Chapter 74 Reading KURKUKUN KADDARA FINAL STEP BY HAFSAT BATURE BOSS.txt Arewa Novels

KURKUKUN KADDARA FINAL STEP BY HAFSAT BATURE BOSS.txt

Author :  Boss Barture Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   74 / 107

219K to 222K   out of 319.4K words

zafin abun aransa.


"Baba, Baka taba jin tausayi ko irin danasani, a lokacin da ka raba uwa da danta, ko ka kona mutun da ransa, ko ka keta haddin kananun Yara..."

dakyar ya iya ƙarashe maganar saboda nauyin furtawa da ya ji.

"bana jin komai, na fada maka, duniya nasa agaba, evils din jikina babu Allah aransu, bansan tausayi ko imani ba.."

"Amma yanzu ina fata babu evils a jikinka da sauran Elders dama kowa dake da sihiri ta 6angaren ka"

Yar dariya baba Obie yayi"kana tambayata ne saboda bakason in an tashi hukuntamu mu 6ace ko evils su taimake mu"? Girgiza kai Owais yayi"a'a kawai inaso na sani ne"

"Babu Owais, Evils sun koma mazaunin su, na kuma binne sihirina babu wanda zai iya tono shi, In ba magajina ba"

"In sha Allah shima magajin naka bazai ta6a binno shi ba har abada, mun rabu da annoba"

dariya baba Obie yayi yadda kasan baida wata damuwa.


"karka damu Owais, ai magajin nawa ya ƙyamaci abun a zuciyarsa tun farko shiyasa ko evils suka gaza yin tasiri akan shi, gadai shi amatsayin Evil giant amma bamu isa mu juya shi son ran mu ba, duk da nasan Allah ne ke tsare shi, akwai kariyarsa atare da shi, bayan haka sai gashi Kaddarar da muke tunanin killace ta zai zamar mana mafita, tazo ta sace Zuciyarsa har ma da evils dinsa, ni kaina nagaza sarrafa shi son raina, wannan yarinyar ba ƙaramar ta'asa tayi mana ba, yar mitsila da ita, owais nifa ban ta6a ganinta ido da ido ba, sai dai a madubin tsafina, sai kuma ranar dinner din Hateem, amma ina jin labarin taƙadarancin ta..."


baisan ya akai maganar baba Obie taso bashi dariya ba.


"Kana jin haushin tayi silar lalata komai naku"?


"Bana jin haushinta Owais, hasalima burge ni ta ke yi, Ina son yaro masifaffe mara tsoro, mai ƙwarin gwiwa, kuma kaga tayi silar da kuka kawo karshen kurkukun ƙaddara, gaskiya na jinjina mata,..." ya fada da murmushi akan fuskarsa.


"owais nifa lamarin Ubangiji Ya razana ni wlh, yadda komai ya sauya, duk wani munafunci da makircin da muka daɗe mu na yi a boye, tsawon shekaru bamu ta6a yin Kuskuren da wani zaisan koda suffar mu ta asali ba, amma wani abun daure kai, Cikin yan watanni komai ya warware, asirin mu Ya tonu, gamu a cikin cell, mu da muka saba garƙame ya'yan mutane kamar dabbobi, Yau mune a garƙame? Kurkukun da muke ƙuntata rayuwar mutane, mu azabtar da su a cikin sa, yanzu babu shi, muma nan da ƴan kwanaki ka ɗan zamu shige shi, Owais Allah abun tsoro duniya abun tsoro! owais komai dana mallaka ayanzu babu shi, na rasa dukiyata, ya'yana, yancina, mutuncina, gidana, farin cikina, komai owais, ban taba zaton ma rana irin wannan zata zo ba, owais inaga idan na mutu? Aka binne ni daga ni sai mugun halina? Meyasa ban fara tunanin menene makomata ba kafin na aikata badaidai ba? Meyasa banyi tunanin dole fa wata rana in mutu ba? Kuma komai dana mallaka a gidan duniya zan bar shi? kuma ita duniya ba madawwama bace, zama ne na dan lokaci, Kodai kayi ayyuka nagari ka ceci kanka duniya da lahira ko kuma ka dawwama cikin nadama da bakin ciki.."

ya faɗa da damuwa akan fuskarsa.

"Owais na shiga Uku, na bani na lalace! Ya zanyi Owais! Na riga na 6ata komai! Koda zan tuba Allah bazai yafe hakkin wadanda na zalunta ba, shine zunubi mafi muni da haɗari arayuwa, basa araye balle in nemi yafiyarsu, da zan curo maka zuciyata kaga yadda bakin ciki ke konata da raɗaɗi wlh zakayi mamakin meyasa bata dakata da bugawa ba"

Tausayin sa ne ya kama Owais, har baisan sa'adda ya mike ya zagaya ta bangarensa ya zauna kan table din gaban sa ya rungumo shi a kirjin shi, kukan ma kasa zuwa masu yayi sai dai suka kama yin kukan zuciya, wata irin soyayyar shi Allah ya jarabceshi da ita, bamashi ba duk Wanda yake rayuwa da Obie zaiji irin ta a zuciyarshi saboda yadda yake kyautata ma ahlinshi dama wadanda ba ahlinsa ba kowa nashi ne ga jin kan na kasa dashi da son taimakon wanda baida shi, in badan haka ba karamar tsanarshi zaiyi ba baba Obie ya cici kanshi suma ya cucesu ..


Kwana su ka yi a rungume da juna, ba bacci, sai zullumi da fargaban hukuncin da kotu zata yan ke mashi.


Kamar yadda suma can Ahlin nasa basu iya runtsawa ba, kwana sukayi a zaune, sun yi kuka har sun gaji damuwa taci tacinye su, saura jiran tsammani





*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥🌹*




~_______________________________🔥~




*COURTROOM, FEDERAL HIGH COURT*


*BABBAR KOTUN TARAYYA*



A ranar da za'a yi zaman shiri'ar Elders kar ku so ku ga yadda jama'a suka dadda6e babbar kotun tarayya, ta ko'ina zauren kotun ya cika maƙil da ƴan jarida, da kuma human rights activists) masu fafutukar kare hakkin ɗan adam) ƴan majalissa da ministoci, gwamnoni da sauran manyan ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki a ƙasa. Wasu daga cikin iyalan Elders sun hallara, kuma abun ƙayatarwar, gaba ɗaya an buƙaci a zo da fursinonin kurkukun ƙaddara da suka rage. Ba'a ta6a yin shari'ar da ta ja hankalin duniya ba irin wannan, saboda kowa jiran ta yake yi, idon duniya ne akan kotun tarayyar Abuja, kowa ya ƙagara da ya ji hukuncin da za a yanke masu, sa'ilin da Isod Agents suke shigowa cikin zauren kotu tare da Elders sun yi masu ƙawanya, baka iya ganin fuskokinsu saboda an yi masu alfarmar rufe fuskar su da mask, amma idanunsu a buɗe suke.



Alƙalin da zai yi shari'ar babban mutunne dattijo, Justice Salahuddeen Muhammad tsohon abokin baba Obie ne, yana a zaune kan kujerarsa, cikin shigar sa ta alƙalai, idanunsa sanye da farin glass.



Bangaren Prosecutors gaba ɗaya sun hallara kowan nan su yana zaune kan kujerar sa, ga uban case files na kurkukun ƙaddara a gaban su suna duddubawa.



Dangin baba Obie sun fi kowa shiga tashin hankali da damuwa.


Lokacin da Justice Salahuddeen ya fara magana kotun ta yi tsit kamar mutuwa ta gifta, ko sautin tari baka ji saboda kowa burinsa ya ji me alƙalin ya ke cewa..

"This court is now in session..." Ya faɗa a nutse tare da kallon al'ummar dake cikin kotun, umarni ya ba court registrar na ya yi announcing shari'ar da za a saurara, bayan ya miƙe ya soma karantowa kamar haka,

"The case before us today is that of the Federal Republic of Nigeria and Mr. Obinna Chimaobi wanda kowa ya fi sani da dattijon arziƙi, Alhaji Musa Wadata former president of our country, Ifeanyichukwu Lucas, Ja'afar Falgore wanda aka fi sani da Ɗan Iya......"



Gaba ɗaya saida ya zayyana sunayen su, kafin alƙali ya buƙaci da a fiddo su gaban kotu, gaba ɗaya idanu suka koma kan su, kunyar duniya ta kama su, sun muzanta sosai, duk suka kasa haɗa idanunsu da na kowa bayan da aka buɗe fuskokinsu, hannayensu da ƙafafuwansu gaba ɗaya ɗaure suke da sarƙa, kamar dabbobi da ƙyar suke ɗangyasa ƙafafunsu. Har suka ƙarasa da su inda za su tsaya wato cikin dock, ba su ɗago da ido sun dubi al'umar da ke a cikin kotun ba, iyalin baba Obie sun shiga matsananciyar damuwa, hankalinsu na kan mahaifinsu tun lokacin da aka shigo da su suke ta kallon shi idanunsu cike da ƙwallar baƙin ciki, gaba ɗaya zuciyoyinsu a cike suke da zullumi da fargaba, haka ma sauran iyalan elders da suke a cikin kotun baƙin ciki ne ƙumshe cikin zukatansu. A duniya kenan ina ga ranar tonan asiri ta lahira.


Bayan an fiddo su aka fara announcing of appearance, in da prosecutor ya miƙe cikin natsuwa, bayan ya yi kalamin girmamawa ga alƙali ya soma bayyana kan shi tare da sunan shi, ya ɗaura da faɗin, "...On my humble appearance is for the prosecution." Bayan ya gama ya koma ya zauna, wani ma ya miƙe bayan ya gyara rigar shi ta lauyoyi ya fara bayanin kan shi kamar yadda wanccan ya yi, ya ɗaura shima da faɗin, "...My humble appearance is for the defendants. (lauyan waɗanda ake ƙara) Haka duk suka rinƙa tashi suna gabatar da kawunan su.


Bayan sun kammala prosecution counsel (Lauyan da ya yi filing case ɗin daga hukumar Isod) ya sake miƙewa ya bayyana charges da ke gare su tare da ranar da aka shigar, ya ɗaura da faɗin, "...The defendants are accused of dark magic cult, human sacrifices, kidnapping, torture, murder, and human trafficking."


("Waɗanda ake tuhuma, ana tuhumar su da laifin baƙin sihiri, sadaukarwar mutane, garkuwa da mutane, azabtarwa, kisan kai, da fataucin mutane.") Bayan ya gama zayyana laifukan da ake tuhumar su da su ya buƙaci da a karanta ma masu laifin charges ɗin don su amsa, bayan alƙali ya bada damar hakan court registrar ya miƙe idonshi akan elders ya ce masu ga abubuwan da ake ƙarar su akai su saurara don su ji, he reads the charges to them openly, da turanci ya zayyana masu kamar yadda ake magana a cikin kotun, amman duk da haka bayan ya gama sai da ya tambaye su sun ji abun da ya karanta ko akwai wanda bai fahimta ba bai jin yaren da aka faɗi da shi, wasu daga ciki ne suka jinjina kai alamar sun fahimta, yayin da wasu sukai shiru ba tare da sun ɗago kai ba, sanin su su waye kuma an san suna fahimtar yaren da ake magana da shi ya sa aka ci gaba,


Prosecution Counsel ya sake miƙewa cikin nutsuwa ya soma kora jawabi dangane da kurkukun ƙaddara, bai yi kuskuren ko da harafi ɗaya ba, komai da Elders suke aikatawa a gidan kurkukun ƙaddara da irin azabtarwar da suke yi wa fursinoni saida ya zayyana su tiryan tiryan...."


Kowa da ke a kotun ya nutsu yana sauraron shi, idanun mutane suka cuccuko da ƙwalla saboda tausayin prisoners da ya kama zuciyoyinsu, shi kan shi alƙalin farin ruwa ne kwance a cikin idanun shi.

Kowa ya shiga tashin hankali da firgici, mutane sai girgiza kai suke wasu har da matse ƙwalla.


Elders kuwa cikinsu ya ɗuri ruwa, sai zazzare idanu suke yi, cikin tashin hankali da kunyar duniya..


Bayan da me gabatar da ƙara ya ƙarasa zayyana komai da kuma hujjoji da shaidu..

A ƙarshe ya ce, "We urge the court to impose the maximum penalty for these heinous crimes."


(Muna roƙon kotu da ta zartar da mafi girman hukunci kan waɗannan munanan laifukun) Ya koma ya zauna a mazauninsa.


Jinjina kai Alƙali Salahudeen ya yi tare da numfasawa cikin murya mai kaushi ya furta, "Thank you, Br. Nawaz."

Maida duban shi ya yi kan elders ya ce sun ji laifukan da ake tuhumar su da aikatawa sun amince? Farko duk shiru suka yi idanun mutanen kotun na akan su, kowa na su ya ji mi za su ce, Baba Obie ne ya fara jinjina kan shi tare da furta ya amince, duk sauran ma suka yi hakan, amman abun mamaki Musa nunawa ya yi bai amince ba, fuska a murtuke rabinta an rufe da bandeji ya ce yasan ya ta6a yin sadaukarwa don biyan buƙatun shi, kuma duk yaran da ya sadaukar jinin shi ne, don haka ƙazafi ne aka yi mashi shi bai aikata sauran laifukan ba kuma shi baya a cikin elders, jin abun da ya ce yasa Pravin a ruɗe shima ya ce sadaukarwa kawai ya ta6a yi bai aikata sauran laifukan ba baya a cikin elders, bayan da farko ya jinjina kai alamar ya amince, Ɗan-iya na so shima ya musa tuhumar da ake mashi amman ba dama don yasan iya gawar Anah da aka tono ta isa hujja akan shi, duk da halin damuwa da Chief Owais yake a ciki sai da ya ɗan yi murmushin takaici ganin yadda suke son naɗe tabarmar kunya da hauka,

Jin haka ya sa alƙalin maida duban shi kan lauya masu ƙara ya ce mashi ya ji abun da suka ce na basu amince ba, miƙewa ya yi ya ce in an bashi dama zai gabatar da hujjoji alƙalin ya ce an bashi, lauyan ya buƙaci a fiddo da prisoners gaban kotu, bayan sun fito gaba ɗaya sun tsaya a cikin witness stand lauyan ya je gaban su a nutse ya fara yi masu tambayoyi game da kurkukun kaddara da abubuwan da ake aikatawa, gaba ɗaya sai da suka faɗi komai da ake aikatawa, bayan ya gama yi masu tambayoyi ya gabatar ma da kotun hotunan kurkukun ƙaddara da aka ɗauka lokacin da su Owais suka kai farmaki na biyu, bayan su ya ƙara gabatar ma kotun da wasu shaidu wanda suka samu daga wurin Baba Obie ciki harda vediotape na elders da su kan su basu san da shi ba da kuma list na sunayen su da bayanan su, harda hotunan abubuwan da aka samu a gidajensu da aka je bincike.


Bayan ya gama gabatar ma da kotu duk hujjojin, alƙali ya maida duban shi kan lauyoyi masu kare waɗanda ake tuhuma ya ce, "Defenses, do you have any statements to make?"

Farko duk shiru suka yi kafin wani ya miƙe ya gabatar da kan shi a matsayin lauya mai kare Alhaji Musa (Dama kafin a zauna zaman shari'a, waɗanda ake tuhuma da laifi suna da hakkin ɗaukar lauyoyi da za su kare su), Ya fara bayani da cewa sam bai gamsu da hujjojin da aka gabatar akan alhaji Musa ba saboda za a iya yi mashi ƙazafi tun da shi babban mutum ne ɗan siyasa dole bai rasa maƙiya masu son ganin bayan shi, kuma duk hujjojin da aka bayar basu isa su gamsar da ya aikata sauran laifukan da ya ce bai aikata ba tun da yanzu muna a lokacin technology duk za a iya ƙagar su, har prisoners ya tambaya kan ko lokacin da suke a kurkukun sun san su waye elders duk suka amsa da basu sani ba, ya ce ko wannan ma hujja ce da zata sa kotu ta yarda ba lalle yana cikin su ba, bayan ya gama jawabin shi ya roƙi kotu da ta yi nazari sosai kada ta amince da hujjojin da aka bayar kafin ya koma ya zauna, hannu chief Owais ya kai ya ruƙe ha6ar shi, a ranshi yana mai mamakin wani alƙawari Alhaji Musa ya yi ma lauyan da har ya iya yin wannan ƙarfin halin.


Bayan lauyan masu ƙara ya sake miƙewa ya buƙaci da a bashi dama zai ƙara gabatar da wasu hujjojin alƙali ya bashi, Unaisah ya buƙaci ta fito, bayan ta tsaya a wurin da aka tanada ya fara yi mata tambayoyi kan ko tasan alhaji Musa, aikuwa kaman tana jira nan ta shiga kora jawabi tun daga kan zuwan Unaizah kurkukun ƙaddara da yadda ta mutu da wasiƙar da ta bata da diary ɗinta mai ɗauke da hotunan su har da shi, daga ƙarshe ta yi bayanin yadda ya sace su ita da Batool ya sake maida su kurkukun kaddara don cika ƙudirin shi na zamowa shugaba inda har ta yi nasarar watsa mashi acid ta kuma buga mashi zarto a kafaɗa, bayan ta gama lauyan ya yi ƙarin bayani tare da nuna ma alƙali ciwukan da Unaisah ta ji ma alhaji Musa, daga baya ya gabatar ma kotu da wasiƙar tare da diary ɗin Unaizah. Bayan alƙali ya gama duba su ya tambayi lauya mai kare Alhaji Musa ko akwai abun da zai ce, miƙewa ya yi ya ce duk abun da Unaisah ta faɗa zasu iya zamowa ba gaskiya ba shirya mata aka yi amman yana son a bashi dama ya yi mata tambayoyi alƙali ya ce an bashi, tun da ya tsaya a gabanta ta wani murtuke fuska, tambayoyi ya fara yi mata kan yadda ta ce alhaji Musa ya sace su ya maida su kurkuku, duk tambayar da ya yi mata sai ta bashi amsa,

"Kin ce bayan ya maida ku kurkukun, ya sanar da ke kudirin shi na son kashe ki sannan kuma ya cire zuciyar ƴar'uwarki, a ƙarshe kuma kika yi nasarar watsa mashi acid kika kuma raunata mashi kafaɗa, duk yana mi har kika samu damar da ke kika aiwatar masa da hakan ba tare da shi ya aiwatar da ƙudirin na shi a kan ki ba?" Wani kallo ta jefa mashi tana tura baki tare da hura hanci ta ce, "Allah ne bai nufa zai cutar da ni ba duk da ya samu damar hakan, kuma dama Allah Yana yiwa azzalumi jinkiri har zuwa ranar da idan ya kama shi ba zai iya ku6uce masa ba, haka na sanar da shi a lokacin, to a ranar dama Allah ya ƙaddara dubun shi zata cika, dama na sanar da shi idan muka roƙi Allah ba kai tsaye yake taimakon mu ba don shi ba a ganin shi sai dai ya yi mana hanyar da taimakon shi zai iso gare mu, a lokacin na ce mashi in sha Allah zai ga yadda addu'ar wanda aka zalunta take tasiri har ya yi nasara akan wanda ya zalunce shi, amman sai ya ƙalubalanci hakan da na faɗa ya ce wai zai jira ya ga ta yadda taimakon Allah zai iso gare mu, nasan Allah ne ya nuna masa ishara shine dalilin da ya sa ya jinkirta aikata abun da ya yi niyya a gare mu." Ba ƙaramin burge mutane ta yi ba yadda ta kora mashi jawabin, mutane suka shiga jinjina kai wasu da murmushi akan fuskokin su.


Ƙarshe lauyan ya ƙaryata cewa Alhaji Musa ya aikata masu hakan ya ce duk sashi faɗi ne, ba yadda za ai ya samu dama irin haka amman ya kasa aiwatar masu da kudirin shi har ita ta yi nasara akan shi, in ma da gaske ne hakan ya faru da su to akwai yuwuwar bata a cikin hayyacinta ne ta ruɗe har ta kasa tantance wanda ya aikata masu hakan, yana rufe baki a tsiwace ta ce,


"Ina a cikin hayyacina! Na yi rayuwa a cikin kurkukun ƙaddara na tsawon lokaci, tun ina da shekara 11 na tsinci kaina a kurkukun, ba irin tashin hankalin da ban gani ba, an yanka mutum an feɗe gaba na, an yi mani wankan jini! Na ga abubuwan tashin hankalin da sun isa su saka ni in haukace amman hakan

74 / 107