DAFIN HARSHE BOOK ONE BY Maimunatu Iyam.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 32

33K to 36K   out of 95.1K words

da kin ci komai ba. Ki faɗi duk abin da kike son ci ni kuma na yi miki alƙawarin samo miki shi matuƙar dai akwai shi a cikin wannan duniyar da muke rayuwa".

"Gandan shanu nake so ci da matsatstsan ruwan rake".
Babu shiri na cira kai ina ganin Abba da ya miƙe tsam yana faɗin"yanzu zan fita neman sa ba kuma ba zan dawo ba har sai na samu miki su".
"Abba ka kawo na je na nemo mata, tun da kai ka ga wajen aiki za ka je. Kar ka yi latti ka kawo kawai".

"A'a Amatullah ni nake da alhakin nema mata duk abin da take buƙata. Don haka ki bar ni na je da kaina don sauƙe haƙƙinta da yake kaina".

Yana rufe bakinsa ya fita daga cikin falon da hakan ya yi daidai da sa'ilin da Umma take tuntsirewa da dariya mai ƙarfin gaske har da tafa hannu.
"Wa ya faɗa maka borno gabas yake Manniru?. Ai kowa ya ce bai iya kuka ba to uwarsa ce ba ta mutu ba, mu zuba ni da kai ɗan halak ka fasa". Ban san lokacin da idanuna suna fara tsiyayar da ƙwalla ba sai ɗumin su da na ji a bisa dandamalin kuncina suna sauƙa har izuwa tudun wuyana. Har na buɗe baki zan yi magana Umma ta watsa nuni wani hargitsatstsen kallon da ya tursasa mini yi wa bakina linzami.
Kalaman da ta yi mini da ƙarfin sanin halinta da na yi suka soma yi mini shawagi a tsakiyar kwanyata. Kif na rufe bakina na juya na fita ban tsaya a ko'ina sai cikin banɗaki na zauna na ci kuka kamar raina zai fita har sai da na godewa Allah.

Na fito na zauna na yi jigum na kasa shiga cikin ɗakin kuma na rasa wanda zan sanarwa damuwata ko da zan ji sanyi a cikin raina. Ko na yi yunƙurin aikata hakan ikirarin tsinuwan da Umma da yi mini idan na yi maganar da kowa sai na ji duk jikina ya yi sanyi ƙalau kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri.
"Amatullahi baiwar Allah. Ina fatan dai lafiya ko? Kin zabga tagumi da safiyar nan".
Muryar Baban Adnan ya dira a ƙofofin kunnuwana da ya tursasa mini cira kaina ina duban sa yana tsaye a kaina ya zuba mini idanuna kamar yau ya saba kallona.

"Ina kwana".

Na jefa masa gaisuwa maimakon ya amsa sai ta jefa muni wata tambayar ta daban da ba ta da haɗi da zancen da na yi masa.
"Murmushi ne ya fi dacewa da fuskarki ba tagumi ba". Ban ce da shi uffan ba na tashi zan shige ɗaki muka yi kiciɓus da Umma za ta fito daga ɗakin na matsa na ba ta hanya ta wuce kafin ni ma na shige ciki. Kai tsaye cikin ɗaki na nufa raina a jagule gabaɗaya na rasa gane abin da yake damuna balle har na iya siffanta shi cikin kalma guda. Duk wani addu'ar da ya zo kaina a lokacin sai na yi sa don kawai na samarwa kaina sauƙin halin da nake ciki na suya da radaɗin zuciya.

Ina kwance akan gado na ji an ɗanna mini dundun a gadon bayana ban motsa ba. Illa runtse idanuna da na yi ina cije leɓena don na san babu wanda zai yi nuni hakan face Amira. Ba tare da na buɗe idona ba na furta"don Allah Amira ki bar ni, ba na cikin yanayin da za ki yi mini irin wannan wasan. Ki bar ni da abin da yake damuna kawai.....". Kafin na rufe bakina na ji ta ɗane kan gado ya na jan ƙafata take faɗin"tashi ki sanar da ni abin da yake damun nan ki".
Na ƙare runtse idanuna"don Allah ki bar ni". Na ƙare zancen ina juya mata baya amma hakan bai hana ta aikata abin da ta yi niyya ba.

"Wallahi sai kin tashi ki yi min bayani. Tun jiya na fahimci kina cikin damuwa amma kika ce da ni babu abin da yake damun ki. Amatullah ni da ke fa yanzu mun wuce matakin ƙawayen da zaman gidan haya ya haɗa mu, mun zama tamkar ƴan uwan da suka fito daga cikin ɗaya da ba za iya ɓoyewa junansu komai".

Na ja dogon numfashi na fesar ina tashi na zauna kana na sama zarafin faɗin"tabbas ina cikin matuƙar damuwa amma ba zan iya sanar da ke abin da yake damuna ba. Iya ƙaunar da za ki gwada mini shi ne ki taya ni da addu'a Allah ya kawo mini sauƙi da mafitan halin da nake ciki".

Ta yi ƙuri tana kallona har na kammala zancen ba tare da ni komai. Ta riƙo hannuna ta sa cikin nata tana murzawa a hankali kafin ta soma cewa"in sha Allah zan taya ki da addu'a Allah ya yaye miki duk abin da yake damunki. Amma don Allah ke ma ki cire damuwa daga cikin ranki. Rayuwar nan fa kowa kike gani yana da na shi matsalar, idan kika zauna kika ji damuwa da matsalar wani wallahi sai kin yi mamakin yadda zuciyarsa ta iya ɗaukar wannan abun kuma har take iya yin dariya da walwala. Amatullah haƙuri, juriya da miƙa lamuranka ga Allah su ne kaɗai abubuwan da suke wadata rayuwar ɗan Adam da haske kowa kuwa ƙunci da baƙin ciki ya yi masa katutu".

"In sha Allah zan yi amfani da shawarwarinki Amira na gode sosai". Na ƙare zancen hawaye suna gudu a fuskana, ta sa hannu tana share mini su tana yi mini tsiya.
"Daɗina da ke ragwanta abu kaɗan sai kuka, kamar yaron da aka ƙwace wa alawa".
Dariyar yaƙe na yi ina kallonta kan ka ce kwabo ta warware mini duk ƙullin da yake ƙasan raina. Ta ja hannuna muka sauƙa daga kan gadon.
"Mu je mu ci abinci ga shi can sai mu fita tallan ko?". Kaina kawai gyaɗa mata muka fito daga ɗakin muka shiga na su, muka ci abincin tare tana ta ja na da hira har muka gama. Muna gamawa na yi wanka na shirya ita ma ta kimtsa ta fito lokacin har ƙarfe taran safiya ya wuce amma har lokacin babu Abba babu labarinsa.

Muna fitowa ƙofar gida na hango Abba ya ɓullo daga can ƙarshen layinmu yana turo keken sa hannunsa ɗaya riƙe da leda. Ina ganinsa na ji duk jikina ya mutu murus hawaye suka ciko mini kurmin idanuna ganin yadda yake ta gumi ga takalmin ƙafarsa da ya tsinke yana tafe yana tura keken da yake ƙara gaskata mini hashashen zuciyata na cewa faci keken ta yi.
Ba mu gusa ba har sai da ya iso na isa zan karɓa ledan hannunsa ya dakatar da ni.

"A'a Uwata bar shi kawai, ai na iso ma".
Cikin wani irin yanayi na karyewar zuciya na furta"sannu da dawowa".
"Yauwa sannu. Har za ku tafi kenan? To Allah ya kiyaye ya ba da kasuwa mai albarka".
Yana dasa aya ya sa kai zai wuce cikin gidan ko gaisuwar da Amira ta yi masa sama-sama ya amsa.

"Yau kuwa lafiya na ga Abba a wani irin yanayi?".
Ta tambaye ni cikin tsantsan mamakin da ya bayyana ƙarara akan fuskanta.
Na sauƙe numfashi kafin na ce"yadda kika gan sa ni ma haka na gan shi yau". Daga haka na wuce gaba tana biye da ni a baya. Muna zuwa ƙarshen layinmu na ji ana ƙira sunana, tare muka waiga dukkanmu ni da Amira muna kai dubanmu izuwa idan muke jiyo sautin ƙiran.

Na dafe ƙirjina ina waro idanuna waje"na shiga ukuna! Sarkin Aska". Amira ta bi shi da kallo har ya iso gabanmu ya zube dukkan hannayensa a cikin aljihun wandon jamfan da yake jikinsa yana kallona.
"Barka da fitowa yake tauraruwar da take haska duniyata".

"Me ya kawo ka unguwanmu?"
Ya saki taƙaitaccen murmushi kafin ya amsa mini cikin faɗin"laifi ne don na zo inda kike? Ko kin manta an ce garin masoyi ba ya nisa. Kusan kullum sai na zo nan na tsaya don kawai na ga wucewar ki hakan ya na taimakawa wajen saisaita bugun zuciyata da daidaita fitar numfashina. Amatullah ke ce sanyin idaniyata, ke ce a cikin tunanina a farke ko a cikin bacci....". Bai gama ba na ɗaga masa hannu alamar ba na ƙaunar jin ragowar zantukan da za a fito daga bakinsa.

"Ya isa haka ya isa. Ban tsaya a nan don ka dinga zayyana mini abin da yake cikin zuciyarka ba. Zan ƙara jadadda maka ka fita a harkata don girman Allah na roƙe ka".

"Ba ni da ikon akan zuciyata balle na sama damar kitsa abin da zai zauna a cikinta ko wanda zai fita. Ina sonki shi ne kawai abin da na sani kuma na yi imanin babu abin da zai sauya hakan komai wuya komai runtsi".

Tsaki mai dogon zango na saka ina wurga masa harara na ja hannun Amira muka bar wajen cikin sauti. Har muka isa tashan raina a ƙuntume kamar wacce aka aikowa da sauƙon mutuwar uwa da ubanta.
[7/29, 5:39 PM] Maimunatu Iyam: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

___________________________________

Page 1️⃣7️⃣

Haka na zauna fuskana gabaɗaya babu annuri raina, akan idona Amira ta ware wasu ta away ta ajiye a gefenta ta ce wannan ba na sayarwa ba ne. Dafo kafaɗana da ta yi shi ya fizgo hankalina zuwa jikina na cira kai ina duban ta tare da ɗage mata ido ɗaya alamar lafiya. Ta yi mini ishara da idonta na bi inda take kallo da ido can na hango Bashir tafe ya nufo inda muke zaune, yana tafe yana washe baki kamar gonar auduga. Tsaki mai dogon zango na ja ina ɗauke kaina gefe guda na buɗe baki zan yi magana kenan ta riga ni.

"Don Allah kar ki ce komai Amatullah. Ki yi wa Allah ki yi wa annabi ki saki fuskarki a bawan Allahn nan. Ko sau ɗaya ne in ya yi miki magana i masa masa, kin san fa an ce gaida mai gaishe ka ko ba zai amsa ba".
"Don girman Allah ki bar ni Amira ki bar ni da abin da yake damuna ma ya ishe ni. Ba sai kin ƙara mini wani ba".

Ina rufe bakina yana isowa wajen ya zauna a kan bencin da yake fuskantar mu. Ya soma zuba kamar bishiyar magarya.
"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yake da ikon juya dare zuwa safiya. Kuma ya yi mini tagomashin yin tozali da kyakykyawan suranki a matsayi abin mafi kyau da burgewa da na fara gani a wayewar garin yau. Da ke da na kwana a cikin ƙirjina shi yasa yau na yi ƙudurin zuwa na ganki kafin na aiwatar da dukkan ayyukan na ranan yau".

"Kan bala'i! Bash yana kashe wuta ina bin ka da fetur. Irin wannan kalaman tashin kai haka ai ni da nake gefe ma kana sawa na fice daga cikin duniyar balle ita kuma wacce ake yi domin ta".

"Babbar yarinya ke dai ki kawai lamarin ya wuce duk yadda kike tunani da zato a cikin zuciyata. Ban taɓa ɗanɗana garɗin soyayya ba sai yanzu da na faɗa kogin soyayyar Amatullah".
Raina ya cika fam zuciyata tana tafasa tamkar talgen da aka aza a bisa wuta, na gaza cewa da su komai illa hararar da nake banka musu a faƙaice.
"A zuba min kunun. Don yau na yi wa kaina alƙawarin ba zan sha komai dangin abin sha ba sai na fara shan wannan daddaɗan kunun nakin, ya ke Gimbiyata".

"Na nawa kake so?".

Na furta zancen a zaffafe kamar zai kai masa duka. Hakan ya sanya Amira kallo ni tare da faɗin"Haba! Amatullah ya haka kamar da gaba? Ki tuna wanda ya ce yana sonka fa, komai lalacewarsa ya fi maƙiyi".
"To laifi ne don na tambaya na nawa yake so?". Ta jijjiga kanta alamar a'a tana ƙunshe dariyar da yake son kufce mata.
"Ban so kika dakatar da ita ba, ko kalmar zagi da cin mutumci ne zai fito daga bakinta ina son na ga waɗannan kyawawan leɓan natan suna motsawa. Ki ba ni na ɗari biyu".
Ban tanka masa ba na zuba masa na dosara masa a gabansa. Ya ɗauka yana sha yana ta suturan da sam ba na gane kansu balle gindinsu, da na ga zaman ba zai fishshe ni ba na amshi wayar Amira ina kallon hotuna.

Muna zaune har masan ya ƙare duk wanda ya zo sayan kunun ya yi mini wata maganar ko ya yabi surar jikina, sai na fasa sayar masa na kuma buga masa rashin mutunci. Hakan ya sa ban yi ciniki da yawa ba.
"Bari na kai wa Naziru masarsa". Na bita da kallo yayin da take miƙewa tana ɗaukar take away ɗin. Na janye hannuna daga tagumin da na zagba kafin na sama zarafin faɗin.
"Ni fa Amira na lura zaman cikin tashan nan ban gishiri a baka manda ne. Sai ka mayar da kanka bolar da kowa ta kwaso jujinsa zau juye akai. Allah ya sani ba zan iya wannan rayuwar ba".

Ta tsaya tana kallona"bari na je na dawo sai mu yi magana. Kar na bar shi yana jira na". Tana dire zancen ta juya ta bar wajen wanda hakan ya yi daidai da sauƙe sakakken ajiyar zuciyar da na yi ina zabga wani uban tagumi kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa.
"Yan mata adon gari idan ba ku gari ya ɓaci idan kuka yi yawa gari ya ɓaci". Kalaman da suka dira a ƙofofin kunnuwana kenan da suka tursasa mini ɗago kaina ina ƙarewa mutumin kallo tun daga sama har ƙasa. Babban mutum ne wanda a ƙalla zai kai sa'an Abbana a kwanakin duniya ya yi shigar kamala cikin cikakken jamfa har ƙasa ga jakar kaya riƙe a hannunsa.
"Me ye kike tsayarwa ne ƴan mata?". Ya kuma jefa mini wani tambayar a karo na biyu har lokacin idanunsa ƙar a kaina ba ya ko ƙiftawa.

"Kunu ne. Na nawa za a zuba maka?".
"Ga shi kuma ni ba na shan kunu. Sai dai na sha mai tsayar kunun".
Tsam! Na miƙe kamar wacce aka tsigarawa alluran doki na tsaya ƙyam akan ƙafafuna duk da rawar da suke yi mini tsabar firgicin da zancen nasan ya jefa ni a ciki.
Muryarta har sarƙewa yake yi idanuna yana kawo ruwa na soma faɗin"wani irin banzan magana ne wannan bawan Allah?. Babban mutum ne kai don haka ka ja girmanka don billahillazi idan ka yi gigin zubar da ni babu abun da zai sa ba zan sanya ƙafa na tatttake sa ba. Ni ba iskanci ne ta fito da ita daga gidanmu ba face sana'a".
Kafin na rufe bakina na ji ya ɗauke ni da mari kafin na yi aune ya ƙara sauƙe nuni wani marin a karo na biyu na ɗayan kuncina. Na ɗago kaina a gigice sai dai kafin na sama zarafin cewa wani abun tunin ya tari numfashina.

"Ke yarinya kar ki sake ki yi min rashin kunya irin na ku na ƴaƴan zamani. Ni nan da kike gani na shekaruna ɗaɗɗaya shekaru sittin da biyu a duniya. Jikata da farko yanzu haka tana gidan aurenta har da ƴaƴa, da kina da mutuncin ni ɗin nan na matsayin uba ya kamata ki kalle ni".

Na dafe kuncina raina cike da fal da takaici. Ƙirjina yana dakan lugudan tara-tara sau goma sha tara. Ruwan da ya wadaci kurmin idanuna suka kwaranyo akan kuncina.
"Ai ba ka riƙe girmanka ba ne shi yasa har na sama fuskar gaya maka ko wani irin magana". Na yi maganar jikina har ɓari yake yi tsabar ɓacin rai da ƙuncin da nake cikinsa. Kafin ka ce kwabo mutane sun cika a wajen kamar kai ka ce kisan kai aka yi a wajen ko kuma wani babban laifi.
Girmamawa da mutuntawan da duk wanda ya zo wajen yake yi wa mutumin shi ya fi komai ɗaure mini kai da jefa ni cikin kokonto. Wasu har tsunguwana suke yi har ƙasa kafin su gaishe shi ko ya miƙo musu hannu don su yi musabaha ba sa miƙa nasu.

"Wai me ye yake faruwa ne ya Sheik? Me ye ya haɗa ka da wannan yarinyar?". Ɗaga daga cikin mutanen da suka cika a wajen ya jefawa mutumin tambaya kafin ya amsa masa wani ya amshe zanen ya soma furzar da zancen da yake cikinsa cikin tsananin fusata, tamkar zai kai mini bugu.
"Allah dai wadaran naka ya lalace. Yanzu ke don fitsara da rashin kunya ki dubi tsabar idanun wannan mutumin da ya yi kusan jika da ke kina yi masa rashin kunya irin na ku na ƴaƴan zamani. Ke kam alla wadaran halinki hakan ya nuna ba ki sama kyakykyawan tarbiyya ba a gida".

"Alhaji Mamman ka yi haƙuri mana mu ji ta bakinta. Kafin mu yanke hukunci".
Ɗaya daga cikin mutanen wajen ya furta kafin ya juyo yana dubana tare da faɗin"ke yarinya me ye haɗinki da wannan mutumin kar kika nema ki yi masa raini da rashin kunya". Duk yadda na so na yi magana lamarin ya gagara hawaye ne kawai suke gudun famfalaƙi akan kuncina na kasa furta ko da kalma guda.
Ana cikin haka Amira ta dawo ta tambayi me ke faru aka mayar mata da ba'asi ita ta yi ta masu haƙuri, amma da farko tsayawa suka yi tsayin dakan akan sai sun lakaɗa mini na jakuna. Yayin da manyan wajen suke ta ba wa mutumin haƙuri kamar wanda aka yi mata wani gagarumin zunubi. Da ƙyar Amira ta shawo kansu shi ma sai da taimakon samarinta na wajen da suka sanya baki.
Ƙurar tana lafawa na fara harhaɗa kayan tallana, Amira ta riƙe ni tana jijjiga ni"wai Amatullah me ye yake damunki ne? Hauka kika yi ko kuma aljanu ne suka shafe ki?".

Na kawar da hawayen idanuna kafin na sama lasisin faɗin"babu ko ɗaya kawai tafiya zan yi ne".
"To ki tsaya mu nema almajirai su ɗeba mana kayan mana". Ban kula ta ba na ci gaba da tattare tattaren da nake yi. Ta nema almajirai suka ɗeba mana kayan muka bar wajen har yanzu hawaye ba su daina kwaranya daga idanuna ba.

"Don girman Allah ki nutsu ki daina wannan kukan haka ya isa mana. Ki bari mu je gida mu zauna sai mu tattauna akan lamarin".
Na shece majinan kukan da ya zo mini kafin na ce"Amira ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba har sai na san

12 / 32