DAFIN HARSHE BOOK ONE BY Maimunatu Iyam.txt

Author :  Maimuna Tijjani Iyam Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 32

3K to 6K   out of 95.1K words

yanzu kasuwa ta watse ɗan koli ya ci riba".

Sake da baki Umma take bin Sahura da ido kuɗin da Amira ta kawo kuwa cas sai da ta irga su, duk kusan tare suka irga da Sahura. Kamar kububuwa ta juyo kaina.
"Dan ubanki za ki ɗauki kunun nan ki tafi ko sai na lahanta ki? Shegiya ƴar iska mai mataccen zuciya. Kowa yana abun kansa amma ban da ni, ni kam na haiho ruwan dafa kaina gantafalalla ɗan kurciya da gashin baki".

Babu shiri ya suri bokitin na ɗaura a kaina har ina ƙoƙarin cin karo da Baban Adnan da ya fito fu ya fice daga gidan kamar iska. Har yanzun Ummi da saurayinta suna zaune a zaure ina jin ta tana tambayata lafiya na fito ina kuka ko kanzil ban ce da ita ba sai tsaki da na ja saboda mau kallon da Saurayin natan yake bi na da shi na yi ficewa ta. Tun da na fito daga gida na rasa takamanmen inda zan nufa a saye kunun haka na yi gararamba a titi daga ƙarshe da na gaji na nema gefen hanya na zauna na tisa bokatin kunun a gabana na zabga tagumi.
Ko dai maganar da Umma take faɗa na cewar ina da matacciyar zuciya gaskiya ce? Tun da gashi tun fitowata daga gida babu wanda ya sayi kunun ko na sule biyar. Sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina bin bokitin kunun da kallo har na kai hannuna na taɓa ya yi sanyi ƙalau yanzu kam ina da tabbacin duk wanda ya saya ba zai ji daɗi sha ba.

Sallamar da na yi a tsakiyar kaina ya dawo daga ni duniyar zahiri daga karatu wasiƙar jakin da na faɗa. Na cira kai ina duban matar dake tsaye a gabana tana riƙe da hannun ɗanta da alama daga makaranta ta ɗauko shi don yana cikin cikakken shirgar kayan makaranta har da kulan abinci riƙe a hannunsa. Sai a lokacin na ankara lokaci ya ƙure kuma ina da islamiyya ƙarfe biyu. Kafin ta yi magana ta riga ta.

"Na nawa za a zuba miki?".

Ta kafe ni da ido"ba kunu nake so ba, mai sayar da kwankwan can nake tambaya". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kafin na ƙara cewa komai mai sayar da kwankwan ya zo wajen ta juya za ta bi bayan sa bayan ta sanar da shi na adadin kuɗin da take buƙata. Na marairace ina roƙonta tare da yi mata magiya.
"Don Allah Hajiya ki saya ko na Naira hamsin ne, wallahi tun safe da na fito ko naira biyar ban yi ba. Ki taimake ni ki yi mini rai".
Ta waigo tana duba na kamar ba za ta yi magana ba sai kuma can ta ce"zuba min na ɗari biyar". Ta zaro kuɗin daga jakarta ta miƙa mini, jikina yana rawa na amsa zan zuba mata ta dakatar da ni.

"Ki raba wa waɗancan almajiran".

Na gyaɗa kai ina jeranta mata godiya kamar kyauta ta ba ni kuɗi. Almajiran suka taso su ma suka dinga yi mata godiya. Na zuzzuba musu na zauna zaman jiran su shanye su ba ni kwanon da ludayin.
"Ƴan matan me ye sunan ki ne?".
Furucin mai sayar da kwankwan ya ratsa kofofin kunnuwana.

"Amatullah".

Na furta a taƙaice da hakan ya ba shi lasisin ci gaba da zuba kamar ƴaƴan magarya.
"Kyakkyawan suna sai kuma ya dace da kyakykyawa mai kyawun sura kamar ki. Gaskiya ki godewa Allah". Rai a jagule na cira kai na yi masa kallo guda tare da cewa"kullum cikin gode masa nake yi Malam".

"Ya kamata ki ƙara masa don ba kowacce mace ba ce ta haɗa abubuwan da kika haɗa. Ga kyau ga sura ga kuma cikakken diri". Zumbur na miƙe ina nuna da ƴatsa"Malam ba na son maganar banza, ka ja girmanka in kana son na girmama ka".
"Ba Malam nake ba sunana Haruna". Na ja doguwar tsaki ina tattare robina da almajiran suka gama sha na bar wajen zuciyata tana tafasa kamar talgen da ke bisa wuta. Duk da ɓacin ran da nake ciki wani sashin zuciyata yana cike da murna tun da na yi ɗari biyar don a tunanina na yi abun a yana mini har zuciyata tana kwaɗaita mini samun albarka daga bakin Umma abin da tun da na buɗi ido ban taɓa jin ta furta mini ba.
A ƙofar zaure na yi kiciɓus da Auwal saurayin Ummi saura ƙiris jikina ya goge shi na yi hanzarin ja da baya .

"A'uzubillahi mini shaiɗanir rajim!".

Idanunsa ƙar a kaina ya ce"me ye haka? Kamar wacce ta yi karo da aljani?". Ban ba shi amsa ba na raɓa zan wuce ya sha gabana.
"Ka matsa na wuce ba na son Ummi ta zo ta same ni a nan".

"To ta zo mana ai ita ma kanta ta san kin fi ta diri da sura. Amatullah babu lafiyayyan namijin da zai ganki bai ji wani abu a ransa ba".
Yanda ya yi zancen yana lumshe idanu shi ya fi komai ba ni tsoro. Ban ƙara firgita ba sai da na ji hannunsa a bisa ƙuguna. Na juye masa kunun a jikinsa na ɗauke sa da mari a kuncinsa. Jikina gabaɗaya yana rawa na kasa cewa komai kamar yadda na gaza motsawa daga wajen. Sautin marin da na yi masa shi ya ja hankulan mutanen gidan suka cika a zauren.

"Amatullah lafiya? Auwal me yake faruwa?". Ummi da zuwan ta kenan ta jefa mana tambayar a haɗe. Na kasa cewa komai don bakina ya ƙi ba ni wannan damar sai Auwal ne ya soma cewa.
"Babu abin da ya faru, wai daga ta shigo na ce in ta shiga ciki ta yi min magana da ke ina so na wuce. Shi ne ta fara gaggaya min maganganu da na tsawarta mata ta juye min kunun a jikina".
Kowa ya saki salati da sallallami gami da tafa hannu.

Sai a lokacin na sama zarafin magana"Auwal ka ji tsoron Allah. Wallahi Ummi ba haka ba ne ya faru, maganar banza ya tare ni da shi....". Kafin na rufe bakina ta ɗauke ni da wani gigitaccen marin da ya sani ganin baƙin duhu yana gilmawa. Za ta ƙara nuni wani Umma ta iso wajen ta riƙe hannunta.
"Kar ki sake ki ƙara yin gangancin marinta. Don wallahi sai kin yi dana sani". Ummi ta fizge hannunta"ai kuwa dole na mare ta har ma da abin da ya ci uwar mari, ko ba ki ga abin da ta yi wa Auwal ba ne?".

"Na gani shi uban waye ya ce ya aike ta ƙiranki? Ko zamansa take yi a cikin gidan da zai aike ba? Yanzu kuke biya kuɗi fa haka muke lalewa mu ma mu biya don haka muna da damar da za mu sakata mu wala a cikin gidan nan. Ke ma mai naman neman magana haka kike so ai, kullum burinki ki hannu cikin tashin hankali. Ƴar iska dantalalliya marar kishin uwarta".
Tana dure zancen ta jawo ni kamar za ta fige mini hannu muka shiga ciki, ɗaki ta wurga ni ta hau huce takaicinta a kaina.
[6/12, 6:29 PM] iyammaimuna: *DAFIN HARSHE*

©️ Maimuna Tijjani Iyam

__________________________________

Page 0️⃣3️⃣

Da ƙyar na ƙwaci kaina na koma gefe guda na takure ina ji wani zazzaɓi yana ƙoƙarin rufe ni.
"Ni kam ban san ke wacce iriyar yarinya ba ce mai baƙin jinin tsiya. Yarinya kamar ƴar zina ko wacce take da bakin iyaye komai aka yi miki babu alkarba sai ka ce karfa. Kunu abin banza ma ba za ki iya sayar da shi to ina da wani abun na daman, kina gani ganin idonki yadda Amira ta hucewa uwarta Sahura takaici da tallan wainar da take yi a kowacce rana a ƙalla tana yin dubu goma zuwa sha biyar amma ke kamar wacce aka sawa hannu komai aka yi miki babu sa'a. Oh! Ni Hafsatu ina ganin takaicin duniya".

Muryata a raunane na ce"Umma na yi naira ɗari biyar fa". Ta wurga mini watsa uwar harara kafin ta ce"ina ɗari biyar ɗin?". Na soma laluma jikina sai dai wayam babu kuɗi babu alamarsa na yi tsilli-tsilli da idanu iwa kwarton da aka kama a cikin turaka.
"Wallahi tallahi billahillazi la iya ha illa huwa Umma na yi naira ɗari biyar sai dai in ya faɗi a zaure". Ba ta ce da ni uffan ba illa kaɗa kanta da ta yi ta juya za ta fice sai da ta kai ƙofar fita kana ta ce"ki yi shirin makaranta". Tana rufe bakinta ta fice ta bar ni da saki sakakken ajiyan zuciya ina ƙara laluma jikina ko zan ga kuɗi.

Har zanina na since amma babu kuɗi babu alamarsa na ƙara tabbatarwa kaina ba ya jikina, na zauna na yi shiru ina faman tunani barkatai.
"Za ki fito ki tafi makarantar ko sai na shigo". Na tsinkayo muryar Umma kamar daga sama, zumbur na miƙe ina amsa da faɗin"Umma zan sauya kaya ne".

Kayana na sauya na saka na islamiyya sai da na fito na yi alwala na koma ciki na yi salla kana na ɗauko jakata da sallaya na fito. Umma tana zaune tana ƙula farar aya a leda.
"Na fito zan tafi".
Ba tare da kalle ni ba ta ce"ki je ɗaki cikin samira ki ɗauki ɗari ki sayi wani abun ki ci, tun da baƙin hali ya hana ki ki sayar da kunun ". Godiya na yi mata na shiga na ɗauko kuɗin na fito sai a lokacin ta ɗaga kai kalle ni.
"Ki maida hankali ki yi abin da ya kai ki sannan kuna tashi ki kamo hanyar gida. Ki zo ki kasa min ayar nan a ƙofar gida".

"To in sha Allah". Na amsa da shi yana jin kamar ana yaye nuni wani nauyi daga ƙirjina. Ta inda na sama sauƙi duk zafin Umma da hargaginta gami da son kuɗinta ba ta taɓa gana ni zuwa neman ilmi, a lokuta da yawa ita take kora ni ko da raina baya so. Haka na fice ina zuwa zaure abin da ya faru tsakanina da Auwal ya fara dawo mini sabo a cikin kwanyata sai da na ƙare wa kaina kallon tsaf.
Allah ya yi ni mace mai matuƙar diri da kyawun sura wanda ba maza kaɗai ba hatta ƴan uwana mata suna yabon dirin da nake da shi. Duk da ba ni da kyawun fuska amma ina da cikakken zubin diri, shekarata goma sha biyar amma ga wanda bai sani ba zai yi zaton na kai shekaru goma sha tara saboda girman jikin da nake da shi.

Sai da na muka fito sallan asr sannan na sayi awarar ɗari na ci na sha ruwa muka koma aji, ƙarfe biyar daidai na yammaci muka tashi. Muka tsaya tattaunawa batun walimar sauƙar da za mu nan da satikai shida sai da aka tsara komai sannan muka watse. Muka kamo hanyar gida ni da ƙawayena biyu Ammi da Rauda.
"Don Allah ku raka ni shagon Abbana na amso cefane". Rauda ta yi zancen cikin kwantar da murna.

"Ni fa Ummata tana jira na na fitar mata da farar ayan da ta yi. Kin ga kuma yanzu lokaci har ya ja". Ta kuma marairace"don Allah ki yi haƙuri mu je ba za mu daɗe ba, kin ga Ammi yanzu za mu rabu da ita ta iso gida". Na jim ina tunani kafin na ce"mu je amma ba za mu daɗe ba".
Muka nufin shagon muna tsallake kwalta muka rabu da Ammi ta shige gidansu. Babu daɗewa muka isa shagon muka duƙa muka gaishe shi ya amsa fuskarsa a washe ya ɗauko ledar ya ba ta ta amsa da godiya. Har muka har ƙofar shagon bai daina sa mana albarka ba. Lamarin da ya yi matuƙar burge ƙalbina sai da ta taɓo ni kafin na dawo daga kogin tunanin da na faɗa.

Ta ɗage mini ido guda"tunanin me ye kike yi haka? Ina ta magana kin yi shuru". Na sauƙe ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya mai sauti kafin na sama zarafin cewa" ba zan miki ƙarya ba Rauda rayuwar gidanku yana burge ni, yadda muke mu'amala da iyayenku abin sha'awa. Babu tsangwama balle hantara uwa uba kullum cikin sa muku albarka suke yi da yi muku addu'ar shiriya. Ku kam kun dace".
Sai da ta murmusa kafin ta ce da ni"haka kowa yake cewa amma ke ma ai kin dacen mahaifi Amatullah, kowa ya shaida cewar mutumin kirki ne mai ƙoƙarin kiyaye halak da haram. Sannan duk layinku da ke ake kwatance wajen kyawawan ɗabi'u da halayen ƙwarai, ga nutsuwa ga ƙur'ani". Duk mu biyun muka fashe da dariya haka muka ci gaba da tattauna har na iso gida kana muka yi sallama na shiga gida ita kuma ta wuce, layin gabanmu inda za ta iske gidansu.

"Mun rantse da girman zafin Allah ba za ta taɓa saɓuwa ba wai bingida a ruwa. Dole mu ƙwatawa ƴar uwarmu haƙƙinta. Don ba daga sama ta faɗo ba ita ma ƴa ce kamar kowa mai gata da galihu yau sai mun ga abin da ya turewa buzu naɗi".

Kalaman da suka fara sauƙa a ƙofofin kunnuwana kenan yayin da na kutsa kai cikin gidan. Maman Adnan ce tsaye ta sha ɗamara ga kuma wasu jibga-jibgan mata uku masu ƙiran samudawa tsaye a kutsa da ita wanda suka kasance ƴan uwanta ne na jini. Da ƙyar na jan ƙafafuna na ƙariso ƙofar ɗakinmu na rakuɓe jikin Ummata da take zaune tana sauraran rediyo ta yi bakam kamar ba ta san wainar da ake toyawa ba.
Na durƙusa kusa da ita ina cewa"Umma wai me yake faruwa ne?".

"Safina ce ta ɗebo ƴan tashan ƴan uwantan suka zo cikin nan suke yin tijara. Wai don mijinta ya lakaɗa mata ɗan banzan duka, yo daman wacce ta mai da kanta jaka kam ai dole ta zama abin jibga a wajen miji a ko yaushe".

Ɗaya daga cikin matan ta yi kukan kura ta yo kan Umma, kallo kawai Umma ta yi mata ta tsaya cak ta kasa gaba balle baya. Na sha jin ana cewa Umma tana kwarjini da cika ido wannan dalilin ya sanya kowa a gidan yake matuƙar shakka da tsoron shiga gonarta ban gama gaskata hakan ba sai yau ɗin nan.
Ƙafarta ta ɗaura ɗaya bisa ɗaya tana ƙare musu kallon ɗaɗɗaya"ai ko giwa ta faɗi ta fi ƙarfin kare ya ja ta. Idan ki na ji da rashin kunya da tashanci ne to gidansa kika zo. Da kin ƙariso ai da na nuna miki yadda ake yin wasan".

Maman Adnan ta ɗaura hannu a ka ta fasa ihu tana durƙushewa akan gwiwoyinta"shikenan na shiga uku na lalace wannan matar so take yi ta guntile min igiyoyin aurena. Anti ku taimake so take ta ƙwace min miji, jama'ar gidan nan muna gani kun kasa cewa komai".
U
Ɗaya daga cikin mata ta ɗago ta tana faɗin"ta yi tsararo ta raba ki da mijinki Safina. Idan taƙamarta sammako da to mu a hanya muka kwana idan ta san wata ai ba ta san wata, sai mun nuna mata faɗa da aljani sai an shirya wallahi kin taɓo tsuliyar dodo". Tana ada aya ta figi hannun Maman Adnan suka wuce ɗakinta raguwar mata biyun suka rufa musu baya. Shewa Umma ta saka har da tafa hannu tana faɗi"ai ni wargi ce daidai ƙugun ko wani ɗan iska, mu zuba mu gani ɗan halak ka fasa".

"Umma don girman Allah ki fita daga harkan mutanen nan ki bar su su zauna lafiya da mijinta..".

Kafin na ƙarisa ta sauƙe mini ƴatsunta biyar a fuskana, a kufule take cewa"ke har me ye kika sani da za ki zaunar da ni kina faɗa min abin da ya dace na yi ko kar na yi. Amatullah ki fita daga idona na rufe daman ina cike da ke ƴar iska mai kunnen ƙashi, ban ce da ke ki dawo da wuri ki fita min da farar ayan nan ƙofar gida ba?".
Kaina a sunkuye na ce"mun tsaya tsara yadda walimar sauƙar mu za ta kasance ne". Ba ta ce da ni komai ba kamar yadda ba ta ba ni umarnin tashi ba, haka na ci gaba da tsugunawa akan ƙafafuna don na san idan na tashi ni na san abin da na taro. Sai da aka yi ƙiran sallan magrib kafin na tashi daga wajen na je na yi alwala na shiga ɗaki na yi salla na fito na soma ciki-cikin haɗa wutan dare.
Sai da na sha baƙar wahala kafin wutan ya kama na aza sanwa na ɗauko kayan miya na soma yankawa. Ganin mutum tsaye a kaina ya sani hanzari ɗaga kaina ina dafe ƙirjina ganin Ummi ce ya tursasa mini sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya.

"Ummi lafiya? Kika zo kika yi mini tsaye a tsakiyar kaina?".

"Watau har kin manta abin da ya faru ko?". Ta yi ƙwafa kafin ta ɗaura da cewa"ai idan maye ya manta uwar ɗa ba za ta manta ba. Ke har kin mance rashin mutuncin da kika yi wa Auwal ɗazu watau a tunaninki kin ci banza ko?".

"Ni kin ga na har na kanta kimai. Kin ga Ummi ki tsaya mu yi magana ta fahimta wallahi Auwal ƙarya ya faɗa ba abin da ya faru ba kenan, shi ne fa ya tare ni da maganar banza".

Ta doka mini tsawa"dalla! Rufe min baki, ko da Auwal ya kasance ɗan iska ai ba kuma kai matsayin da zai tunkare ki da maganar banza ba. Amatullah zan miki gargaɗin dab da mari ki fita daga harkan Auwal, don tun ba yau ba ina ankare da ke a duk lokacin da ya zo hira kin ginda shiga da fita kenan kina shawagi a gabansa kina juya manyan mazaunanki don kawai ki ja hankalinsa. To hawainiyarki ta kiyaye rama ta kuma wallahi Auwal dai nan gani nan bari ɗumamen maya na gaba ya yi gaba".
Sake da baki da hanci nake kallon ta har ta kammala zancen tsabar mamakin da ta ba ni.

"Allah ya ba ku haƙuri ke da shi". Na furta a taƙaice ina mayar da hankalina ga aikin da ke gabana.
"Idan ya ba ni ki ƙwace banza shashasha, girman buredi kawai". Ban tanka mata ba har ta ƙarishe tsayiwarta ta gaji ta tafi, tana barin wajen Amira tana isowa ta ja kujera ta zauna.

"Wai me ye take faɗa miki

2 / 32