Chapter 91 Reading KURKUKUN KADDARA FINAL STEP BY HAFSAT BATURE BOSS.txt Arewa Novels

KURKUKUN KADDARA FINAL STEP BY HAFSAT BATURE BOSS.txt

Author :  Boss Barture Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   91 / 107

270K to 273K   out of 319.4K words

fito a balarabiyarta.

Miƙewa yayi tare da nufar kofar dining room "ki biyoni" cike da jin shakkar shi tabi bayansa.

Saman dining chairs suka zauna suna fuskantar Juna, ga kayan dinner shaƙe da table din gabansu, ya lura har yanzu a tsorace take da shi, duba da yadda Jikin ta ke kerma..

"Zaki iya ci da hannunki! Ko in baki abaki"!

Da jin Hakan Yasa cikin sauri ta ɗauki glass of juice me sanyi ta kwafa abaki tana sha tana satar kallon shi yayin daya sadda kan shi ƙasa sai taga kamar murmushi ya ke yi amma bata gaskata hakan ba.


Bai yi zaton yarinyar ta samu tarbiya har haka ba, da wuya ya jaraba mace da tayin kanshi taƙi amincewa sai akan Batool, tsoron Allahnta, da kamun kanta, da kuma yardar da tayi masa sunfi komai Jan hankalin shi a gare ta.


Satar kallonta yayi, tana tsaka da cin meatloaf mai dan karan daɗi, Yatsun hannunta nata kerma kaf kaf kamar wacce sanyi ya kama, Allah Allah take ta gama ta tafi gida.


Kaɗan taci ta dakata, tare da duban shi "yaya Owais, na koshi, dama dazu naci abinci gidan biki, zan tafi basai ka kaini a mota ba, Unaisah tana can tana jiran ka, kaga dare ya yi sosai"

Yanayin yadda ta ke yin magana cikin sanyin murya ba ƙaramin jan hankalinsa ta ke yi ba.

Bata ƙare maganar ba, Ya katse ta da cewa"ban yarda kin koshi ba, You're still hungry, Either eat more, or we'll stay here forever"

arude ta soma cuccusawa abaki, taci samosa, taci spring rolls, ta hada da straw berry shortcake, Tana gamawa ta kai hannu ta dauki milk shake ta sha sosai duk yana kallonta, bakin ta yayi dama dama da cake.

Tana haki ta furta"yaya Owais na ci da yawa yanzu, zan tafi"

bata jira amsar shi ba ta mike tana zazzare idanun ta.

"Muje nakai ki a mota ta, idan kikayi min gaddama zamu kwana anan ne" a firgice ta amsa da toh.

"Ki jira ni a falo, zan shiga ciki in sanya suturana" amsawa tayi da toh.

Akan idonta ya fuce daga falon ya nufi Cikin bedroom.

Cike da zullumi take ta jiran shi, babban tashin hankalinta, ummin ta da daddynta tasan zasu nemeta, gashi ta manta ma inda ta jefa wayarta.



Tasan idan ta koma gida zasu iya yi mata faɗan daren da tayi a waje, kuma zasu tuhumeta akan Kayan da ta canza a jikin ta, Ya ilahi ta furta tana dafe goshinta daya jike da gumi.


Fitowa yayi jikin shi sanye da jallabiya ash, ya ruƙe car key dinsa a hannu.


"Na manta kayan dana cire a closet room"


ta faɗa batare da ta bari sun haɗa idanunsu ba.


"Zaki iya zuwa ki dauka"

cikin sauri taje ta ɗauko kayan ta ƙuɗundunesu a hannunta.


Bata iske shi a falon ba, hakan yasa ta fito harabar part din, a parking space ta hango shi a tsaye Ya jingina bayan shi jikin motar shi, ba wadda sukazo gidan da ita ba.


Kafin ta ƙaraso Ya buɗe mazaunin driver Ya shiga, tana ƙoƙarin buɗe back seat muryarsa ta katse ta"Am I your driver"? Cike da izza ya furta.

Da sauri ta dawo mazaunin gaba Ta bude ta shiga ta zauna tana ta faman sauke a jiyar zuciya, ta ɗanyi mamakin ganin shi ne zai yi driving da kan shi bayan bata saba ganinsa yana driving ba.


Bayan ya tashi motar, ya yi reverse ya fusgeta da matsakaicin gudu motar ta fuce daga gida.



~____💘_____💋______🌹______💕_______💗________🔥~



*🔥UNAISAH💗*



tana tsaka da sharar baccin ta, Kwatsam hasken ɗakin Ya ɗauke ɗuff, sai na Candles da ke ci, ƙarar qira'ar alqur'anin daya karaɗe ɗakin ne Ya farkar da ita a firgice ta farka tana zare sleepy eyes ɗin ta, wata irin faɗuwar gaba taji sa'ad da ta lura babu hasken fitilun ɗakin sai na candle lights!


Zuciyarta ta shiga harbawa da sauri da sauri kamar ana mata lugudan ta6are a ƙirjin ta.

Bata ta6a tsintar kanta a cikin tsoro irin na wannan lokacin ba tun bayan rabuwarta da kurkukun ƙaddara!

Abu biyu ne yazo aranta, watakil Yaya Owais ne Ya kashe hasken ɗakin sa'ilin da take bacci don ya bata mamaki, ko kuma Electricity din gidan ne Ya samu matsala, gaba daya ta manta menene yayi silar farkawarta daga bacci.

A tsorace ta furta"Yaya Owais? Kai ne ka shigo? Kana ina? Nasan kaine ka kashe min hasken ɗaki, dan Allah kayi min magana, gaba daya na tsorata.."


Ta faɗa tare da miƙewa daga kan kujerar, jikinta nata kerma kamar mazari.

La66anta na kerma ta kuma cewa"hubby, pls kada ka wahalar dani, bazan iya jurewa ba, idan kaine ka yi min magana ko hankalina ya kwanta, tun ɗazu nake jiran zuwanka... "

bata ƙarashe maganar ba, Unexpected ta tsinkayi sautin takun tafiya a cikin kunnanta daga bayanta, tuni tasha jinin jikin ta, jin yaƙi amsa mata yasa tayi tunanin ba ya ya Owais ba ne, wani ne ya shigo gidan, nan fa ta ƙara shiga tashin hankali, tsoro ya hana ta juya ta fuskance shi, sai faman zazzare idanunta ta ke yi, dakyar ta iya ƙyalla idanun ta ta cikin mirror ɗin gaban ta ta soma hango shi da taimakon Candle lights...


Walking magestically ya ke nufo cikin bedroom ɗin kamar baison taka ƙasa, daga ƙasa ta soma ƙare ma shi kallon ƙurullah da tsantsar ruɗani da fargaba saboda bata tantance wanene ba, tsayin sa ya zarce na Chief Owais.

Sanye ya ke cikin shiga ta larabawa, wata hadaddiyar dishdasha long tunic, launin ivory white ta bayyana tsantsar zazzafar surar sa mai matuƙar jan hankali, daga fadadan kafadunsa wata madaidaiciyar bisht cloak ce (alkyabba ) launin Golden-brown, daga gefenta da bakin ta gaba daya adon duwatsu masu daraja ne lullu6e da rigar, sai kyalli su ke yi suna sheƙi, wuyan hannunsa na dama yana asanye da Expensive rolex Watch irin wadda sai dan wane da wane su ke sanyata, both mid fingers dinsa suna a sanye da gemstone-encrusted rings, yayin da kafafunsa ke asanye da hand made Leather arabian shoes, mayar da idanunta tayi akan fuskarsa cike da fargaba take kokarin gano wanene sai dai kash rabin fuskar tasa yayi covering dinta da Gold leaf Mask, gaba ɗaya kansa a naɗe ya ke da turban, irin naɗin larabawa, daga kasan rawanin doguwar sumar kansa ce ta zubo, wutsiyoyin kitsonsa biyu suka hauro ta saman kafaɗarsa har izuwa kan broad chest dinsa, daga bayan sa wata sumarce har mid back dinsa mai kyan gaske tana ta sheƙi brown shar da ita..

Duk ƙamshim da bedroom din ta ke yi saida Ƙamshin turarensa ya disashe shi, wani irin sweet fragrance mai rikita shauƙin bawa, daga yanayin tafiyarsa ta fahimci yana da izza da qasaita daga gani mutum ne mai tsantsar ilmi da aji kuma wayayye mai cikar kamala da nutsuwa.

Unaisah ta gama ruɗewa, Tsoro da fargaba suka cika Zuciyarta da ke tayi mata dakan sakwara, aranta tana ta tunanin wanene wannan Hamshaƙin saurayin? shin tayaya akai ya shigo gidan Auranta? Kwata kwata bata yarda Mutun ne ba, tafi alakanta shi da jinsin jinn saboda zubin sa!


Anya kuwa Yaya Owais ya sanya malamai suyi safkar alkur'ani a gidan kafin ta tare?


Tana kokwanto saboda gayanan tunkan aje ko'ina ta fara ganin ifritun Aljani..



Yawu ta haɗiya mai zafi makoshin ta ya bada sauti ƙutt, cikin rawar jiki ta fara tunanin mafita! Gashi tamanta waya agida balle ta kira wani ta fada masa Aljani Ya kawo mata farmaki, ita kadai baiwar Allah, tunanin guduwa tayi duk da tasan ba lallai takalman kafarta su bata hadin kai ba saboda tsinin su.

Ganin Ya kusa karasowa cikin ɗakinne Yasa Ta fara neman gurin da zata 6uya cikin rawar jiki ta soma ja da baya cikin sanɗa don karya ji takun ta.


zukunnawa tayi ƙasa da rarrafe ta dinga yin tafiya ta nufi karkashin gado ta shige ciki ta 6uya gabanta nata faɗuwa, aranta tana mai cigaba da ambaton La'Ila ha'illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin"


~________________________________🌹~



A hankali ya ƙarasa shigowa tsakiyar dakin, cikin takun ƙasaita ya nufi gaban gadon, Unaisah dake a karkashinsa tana leƙen ƙafafunsa da ke tunkaro gadon, tashin hankali tuni gumi ya wanke fuskarta, runtse idanunta ta yi gam ta dinga karanto Ayatul kursiyo a cikin zuciyarta da sauran addu'o'in neman kariya daga sharrin jin.


A hankali ya zauna daga gefen gadon ya ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya..


Zuciyarta ce ta tunzurata akan ta duba ƙafarsa taga idan irin na mutanene ko kofaton jaki irin na aljanu kamar yadda Aunty Danejo ta ta6a bata labarin cewa Idan aljanu suka yi suffar mutane zaka iya gane su ta kafarsu saboda ba irin na mutane bane, Kofaton Jaki gare su.


Cikin sanɗa ta zuƙunno da kanta ta ƙurawa fatar ƙafarsa ido, Har saida gabanta ya faɗi ganin kafar tasa fara sol kamar ta jariri yadda kasan bai ta6a taka ƙasa ba, hasken fatar sa irin pure shining white ɗin da ba acika samun shi ba ne naturally.


Ruɗewa tayi, duk da tana kokwanton kamar mutunne tun da bata hango kofaton jaki ba, zuciyarta ce ta raya mata idanunta ne suke nuna mata ba daidai ba, watakil owais ne girgiza kai tayi in har Owais ne bazai ta6a zama fari ba.

Ganin Ya motsa kamar ya miƙe yasa ta katse zancen zucin nata, kanta harya fara ciwo, ga yunwa da bacci tana ji, ga zullumi da fargaba sun cika zuciyarta..

Shigewa toilet ya yi, tana lekensa taga glashin bangon toilet din ya disashe, aranta ta ayyana ya koma mazauninsa kenan, tunda ance toilet gurin zaman aljanu ne, cikin sauri da rawar jiki ta fito da niyar ta fece, kwatsam ta hango tamfatsetsiyar waya ajiye saman bedside drawer, fasa fita tayi

Yatsun hannunta na kerma ta dauki wayar ta danna number din daddynta ta kira ta kara a kunne cike da fargaba..


Unexpected wayar Taj dake aje kan bedside drawer ta fara ringing, at same time suka farka.


"Wanene Ke kira" ta tambaya tana duban Taj daya dauko wayar yana kallon screen dinta yace"ban sani ba amma bari na ɗaga maybe wani emergency call ne"

Amsawa tayi da ''to'' Picking yayi ya kara a kunne

ko sallama batayi ba ta fashe da kuka kamar ranta zai fita.

Har Benazir saida taji yo kukanta, hankali atashe suka dubi Juna..

Har suna haɗa baki gurin furta"Unaisah! Meke damunki? Meyasa ki kuka um miya faru wayar waye kuma wannan"?

Dakyar ta shanye kukan, Cikin shesshekar murya tace"yaya Owais baizo ba, Inata jiran shi ni kadai agidan tsoro nake ji, kuma yanzu wani ifritun aljani ƙaton maridi ya shigo dakina, baka ganshi ba daddy, dogo fari fat kamar fatalwa ya saka kayan larabawa, tun dazu nake boye a karkashin gado har saida Ya shiga toilet sannan na samu na fito har na dauki waya, wallahi daddy Mutuwa zanyi in baka zo ka ɗauke ni ba, kashe ni zai yi, dan Allah daddy ka zo tare da Baba Imam ya kora mana aljanun gidan da ayar Allah, in har ba so ku ke ku rasa ni ba.... "


daƙyar ta ƙare maganar..

Hankalin Benazir idan yai dubu to Ya tashi, Taj ne kadai bai ɗaga hankalinsa ba, kallon juna su ka yi.

Kafin wani ya furta kalma kiran ya katse.

"Bazan iya jira ba, zanje kawai na tafo da ita, tayaya zai barmin ƴa a irin wannan lokacin tana ta jiran shi, wunin yau ko abinci bata ci ba saboda sunce zasu ci agidan su, gashi harta fara gane ganen aljanu"

Cikin 6acin rai ta ƙarashe maganar tana ƙokarin saukowa daga kan gadon Taj yayi saurin ruƙo hannunta, cikin fushi kamar zatayi kuka tace"kana fa jin abun da tace! So ka ke mu rasa ta ne? Tun kan aje ko'ina har ya fara nuna rashin kulawa akanta! Ba fa dan na gaji da ita na bashi ita ba"

Murmushin gefen fuska Taj yayi"Ummu Unaisah, Ki kwantar da hankalinki, ruɗewa tayi ne amma ba aljani bane tagani, Mijin ta ne"

Aruɗe Benazir tace"ita fa da kanta tace aljani ne! Unaisah batasan fuskar Owais bane da zata rasa gane shi!? ina Owais yaga hasken fata? idan kai baka dauki maganarta serious ba nina ɗauka.."

tana ƙarashe maganar ta fusge hannunta daga nashi ta nufi closet ta dauko veil ta yafa.

"Karki Fita Benazir, ban baki izni ba, ki dawo zanyi maki bayani.."


"Ai fa sai ka yi Tajo, kaima kasan ba sauraron ka zan yi ba... "


~____________________________________🥺💘~


_A 6angaren Unaisah, batasan ya akai kiran ya katse ba, ta dinga trying baya zuwa, kamar ta yi hauka, batai aune ba, kwatsam ba zato ba tsammani taji motsinsa abayanta, Kamar numfashinta zai ɗauke tsabar razana, bugun Zuciyarta ya tsananta, gumi Ya cigaba da tsastsafo mata ta saman goshinta da hancin ta, wani irin tsoro ne ya ziyar ce ta, duk tabi tasha jinin jikin ta..._

Kafin tayi wani ƙwaƙƙwaran motsi sanyayyar Muryarsa ta ratsa kunnanta"My Phone.... "


Ya Ilahi Wani irin ruɗanine Ya cika zuciyarta jin muryar ifritun Aljanin tayi mata shige da ta wani wanda ta daɗe da rasa shi arayuwar ta, muryarsa da ko a mafarki taji ta saita shaideta, ko da tana a cikin maye ne..

Kwata kwata batasan wayar wacece ta ɗauka ba, sai da taji maganarsa, tana zazzare idanu ta ɗan saci kallon wayar da ta ruke a hannun ta, ƙara zare idanunta tayi tamkar ƙwayar idon zata faɗo ƙasa a kiɗime take kallon hoton ta da ke akan Wallpaper ɗin wayar ganin abin ta ke kamar a mafarki kamar idanunta sun samu matsala....!


Mutun ɗaya ta ta6a turama hoton ta whatsapp dinsa, kuma a time din data tura masa hoton view once ne ba a iya ɗaukarsa ko ayi sharing even screenshot amma tayaya ya samu hoton? Nan ta ke ta ƙara tabbatarwa kanta ba mutun bane, sakin wayar tayi ta faɗi kan floor


Ƙarfin halin juyawa tayi slowly ta fuskance shi cike da fargaba ta ɗan saci kallon fuskarshi, bata iya ganin ta dakyau sai dai Kyawawan sleepy eyes din sa waɗanda ke a lumshe

Ko a mafarki taga me irin tsayuwarsa sai ta gane shi, Amma tagaza yarda da abun da zuciyarta ke raya mata, a ganin ta bame yiwuwa ba ne, cike da fargaba ta ɗan matsa dab da shi ta ɗan tsaya jikin ta na kerma ta ke ƙare mashi kallon ƙurulla...

A ranta tana ta ambaton La'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin..

Cikin rawar Murya tace"Bab.. Bawan Allah kaji tsoron Allah kada ka cutar dani! Ka faɗamin Wanene Kai? Mutun ko aljan? Kasan ni ne? A ina ka sami hoto na? Me kuma ya kawo ka gidan aure na har cikin ɗaki na"?


shiru babu alamun zai furta kalma, ko motsi bai yi ba bai kuma ɗaga idanunsa ya dube ta ba..

Almost minutes..

Batasan ya akai take jin wani abu a zuciyarta wanda bazata iya misalta shi ba, kuma duk duniya mutun ɗaya ne idan tana atare da shi a kusa da ita take jin wannan abun...

Kafin ta ƙara furta kalma, taga Ya motsa ta ɗan zare ido tana duban shi, gently ya sanya hannu ɗaya akan fuskarsa ya soma ƙoƙarin cire mask ɗin sa..

Lokacin daya zame Mask din gaba ɗaya Ya sake shi Ya faɗi ƙasa wata irin zabura Unaisah tayi kamar zata watsa aguje saboda ruɗewar da ta yi, Ilahirin jikinta Ya kama kerma kamar mazari, gaba daya ta rikice tabi ta ruɗe ta razana da ganin fuskar mutumin data rasa tsawon shekaru akan fuskar Ifritun Aljanin nan, tsigar jikinta duk ta tashi, wani irin faduwar gaba take ji a kirjinta kamar ana buga ganguna.

Kyakkyawar fuskarsa da bazata taba manta kamanninta ba saboda haddar da tayi mata.

cikin ɗimuwa ta soma murza idanunta da yatsunta sosai don taji aranta gizau ya ke mata bashi bane, saida ta gama murje idanun ta buɗe su still babu abun daya sauya yana nan yadda ya ke.

Kamar mahaukaciya Ta bushe da dariya lokacin ɗaya kuma takama kuka tana fadin"ba zaka ta6a bari in zauna lafiya ba, ka mutu ban huta ba, fatalwarka bazata bari in zauna gidan aurena lafiya ba, ka hana zuciyata sukuni a gidan iyayena nan ma ka biyoni don ka tarwatsa aurena! Meyasa zakayi min haka? ya ka ke so nayi da raina? ko so ka ke nima na mutu nabiyoka mu rayu a kabari ɗayane um"? tuni idanunta sun kaɗa jajir.


"Idan so kake mu rayu a tare, ka kashe ni sai mu koma kabarin ka a tare, nima zanso hakan saboda bana jin dadin rayuwana batare da kai ba.."


ta ƙarashe maganar tana matsawa kusa da shi, kamar ancire mata tsoronsa da fargabansa daga zuciyarta, tun da ta sama ranta cewa fatalwarsa ce.

A hankali ta kwantar da kanta saman broad chest dinsa, ta zagayo da hannayenta ta saman bayansa, batasan ya akai ta tsinci kanta da jin wani bakon al'amari atare da ita, bugun zuciyarta a cikin nashi, nutsuwa da kwanciyar hankalin da taji a jikin ta sa'ilin data haɗa jikinta da nashine yasa ta kara ruɗewa, ta dinga jin kamar shine ba fatalwarsa bace tunda in fatalwace bazata iya riqeta ba duk da haka ta kasa gaskata cewa Danish ne.

Cikin kuka tace "Ka ɗauke ni, mu tafi ƙabarinka, mu rayu a tare, bazan ta6a gudun fatalwarka ba my Man, nasan nice na hanaka kwanciyar kabarinka" ta riga ta sallama masa kanta yayi duk abin da zai yi.

Duk wani motsinta yana jinshi a jikin sa, bugun zuciyarta, shesshekar kukanta, fitar numfashinta, dumin jikin ta da ƙamshin ta.


Tayaya zai iya fahimtar da ita cewa ba fatalwarsa bace! bai mutu ba yana araye? Tayaya zai iya kare kansa daga gare ta, yana jin fiye da abun da take ji aranta, banbancin ɗayane shi yasan tana araye kuma ya nisanta kanshi da ita saboda manufar sa..


Yana jin yadda take ƙara narƙe mashi a jiki kamar zasu koma mutun ɗaya...


Numfasawa yayi a hankali cikin nutsatstsiyar muryarsa ya furta.


*_"UNAISAH, I'M NOT A GHOST! I'M NOT A DEMON AS YOU THINK, I'M NOT DEAD, I'M ALIVE, I'M YOUR DANISH! YOUR SHIELD, I KNOW IT WILL BE HARD FOR YOU TO BELIEVE ME"!*_


(UNAISAH NI BA FATALWA BA NE! BA KUMA ALJANI BANE KAMAR YADDA KIKA ZATA, NI BAN MUTU BA, INA ARAYE, NI NE DANISH DINKI! GARKUWAR KI, NASAN ZAI YI WUYA KI YARDA DANI..... " )


bai kai ƙarshen maganar tashi ba ganin yadda ta fisge jikin ta daga nashi, ta sanya runannun idanunta a cikin kyawawan

91 / 107