Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Romantic Hausa Novels
mata da jini da Maman Adnan ta yi ba gaira ba dalili. Yayin da mahaifiyar Ummin take ƙara rura wutar rikicin. Can ka ce kwabo yaran unguwa da uwayensu sun cika ƙofar gidan har cikin zaure babu masaka tsinke.
Muka shige ɗakinmu tare da Amira muka tarar da Umma tana zaune a falo tamkar ba ta san wainar da ake toyawa a cikin gidan ba. Duk rusuna muka gaishe ta ta amsa mana fuskarta babu yabo babu fallasa. Amira ta yi mata bayyanin mun sayar har mun dawo Umma ta cika da farin cikin mussamman lokacin da ta miƙa mata wannan dubu huɗu ta haɗa mata da bayanin inda muka same su. Lamarin da ya faranta ran Umma har ya kai ta ga rangaɗa guɗa.
"Aw ashe fa gidan ba lafiya? Amira ai irin ki ake so ɗiyar azirki irin albarka. Ga Amatullah nan na bar ta a hannunki ki ci gaba da ɗaura ta akan hanya".
"Ba ki da damuwa Umma. Yanzu dai bari na je na huta".
"To yarinyar kirki ɗiyar fita kunya, na gode sosai ko". Murmushi kawai Amira take ta baza wa ta tashi ta fita. Ta bar ni da ƙuncin rai don ban yi zaton za ta iya faɗawa Umma yadda aka sama kuɗin nan ba sai gashi ta shafe idonta ta aikata.
"Umma ga cinikin da aka yi, bari na yi salla na yi shirin islamiyya". Na furta yayin da nake miƙa mata kuɗin cinikin da yake wajena. Ta amsa tana washe baki har kunne, ganin ba ta da niyyar ce mini komai ya sani fallasa abin da yake raina.
"Umma ni ma ko sau ɗaya ai sai ki sa mini albarka".
"To Allah ya yi albarka. In ce dai shikenan ko?". Babu shiri wani ƙayataccen murmushi ya suɓuce mini"na gode sosai".
Sallan na yi kana na yi wanka na ci abinci na yi shirin islamiyya na tafi. Bayan mun fito sallan Malam Suleiman ya aiko ƙura na na je na same shi a cikin staff room.
[7/22, 6:43 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
________________________________________
Page 1️⃣5️⃣
Shuru ya biyo bayan gaisuwar da na yi masa ya amsa. Sai da aka yi nisa kafin ya kawar da shurun ta hanyar soma faɗin"Amatullah na je na yi nazari akan maganganun da muka fara tattaunawa da ke jiya, mataki na farko da za ki ɗauka wanda babu nadama shi ne ki dage da addu'a, ki dinga tashi cikin dare yayin da kowa ya kwanta ki yi alwala ki yi salla ki yi kuka a Allah ki ƙasƙantar da kanki gare sa. Ki yi tawassali da sunanyensa ɗari ba ɗaya tsarkaka ki roƙe sa mafita. Ki nema wa mahaifiyarki shiriya Allah ya sa ta gane illar abin da take aikata. Sannan ɗabar da nake son na ja hankalinki sosai akan sa shi ne kar ki sake shaiɗan ya yi nasara akanki ki wa mahaifiyarki rashin kunya ko ki raina ta ki daina ba ta girma da kimarta a matsayinta na uwa. Allah ya kan jarabci bawansa ta ko wani fage a rayuwa kamar yadda ya zo a tarihin Allah ya jarabci Annabi Ibrahim ta ɓangaren mahaifinsa wanda ya kasance mushiriki. Daidai da rana guda bai taɓa ƙin aikata masa abin da yake so ba, Annabi Ibrahim har tallen gumaka ya yi don jaddada biyayarsa ga mahaifinsa. Don Allah ina mai jan hankalinki da duk runtsi duk wuya da yadda lamura za su sauya kar ki kuskura ki yi wa mahaifiyarki rashin ɗa'a".
Na sauƙe ɓoyayyan ajiyar zuciya kafin na ce"in Sha Allah Malam zan yi amfani da duk shawaran da ka ba ni. Ba zan taɓa kauce wa daga wannan turban ba". Cike da jin daɗin kalamaina ya ci gaba da cewa"Allah ya yi miki albarka ya kawo miki sauƙi da mafita a cikin dukkan lamuranki. Zan ba ki wasu addu'ar da Annabi ya yi amfani da su kuma ya umarce mu da mu yi amfani da su, a duk lokacin da muka tashi roƙon wani buƙata a wajen Allah. Babu inkari matuƙar ka yi su Allah da kansa ya ce yana jin kunyar wanda zai roƙo sa da wannan addu'ar ba tare da ya ba shi duk abin da ya roƙo ba".
"Na gode sosai Malam Allah ya saka da alkhairi ya biya buƙata".
"Amin ya Allah".
Ya amsa yana miƙo mini watar farar fefe da ya rubuta mini addu'ar a jiki, na amsa ina ƙara yi masa godiya. Tun kafin a tashi daga islamiyyar na haddace addu'ar kafin na iso gida ta zauna ɗas a kwanya da saman harshena.
Ina isowa gida na wuce ɗaki na sauya kayan da ke jikina na fito kasancewar ban tarar da Umma ba. Ɗakin su Amira na nufi don karanta mata dashin dacewar abin da ta aikata mini ɗazu, tana kwance a cikin kujera a falo ta duƙunƙune waje guda yayin da ta lumshe idanunta tana ƙare matse wayar da yake kunnenta. Da hakan ya hana ta jin sallamar da na shigo da ita ɗauke a bakina.
Ganin ba ta da niyyar saurara ta ya sani na fizge wayar, ta tashi ta zauna tana kallona bayan ta dafe kanta.
"Wallahi na san duk gidan nan babu wanda zai yi min wannan wulaƙanci sai ke Amatullah". Na galla mata harara"kin kyauta abin da kika yi min kenan ko?".
Cikin rashin fahimta ta ce"da na yi me ye kenan?".
"Ya dace ki je ki sama Umma ki sanar da ita inda aka sama wannan kuɗin? Ni da nasan haka ne ma ba zan bari ki ɗauka ba". Ta tuntsire da dariya har da riƙe ciki lamarin da ya ƙara fusata ni na cika na yi fam na zo har wuya.
"Au! Dariya ma maganar ta ba ki kenan?".
"To Amatullah idan ban yi dariya kuka kike so na yi? Me ye don na sanar da Ummar hanyar da muka sama kuɗin?. Ince dai ke ce kullum kike jan hankalina da yi min nasiha akan na guji faɗar abin da daidai ba duk runtsi da matsin lambar da za a yi min na faɗi iya gaskiyata a cikin ko wani irin yanayi. Cikin ikon Allah kuma yau na faɗi gaskiya kin zo kin titsiye ni".
"Ni ba titsiye ki na yi ba amma ai kin san zancen da ya dace a faɗa da akasin hakan".
"Ni dalla ba ni wayata ina shan soyyaya da masoyi kin zo ki katse min jin daɗina".
Ta ƙare zancen tana fizge wayarta da yake hannu ta koma ta kwanta ta ci gaba da wayarta, yayin da na nema waje na zauna na yi tagumi. Babu abin da yake yi mini yawo da kai kawo a cikin raina face yanayin da na sama Umma jiya da yadda Abba ya sauya a safiyar yau. Duk da Abba yana da sauƙin kai da hakan yake sa mutane da yawa tunanin ya fiye sanyi, amma tsayayye ne kuma jajirtaccen mutum ne akan iyalinsa da ba ya ɗaukar wargi a wannan fanni ko kaɗan.
Kamar daga sama na ji an manna mini ways a kunnuna hakan ya dawo da hankali da tunanina da suka yi nisan kiwo gare ni. Na cira kai ina duban Amira.
"Mansur ne za ku gaisa".
Na amshi wayar muka gaisa da shi sannan na yi masa ya hanya ya amsa mini da sun sauƙa, kafin mu yi sallama ya dinga jeranta roƙo akan na kula masa da Amira kafin ya dawo ya ba ni amanarta ya bar ta a hannuna da makamantan su. Sai da na dara sosai kafin na amsa da cewar zai dawo ya same amanarsa yadda ya bar ta da iznin Allah. Da haka muka yi sallama na miƙa mata waya ita ma ɗin sallama suka yi ta ajiye wayar.
Na gyara zamana ina kallonta haɗe da cewa"Mansur yana matuƙar sonki ta yadda ba iya ɓoye hakan har a cikin kalaman da suke fita daga bakinsa. Don Allah kar ki ba wa kowa irin damar shiga zuciyarki balle har ya kai inda Mansur yake, kar ki ci amanar bawan Allah nan ko da wasa". Numfashi mai ƙarfi ta sauƙe da har sai da na ji sautin fitarsa kafin ta soma magana a hankali alamar na taɓo mata inda yake yi mata ƙaiƙayi.
"Ni ma ina jin sa har ƙasan raina, kuma ina sonki fiye da tunaninki. In sha Allah zan yi amfani da duk shawarwarin da kika ba ni".
Daga haka na daina fahimtar abin da take faɗa sai dai na ƙura mata idanu ina ganin leɓanta yana motsawa da hakan ya tabbatar mini da har yanzu ba ta daina maganar ba. Sai da ta taɓo ni kana na dawo daga karatun wasiƙan jakin da na afka na figigi na ɗaga kai ina kallonta.
"Tunanin me ye kike yi ne haka Amatullah? Tun da safe na fahimci akwai abin da yake damunki, amma kika ce min babu komai. Me ye amfanin muna ƙiran kan mu aminai kuma ƴan uwa amma ba ma iya sanarwa junanmu abin da yake damun mu?".
Na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama lasisin faɗin"Amira babu abin da yake damuna akwai dai matsaloli ne na yau da kullum, kuma kin san ba'a raba bawa da tunani komai daular da yake cikinta".
"Ko kin ɓoye min abin da yake damun ki fuskarki ba zai ƙi bayyanar da labarin zuciyarki ba. Tabbas akwai abin da yake damun ki".
"Babu komai na ce miki babu komai. Ki yarda da ni mana Amira". Ina ƙare zancen na miƙe tsaye na ɗaura daga inda na tsaya"kin ga ni bari na je na duba ko Umma ta dawo". Ban jira abin da za ta ce ba na yi wuf na fice.
Kai tsaye ɗakinmu na nufa sai dai kafin na kai ga shiga muryar Baban Adnan ya tursasa mini dakatawa.
"Amatullah ƴan mata, kwana biyu kamar ba kya cikin gidan nan". Maimaikon na ba shi amsa sai na rusuna na gaishe shi na yi wucewa ta cikin ɗaki da mamakina na tarar da har yanzu Umma ba ta dawo ba. Na fito na yi alwalan sallan magrib na zo na yi ina raka'ar ƙarshe Umma ta shigo cikin ɗakin ta zauna tana huce gajiyar da ta kwaso.
Sai da na iddar na shafa addu'ar da na yi kafin na yi mata sannu da zuwa ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa, so nake yi na tambaye ta inda ta je amma sam tsoro ya yi mini katutu na kasa cewa komai.
"Umma me ye za a dafa ne?"
"Ki tafasa doya".
"To".
Na amsa da shi a taƙaice ina tashi na fita na haɗa wuta na ɗaura ruwa. Yayin da na ɗauko doyar ina ferewa na zuba a cikin tukunyar. Na ɗaukar jakar islamiyyata ina duba litattafaina. Ban tashi daga wajen ba sai da doyar ta dahu ba soya manja kana na shiga ciki na zuba nawa na ci na yi sallan isha'i na fito zaure wajen yaran da suke jirana. Sosai na zage damtse na yi musu karantu duk wani ƙoƙarin manta abin da yake ta'azzaran raina na yi shi. Muna tsaka da karatun Ummi ta fito daga cikin gida ta tsaye mini a kai kamar mai karɓan bashi.
"Ummi lafiya?".
Ta riƙe ƙugunta tana yi mini kallon hadirin kaji ta ce"ku tashi ku nema wani wajen, zan shigo da Auwal".
Na cira kai ina duban ta da mamakin rainin wayon da yake tafe da ita.
"Ban gane mu nema wani wajen ba? Sanin kanki ne a ko wani daren duniya a cikin zauren nan muke yi karatu a daidai irin wannan lokacin. Sai yau kawai za ki ce mu nema wani wajen don za ki yi zancen, ai kuwa sai dai ke da shi Auwal ɗin ku nema wani wajen".
Ta yi poster tana ganina da nake da tabbacin mamakin furucina ne ya hana ta motsawa.
"Lalle Amatullah wuyanki ya yi kauri ya isa yanka. Yau zan bar ki ne kawai amma wallahi gobe ba za ku yi karatu a nan ba".
"Ba gobe ba har jibi da gata ma a nan za mu yi, ki sa hakan a cikin ranki". Ba ta tanka mini ba illa dogon tsakin da ta ja ta fice daga ciki zauren tana shuri da takalmar yaran, na raka ta da kallo har ta fice kafin na ɗauke kaina. Babu jimawa Abba ya dawo na tashi na yi masa sannu da zuwa kana ya shige cikin gida. Ƙarfe tara muka yi addu'a kowa ya watse na naɗe tabarmar na shigo cikin gidan, muka yi kiciɓus da Amira za ta fita daga ni har ita dariya muka sakarwa juna. Na matsa na ba ta waje ta wuce ina faɗin"Allah ya shirya ki ke kam".
Ta bangaje ni"ki sa munjaye Allah dai ya shirya mu". Daga haka ta fice ni ma na ƙarisa ɗakinmu.
Cak! Na tsaya na ɗaga ƙafarta ɗaya amma na gaza sauƙe ta sakamakon zancen da suka sauƙa a ƙofifin kunnuwa tamkar sauƙar aradu, take jikina ya soma rawa kamar ana jona mini wutar lantarki. Zuffa ya soma tsatstsafo wa daga dukkan mafitan gashin jikina, tsoro da firgici ya bayyana ƙarara a fuskata. In dai ba matsalar ji na samu ba tabbas muryar Abba na ji yana cewa"Hafsatu na gama ki da girman Allah kar ki yi fushi da ni zuciyata ba za ta iya jura ba, na yarda ki hukunta da ko wani irin nau'in hukunci amma ban da wannan. Na biya ta wajen Maman Umar ne shi yasa ban dawo da wuri ba ban san hakan zai ɓata miki ba da ban tun magriban fari na dawo cikin gidan nan".
"Manniru ni fa ba zan juri wannan cin mutuncin ba. Sati ba ta cika ba tare da matar nan ta wanko ƙafarta ta zo cikin gidan nan ba yanzu kuma kai da ka baro wajen aiki sai ka wuce wajenta kafin ka iso gida. In ce dai tun ƙarfe biyar kuke tashi daga makarantar amma don kuturun wulaƙanci sai ƙarfe taran dare za ka shigo min cikin gida".
Cikin wani irin yanayin na tsinkayo muryar Abba yana faɗin" ki yi haƙuri in Sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba".
"Wai Maman Umar ɗin nan ita ta haife ka ne? Ko ita ta yi naƙudarka sai haka. Ni fa na gaji ba zan ɗauki wannan rainin hankalin ba".
Kamar an jawo ni haka na ji na faɗa cikin ɗakin sai dai na yi nadamar shiga ta saboda yanayin da na iske su a ciki. Umma tana tsaye yayin da Abba kuma yake durƙushe akan gwiyoyinsa ya riƙe ƙafarta.
Zuciyata ta yi wani irin harbawa sai da na ji duniyar gabaɗaya tana juya mini a lokacin. Da gudu na shige ɗaki na zube akan gado, sai dai sam na gaza yin ko ɗigon hawaye duk da suyan da zuciyata yake yi mini. Na sa hannuna na toshe dukkan kunnuwana saboda amsa-kuwwar da zancen da na ji suka yi mini a na'urar naɗar sautina.
Har Umma ta shigo cikin ɗakin ban motsa daga kwanciyar ruf da cikin da na yi ba, ba ta ce da ni ko kanzil ba ta ɗauki abin da ya shigo da ita ta fita. Ba ta dawo ba sai da dare ta raba sosai ta shigo ta kwanta.
[7/25, 11:19 AM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
___________________________________
Page1️⃣6️⃣
Har dare ta raba bacci ta ƙi kusanta na illa juyin da nake yi raina cike da wani irin zogin da raɗaɗin da yake tasowa tun daga ƙasan raina yana mamaye mini dukkan sashin da sassan ruhina. Sai da na tabbatar da Umma ta yi nisa a baccin da take har da munshari kafin na tashi na fito na yi alwala na zo na tada salla. Raka'a biyu na yi na sallame na ɗaga dukkan hannayena sama ina yi wa Allah kirari kafin na soma zayyana matsalolina na ƙarƙare da yin addu'ar da Malam Suleiman ya ba ni kafin na shafa addu'ar cikin sanyi da mutuwar jiki.
A zaune a wajen na ƙarisa daren yau sai can gabannin asubahi na runtsa ban yi nisa ba na ji an soma ƙiran sallan asubahi, na yi figigi na tashi ina murtsule idona tare da ƙara kasa kunna don tabbatar da abin da kunnuwana suke jiyo mini. Sai da na tabbatar da cewa lalle sallan ake ƙira kafin na tashi riƙe da kaina da yake matuƙar sarawa, na buɗe ƙofan ɗakin raina cike tal da mamakin abin da ya hana Abba tashi akan lokaci.
Turus na ja na tsaya bayan na kunna ƙwan wuta haske ya gauraye ɗakin. Na hangen Abba kwance a makwancinsa ko tashi bai yi ba, na je na tsuguna a gaban sa na ɗan buga matashin take ya buɗe idonsa ya tashi ya zauna.
"Subhanallahi! Kar dai har an yi ƙiran salla?".
"Tun ɗazu aka ƙira".
"Wallahi gabaɗaya na tara gajiya ne a jikina jiya. Shi yasa tun da na wanka ko juyi ban yi ba".
Na jinjina kaina"bari na je na sama maka ruwa a buta". Zan tashi ya dakatar da ni.
"Ki fara zuba wa Ummanki tukunnan. Bari na je na tashe ta". Na sakake ina kallonsa har ya tashi ya shiga cikin ɗakin na kasa tashi daga wajen. Sai da na sauƙe gwauron ajiyar zuciya kafin na tashi kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki na fita waje. A buta biyu na zuba ruwan kana ni ma na zuba nawa na yi na koma ciki na gabatar da sallan ko da na iddar ban tashi daga kan slalayan ba na ɗauko al'ƙur'ani na soma karantawa a ƙoƙarin dawo da nutsuwar zuciyata. Ban gushe ina yi ba har sai da na jin ɗan sanyi a cikin raina kana na rufe na ajiye na tashi na soma gyara ɗakin na gyara ko'ina kana na ɗaura mana abin kari.
Na kawo wa Umma da Abba na su, ko gama ajiye wa ban yi ba Umma ta soma faɗin"A'a ni kam ba zan ci ma wannan abincin ba ɗauke shi kawai".
A hanzarce Abba ya ce"to me ye kike so ki ci?".
Ta yatsina fuska"ba na jin sha'awar cin komai".
"A'a haka kuma ai ba zai yiyu ba ace kin zauna ba tare