Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : Romantic Hausa Novels
dai alfarman da za ki yi min shi ne ki goge fuskarki ki daina wannan kukan har tsakiyan kaina nake jin sa".
Ya ƙarƙare zancen yana zaro handkerchief ɗaga aljihun farin jamfan da yake jikinsa ya soma goge mini fuskana da shi, na koma sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani tamkar wacce ta yi aikin fasa dutse.
Tamkar daga sama muka ji an sheƙa mana ruwan sanyi duk muka yi mutuwar zaune na wucen gadin, sanyin ruwan na ji ya ratsa har jini da jijiyoyin jikina na daskare a wajen na kasa motsa gaɓoɓin jikina illa idanuna da nake sarrafa su daga wannan gefen zuwa wani.
Ummi da mahaifiyarta ce tsaye a kanta sun riƙe ƙugu suna jefanmu da wani irin kallo da na gaza gano manufarsa.
"Bayin Allah lafiya? Za ku yi mana wannan aika-aikan?".
Yaya Alhassan ya jefa musu tambayar yayin da yake miƙewa tsaye yana kakkaɓe jikinsa da ruwan ya yi masa lajab.
"Ahayye! Yau ina ganin iskanci da wasalinsa. Ai kamata ma ya yi idan ka dawo cikin hankalinka ka yi mana godiya".
Cikin rashin fahimta ya ce"godiya kuma? Na meye kenan?".
"Aw tambaya ma kake yi? To bari ka gani". Take Umman Ummi ta soma kurma shewa kan ka ce kwabo ta tara mana mutanen gidan manyansu da ƙanana suka cika akan mu suna rige-rigen kallon mu tamkar jinjirin watan Ramadana.
"Wai me ye yake faruwa ne?". Baba Habu ya tambaya, Ummi ta yi caraf ta ce"ga su nan kama su muka yi suna aikata baɗala sun fita daga cikin hayyacinsu. Har sai da muka watsa musu ruwa kana suka dawo cikin hayyacinsu". Take wajen ya ruɗe da salati da sallallami kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake yi ba tare da su ba mu damar cewa komai ba. Cikin tururuwan mutanen ban ga Ummana ba amma Abba kam tun da Ummi ta yi jawabin da ya hargitsa wajen bai ce komai ba, illa dafe kansa da ya yi cikin wani irin yanayin da kalmomin baki sun yi kaɗan wajen siffanta su.
"Me kuke jira? Ba za ku taru ku lakaɗa musu ɗan banzan duka ba".
Na jiyo maganar ta gefen inda nake yashe sai dai na kasa tantance mai muryar, kafin na yi yunƙurin tashi na jiyo muryar Abba a karon farko.
"Ku yi haƙuri su ɗin dukkan su ƴaƴana, a ba ni damar ganawa da su kafin yanke ko wani irin hukunci". Aka wani ƙananun maganganu kafin a hankali-hankali aka fara watsewa daga wajen.
"Kawu wallahi wallahi sharri suke yi mana, ba mu aikata abin da suke zarginmu da shi ba. Amatullah ƴarka ce ka fi kowa sanin irin tarbiyan da ka yi mata ni ma kuma ka san halina, ka san abin da za mu yi iya aikatawa da akasin hakan. Kawu ka yarda da ni sharri ne kawai.....".
Abba ya ɗaga masa hannu alamar ba ya ƙaunar jin komai daga gare sa.
"Alhassan ka wuce ka tafi, ina roƙanka da ka ɗauke ƙafarka daga zuwa gidan nan har sai wannan ƙurar ta lafa".
"Kawu don Allah ka saurare ni na yi maka bayani...".
"Alhassan ka wuce ka tafi ka tafi na ce, zan zo gidan na same ka". A tsawace Abba ya yi zancen har sai da zauren ya amsa. Cikin sanyin jiki da na murya Yaya Alhassan ya ce"shikenan Kawu na gode mu kwana lafiya".
"Amin".
Abba ya amsa da shi ciki-ciki bai ko kalle inda nake ba ya juya zai bar wajen, daidai sa'ilin da Amira ta iso tamkar an jefo ta sai da ta matsa kana Abba ya wuce. Ta iso inda nake yashe ta ɗago ni tsaye sai dai na kasa tsayiwa akan ƙafafuna.
"Wai me yake faruwa ne Amatullah? Tun ina wanka nake jiyo tashin hayaniya, na fito kuma na zo na tarar da taron mutane".
Na kasa cewa da ita komai illa kukan da nake yi tamkar raina zai fita, ƙafafuna suka fara rawa alamar sun gaji da ɗaukar nauyin sanƙararren gangar jiki da ba shi da maraba da bishiyar da ta baza jijiyoyinta a ƙarƙashin ƙasa. Na kwantar da kaina a saman kafaɗunta saboda jiri da hajijiyan da yake kwasa ta yana ƙoƙarin buga ni da ƙasa.
Haka har muka iso cikin ɗakinsu muka yada zango a falo har izuwa lokacin hawaye ba su bar kwaranya daga idanuna ba. Take jikina ya ɗauki zafi gau zazzaɓi mai ƙarfi ya rufe ni babu shiri na soma rawar ɗari tamkar jinjirin kazan da ruwa ya yi masa ɗan banzan duka.
"Don Allah ki yi haƙuri ki daina wannan kukan. Ki nutsu ki yi min bayanin abin da ya faru"
Amira ta yi zancen cikin damuwar da ya bayyana har a kalamanta. Na ja dogon numfashi na fesar daga bakina ina kafe ta da rinannun idanuna da suka sha kuka har suka saduda.
"Sharri suke yi mana, wallahi ba mu aikata ba".
"Sharrin kuma? Su waye suka yi muku sharrin kuma ke da waye?".
"Yaya Alhassan".
Ta maimaita sunan kafin ta zarce da faɗin"wani irin sharri? Kuma waye ya yi muku sharrin?". Sai da na cije leɓena saboda takaicin da ya cika mini raina kafin na sama zarafin cewa"Ummi da mahaifiyarta, su yi mana sharrin aikata baɗala ni da Yaya Alhassan. Lamarin da ya fusata Abba matuƙar har ya juya baya a Yaya Alhassan, Amira zuciyata bugawa take yi wallahi". Na ƙare zancen cikin rauni haɗe da ƙara fashewa da wani irin kuka mai cin rai da ruhi, na riƙo hannunta na ɗaura a saman ƙirjina da nufin ta ji yadda yake bugawa fiye da kima a kimiyance.
Duk ƙarfin hali irin na Amira sai gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ƙalau ta kasa cewa da ni komai balle ta iya furta kalaman rarrashi a gare ni illa kallo na da ido tamkar majigi.
"Amira zan je na yi Abba bayanin duk abin da ya faruwa. Zan je na goge zargin da ya ɗarsu a cikin ransa". Na ƙare zancen tare da yin zumbur zan miƙe ta riƙo hannuna gam.
"Kar ki je kar ki je yanzu, ki bari sai ya huce tukunnan kafin ki je masa da kowani bayani". Na girgiza kaina"ba zan iya jira ba don hankalina ba zai taɓa kwanciya ba". Na yi kai aya ina ƙoƙarin fizge hannuna daga riƙon da ta yi mini sai dai ban yi nasarar yin hakan ba.
"Amatullah ki nutsu mana. Ba ki da kalmomin da za ki yi amfani da shi a yanzu wajen fahimtar da Abba ya fahimce ki saboda ransa ya riga da ya ɓaci. Ki yi haƙuri ko zuwa gobe da safe ne sai ki yi masa magana".
Na gaza cewa komai na faɗa jikinta ina ƙara sakin wani kukan mai matuƙar sauti, haka na ci gaba da yi duk lallashin da take yi mini bai yi amfani ba. Har sai da mahaifiyarta ta shigo ta sanya baki haka na lafa ta tashi ta shiga cikin uwar ɗaka ta bar mu.
"Yanzu za ki tashi ki je ki kwanta ne ko kuma? Don kin ga Baba Habu yana gari ni zan je gidan Ta salla ne na kwana....".
Na ji caraf na katse ta"daman kina zuwa wani wajen kwana ne?".
"Ban taɓa zuwa ko ina ba yau ne dai zan fara. Don ko Umma ba ta fito ta faɗa min ba na lura akwai takura a zaman, na yanke shawarar in dai Baba Habu yana gari zan dinga zuwa kwana sanda baya nan sai na kwana a gida".
"Waye ya ba ki wannan gurguwar shawarar Amira?. Duk wata ƴa mace fa kwana a cikin gidan mahaifinta ko da kuma filin taku ɗaya ne shi ne cikar darajarta".
"Ya kamata ki fahimce ni Amatullah don ke ma a cikin wannan yanayin kike. Ki na gaji dai gidan kowa ɗaki ne da falo gare shi, in dan Baba Habu ya dawo shi da Umma suna cikin ɗaki ni kuma ina kwanciya a falo amma hakan bai hana ni sauraron duk abin da suke yi kamar a gabana suke aiwatarwa ba, hatta idan suna raya sunna ina ji yi sumbatun da suke yi. To da hakan ya ci gaba da faruwa ai gwara na nemawa kaina mafita ko?".
Kalamanta suka sanya jikin mutuwa murus, tabbas indai zan yi wa zancenta adalci da duba irin na hankali haƙiƙa hukuncin da ta yanke shi ne daidai.
"Haka ne kam ki na da gaskiya".
"Ke ma kuma zan so ki bi hanyar da na bi". Murmushin ƙarfin hali kawai na sakar mata kafin na ce"sai Abba ya sauƙo tukunnan, amma kema da kin yi haƙuri yau dai mun kwana tare a nan tun da kin ga halin da nake ciki. Wallahi ba zan iya komawa ɗakinmu alhalin na san Abba yana fushi da ni ba".
"Ba matsala kin san ina son duk abin da zai sanya ka farin ciki ai".
Murmushi kawai na sakar mata, muka yi salla ta kawo mana abinci sai dai na kasa kai koda loma guda cikin bakina haka na kwanta. Raina cike fal da tarin damuwa da fargabar abin da gobe za ta haifar.
[10/16, 12:34 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE*
©️ Maimuna Tijjani Iyam
______________________________________
Page 3️⃣0️⃣
Haka na ji ta juye- juye a bisa shimfiɗan bacci ya gagari idanuna, ya bushe ƙamas kamar soyayyen fikin da aka zuba a cikin mai. Ina jin Amira ta na ta hira da masoyinta Mansur a waya cikin nishaɗi da walwala.
Sun daɗe suna wayar har sai da dare ta raba kana suka yi sallama, na juya ina kallon ta duk da duhun da ya mamaye ɗakin na furta"masoya kun yi sallama kenan? Na yi tunanin ai yau soyayyar za ta hana ku bacci". Ta murmusa kafin ta ce"ai ba mu ƙi mu kwana muna wannan wayar ba, wallahi idan ina tare da Mansur ko a waya ne sai na ji duk na manta duk wani damuwar da yake addaban raina. Ina samu nutsuwa sosai daga gare shi".
Na taɓe baki"kuma duk kin san da hakan amma kika kasa sakan kowa ki kama shi. Duk da nutsuwar da kike samu daga gare shi hakan bai hana ki ganin wasu mazan ba har alaƙar soyayya ta gifta a tsakaninku".
Ta sauƙe numfashi mai zafin da har sai da na jiyo sautinsa kafin ta sama lasisin faɗin"duk na san da hakan Amatullah amma kin sa komai na rayuwar nan sai ana yi ana lissafi, sama da saurayi ɗaya ai tsautsayi ne babba idan ya juya min baya lokaci guda kuma ya ya zan yi ni ƴasu".
"Amira kenan! Ki na raina ikon Ubangiji kenan? Allahn da ya ba ki Mansur a lokacin da ba ki yi tsammani ba shi zai kawo miki wani a lokacin da ba ki yi zato ba. Ki tsarkake zuciyarki kawai ki so mutum guda in sha Allah ba za ki kunyata ba".
"Ki kwanta ki huce gajiyar da kika kwaso wa jikinki Amatullah, don wannan maganar takin ba ta da matsuguni a cikin kwanyanta".
Ta yi zancen tana gyaran kwanciyarta, taƙaitaccen murmushi kawai na yi ina sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya mai nauyin gaske. Duk yadda na so baccin ya zo mini lamarin ya gagare ni wai ƙoƙarin cire wando ta kai, haka na ci gaba da juyi ina sauƙe numfaffashi tamkar wacce ta yi aikin fasa dutse.
Runtse idanuna na yi da ƙarfin gaske ina karanto ƙarin da Malam Suleiman ya yi mana yau, har aka yi ƙiran assalatu ban runtsa, ladanin yana ƙwala ƙiran sallan farko na tashi na zauna tamkar a daidai ƙofar kunnena ya ƙwala.
Na tashi Amira muka fito muka yi alwala, muka koma muka yi sallan, ina kammala azkar ɗina na miƙe Amira ta bi ni da kallo.
"Ina kuma za ki je?".
"Zan je wajen Abba ne. Don wallahi daren jiya ko runtsawa ban iya yi ba tsabar firgicin da zulumin da ya cika mini zuciya". A sanyaye ta ce"to ki dai nutsu kar ki je ki tsaya kuka kawai maimakon bayani. Kuma ki je ki dawo ki same ni don Ummi ba za ta ci banzan ba billahillazi".
Ban ce da ita komai ba don na fahimci ko na furta ba za su shiga cikin ƙoƙon kanta ba.
Ina fitowa Baba Habu tare da Abba suna shigowa sun dawo daga masallaci, na tsaya a inda nake cak har sai da Abba ya wuce ɗakinmu Baba Habu ma ya nufo ƙofar su kaina a ƙasa na gaishe shi ya amsa tamkar wanda aka yi wa dole tana ɗaure fuskarsa tamau, ajiyar zuciya na sauƙe mai ƙarfi don tun daren jiya na lura tamkar bai so kwanan da na yi tare da Amira ba, kawai dai da yake Umman Amira ta fi shi ƙarfin faɗa a ji ne a zamantakewar su, shi yasa ya saduda.
Tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki haka nake ɗaga ƙafafuna da nake jin su tamkar ba a a jikin gangar jikina, na iso ƙofar ɗakinmu na raba tsakanin haƙwaraina da ƙyar kafin na shiga doka sallama, sai da na yi baki uku ana huɗu na jiyo muryan Abba ya amsa.
Haka kawai na tsinci kaina cikina matsanancin faɗuwar gaba yayin da nake shigowa cikin ɗakin, da ya gauraye da hasken rana tocila.
Na zaune a ƙasa zan nesa da shi kaina a ƙasa na gaishe shi fuskarsa babu yabo babu fallasa. Sai da na aro jarumta na yafawa kaina kafin na soma magana cikin sarƙafewar harshe.
"Abba wallahi sharri Ummi take yi mana ba mu aikata abin da suke zargin mu ba da Yaya Alhassan. Hasalima na bi shi waje ne don na ba shi haƙuri akan abin da ya faru, shi ne ya zaro handkerchief daga ajihunsa......". Ya ɗaga mini hannu alamar na dakata.
"Ni ma na san ba ku aikata ba Amatullah, tun kafin a haife ki na san wane ne Alhassan na kuma san ɗabi'u da halayansa baki ɗaya. Amma dole ya janye ƙafafunsa daga zuwa gidan nan na ɗan wani lokaci ko da kuwa wannan abun bai faru ba ma, ko don rashin fahimtan da suka samu da mahaifiyarki".
Na ja jikina na iso gabansa na haɗe hannayena waje guda alamar roƙo ina cewa"Abba ka yafe mini na san jinya ka kwana da ɓacin raina a cikin zuciyarka, wannan dalilin ne ya sa na kwana a ɗakin su Amira don ba zan iya fuskantan ka a irin wannan yanayin ba".
"Uwata ba ki yi min komai ba da har za ki nema gafarana, kuma ban kwana da baƙin cikinki ko takaicinki a cikin raina ba. Babban damuwata ma shi ne yadda ran Ummanki ya yi maƙurar ɓaci".
Jikina gabaɗaya ya yi luƙus jin abin da Abba ya furta na zame na yi zaman dirshan ina ci gaba da sauraron jawabin da ya ɗaura da shi.
"Allah ya jarabce ni akan mahaifiyarki har cikin raina na tsani duk wani abun da zai sosa mata rai. Na ƙi jinin duk wanda zai tsaya a gabanta ya yi furucin da zai baƙanta mata rai ko wane ne shi, kuma komai girman alaƙar dake tsakanin mu da shi zan iya yanke alaƙa da shi".
Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya kafin a sanyaye na ce"in sha Allah komai zai wuce Abba, amma su Yaya Alhassan kam ai ni da su mun zama abu guda a gare ka. Idan har zuciyarka za ta iya yafe mini to tabbas su ma sun cancanci hakan". Ya yi hanzarin taran numfashina"akwai bambanci ke a ni kika yi wa laifi yayin da su kuma ran Hafsatu suka baƙanta. Zan iya yafe duk girman laifi amma ban da wannan". Ban iya cewa komai ba saboda zallar ruwan mamakin da zantukansa suka shayar da ni, na tashi na fito na soma shara ina jin ciki tamkar an yi yasa don rabo na da abinci tun jiya da rana.
Sai da na gama na hura wuta na ɗaura girki ina kammalawa na ɗeba nawa na ci a wajen kana na shigarwa Abba na sa ciki. Kamar ƙaramin yaro haka ya ke cin abincin hannu baka hannu ƙwarya na yi sakeke ina kallon sa raina cike da tarin tausayinsa don na tabbatar shi ma rabon sa da abinci tun jiya, hawaye suka zubo daga idanuna na yi hanzarin kawar da su.
"Uwata tunanin me ye kike yi haka kin yi shuru?".
"Babu komai Abba, Umma ba ta tashi ba ne?".
"Ba ta tashi ba, amma Uwata tabbas akwai wani abun da yake damunki. Ki saki jikinki ki sanar da ni ko mene ne, shin ki na da wanda ya kai ni ne a gare ki?". Na jijjiga kaina cikin sanyin jiki da hakan ya ba shi damar ci gaba da cewa"to mene ne haka a ranki kike wannan dogon tunanin?".
"Abba ina so na roƙi wani alfarma ne a wajen ka".
Ya kai lomar da ya ɗauko kafin ya ce"faɗi kanki tsaye in har ina da halin yi miki to ki sa a ranki kin riga da kin samu". Na ɗan ji jim kafin na ce"daman akwai wani gida ne a nan bayan layin, matar mijinta ya rasu daga ita sai ƴaƴanta biyu kuma duk samari ne ba sa zaman gidan. Shi ne Amira za ta na zuwa gidan ta na kwana saboda Baba Habu ya dawo, zaman cikin da falon akwai takura".
Ya kare ni kafin na isa inda nake son tsayawa"yanzu dai me ke kike so?".
Na sadda kaina ƙasa kafin na sama zarafin ci gaba da cewa"shi ne nake roƙan alfarma a wajenka inda ka amince sai na dinga bin ta muna zuwa can muna kwana tare". Ya yi shuru kamar bai ji ni ba hakan ya ƙara sanyaya mini dukkan jikina, bai amsa mini ba ya ci gaba da cin abincinsa har sai da ya gama cin abincin tas ya kwance hannunsa ya yi hamdala bayan ya ɗaura da ruwan da na kawo masa.
Na tashi na tattare kwanukan na fitar wajen na wanke su kana na ɗaura ruwan zafin dama kunu, na koma ciki da nufin duba ko Umma ta tashi har yanzu Abba yana nan zaune a inda na bar shi bai ko motsa ba.
Na yi masa sannu ya amsa zan shige ya ƙira sunana na dawo na tsuguna a gabansa.
Ya kafe ni da ido yana faɗin"na yi nazarin maganar da kika faɗa na duba na ga dacewar hakan, sai dai wani gida ne za ku na zuwa kwanan?". Na yi caraf