Chapter 52 Reading KURKUKUN KADDARA FINAL STEP BY HAFSAT BATURE BOSS.txt Arewa Novels

KURKUKUN KADDARA FINAL STEP BY HAFSAT BATURE BOSS.txt

Author :  Boss Barture Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   52 / 107

153K to 156K   out of 319.4K words

da fasiƙar uwarta ta bogi kuka hadu gurin lalata rayuwarta, duk hakan baiyi maka ba, ka hanata sanin komai game da addininka ka barta a matsayin arniya saboda kada Allah Ya tuhumeka a ranar gobe ƙiyama, shiyasa duk ƴa'ƴanka daka sadaukar babu musulmi a cikin su, saboda jakkanci da daƙiƙanci, da kuma shafewar basira irin naka..."


bata ƙarasa maganar ba, ya kwasa mata wani marin da ya ja har hancinta ya fara bleeding..



Idanunta suka cicciko da kwalla, ta ji zafin marin nan, radadin sa ya ratsa ta, kuma bata fasa maganar ba,


"Ai koda hakkin rai ɗaya aka barka wlh makomarka ba zata yi kyau ba, saboda Allah baya barin hakkin wani akan wani, kuma baya yafe hakkin dake a tsakanin bawa da bawa, balle kaida ka daɗe kana zaluntar rayukan da basu ji ba basu gani ba, rai nawa ka kashe? Rai nawa ka zalunta? Rai nawa ka lalata uhym? Ko an gaya maka Allah baya gani ne?" Ta faɗa tana ciccije la66anta tsabar masifa duk ta faffasa su, gaba daya ta kashe mashi baki, ko kaɗan bai girgiza ba bai kuma dakatar da ita ba ya bari ne ya ga iya gudun ruwanta, don shi har yanzu baya mata kallon mai hankali saboda ƙarfin halinta..


Tana jan numfashi cikin fushi ta ɗaura da cewa, "Bayan haka kaine mugun da ya raba mahaifiyata da danginta, kuma kaine shaidanin da ya shiga tsakanin Aunty Ummi da mahaifinta, sannan kuma kaine makirin mutumin da ya hada Aunty Ummi da Uncle Shureim, ka kuma raba su da ƴar su, bayan haka, kaine fasikin da ya mayar da aunty Umminmu karuwa ka rabata da kowa nata ka mayar da ita America, saboda wani dalili naka mara amfani.."



ta6e la66ansa ya yi batare da ya furta kalma ba..


"Jahilin addini jahilin rayuwa, wallahi ka ji haushin rayuwarka, ka daina farin ciki don ka daɗe kana zalunci wlh kanka ka zalunta, ka gur6ata duniyarka da lahirar ka da kanka, shi zalunci ƙaiƙayi ne dake komawa kan mai shiƙa, kuma guba ne dake cin wanda yayi da wanda aka yi mawa, sannan ƙarshen zalunci nadama ne, kuma duhu ne aranar gobe ƙiyama! Wata riba ka ci yanzu? ni Ban ta6a ganin rai mara buri asararre tambaɗaɗɗe irinka ba.."


Ransa ya yi mugun 6aci da jin maganganun da ta gaggaya masa, a rayuwarsa ya tsani mutumin da baya jin shakkar shi, abun da ya fi bashi takaici ƴar ƙaramar yarinyar dake gaya masa magana..

Yana fitar da numfashin bacin rai mai huci ya ce, "Ni ba asararre bane, ni ne mai buri, ban ta6a yin asara ba, komai na nema saina same shi, tun da nata so rayuwata ni mai nasara ne, mai faukaka kuma shahararre mai arziƙi, har matsayin shubagan ƙasa na taka, me yafi wannan?"

Ya faɗa yana ɗage mata gira.

"Kuma na ci riba, tun da na dade ina sheƙe ayata batare da asirina ya tonu ba, ina da karfin ikon da babu wanda ya isa ya ja da ni, ko mutuwa tsorona take ji.."

Ya fada cike da alfahiri,


Girgiza kai ta yi, "Wanda ya 6ace ya 6ace, lokacin mutuwar ka ne bai yi ba, ka daina alfahari saboda har yanzu baka yi nasara ba, Allah baya mantuwa, kuma shi mai ji ne kuma mai gani.



Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Haƙiƙa ALLAH Yana yiwa azzalumi jinkiri har zuwa ranar da idan ya kama shi bazai kuɓuce masa ba.”



"Na fi ki ilimin addini ki daina kokarin yi min wa'azi.."


"Banga alama ba, kuma koda kana da ilmin toh baka aiki da shi sannan baka fahimce shi ba, ka dai yi asara, kuma ka ji kunya. Unaizah ta mutu tana ambaton kalmatusshahada, abun da kake ma baƙin cikin ta samu, kuma ta gane wanene mugun ubanta, mun fayyace mata komai kafin mutuwarta, idan ma kana tunanin ƙarya na ke yi maka, da akwai wasiyyar da ta bar min in baka kai da kwartuwar karuwarka, sannan tasa na yi mata alƙawarin ɗaukar fansa akanka, kana ganin kanka mai wayou da dabara bakasan komai kake yi Allah yana a sane da kai ba, baya mantuwa, dama ce ta ɗan lokaci, Unaizah ita ce silar tonuwar asirinka, nasan ka girgiza da jin hakan lokacin da aka faɗa maka, ƙaramin kuskure ya yi silar tonuwar asirin ka..."

da tsantsar ruɗani akan fuskarsa ya furta, "Unaizah ta musulunta? Kuma kun faɗa mata komai! Ta yaya hakan zai yiwu? ba gaskiya kike fadamin ba, karya ki ke yi..." Ya fada cikin 6acin rai..


Murmushin takaici ta yi. "Ka yarda ko kada ka yarda matsalarka ce, sannan twin ɗinka ya musulunta, nasan ka gane wa nake nufi, duk da bansan ko su kaɗai ne twins din da kake da su ba, tun da na ga kai din bunsurune baka da aikin yi sai zazzaga ya'ya kamar kashin awaki, kai ta sadaukar da su.."

Maganganunta sun ƙona masa rai, cikin ruɗu ya furta, "Wanene twin din da kike magana akai?

ƙyalƙyacewa ta yi da dariya ganin yadda ya 6ata fuska.

"Ina magana akan Sajeed, ko da ya ke bari na yi maka ta yadda zaka gane, Gabriel nake nufi."

"Tayaya akai kika san ɗana ne?" Ya tambaya a ƙagare da son ji.

A takaice ta fayyaca masa komai..


Runtse idanunsa ya yi cikin bakin ciki ya ke tariyo lokacin da ya sadaukar da su, ƙa'ida idan ya sadaukar da yaro zai ƙone komai nasa da yake amfani da shi, amma a lokacin da ya sadaukar da twins dinsa, sai bai ƙone wayar Gabriel ba, sabuwa ce bai jima da siya masa ita ba, sai ya yi restore din wayar, sham ya manta bai cire sim card ɗinta ba, ya dawo da ita gidansa na Abuja, ya ba Hajiya Sarah ya ce taba Zeenatu ta dinga karatu da ita kafin ya mayar da ita school, bai ta6a zaton ƙananun kuskuren da ya yi zasu iya zamar masa matsala ba, lamarin ya ɗaga hankalinsa, ta yadda kwakwalwarsa ta toshe a lokacin da ya kawo wayar batare da ya tuna da sim card ba! Abun da ya fi daure masa kai meyasa bai tuna ba? Meyasa kuma bai yi tunanin siya mata wata wayar ba sai ya kai mata ta Gabriel ( Ga dukkan alamu Musa baisan ƙarfin Ikon Allah ba, idan Allah ya so ya tona maka asiri, wallahi da kanka zaka aikata ƙaramin kuskuren da zai yi silar tonuwar asirinka, dubararka ko wayonka baza su ta6a amfanar da kai ba, dole ne ka aikata ta hanyar da ya so)


Yayi zurfi a tunaninsa muryar Unaisah ta katse shi,


"Dukiyar da ka ke taƙama da ita ay bada guminka ka same ta ba, haka itama ɗaukakar taka bata Allah bace, daga gani kai din irin faƙiran talakawan nan ne marasa galihu marasa godiyar Allah masu kwaɗayin abun duniya, wadanda zuciyarsu ta mutu, ai ba a tunƙaho da dukiyar da aka tara ta haramtacciyar hanya. Tausayi ka ke bani saboda na fahimci har yanzu baka san musibar da kake a ciki ba, kaifa yanzu taka ta ƙare, asirinka ya riga da ya gama tonuwa, yanzu ne zaka gane komai daka tara baida amfani, zaka rasa darajar ka! mutuncinka da ƙimarka zasu lalace, al'ummar duniya zasu fara yi maka kallon ƙasƙantaccen ɗan ta'adda, ƴan jam'iyarka da yan uwanka da abokananka kowa zai juya maka baya, zaka zama abun gudu, zaka rasa su na har abada, lalacewa ta same ta, daga inda duniya tasan me ka aikata zaka tashi daga Alhaji Musa richest former president ka koma gur6ataccen ɗan ta'adda, mutane zasu fara aibata ka, za a dinga zagin ka da tsine maka albarka kuma ko bayan ranka ba za a daina sukar ka ba, waɗanda ma basu san da tarihinka ba, idan sun zo duniya zasu ji, amma ba a matsayin mutun mai daraja ba, a matsayin fasiƙi, azzalumin ɗan ta'adda. Kuma ina taya ka murna bayan tozarcin da zaka fuskanta, da kuma azabtarwar hukuma, zaka fara ganin sakayyar mutanan da ka zalunta, ka aikata sin jariya, zunubi mai wanzuwa, idan mutun ya mutu halinsa ne ke cetonsa, Musa da wani hali zaka ceci kanka? tun wurin zare ranka zaka fara shan azaba, ka yi tunanin makomar wanda ya sani ya take sanin, ai kai kana a can cikin ƙwarin azaba, ƙasa da kafiri, a halin yanzu ko titi baka isa ka ƙetare ba matsoraci, rundunar sojoji tana jiranka, ga al'ummar gari, kana dira kafarka zasu fara jifarka... ." Ta ƙarashe maganar tana sakin dariya kamar zautatta.

Ransa yayi mugun 6aci, daga yanayin fuskarsa zaga gane ya ji zafin kalamanta kuma ya girgiza, tsabar yadda zuciyarsa ke tafarfasa har wani gurnani gurnani ya ke yi..

Shaƙe wuyanta ya kuma yi, kamar zai tsinka shi, numfashinta ya dinga kokawar daukewa tana ta nishi, yadda zufa ke tsattsafo mashi kan goshin shi itama haka gumi ke tsattsafo mata, tana ta kokarin kwatar kanta sai dai ta kasa saboda a ɗaɗɗaure ta ke da sarƙa.


"Dole in yi maki azaba mai radadi, tun da nake wani ɗan adam bai ta6a gaya min bakaken maganganu ba sai a kan ki, duk da ba na yi maki kallon mai hankali hakan bazai hana in hukunta ki ba, daga yau ba zaki ƙara shaƙar numfashi ba, kashe ki zan yi mahaukaciya, laifi ɗaya da nake danasani a rayuwata shine barin ki da na yi a raye, duk abun da kika faɗa akaina ba zai ta6a faruwa ba, ina da sihirin da zan kare kaina da shi..." Yana fada yana fitar da numfashi mai huci, baiwar Allah ta gaza taimakon kanta, idanunta kamar zasu zazzago ƙasa sunyi luhu luhu.


"Ni fa Uncle din Uwarki ne, kamar kaka nake a gurinki, ko dan haka yakamata ki girmamani don ubanki, ba zan kashe ki cikin sauƙi ba, ina so na saka tsorona a cikin zuciyarki, ta yadda ko haɗa idanu da ni ba zaki iya ba, ko kin manta da ƴar uwarki dana ɗaukko ku a tare? Baki tunanin a ina take? Tana a raye ko ta mutu? Ya tambaya cike da izgilanci yake ɗage mata gira, sakin wuyanta ya yi ta fashe da kuka kamar ranta zai fita.


Daƙyar ta iya furta, "Allah yana a tare da ita a duk inda take."


"Ki daina ambaton sunan Allah, kina wahalar da kanki ne, Allah bazai ta6a taimakonki ba, ko kin taba ganin inda ka nemi taimakon Allah ya amsa maka nan ta ke?"


"Tunaninka irin na marasa hankali ne, masu gajan hakuri, addu'a ita ce ta kare mutanan da ka so ka wulakanta rayuwarsu, Addu'a ita ce ta yi silar barin mu gidan kurkukun ƙaddara batare da saninku ba, baku iya yi mana komai ba har muka kawo wannan lokacin a raye.."


"Ki daina tutiya, ba addu'arku ba ce ta cece ku, Danish ne ya zama garkuwar ku, badan yana a tare da ku ba, ko gidan kurkukun nan baku isa ku ƙetare ba.."


sunan Danish da ya ambata ba ƙaramin karya mata zuciya ya yi ba.


"Idan muka nemi taimakon Allah, ba kaitsaye ya ke taimakon mu ba, ba ganinsa muke da ido ba, sai dai ya yi mana hanyar da taimakonsa zai isa gare mu, Danish ya taimake mune saboda Allah ya kaddara shi ne zai zama garkuwar mu..."



Shu'umar dariyarsa ya saki...


"Meyasa na ga kamar jikinki ya yi sanyi? Saboda na ambaci sunan shi?" Harara ta watsa mashi batare da ta furta kalma ba.


"Ko har yanzu kina son shi? Ya faɗa yana ɗage mata gira.


Ta6e bakinsa ya yi, "Ni ban ga abun da ya gani a jikinki da ya ja hankalinsa ba har ya fada tarkon son ki, ko da ya ke ba yin kansa bane, Danish bai ta6a sonki ba, nasan ba a ta6a faɗa maki hakan ba, amma Danish bashi ne ya ke sonki ba, Evils din jikin shi ne suke son ki...."


Wani irin faduwar gaba ta ji, maganarsa ta razanar da ita, saboda tunawa da maganar Salsabeel da ya ta6a cewa wasu abubuwan da Danish ya ke yi bayin kansa bane, kenan maganar Musa zata iya zama gaskiya.


Shu'umin murmushi ya yi ganin ya fara baƙanta mata rai.


"Tayaya ki ke tunanin zankaɗeɗan saurayi kamar shi zai so kucaka irin ki? Shi ba ajinki bane, Danish ya fi karfinki nesa ba kusa ba, ba abun da zai yi da ke, abun da baki sani ba, Danish ɗan homo ne shi, baisan daɗin mace ba sai na namiji, he's my guy, na daɗe ina kwanciya da shi, tun kafin ya mallaki hankalinsa, yana da dad..."


Bai ƙare maganar ba ta kwatsa mashi tsawa, tsigar jikinta na tashi ta furta, "Bana son ji, ka daina faɗa min, ƙarya ka ke yi mini, Danish dina ba ɗan homo bane, meyasa ka ke min magana akan shi? Bayan Danish ya mutu, ka barsa ya kwanta a ƙabarinsa lafiya..."


wata yar iskar dariya ya tuntsire da ita yana kallon baƙin cikin dake a cikin idanunta

"Na ga kishi tsantsa a cikin idanunki, har yanzu bakisan wanene Danish ba, bakisan reality dinsa ba, he's really a bad guy, da kinsan adadin fursinonin da muka sa ya kwanta da su da baki 6ata ma kanki lokaci ba, kuma ba don baya haihuwa ba, da yanzu an samu ƴa'yansa a cikin fursinoni. "


Fashewa ta yi da kukan baƙin ciki duk da tana kokwanto akan abun da ya fada, amma kalamansa sun rikita tunaninta, jikinta har kerma yake yi, "Ni ban damu da komai Danish zai aikata ba, idan ma kana faɗamin ne don ka baƙanta raina to ka sani ba zaka ta6a yin nasara ba, har yanzu ina son Danish fiye da yadda nake son raina, kuma na yi masa uziri saboda nasan komai da ya aikata ba yin kansa bane, tursasa masa ku ka yi, don haka ka daina 6ata shi a gurina, kuma ka daina yi min magana akan shi, saboda a yanzu shi ba rayayye bane..." Bata ƙare maganar ba ya katse ta, "Waya fada maki Danish ya mutu um? Kin ga gawarsa ne?" A ruɗe ta ke kallon cikin idanun sa.


Makirin murmushi ya saki. "Danish yana a raye, kuma yana a tare da ni, bayan da ya faɗa rijiya, batare da sanin kowa ba, na taimaka masa ya fito sannan na kashe Jeremiah..."


tsantsar ruɗani ne akan fuskarta, ta kasa yarda da maganar shi, "ƙarya ka ke yi, Danish ya mutu, baya a raye, saboda in har yana a raye bazai iya rayuwa batare da ni a kusa da shi ba..."

dariya ya saki tare da buga tafin hannunsa ga ƙasa, nan take wani madubi ya bayyana a saman iska..

"Ki kalla ki gani wanene wannan?"

Kura idanu ta yi akan madubin, su biyu ta gani a kwance saman gado, sun rungume junansu sunata aikata alfasha, kwata kwata babu sutura a jikin su...."


runtse idanunta ta yi gam ta cicccije la66anta, saboda kishi har saida ta fasa lower lip ɗinta jini ya shiga daddigowa, nan take wani zazza6i mai zafi ya lullu6e jikinta.


Cike da nishaɗi ya ke kallon ta.


Cikin karyayyar murya ta ce,"Ba Danish ɗina bane, Danish ba zai iya aikata fasiƙancin nan ba, kawai ka yi amfani da tsafin ka ne don ka baƙanta raina, kamar yadda ka yi editing hotunan Aunty Ummi don ka cutar da mahaifinta..."


haushi ya ji ganin ta ƙi yarda da gaske ne, sumar kanta ya damƙa kamar zai tsige gashin ta.

"Dole ki yarda da abun da idanunki suka gane maki, Danish yana a raye, kuma yana a tare da ni ."



"Ban damu ba ko kaɗan, saboda nasan cewa Danish ya mutu.."


"Bansan meyasa ka matsa saina yarda da ƙarairayin ka ba, dan Allah ka tafi ka bani guri, ka rabu da ni, idan kuma kashe ni zaka yi ka kasheni kawai zai fi min kwanciyar hankali saboda na gaji da ganin ka, na tsani ganin mummunar fuskarka wallahi..." Girgiza kanshi ya yi cike da takaici yake rarraba idanunsa akan fuskarta..

"Nasan bakisan dalilin da yasa na dauko ku ba ko?" Banza ta yi da shi.


"Saboda in dawo da ran kurkukun ƙaddara, saboda in samu ƙarfin sihirin da babu wanda zai iya ja da ni, zan gagari kowa, zan zama mai power, zan juya kowa, zan kuma sake gina kurkukun kaddara, bazan iya yin hakan ba dole saina cire zuciyar ƴar uwarki Batool na ba dodon tsafin mu ya haɗiyeta, sannan kuma in kashe ki, idan na yi hakan zan samu karfin iko fiye da na Elder."


Abun da ya ɗaga hankalinta jin zai cire zuciyar Batool yaba dodon tsafi don ya cika mugun nufinsa, kwata kwata bata damu da ta mutu ba amma bata jin zata iya bari Batool ta salwanta, no matter what..

A ruɗe ta furta, "Ni bazan iya maye gurbinta ba? Ka cire zuciyata, ka bar batool a raye, kada ka kashe ta, ko da baka da imani amma yakamata ka tausayawa Aunty Ummi, wani irin bauta ne bata yi maka ba? Ka rasa dame zaka saka mata saida hakan? Dan Allah ka da ka kashe mata babynta, gaba daya rayuwarta a cikin jarabawa take, tun tana jaririya kasa daddynta ya binne ta da ranta, sannan ka bi ta bayan fage kasa aka ɗauko maka ita, sannan ka sadaukar da ita, meyasa wai ba zaka rabu da ita ba ne? Ka hana ta rayu da iyayenta, gaba daya ta ko'ina ka tauye mata hakkin rayuwarta, wai wata irin shaiɗaniyar zuciya gare ka??" Ta faɗa cikin kuka.


Cikin halin ko in kula ya ce, "Ba shawararki nake nema ba, babu wanda ya isa ya dakatar da ni, dole in cika burina ko ta halin ƙaƙa, yanzu haka suna can zasu cire mini zuciyarta, ko zaki iya taimakonta ne?"

Tana kuka tace bazan iya ba amma Allah zai taimaketa, kuma in sha Allah ba zaka ta6a cika burinka ba, ina ji araina zasu farmake ku a yau din nan, ka jira ka gani, ƙarshenka ne ya zo, tun da har ka yi kuskuren daukko mu, In sha Allahu daga yau ka gama yawo.

Bushewa yayi da dariya,

"Tayaya Allah zai taimake ta? Kefa da kanki ki ka ce Allah baya taimakon mutun kaitsaye sai dai yayi masa hanyar da taimakonsa zai iso gare shi? tayaya Allah da ya ke jinkirta amsa addu'ar bayinsa zai iya taimakon ku cikin sauri a irin wannan lokacin? Ki daina saka rai, saboda babu wanda zai taimake ku, babu wanda yasan a inda ku

52 / 107