Chapter 53 Reading KURKUKUN KADDARA FINAL STEP BY HAFSAT BATURE BOSS.txt Arewa Novels

KURKUKUN KADDARA FINAL STEP BY HAFSAT BATURE BOSS.txt

Author :  Boss Barture Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   53 / 107

156K to 159K   out of 319.4K words

ke, babu network din da ma za'a iya bin diddigin ku, babu wanda zai iya tunkarar kurkukun nan a halin yanzu, saboda a kewaye yake da Evil Giants, sun ci nasara a karo na farko amma wannan karon babu wanda zai ƙara farmakar mu ya zauna lafiya.."


girgiza kai ta yi, "In sha Allah zaka ga yadda addu'ar wanda aka zalunta take tasiri akan wanda ya zalunce shi, zan kuma gwada maka yadda addu'ar mai imani wanda ya dogara da Allah take tasiri, ka jira ka gani, ni da kai wa zai yi nasara"


Ido cikin ido suke kallon juna, fuskarsa a murtuke ya ce, "Mafarkinki ba zai ta6a zama gaskiya ba, baki isa inyi jayayya dake ba, nasara tawa ce, ke da zaki mutu ...." Ya faɗa tare da miƙewa tsaye yana kallonta..


"Waliyiya Unaisah, zan jira in gani idan addu'ar taki zata yi tasiri, sannan ki taimaki kanki da kuma yar uwarki." Ya faɗa tare da nuna mata ƙwarin dake daddabe jikin nama.

"Ba irin ƙwarin da kika saba gani bane, wadannan na gidan kurkukun ƙaddara ne, mun tsaface su, jinin jikin mutun suke tsotsewa, su sanya mashi dafin da zai lalata yan hanjin jikin shi, ya ru6e." Wani irin tsoro ne ya mamaye ta.

"Da zarar sun gama tsotse jinin da ke a jikin naman zasu dawo kanki ne."


Hankalinta a tashe ta zazzare idanunta cike da fargaba ta wurga idanunta kan su, yawu ta haɗiya ilahirin jikinta ya kama kerma.


"Na barki lafiya.." Juyawa ya yi taku ɗaya biyu ya 6ace ma ganin ta..


Fitar sa ke da wuya, ta lura ƙwarin sun kusa gama tsotse jinin naman, kafin kyaftawar ido har sun gama tsotse gaba ɗaya jinin dake a ɗakin sun fara bin bango suna tunkarota da saurin su, ga kukansu mai tsiwar gaske..


Cike da tashin hankali ta zazzare idanunta akan su, gwanin ban ƙyama, cikin rawar murya ta shiga furta duk wata addu'a da ta zo bakinta, batasan ya zata yi ba, ga hannayenta a ɗaɗɗaure kafafuwanta ma, kuma ba halin ta motsa saboda inda suka ɗaure ta jikin taga, lokacin da ƙwarin suka fara gangarowa kan floor gungu guda suka nufo ta sai sauri suke yi, ƙararsu ta cika kunnanta..

Tana ta tunanin wata dubara zata yi me yakamata ta yi? Saboda bata son ta mutu batare da ta ceci rayuwar Batool ba..

Juyawa ta yi da sauri ta dubi tagar da suka ɗaure sarƙar hannayenta a jikin iron bars ɗinta (sandunan baƙin ƙarfe) mai gida gida, yunƙurawa ta yi a tsorace tana nishi ta soma ƙoƙarin tura kanta a tsakankanin ƙarfen, daƙyar ta samu ya shiga ta dinga ingiza jikinta ya ƙi wucewa, fashewa ta yi da kuka jin kukan ƙwarin dab da ita, bata yi aune ba, ta ji sun fara hawa kan kafafunta suka soma caccaka mata tsinin bakinsu suna tsotsar jinin ta,Ya salam! wani maganaɗisun raɗaɗi ne ya ziyarce ta, ta fasa ƙara kamar ana zare ranta, ta dinga kuka tana bubbuga kafafunta har ta samu ta kakka6e su.

Karkata jikinta ta yi ta fuskanci hannun damanta, a haka ta ci gaba da tura jikinta, daƙyar da siɗin goshi ta samu qugunta ya wuce, gaba ɗaya ta kundumo ta bayan tagar ta fado cikin wani ɗaki, still bata tsira ba saboda sarƙar da aka ɗaure hannayenta da su tana a jikin tagar, kuma a buɗe take zasu iya faɗowa ciki, kwata kwata bata lura da inda ta faɗo ba, Saboda hankalinta ba a kwance ya ke ba, karfen jikin tagar ta lura da tsatsa a jikin shi alamun ya daɗe ba a musanya shi ba, daddagewa ta yi da iya karfinta na karshe ta dinga jan hannunta tana nishi, gumi ya wanke jikinta, kukan ƙwarinne ya cika kunnanta kamar zai fasa dodon kunnanta.

Saida ta galabaita, wuyan hannunta ya yi jawur kamar zai fashe saboda sarkar da ta takure gurin ga kuma jan gurin da take yi, dai dai lokacin da ƙwarin suka fara hawa jikin ƙarafunan tagar, a gigice ta fasa wata irin ƙara mai sauti tare da rufe idanunta, buɗe idanun da zata yi keda wuya, ta ga abun da bata yi zato ba, ƙarfen da aka daure sarƙar hannunta da shi ya 6alle biyu sakamakon jan da ta dinga yi, jikinta na 6ari ta buga murfin tagar da hannunta, ta danne da bayanta, tana jiyo kwarin dake ta bugun tagar kamar zasu fasa ta yadda kasan wata ƙatuwar halitta, lumshe idanunta ta yi gabanta na ci gaba da faɗuwa.


Buɗe idanun da zata yi keda wuya, ta yi arba da tarin kawunan ƙwarangwal cike da dakin da ta faɗo, kwata kwata bata tsorata ba, saboda mawuyacin halin da take a ciki.


Shiru ta ji ƙwarin sun daina fitar da sautin su, miƙewa ta yi tsaye kan kafafunta da ke a ɗaure, ta ɗan buɗe tagar kaɗan ta leƙa kanta, ruɗewa ta yi ganin ƙwarin kwakkwance a ƙasa basa motsi kamar sun mutu, lamarin ya daure mata kai, har ƙara zare idanunta take yi don ta tabbatar da sun mutun ko lambo ne suka yi mata, dabara ce ta faɗo mata a rai, da sauri ta tsotsi jinin dake akan le6anta, ta watsa shi cikin ɗakin don ta ga idan za su tsotse shi, still ba su motsa ba, shiru ta yi jim tana yanke shawara da zuciyarta, so take ta koma cikin ɗakin don ta kwance leg irons ɗin ƙafarta, shahada ta yi duk da shakkar da take ji, ta daddake ta ruke sandunan kofar da hannayenta ta kutsa kanta ciki, wannan karan bata sha wahala ba, ta burma cikin ɗakin gaba ɗaya ta faɗo kan ƙwarin dake yashe a ƙasa, anan ta ƙara tabbatarwa kanta sun mutu.

daƙyar ta iya miƙewa, kamar yar tsana ta dinga yin tsalle tana tunkarar teburin ɗakin dama shi take hari, har kifewa ta yi ƙasa ta kuma miƙewa daƙyar ta ƙaraso gaban shi, ta zube kan gwiwowinta, jikin ƙarfen table din ta dinga buga sarƙar hannayenta da ƙarfi, duk ta hada gumi akan fuskarta, sai nishi take tana jan numfashi, dakyar da sidin goshi ta samu sarkar ta saki daga tamkewar da ta yi, 6an6areta ta yi daga hannayenta ta jefar da ita ƙasa, ta kai hannunta da ke kerma ta ɗauki zarto ta kunna shi tare da saita shi daidai saitin leg irons din kafafunta, duk da fargaban kada ta datse ƙafar saboda jikinta dake kerma a haka ta daddage ta dadara zarton da ƙarfi kamar ranta zai fita har fitsari saida tayi a cikin wandonta saboda wahala, dakyar ta yi nasarar 6alle irons din ta zame ƙafafunta daga cikin shi ta miƙe tana haki, tsayuwarma daƙyar ta yi ta saboda raunin da legs dinta suka yi, saida ta dan sarara tukunna ta miƙa hannu ta sungumi zarton ta rataya shi akan kafaɗarta, hakan bai isheta ba saida ta ƙara da tsinken ƙarfe ta soke shi a cikin aljihu, duk don ta kare kanta kamar wata mai ƙarfi, duk da ta zuciya, jinin ta akan akaifa ya ke, ƙwara ayi ta ta ƙare, ko a mutu ko ai rai.


Gaba ɗaya ta sauya kamar ba Unaisah ba, ta zama kamar ƴar daba, Overroll ɗin jikinta duk ta 6aci da jininta, haka fuskarta ma a 6ace take da jini, sumar kanta kuwa bata da maraba da ta mahaukaciya, tana ɗangyasa ƙafarta ta nufi tagar nan ganin babu ƙofar da zata bi ta fita daga dakin duk a kulle suke, bayan da ta dira cikin ɗayan ɗakin ta shiga rarraba idanunta tana neman ta wace hanya zata fita daga ɗakin, ganin shima duka tagoginsa a kulle suke haka ƙofofin ɗakin ma. Da zarton ta soma kokarin 6alle ƙofa ɗaya, sai dai ta kasa saboda rashin kuzarin dake a tare da ita, gaba ɗayanta a raunace take...

Langwa6e kanta ta yi jikin kofar, tana nishi yayin da zuciyarta ke tariyo mata wasu abubuwa da suka faru atsakaninta da Batool, nan take ta ji karfi ya zo mata, tunawa da kalamansa..


Bugu ɗaya ta kara yi ma kofar nan ta ke ta buɗe.


Cike da fargaban me zata taras ta leƙo waje, bata ga kowa ba, wasu hanyoyi ne da babu kowa.


Sama ta kalla don taga ko akwai cctv can kuma ta tuna da inma suna ganinta bai wuci ta madubin zafin su ba, komai zai faru sai dai ya faru amma fa ta ci alwashin ko zata rasa ranta saita ku6utar da Batool, cikin sanɗa take tafiya, duk dakin da ta gani sai ta leƙa tagar shi don ta ga idan nan suka kulle Batool.


Cikin zullumi da fargaba, tana ƙoƙarin karya kwana kwatsam ta hango gungun Giants sun nufo gurin da take, ruɗewa ta yi cikin sauri ta koma da gudu batasan sa'adda ta dura wata windown ɗaya daga cikin ɗakunan dake a gurin ba, sai haki ta ke yi, ajiyar zuciya ta sauke jin alamun sun wuce, bin ɗakin ta yi da kallo, tsofaffin metal bed ne aka jibge ɗaya kan ɗaya a cikinsa, wata dabara ce ta faɗo mata, lokacin da ta dubi ceilling ɗin ɗakin da akwai access panel a jikin shi, duk da a kulle yake amma ta na jin zata iya tsaga shi, kama jikin gadajen tayi ta dinga bin jikinsu tanayin sama dakyar ta haura ta saman su, ta zauna tana mayar da numfashi.


Tunawa da tarin ƙalubalen da ke agabanta yasa ta zaro tsinken karfen da ta soke, ta shiga caccaka ma panel din, kasantuwar yana da quality, ta ci wahala kafin ta 6alle murfin, ta leƙa kanta cikin ceilling din, ba laifi yana da space din da bawa zai iya ratsa cikinsa, tura kanta ta yi, a hankali ta shige dukanta, zafi ya doka mata sallama, ta fara zubda gumi, kwata kwata babu tsoro ko fargaba atattare da ita, jan ciki ta dinga yi tana yin gaba, har wata kwana kwana gare shi, bata tashi sanin ta yi wauta ba sai da ta rasa hanyar da zata 6ula, nan fa ta fara rarraba idanu, kwata kwata ba ta yi tunanin ta kalli ƙasa ba, kawai jan jiki ta ke yi tana yin gaba, sai daga baya tunanin hakan ya zo mata, cikin sauri ta soma bin celling din tana ƙare masa kallo cikin tsantsar ruɗu..



~_____________________JAN WUYA🔥~



A tsaye ya ke gaban dakin fiɗa, zuciyar sa fari fat yau zai cika burin da ya daɗe yana mafarkinsa.


Buɗe kofar ɗakin aka yi, babban yaronsa Dr. Mark ne ya fito, sanye da uniform din tiyata.


"Mark, ka gama tiyatar ne? Ko har yanzu ba ka cire zuciyar ba ne?"


Jinjina mashi kai ya yi, "Ban kaiga farawa ba, ina jira allurar kashe zafin da na yi mata ta fara aiki a jikin ta"


Bai ƙarasa ba ya dakatar da shi. "Ba wannan na ke son ji ba, bana bukatar ka bi ta lalama, ka saka ƙumbunanka ka faffarke kirjin ta, bafa ta da wani amfani zuciyarta kaɗai nake so, in ba zaka iya ba ni ka bani guri in yi!"


"Allah ya huci zuciyarka sir, in har mu ka ce zamu bi ta tsiya zamu iya lalata shirin mu, dole mu bi a sannu don mu cire zuciyar batare da an samu matsala ba."


Tsoki ya ja, "Na baka nan da mintuna biyar ka cire ta kota halin ƙaƙa, don mu yi saurin lunƙumata a bakin dodon tsafi, bana bukatar bata lokaci." Cike da ladabi ya amsa mashi da toh ya juya ya koma dakin..

Bai motsa daga inda ya ke ba, jira kawai yake yi ya gama tiyatar, abun da ya faru tun jiya da daddare da suka zo kurkukun da su, ya so yayi amfani da sihirinsa gurin farke kirjin Batool don ya cire zuciyarta, sai dai matsalar, da aka samu, sihirin sa ya yi ma jikinta ƙarfi, in har ya kuskura yasa ƙarfi don ya cire zuciyar toh gaba ɗaya zata dagargaje, shiyasa dole su bi tsarin tiyatar asibiti.



Gajiya ya yi da tsayuwa, ya fito daga sashen da tiyata room din ya ke, ya koma cikin wani katafaren falo mai kyan gaske komai na cikinsa launin ja ne, zama ya yi kan wata doguwar kujera ya ɗaura ƙafar sa daya kan ɗaya kamar wani basarake, kwata kwata baya tunanin a wani hali iyalinsa suke a ciki, ta kansa ya ke, already an riga da an fada masa sojojin isod sun kewaye gidansa da gidan ɗan iya, hakan bai dame sa ba.


"Musa ya za kai mana haka? Wasa tare ci bambam? Me hakan Ke nufi?"


Unexpected ya tsinkayi muryar Jan Ido a cikin kunnan sa, a sukwane ya miƙe yana duban su.


ɗaya bayan ɗaya suke ratsa bango suna shigowa falon, cikin shigarsu ta dogayen riguna baƙaƙe masu huluna, hannayensu ruƙe da sandunan su, rabin fuskokinsu rufe da mask, idanunsu ne kaɗai a bayyane.


Kansa ya ɗaure da ganinsu saboda bai sanar da kowa shirin shi ba, saboda baya son su sani, shi kadai ya ke so yayi.


"Don me zaka yi komai a sirrin ce batare daka faɗa mana ba? me hakan ke nufi?

Wani daga cikin Elders dinne ya faɗa..


Banza yayi da su bai tanka masu ba, sai ma wani shu'umin murmushin shaƙiyanci da yake saki.


"Ka yi shiru baka ce komai ba? Ko hakan na nufin dagaske ne abun da aka fada mana? Kana so ka ci amanar mu ko? Shiyasa ka shirya komai a boye batare daka fada mana ba bayan mu yakamata a ce ka fara sanarmawa.." A cewar wani elder, wani kallon tuhuma suke jifarshi da su.


Tafa hannayensa ya yi tare da bushewa da dariya cikin takun izza ya nufe su yana fadin, "Sannunku da zuwa! Tayaya akai kuka san ina anan? Wanene ya fada maku um?" Ya fada yana ɗage masu gira.


Wani tsoho daga cikinsu cikin fushi ya ce, "Jan wuya baka isa ka ci amanar mu ba, mune a gaba da kai, baka isa ka yi gaban kanka ba, dama ni ban yarda da kai ba, saboda nasan halin ka ba ƙaramin shaiɗani bane kai, ka ƙware gurin iya haɗama da kulla makirci, wato shine yanzu da ka ga Elder ya yi murabus kuma asirinka ya tonu shine ka kware mana baya, ka sato yaran da kowan nan mu ya ke burin ya ɗauko su, don ka riga mu cika sharuddan allon tsafi saboda ka samu karfin ikon da za ka juya mu..."


Ƙyalƙyacewa ya yi da dariya, tare da nuna su da yatsan shi da izgilanci ya ce, "har kuna da bakin faɗin ban isa in ci amanar ku ba? Dama akwai amana a tsakanin mugu da mugu? To ni ban yarda da kowannan ku ba, babu wani mai iko da ni a cikinku, saboda na fi karfinku nesa ba kusa ba,
.." Ya fada yana huci.


"Buri ne da na daɗe da shi a zuciyata tun farkon dana fara yi ma Elder bauta, duk wani ci gaba da aka samu a gidan kurkukun kaddara nine sila, don haka yanzu lokaci ya yi da zan fanshe wahalata, ni na cancanta in hau karagar Elder Obinna..."


Ransu ya 6aci, yanzu sun gasgata abun da aka faɗa masu game da maƙarƙashiyar da ya ke shirin ƙulla masu.


"You son of a bitch, Musa, you'll never become an Elder over my dead body, You're not worthy, If anyone deserves it, it's one of us, who've been with the Elder for a long time before he even knew you existed."


(ba zaka ta6a zama Elder ba, baka cancanka ka zama ba, idan ma akwai wanda ya cancanta to daya daga cikin mu ne, mu da muka daɗe tare da Elder tunkafin yasan da zamanka a duniya,..." )

jan le6e ne ya faɗa rai a 6ace.


Wani Elder din ya ce, "Ba zamu ta6a lamunta ka zama shugaban mu ba, saboda mun ji maƙarƙashiyan da kake son kulla mana, kana so ka samu ƙarfin sihirin Elder don ka ƙwace sihirinmu sannan ka kashe mu ko?"


tun da suka fara magana hankalinsa kwance babu damuwa a ransa, amma da wannan Elder ɗin ya yi magana sai ya fahimci kamar wani ne ya yi brainwashing ɗin su.



"Na fahimci wani ne ya zugo ku ya faɗa maku karya da gaskiya akaina don ya shiga tsakanin mu! nasan ban kyauta ba da ban sanar da ku ba amma banyi hakan don bana so ku sani ba, kuma ni bani da mummunan nufi akan ku, sai don nafi so in sawwaƙe maku wahala, amma maganar nan ba gaskiya bane, ni bana nufin kowannanku da sharri, burina dukanmu mu gudu tare mu tsira tare, saboda mun riga mun zama ɗaya, yakamata ku fahimce ni..."


Ya faɗa cikin lalama, wani kallo suke yi mashi na rashin yarda duk da kokwanton da zuciyarsu ke yi sai dai ba zasu iya ƙaryata abun da aka faɗa musu akan shi ba, saboda daga majiya mai ƙarfi suka ji.



"Koda zamu yarda da maganarka, ba zamu ta6a bari ka zama Elder ba, saboda baka cancanta ba..." Elder din da ya ɗauko maganar bai kaiga direta ba, Jan wuya ya daka masa tsawa yana huci ya furta, "Saboda me ba zaku bari in zama shugaban ku ba? Ko ina da wani aibu ne? Ko baku yarda da ni bane? Ko kuwa shi Elder Obinnan yana da wani magaji ne ehe? Meyasa ni ban cancanci in hau karagar mulkinsa ba?"


"Bamu yarda da kai ba Musa, saboda ka yi abun da yasa mana zargin ka a cikin zukatan mu, kwata kwata babu gaskiya a tare da kai, kuma kai in ban da abun ka, ka yi tunanin hawa kujerar Elder abu ne mai sauƙi? To bari ka ji in faɗa maka gaskiyar zance, bare baya hawa kan karagar Elder, dole sai idan jinin Elder ne kadai zai iya hawa kan karagarsa, su da suka gaji abun ba kai da ka ke bare ba"

Jan dasashi ne ya furta, ran Musa ya 6aci zuciyar shi ta zo wuya, sun fara harzuƙa shi.

Sauran Elders din da suke haɗamar samun kujerar Elder a ruɗe suke kallon jan dasashi da ya yi maganar.


"Kana nufin babu wanda zai gaje shi a cikin mu? Waya faɗa maka hakan? A ina ka ji eye?"

A cewar Jan Gemu.

Jan le6e ya ce, "Ko ni da nasan sirrin Elder Obinna ciki da bai ban ta6a jin wannan maganar ba, na gani da idona a rubuce ya ke a cikin littafin

53 / 107