujja akan shi ba, kunsan dai ba zai yi maku karya ba....."


Bai kare maganar ba, sharafudeen Ya katse shi, Cikin raunanniyar murya yace"baba, da bakin ka kake fadan hakan? Ka yarda da maganar owais, kaima kana zargina? Baba kaifa mahaifina ne kafi kowa sanin halina, kasan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba, wlh banji zafin kazafin da owais yayi min ba, kamar yadda naji zafin maganar ka..."

dakatar dashi baba Obie yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu"Ni bance ina goyon bayan Owais ba, kuma bana goyon bayanka saboda bansan wanene mai gaskiya acikin ku ba, amma in har zaka iya kare kanka agaban yan uwanka nayi alkawarin zan dauki mataki akan Owais, In kuma ka gaza yin hakan hukuma zatayi aiki akanka, donni bazan bari ka zubarmin da mutuncina ba...."

juwace ta kusa dibar Hateem da sauri Ya nemi sofa ya zauna tare da dafe kanshi dake sarah mashi.

Sir mubarak sam Ya kasa magana, saboda yana da fusatacciyar zuciya in har ya bude baki ran kowa zai 6aci ne.

Sun rasa wa zasu goyama baya a cikin su? owais da baba Obie sun haifar masu da kokwanto akan sharafuddeen, aganinsu son owais ne ya rufe mashi idanun shi shiyasa ya goyi bayan shi.

Munafuki Pravin sai ya fakaici idon mutane yake sakin makirin murmushin nan nashi, Ji yake kamar ya zuba ruwa kasa Yasha saboda farin cikin sabanin da owais ya samu da mahaifinsa dama yajima yana jin haushin Owais..

Fuskar Sharafudeen amarairaice ya dubi Yan uwansa..



"Kuma Kuna zargina akan abunda owais ke tuhuma ta"?


Shirun da su ka yi ne yasa shi tunanin suma sun goyi bayan Owais da baba Obie, zubewa yayi kasa kan gwiwowin sa, hawaye suka wanke fuskarsa, ga wani matsanancin ciwon kai da yake ji, zuciyarshi ta karaya.

"ba mu zargin ka, saboda mu shaida ne akan ka, mun san wanene dan uwan mu, amma abun da muke so da kai shi ne ka fada mana, meyasa ka sanya mashi sleeping pill a cikin coffee? After that! Why ka hana sa zuwa kai farmaki bayan baka taba hana shi ba! sai wannan karon? Sannan Yace ka yi fitar sirri a daren ranar da suka je kai farmaki, Sharafuddeen Ina kaje"? his Excellency abdul razak ne ya jefa mashi tambayar.

Shiru yayi batare daya iya kare kanshi daga abunda suke tuhumar shi ba.

A hankali Chief owais Ya sadda kanshi Kasa ko kallonsa baison yi saboda baison tausayin shi ya kama shi, gaba daya komai dake faruwa akan idanun Hajiya saratu dake atsaye bakin kofar shiga part dinta, taji komai daya faru saboda bata kaiga shiga ciki ba..



Hannayen shi dake kerma ya ɗaga sama cikin karyayyar murya ya ce


_"Ya Allah, bani da mafita daya wuce kai! Kaine shaida ta, kafi kowa sanin wanene bawan nan naka...."

bai kaiga ƙarasa maganar ba, sakamakon muryar dattijuwar data karaɗe kunnuwan su



*_"NI INA DA JA AKAN MAGANAR KA OWAIS, JINI NA BAZAI TABA AIKATA MIYAGUN LAIFUKAN DA KAKE TUHUMARSA DA SU BA"!*_



~*_________________________________*~



*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*




*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹





_ * *_



~___________________________________🌹✍️~





A matuƙar ruɗe suka juya tare da kallon mai shigowa...

Sandar hannunta ce ta fara zurowa cikin falon, Kafin ta kunno kai, farar jallabiya ce a jikinta ta lullu6e kanta da head scarf ta rufe fuskarta da takunkumi, haka zalika idanunta suna asanye da shade fari, daƙyar ta ke dogara sandar hakan ya bayyana rashin kuzari a tattare da jikin ta, daga gani bata da koshin lafiya duba da yadda jikinta ke kerma.

Cike da tsantsar ruɗani suke kallon ta daga ƙasa har sama, basu san wacece ba, amma maganar da ta furta ta tsaya masu a ƙahon zuciya.


A sukwane Sharafudeen Ya miƙe yana duban ta, Muryarta ta yi masu kama da ta mahaifiyarsu da suka rasa tsawon shekaru wanda basu mance da yanayin sautin muryar tata ba.


Pravin sai faman zazzare Idanunsa ya ke yi burinsa kawai ya ga wacece ita duk da fargabar da ta shige shi saboda muryarta ta yi masa kama da ta wata da ya ta6a sani..



Baba Obie sam ya kasa motsawa, zuciyar shi ta ƙi aminta da abunda kunnuwanshi suke juyo mashi, haka kuma ya kasa yarda da abunda idanunsa ke nuna mashi, kokwanto ya ke aransa ya ayyana hakan ma bazai ta6a yiwuwa ba, wanda ya mutu ba ya ta6a dawowa, duk da yanayin fuskarsa ya nuna tsantsar ruɗani, sai dai babu alamun fargaba atare da shi saboda ya yi imanin hakan bazai taba yiwuwa ba, sai dai idan fatalwarta ce ta dawo...


"Wace ce ita? Da izinin wa ta shigo estate din nan?" Tambayar da ta cika zuciyoyinsu kenan, gaba ɗaya sun ƙagara da su ji dame ta zo musu.


"Baiwar Allah daga ina ki ke? Wa kike nema ne? Kuma tayaya akai kika shigo estate ɗin?" His excellency Deen ne ya tambaya fuskarsa a murtuke.


Hajiya saratu dake a tsaye bakin kofar shiga part dinta tayi sototo tana kallon Ikon Allah..

Kusan atare Sir Mubarak Da Hateem suka miƙe daga zaunan da suke akan Sofas suka bi ta da kallo...

"Wacece wannan dattijuwar ne? Me ya kawo ta nan? Da iznin wa ta shigo Estate din nan uhum"! Acewar His excellency Abdul Razaq...

"Dan Allah ku yi wani abu akai, matar nan ba mutun bace, ku duba ku ga yadda jikinta ke kerma," Pravin ne ya faɗa yana zare idanun sa..

"Ku kira Security Officers ku tambaye su ta ya akai suka bar bare ya shigo mana estate! Da iznin Uban wa..."

Senate Lateef ne ya ɗauko maganar yana huci idanunsa akan tsohuwar, ƙoƙari take ta cimmusu sai dai rawar da jikinta ke yi da rashin kuzari ya hanata yin saurin.

Tana gab da zata ƙarasa gaban Sofas ta ɗan dakata tana mayar da numfashi.

Cikin sauri Chief ya nufe ta, a hankali ya sanya tafin hannunsa ya dafe bayanta ya taimaka mata ta ci gaba da tafiya suka ƙaraso tsakiyar Sofas ɗin, rai a 6ace Sir mubarak Ya ce,"Kana acikin hankalinka kuwa? Ko ka san ta ne?...."


Bai ƙarasa Maganar ba tsohuwar ta yi kukan kura ta dira agaban Baba Obie ta jefar da sandar hannunta, bai aune ba ta wanka masa zazzafan mari tare da cakumar gaban rigarshi da yatsun hannayenta dake ta kerma.


Tashin Hankalin da ba'a saka masa rana! zazzare idanunsu suka yi cikin tsananin al'ajabin karfin halin dattijuwar nan take ran su ya 6aci, ta tako har cikin estate ɗinsu ta mari mahaifinsu a gaban idanunsu!!'

Ransu ya yi mugu mugun 6aci har sun harzuƙa za su kai mata bugu Sharafuddeen ya yi hanzarin kare ta.

Sir Mubarak yana huci ya ce, "Don Ubanki wacece ke?? Uban me ya kawo ki estate din nan? Da me kike taƙama ne?"

Senate ya amshe da fadin, "Sharafudeen ka matsa ka bamu guri! Baka ga abunda ta aikata bane? mahaifinmu fa ta mara agaban idanunmu!"

Cikin rawar murya Pravin ya ce, "Wallahi mahaukaciya ce, daga gani irin mahaukatan nanne masu yin hauka tuburan a dawanau ta gudo Allah Ya hankaɗo mana ita nan, wlh ku yi gaggawar korarta daga estate din nan idan ba haka ba zata manna maku hauka ne..."


Baba Obie bai motsa ba amma fa ya girgiza sosai, da ruɗu yake kallon fuskarta da idanunsa wadanda suka kaɗa jawur, sam ya kasa magana saboda rudewar da ya yi ya rasa gane wacece ita meyasa ta mare shi?"

"Ba zaku ɗauki mataki ba? Kuna gani a gaban idonku ta mari Baba? Matar nan fa mahaukaciya ce wlh, babu lafiya a tare da ita, da gani tana tattare da baƙaƙen aljanu shiyasa har ta yi nasarar shigo mana nan..."

Pravin ne Ya faɗa Yana zare idanunshi yadda kasan na kwarton mazuru.

Ran Hajiya Saratu ya 6aci ganin abun da dattijuwar ta yiwa mahaifinsu, cikin fushi ta nufe su tana ƙarasowa bata bi takan Sharafudeen ba, ta damƙi mayafin tsohuwar kokawa ta barke a tsakaninsu, tana huci ta ce, "Wlh bazata sa6uba, na rantse sai kin yabawa aya zaƙinta, ki shigo har estate dinmu ki mari ubanmu a gaban idanunmu? Kina acikin hayyacinki kuwa? Na shiga ukuna! Wai dan Allah uban wanene ya gayyaci tsohuwar najadun nan acikin gidan nan? Da iznin Ubanwa Securities suka bari ki ka shigo.."

Balbaleta da faɗa Hajiya Saratu ta yi ta inda take shiga bata nan take fita ba.

Sai da suka gama harzuƙa kowa zuciyarshi ta zo a wuya.

Pravin yana ƙoƙarin zaro waya daga aljihu don ya kira Security Officers din gidan, Kwatsam ba zato ba tsammani Hajiya Saratu ta yakice takunkumin dake akan fuskarta, Ta fusge shade din dake akan idanun tsohuwar ya faɗo ƙasa ta bi tasa ƙafarta ta take shi ya faffashe.

Ɗagowar da za ta yi da niyyar ta wanka mata mari har ta ɗaga tafin hannunta, idanunta suka sauka akan fuskar tsohuwar cak ta tsaya tana zare idanunta, Gaba ɗaya suka daura idanunsu akan fuskarta, Wani irin faduwar gaba suka ji ya ɗarsu acikin zukatansu, Sun ruɗe da ganin fuskarta kamar sun so su gane ta sai dai sun kasa gane wacece ita.


Sai lokacin ta yi ƙarfin halin buɗe baki murya na rawa ta ce, "Saratu, bani bace tsohuwar najadu, kin ga tsohon najadu nan, ubanku Obinna!"


Ta faɗa tana nunasa da yatsanta sai lokacin ya shaida fuskarta, Wata irin zabura Baba Obie ya yi jikinsa na 6ari ya miƙe tsaye a kiɗime yana zazzare idanunsa! lokaci ɗaya yabi ya rikice, Hankalinsa yayi mugu mugun tashi, kanshi ya daure, Ya yi matuƙar razana da ganinta, tsantsar al'ajabine ya ruƙe shi, ganin abun yake kamar a mafarki sam ya kasa gasgatawa..

Hajiya saratu ta daka mata tsawa tana fadin "Ke! Mahaifin namu ne tsohon Najadu? Baiwar Allah dame kike taƙama ne, wace ce ke wai..."!

Bata ƙare maganar ba Hateem ya daka mata tsawa a ruɗe ta ja baki ta yi shiru, matsawa ya yi kusa da Khala ya dafa kafaɗunta da tafukan hannayen sa, ya kafe ta da idanunshi yana ƙoƙarin gano wacece ita..

Cikin sanyin murya ta ce, "Baku gane ni ba? Hateem! Sharafudeen! Ni ce fa, *AURORA EDWARD* Momman ku!"


Ta faɗa tana ƙoƙarin tuna masu ta juya ta dubi su Saratu ta ce, "Saratu! Lateef! Mubarak! Deeni? Razak! Baku gane ni ba ku ma?" Ta fada idanunta cike tab da ƙwalla.

Cikin shesshekar kuka ta ce,

14 / 107